TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 11

Sponsored Links

 

 

AL KHALIQ ,,,,,,,,,,

1️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

   Sallama nayi part
din suna zaune falo sai mamace ke dakinta gaidasu nayi na nufi dakin mama don
lokacin banda shamakin shiga dakjn nata don da suke lagos nakan je hutu daga
Abuja.

   Bata nuna mjn
banbaci ga komai duk yadda yaranta keyi haka nake mata lokacin wanan ya jawo
shakuwa mai yawa a tsakanin mu duk faruwan hakan ya samo asaline bayan dawowan
mu gida gusau da mukayi ana zaune wuri daya.

   Nakai kofan naji
muryan mama na fadin ain fada maki Saratu da cewa yarta idan banyi da gaske ba
yaron nan musa yana son yafi karfina ne ba halinsu daya da Jafar ba shi sam
baya tsorona .

   Wai shi ya nuna min
ya isa zaiyi dalilin saya mata wanan motar mai uban kudi ta hau ita din yar
waye datafi sauran jikan tallakawa kawai.

   Lokacinne nafada
dakin duk da kunne yaji hakan ina sallama cikin rawan baki ta dakatar da wayan
tana min wani irin kaskantacen kallo tana jifana dashi.

    Har nakai tsakiyan
dakin ta daka min wani uban tsawa daya sani kaduwa tana fadin ke ubanwa yace ki
shigo min daki har nan kina ko da hankali kuwa zarah yadda yan uwana ke kirana
ranan babu maamah din.

    Yi hakkuri mama
bansan kina busy bane na fada a sanyayye zan juya na sake jin muryanta tana
fadin uban mema ya kawo ki nane wai yanzu ?

   A,a mama dama nazo
fada maki zancen motane shine bansan kina busy ba na shigo mota? motar banzan
ku can dake da wan naki munafuki inba sakarcin shi ba komu yaga mun shiga irin
motar nan ne a garin nan balleke zarah.

  Na dago kai na
kalleta jin yadda take kiran sunana a ranan kai tsaye bayan ita ke fada a da
can baya idan yan uwana suna tsokana na da Fatima zarah.

   Yau wai itace ke
fadin haka kai tsaye da bakinta tana kallona a fusace tacigaba da fadin ina key
din motar take na bata amsa nima da yana hannun ummah.

   Jeki zan karba na
juya rai bace zan fita daga dakin naji tana fadin kada ki kara gigin shigo min
daki daga yau idan kin fita kija min kofana ki kiramin Aisha ko Rukkaiya.

   Na amsa da to mama
na fice mata dakinta tare da jawowa na samesu falo na fada masu sakonta kamar
basuji ina magana ba don hakane nima banyi zancen motar dasu ba na fita.

   Ummah suna falo da
yan uwana suna cin abinci na shigo sukuku kamar kwai ya fashe min a ciki kanina
ke fadin wai anty zarah gobe ke zaki kaimu school cikin sabuwar motar ki ko ?

    Zama nayi saman
kujera gefen ummah ina fadin kai khalid wace motar motar da mama tace ban isa
shigarta ba karban key din zatayi hannun ummah.

   Karban key fa a
hannuna aiko da rashin ta idon hjy maimuna yayi yawa Allah ya kawota tace in
bata key din motar zata gane ba salman da nake ba yanzu gidan nan.

   A,a ummah ki bata
tunda dama danta ya saya min kinga ai shike nan dama kafin na shiga naji tana
waya da mama saratu tana fadin wai yaya musa munafukine yana son yafi karfinta
gidan nan.

   Waini jikan talla,
, , ,  sai kuma nayi shiru ummah tace ko
baki fada ba nasan hakane dama duk bakin cikin ta ke nan a kaina ita din yar
waye a garin nan banda Amadu sarkin teloli.

   Allah ya kawota
karban key din nan taga tsiya zan shayar da ita mamaki sosai a gidan nan kuwa
mukaji an turo kofan Rukkaiyace ta shigo tsatsaye dinta yadda take ba ladabi
tana saye da wani dogon rigan body hook a jikin ta duk ya matseta ga mazaunan
ta a fili irin shigan yan Lego’s na rashi tarbiya da mutunci shine dabi,an su
don ma su yaya na taka masu burkine wani lokaci.

    Duk idon mu yana
kanta ba tare da gaida ummah ba take fadin wai mama tace ki ban key din motar
da aka kawo dazun  ?

    Jeki kice mata
tazo da kanta ta dauka yana dakina wani kallo ta watsowa ummah din kamar zatayi
magana sai kuma ta juya ta fice daga part din daga haka ummah bata kara magana
ba sukaci gaba da cin abincin su.

   Saidai da gani
kasan zuciyarta ba dadi a lokacin sosai don yadda fuskanta ya nuna a lokacin
yanayin bacin raine karara a fuskan nata.

    Shiru shiru muna
nan zaune muna dakon zuwan mama karban key bamu ganta ba sai ummah data dago
kanta tana fadin ba zakici abinci bane ke kina zaune tun dazun.

   Nisawa nayi irin
wanda ke nuna mutum ya shiga zurfin tunane a lokacin nake fadin na koshi ummah
tace kin koshi me kikaci ko kin saka zancen nan a ranki ne ko ?

   To banson sha
shanci don maganan nan ba taki bace idan baya kama kiyi ba ki zuba min ido dasu
a gidan nan don haka tashi ki debi abinci kici yanzun nan.

    Kudin aljihunshi
ya fitar gaban Dije ya sake lissafawa suna nan yadda suke aje din ya dago kai
ya kalli Dije dake zaune ta zuba mai ido yace.

    Dije ga kudin
yanzu yaya zamuyi dasu zamu tabane ko kuwa mu aje har mai akuyan nan yazo ya
kama abinshi kafin muyi amfani dasu .

    Amadi akuya ai ya
sayeta ya bamu kudin mu duk sanda ya dawo ga akuyanshi nan a daure ya kama
abinshi ya tafi da ita meye namu a ciki yanzu tunda bamu muka sako mashi ita ta
dawo nan ba.

    Nisawa yayi mai
nauyi yace dana yanke shawaran zan fara sayen gwanjo ina sayarwa layi layi
ranan da ba karatu ko kuma nayi sana,an awo ina shiga kauyu ka ina sayo hatsi
ina kawowa nan na kafa dan table a kofan gidan nan ko yaya kika gani.

    Amadi kudin nan
basu isanka wanan sana,an har buhu nawa kudin zai sayo maka da kake wanan zance
kaidai fara gwanjon mu gani tukun abinda Allah zaiyi in yaso daga baya idan
ubangiji yaima budi sai ka fara wanan din zaifi.

    To Allah yasa mu
dace gobe kafin naje school da safe zanyi asubancin zuwa kasuwa na zabo masu
kyau da zasuyi saukin saye na gwada in gani tace Allah yasa albarka a ciki ya
amsa da Amin.

   Kwanon silver ya
jawo wanda Dije ke saka mai abinci a ciki ya bude kanzone data gyara shi da
ganye ya mike ya wanko hannunshi ya dawo dauke da ruwa cikin tsohon kofi ya
zauna yana bissimillah ya fara ci yana tunane.

   Washegari tunda
safe daga masallaci ya wuce kasuwa da kafa koda yaje ya samu an fara bude kaya
hakan yasa ya zabo wanduna da riguna na maza ya nufo school dasu duk da yasan
ba masayan fili a nan don zasuji kunyar saya.

   Amma shi ko a
jikinshi ya kai wani wuri ya aje ya nufi department din su da sauri don yasan
ya gama makara a ranan sai wadda Allah yayi zai samu shiga ajin safe.

    Ummah ni zan tafi
na fada  tana tsaye ta juyo tana fadin ba
zaki dauki kannen naki bane ki saukesu school sun gama shiryawa fa ummah ta
fada tana kallona.

   Nace Ummah aiba da
motan zan fita ba tace don me ba zaki fita da ita ba ko ajewa zakiyi kina
kallonta baki shiga ba don shiga aka saya maki ita ba.

   Wanan kuma yaya
zanyi da ita sai na ajeta ummah na tambaya ina kallonta wanan ki bari har Abbah
ku ya dawo saiya fadi hukuncin sa a kanta.

    Su fito mu tafi to
na fada kin dauki key din motar ne a, a ban dauka ba kije gun drower mirro yana
nan sama sai ki aje min wanan sin wurin.

   Na juya din na nufi
dakin kwanan ummah na dauko na kuma aje mata wanan din na fito naci karo da
kannena suna sauri kada in fita in barsu a gida.

    Tare muka tafi
yiwa ummah dake hada miya a kitchen sallama tayi muna Allah ya tsare da fatan
alheri a garemu ta kara da fadin in dinga kula Allah ya tsare ya kare na amsa
da amin.

    Hayaniyar da yaran
keyi na karadin shiga sabuwar mota yasa Aisha daga window dakin su tana kallon
mu taga mun nufi wuri sabuwar motar kai tsaye mun bude mun shiga lokacin ta
sake labulen ta juya da sauri zuwa fadawa mama abinda idonta ya gane mata din
lokacin.

    Mama da sauri ta
taso tana fadin yau ga yar iska yar banzan yarinya kawai wai ni zarah zata
rainawa hankali watau nayi abinda zanyi suke nufi ita da uwarta ko ?

    Tana fita muna
fita daga get din gidan namu sai kwalawa maigadi kira takeyi kada ya bude
saboda dan tazaran dake akwai a wurin yasa maigadin baiji me take fadi ba sai
kara wagale kofan dayayi muna na sauka na halba kan titi muka bacewa ganin su .

   Tsuki taja ta nufo
shi da fada shima wurin ta yazo yana faduwa yake fadin ina kwana hjy baka da
hankali ne ina kada ka bude kofan nan su fita ka bude mata au ya fada yana
kallon kofan tare da fadin walle banji hakan ba hjy kimun afuwa don Allah.

  Tsuki taja ta nufi
cikin gida da sauri part din mu ta nufa duk da Tani bata riga da tazo ba amma
ko ina a gyare yake kamar ba yara a part din haka sai kamshi turaren wuta dake
tashi a ciki.

    Tun daga kofa take
kwalawa ummah kira tana fadin ina Salman take wai maimuna lafiya ummah ta fada
kamar yadda ta kira sunan ta babu hjy itama lokacin haka ta kirata dashi
gatsau.

    Maimuna mama ta
fada cikin mamaki eh koba sunan ki ke nan ba ummah ta fada tana kallonta tana
tsame hannunta da ruwa ya taba a kitchen da kyale.

   Lafiya kike min
wanan kiran tsshin hankalin haka meke faruwane wai Rukkaiya bata zo nan ba jiya
tace nace ki ban key din motan nan da aka kawo jiya.

   Wani kallo ummah
tayi mata tana murmushi tace key din motan na maamah za,a baki idan zata fita
sai ta tambayeki ke nan ko ko mulkin naki har yakai ki muna mulkin kama karya
haka ?

   Salma ni kike
fadawa hakan yau ke wacece da ba zan fadawa haka ba ke uwatace ko kanwar ubata
da ina girmamaki don wasu dalilai amma sai ga hakan ke kin dauka fin karfine
hakan ko ?

    Dana dauka kinsan
mutunci yasa nake baki girma da kyaleki a matsayin wace ta girmeni a shekaru
sai kuma sanin girman zumunci da nayi nasan ke yar uwan maigidanane daga baya
kuma ina girmamaki kan yaran ki.

  Amma yanzu tunda na
fahinci manufarki dakyau a kan mu duk wani girma da kima daraja da nake gani
naki na daina bakishi maimuna har abada idan bakin gyara ba.

  Tana kawowa nan taja tsuki ta juya zuwa
kitchen ta karasa aikin da takeyi ta bar mama a tsaye tana yankan sababi a
falon  mu har ta juya ta fita tana fadin.

    Zan hadu dashi a
waya shida ya baki zaizo ya karba ya kawo min ke har zama  bariki kika koya da zaki nuna min kan mage ya
waye a yanzu ?

    Mu zuba dake da
munafukan yarki data sameshi da munafuncin an bata motar Aisha tafi karfin shi
ita ai ban san tafi karfin shiga wanan motar ba sai data nuna hakan yanzu.

    Idanuwan mutane
aka  motana suna duban suga waye ya
shigota haka ya haska kowa saidai na dan jima a ciki ina hada kayana kafin na
bude na fito .

  MAYANA wata ta fada
wanan ai yar gidan mayana ce wace ke 200 level din nan yanzu maganganu irin na
kus kus da jama,a keyi musanman yan makaranta da saka ido shike tashi a wurin
har na shige science bluding na shiga department din mu.

   Kowa na harkan
gaban shi don malamin bai shigo ajiba lokacin ba wuri na samu nakai zaune inawa
wace na sama sallama muka gaisa a musulunce da ita.

    Wai naji suna
fadin yau malam bai samun shigowa son baida lafiya sai lokacin na kallota ina
fadin ayyah Allah ya bashi lafiya gaskiya naga ajin yau a haka.

    Na dauko wayana a
cikin jakkata don in kara tyring din layin ya musa don tun dare nake gwadawa
wayan shi a kashe yasa yanzun ma na kara trying.

   Saidai ban sameshi
ba yasani jan tsuki ta kara fadin lafiya nace ba komai yi hakkuri na dameki ko
?

    Yauwa dama ke nake
duba tun dazun banga shugowan ki ba ya kika tashi fuskana na tsuke lokaci guda
don ganin mai maganan dani danayi.

  Ba kowa bane sai
wanan guy din da nake ganin yana skn ya matsa min da surutu ko samu kan wanan
da bansan komai a kanshi bama.

    Nace don Allah ko
kunyi maganan dashi ya yarda sai mu fara yau wallahi ni nasan  zamu samu karuwa sosai a wurin shi wa ke nan
wanan dana sama take tambayanshi ?

    Kinga ga wata
member mun samu gaki ga abokina sai mu tafi yanzun tunda muna free ko yaya kuka
gani dakata malam don Allah.

  Kai idan kayi mai
magana laifine kaje ka sameshi mana amma ni ba inda zanje na fada ma ya wani
kalleni yace but idan nayi masa magana har ya yarda zakiyi joining din mu dai
don abin yai armashi ?

    Jeka kayi na fada
a dan fusace yace nikan nasan ba wanda yaki karuwa sai in bai samu ba dai barin
dubashi ko yana free yanzu muyi maganan amma fa ki sani da sunan ki zanje in
sameshi.

   Yana fadin haka ya
juya ya tafi naja tsuki ina fadin tunda kowa irin kane kada ka tsaya kai karatu
ka kwaci kanka ka dogara ga wani.

   Ganin yadda class
din ke surutu rashin malami yasa na mike na fice daga ajin naji muryan wanan
tana fadin jirani mu fita tare don Allah dole na tsaya muka fita tare da ita.

    Wata sister ya
tambaya cikin mamaki a,a MAYANA ta class din mu mana wace ka fadawa malam
sister dinkace har malam din ya yafe muna mu shiga saboda ita.

   Ok wallahi so muke
mu hadu dakai ka taimaka muna kadan bamu group discussion tace wallahi kunyar
ka takeji ba zata iya zuwa da kanta ba.

   Ina take yau ai
bata shigo ba nake gani don banga motar taba a park da sauri munir yace  a, a tana nan class zaune ai tazo tun dazun.

   Ka bari zan ganta
muyi magana ya fada a cikin gadara da izza irin nasa na dan tallaka da gadara
din nan don haka yake magana kamar dan basarake dashi .

    To shike nan Done
zamu saurareka amma ka taimaka  ko don
saboda ita please na barka lafiya sai mun jika please.

    Baidai masa magana
ba sai mikewan da shima yayi lokacin don tunawa da kaya  gwajonshi dake ajiye a bayan ajinsu ya duba
ba abinda ya samu kayan ya kara gyarasu ya dago zai koma lokacin ya hangoni
tafe tare da wata muna tafiya a jere muna magana da ita.

   Tun daga nisa na
danna key motar tayi kara daya jawo hankalin mutanen wurin au motarki ke nan ta
tambaya na kada mata kai take fadin wai dankari ashe dai ke din yar masu garice
shiyasa tun zuwan ki baki kula kowa dama ?

   Idan nace bata
isheni ba farawa da iyawa nayi karya don na kula tana da surutu ita sosai
sabanin nida zan iya zama magana saita kama nayi da mutu na bashi amsa daya
haka ummah ke shan fama dani a gida.

    Motar na bude na
dauko goran ruwa guda biyu zan dago naji muryan shi yana fadin ashe kinshigo
school din yau na juyo da sauri ina dagowa.

  Yana tsaye a dan
nesa kadan damu nace eh wallahi  ina ciki
tundazun na mikawa wace muke tare roban ruwa daya ta karba tana min godiya tare
da jingina jikinta a bayan motan .

 Dayan Goran ruwa dake
hannuna na mika mashi sai ya girgiza kanshi yana fadin Alhamdullahi nagode amma
ke baki iya zuwa ki fada min saiki turo min wani.

  Banina turoshi ba
shiyazo da kansa nasan dai da zancen wani kallo yai min kafin yace koda yake
nasan kinfi karfin yin hakan da kanki saidai ki turo wani yazo.

   OK wanan shine dama
ake magana me surutu ta tambayeni na gyada mata kai tace malam ka taimaka muna
mu dan samu sauki wallahi abubuwa suna da rikita kai yanzu sosai.

   Idan nace zan dinga
tsayawa na koya maku kullun zaiyi wuya hakan saidai lokaci lokaci insha Allah
sai mu fara Monday idan Allah ya kaimu don yanzu na riga da na saro kaya ina
son in shigar dasu ko Allah zai taimaka min.

  Kace kai dan
kasuwane ashe kana karatu kake da wanan lokacin to yaya za a ayi ya fada ya
juya da sauri ya wuce ya nufi cikin department din.

    Abba dake kwance
da kyar ya mika hannu ya dauki wayan irin yadda yaji muryan mama din yasan wani
abu ya faru ke nan a gidan ko yana shirin faruwa.

    Meke faruwane hjy
maimuna najiki a hasale dole in hasala Alh tunda yaron nan yana son ya fara
jamin magana a wurin ka yanzu.

    Wani yaro kuma ke
nan kike magana ya tambayeta,  tace wane
yaro  kuwa banda baba wai shine harda
sayawa Zarah mota mai tsada haka tunda ya isa yanzun yake gani shi.

   Na aika a karbo key
din motar a hannun uwarta don hauka ita kuma ta hana naje da kaina tana son
fada min maganan banza wallahi idan salma batai hankali ba zakaji nayi mata
abinda ba,a zata ba.

   Yace ita salma din
kwarai kuwa wai yau ni salma ke kallo tana fada min in na isa na shiga dakinta
key na ciki koko haihuwanta nayi da zan dinga kawo mata raini irin haka ?

   Ai gaskiya ta fada
wanan ya zama wullakanci da raini wayau a gareta wai ko kin manta salma ma
matatace itama kuma tana gaba dake idan ma har wani abune baki kirana kiji
yadda akayi.

    Saiki je mata kai
tsaye wai  ta baki key koda karba ne aini
dana ajeku yakamata na karba a hannunta bake ba don raini saikije mata kai
tsaye haka kimkam.

    Sai zancen motan
da kikeyi wai baba ya dauki kudina ya saiwa maamah mota toh ba dauka yayi ba
nida kaina na bada kudi ya sayo mata wanan motan kamar yadda na sayawa kowa
lokacin fara karatun shi.

    Ke kika tambaya na
bada kudin motan kisaiwa maamah din moto a baya ashe baki sayaba sai kika gyara
mata na Aisha tana shiga .

   Maimuna ina zaki da
wanan alhakin haka a rayuwan ki koso kike duniya ta zagemu don uwarta nada
hakkuri da zama damu sai mu dinga takasu yadda ran mu keso ?

    To ki tuna da baba
da ita maamah din duk nina haifi abina kuma ina son kowa don haka ki kula don
ba zan dauki wanan ba ya kashe wayan.

  Tabi wayan da kallo
ta dafa gado tana zama don da a tsaye take tana shirin zazaga mai bala,i a
lokacin sai taji wani abu na daban daga gareshi wanda bata zata ba a lokacin.

 

Leave a Reply

Back to top button