Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan ko Mazan 24

Sponsored Links

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣4️⃣

Yau nazo da gangariyan rahoto wato PRACTICAL CHINA IMPORTATION class💃💃
Ga inda zaki koyi asalin ilimin saro kaya daga china, za’a koya miki ko dubu 20 kikeda shi zaki iya fara saro kaya Wayyoo Allah na, babu wani dogon zance kuzo mu shiga WAITLIST din nan tare💃

Danna link ki shiga group din waitlist
https://chat.whatsapp.com/FIKdtOLn4vjGOQ1bHuI9l0

24
Sauka kasa yayi zuciyanshi na masifan tafarfasa yabude mota yashiga ko gaisuwan da maigadi kemai be iya ya amsaba yaja motan shi sabida yanda ranshi ke soyuwa yanar gidan, he’s just angry da kowa, Hajiya tunda takoma kano taki daukan wayanshi, koya kira Meena yanason magana da ita bata amsa tace agayamai idanba ya nemi Ummi bane he shouldn’t bother about talking to her, ga kuma Ummi dazata kama tabar gidanshi tanamai zuciya akan abinda baitaka kara ya karyaba dan shi har yau baiga wani takamaimen abu dayamata ba, kuma takama takashe waya irin she doesn’t even wants him to look for her, she’s done dinnan, saikuma Alhaji Musa yana wani gayamai ya sake Ummi shi zai aura sabida an gayamai shi auren dan ya saketa ne yayi, now kuma Hadiza ta tsareshi ta titsiyeshi kaman danda ta haifa saiya mata bayani mesa yayi abinda yayi, why is everyone doing yanda yaga dama dashi he’s just so tired, mesa the peace he’s yearning for at this age yakasa samu? Why? Mesa stubborn women ne suka cika rayuwanshi? Da kyar ya iya kai kanshi office yawuce sama yashiga office nashi yama rasa ina zesa kanshi yaji dadi.

Yanda zuciyan Hadiza ke bugawa zaka dauka kararrawa ake bugawa aciki, hannunta har lokacin nakan kuncinta da Nura ya mata, bakinta kuma asake tabishi da kallo har saida taji tashin motanshi sannan tawani zube zaune awajen, kuka ke zuwan mata sosai amman tahana kanta no bataso tasake zubarma da wanda yamata bakin zagi haka, yau itane Nura zai hurting nata haka for the second time dan auren Ummi was first, wannan kuma nabiyun, ita Nura zai kira zero! Ita, a Cinderella, Nigerian kardashin, business mogul queen, Oga wife like her, yasan how many online business vendors ke shishige mata, all matan abujan nan da gangan suke zuwa shagonta abaje bajinta ayi shopping just sabida aburgeta tayi kawance dasu, infact duk randa take shago anmafiyin ciniki, wani kalan gyarane batayi, saloon treatment daban daban, even a sex din this days she’s trying alot, inhar namiji zai ciki yakawo kuma how dare he calls you zero? Da ace Nura tun farkon aurensu ya nuna yadamu da sex he wants it da babu yanda zatayi dole ta dinga bashi, she’s not lying but itada Nura nazama gida daya for 2months abu bai shiga tsakaninsu ba, wani kalan maita yarinyar nan tazo tazuba ajikin mijinta cus she don’t recognize Nura anymore, ita Nura zai daga hannu ya ketama mari? Why is he so angry? Bata taba ganin Nuri na wannan fushin masifan ba, metamai dazai mata kalan marin nan??? Parking motan dataji anyi yasa ta zabura ta mike tayi stairs tasan shine halan yadawo ya lallasheta ne daidai tana karasa saukowa kasa daidai ana bude kofan falonta ana shigowa.
Baraka da Zeena ne suka shigo rikeda wani hamper na snacks da fruits aciki suka hada ido dasauri wani irin kunya Hadiza taji ganin kawayenta ne ga gidanta kacha kacha ga jan idanunta maybe akwai hawaye aciki dasauri daga Baraka har Zeena suka karaso cikin falon, Zeenah tayi wajenta da gudu tana bude hannu tace “oyoyooo my Sick baby sannu, wlh nida hubs munje Maldives ne ai I told you about the birthday trip dazaimin saisa banzo na gaidaki ba I just greeted you a IG da naga kinsa, jiyan nan nadawo yanzu ma shago mukaje akace kin dawo gida nacema Baraka let’s go gidanki, sannu Haddy, how are you feeling now”? Murmushi Hadiza ta kakalo tana kallon Zeenah dataci gayu tasha gwalagwalai tayi kyau takara kiba sai sheki take, tace “na warware tass nida harnayi resuming zuwa shago ma” dasauri Baraka data ijiye hamper anan falo ta taho wajen benen tace “sannu Hadiza Allah baki lpy, ya duk na ganki wani iri haka” tai maganan tana mika hannunta dasauri zuwa kumatunta tace “an mareki ne naga kaman shatin hannu” dasauri Hadiza zata juyar da kanta Zeenah dabata luraba takama habarta tana zaro idanu tace “what happen to your face? Kinga hannu shaaaa a fatan fuskanki yayi jazur sabida farin fata, who slapped you”? Wani kalan fizge fuskanta Hadiza tayi tace “dalla kubarni waya isa ya mari Hadiza aduniyan nan are you guys for real? Zoku zauna bari nakawo muku drinks” tawuce zata tafi dasauri Zeena takama hannunta dan she’s just like Hadizan saisa itace best friend nata.

Tace “Besty kaman ya bari ki kawo mana drinks I don’t understand, in your own house kene ke serving guest drinks ina yar aikin ki?” Zeenah tamata tambayan kai tsaye dan cikin duka mutanen Hadiza banda yan uwan ta najini babu wanda ta fadiwa Nura yayi aure dan abin kunyane agareta, zatai magana Zeenah tace “tell us we three are childhood friends ku munma juna dariya kanmu mukamawa remember yanda mukema Baraka fada, what’s happening? Who slapped you haka a fuska? Sannan ina yar aikin ki? Why is your house so dirty haka? Look at falon nan see dinning why is everywhere so scattered and disorganized, I don’t even wanna talk about yanda kika rame cus I wanna believe rashin lafiyan dakikayi ne yasaki kika rame but who slapped you this hard eh”? Baki Hadiza tabude zatai magana kun gane irin kukan nan da baka bashi izinin zuwa ba amman kawai sai yazo without permission shiya kufce mata da sauri Zeenah ta yarda jakanta tace “ohhh no come here sweetheart it’s okay, it’s okay, who hurt my Didi this much? What’s going on Didi talk to me, Baraka zo” dasauri Baraka ta zo dukansu suka rungume Hadiza kafin Zeenah tace “muje sama mu sauna kawo mata ruwa Baraka” gyadamusu kai tayi Zeenah tawuce da crying Hadiza sama Baraka kuma tawuce fridge ruwa a dauka suka wuce sama, Zeenah tabude ruwan takai bakinta tace “sha Hadiza” kadan ta kurba ta ijiye ruwan, ahankali tace “menene Hadiza talk to me who slapped you”? Cikeda Jin nauyi da kunya but sun riga sun kamata babu yanda zatayi tace “Nura ya mareni!” Daga Zeenah har Baraka zaro ido sukayi cikeda mamaki Zeenah tace “Nura yamiki wannan kalan marin?” Gydamata kai Hadiza tayi tana fuzarda iska, rai abace Zeenah tace “baki suing nashi for domestic abuse ba are you okay Hadiza? Your husband is abusing you haka, maisa baki daukomai yan sanda ba”? Dasauri Baraka tace “haba Zeenah wani kalan yan sanda kokuma tayi suing nashi sabida just this one time mari is not something dayake faruwa kullum shekaransu nawa tare yataba marinta ne” cikeda masifa Zeenah tadagama Baraka hannu tace “kinga just keep quiet and allow me talk to my friend ke dama kin saba tolerating all sort of trash daga mijinki saisa he doesn’t respect you, Hadiza and you are two different people, she knows her rights unlike you akanme, akuma kan wani dalili Miji zai kama yana taba lafiyar jikinta tai shiru look at her precious face, kinsan da kasan waje ne kalan hukuncin dazaihau kan Nura kuwa look at her face for crying out loud yadauka jaka ya auro ko tumakiya, yadauka bakida gatane am calling my lawyer inama jakana” ta jujjuya ganin bataga jakanta ba yasa ta mike tawuce kasa rai abace, Baraka ta kalli Hadiza dake goge kwalla tace “yanzu zakiyi suing Nura sabida ya mareki Hadiza? Me aciki dan Nura ya mareki yana marinki da ne? Why are you and Zeenah like this eh? Nura fa baban yaranki guda biyu ne shi zaki maka a kotu? Ko darajan yaranku bazaici ba”? Shiru Hadiza tayi daidai Zeenah na karasowa tace “say whatever you wanna say Hadiza is not you and can never be you, duk matan dazata zauna miji na dukanta anytime dayaga dama jakace kuma yar akuya, kuma dakikiya ni Zeenah nafadi haka, and idan tabari wannan to slide to Nura yadingayi kenan kalleni nan Hadiza” Hadiza takalli Zeena tace “ask Baraka dazu da dasu Hanna da Saudat da some members na meeting dinmu zamuzo fa but mukace bazamu iya jiransu ba, da dasu mukazo da bakiji kunyan duniya ba? Da gulmanki saiya zagaye Abuja fa ana mijinki na dukanki, waye Nura? Duka kudin gudanawa gareshi da he feels zai iya miki kome yaga dama haka, waye ubanshi? Shida kudinma nemansu yayi ba haihuwanshi akayi aciki ba, look at you Hadiza yazaci idan kin rabu dashi zaki rasa mijin aure ne? Koya dauka shi Autan maza ne? Kinmasan how beautiful you are kuwa Hadiza? Wlh yarabu dake saikin sami mijin dayaci ubanshi akomi, just like me yanzu minister nake aure, da Bala yafara dukana dayaga I know my right namakashi a kotu ya biya ai yagane koba komi na batamai clean record nashi, sunanshi is registered under domestic violence yanada record dazai bishi ko’ina, sannan na barshi, u were there for me lokacin look at me yau married to minister dakeda mata biyu nine ta uku but nice yar gaban goshi, ki watsar dawani soyayyan nan ki yaki Nura fa, wlh kuka rabu da Nura zaki sami mijin dayaci ubanshi akomi barinma yanda aka sanda ke a abujan nan da business naki haba, kina daga cikin top housewives of Abuja fa dake representing Abuja who d f*ck is Nura? Take action against him now kafin ki zama Baraka part two” rushewa da kuka Hadiza tayi tashiga fadamusu duka abinda ke faruwa tundaga auren Ummi, mutuwan zaune sukayi sai kawai Zeenah tafashe da kuka tace “Baraka let’s go tashi mutafi Hadiza bata dauke mu as family ba, Baraka koda you were going through something, dudda bazakijin shawaran mu but sharing heals right and we are always there for you cus an zama daya we never abandon you” Baraka tace “kwarai, I don’t agree with ways naku but I’m always grateful to have the two of you as friends dina I know sometimes kumun dariya kuji haushina kaman zaku daken but baku taba kai magana ta waje ba it remains among us, and both ke da Hadiza always helps me financially, idan something come up a meeting na association namu zakumin anko baku taba bari an gane inada wata matsala ba kallonmu ake dukanmu ukun daya, I know kuke ganin abu ya bambanta dani but friendship naku is genuine, Hadiza why will you be going through something like this bazaki fadamana ba”? Cikin kuka tace “zakumin dariya barinma ke Baraka I remember yanda nake miki dariya ina kiranki wawiya mara wayau, that’s why” girgiza mata kai Zeenah tayi tace “the three of us are one saidai sauran kawayen mu su mana dariya but never us Hadiza, Nura babban shegen dan buhun uba ne, kici uwarsa wlh yagane ke ba kanwar lasa bace, being a wife doesn’t make you a slave, shi wani kalan mara imani ne, look at how big this house is, taya zaki fara kiyi shara kiyi mopping kiyi wanke wanke ki tattara kayan yara ki wanke a washing machine ki shanya, kiyi kuma nashi, kiyi girki ki wanke plates, u are working class woman fa your business needs you naaa Hadiza this is pure wickedness Nura bayason ci gabanki he wants your business to crumble saisa yakeso kina all those aiki ke kadai without help how will you manage? Ko kula da yara aka barki yimusu wanka feeding them, homework getting them ready for school is it easy? Kananun yara gareki fa 4yrs and 2yrs how will you manage”? Ahankali Baraka tace “ni yarana hudu nike komi” Zeenah tace “you are not working so karki hada kanki da Hadiza you are housewife” takalli Hadiza tace “clean your tears kada ki kara wasting hawayenki akan da namiji barinma wanda yayi betraying naki kaman Nura, wlh da yarinyar nan nanan yau da saina sa an kulleta a barrack su mata jina jina a kwakule tsinanniya, ita harta isa ta yaudareki ta aure miki miji suna cin gindi da daddare suna ihu suna nema su kasheki kuma kika zauna, are you mad Hadiza? Yau idan zaki mutu let’s assume baida wata matan ma kafin 40days wlh Nura yakara wani aure ballema ya auri yar aikin ki shagalinsu zasuyitayi abar family ki da kuka cus yaranki bayi zasuyi ba they’re still very small yan uwan ki kawai zasuyi bakin cikin ki Nura, Nuran uban meyeshi kin nanama kanki sonshi mugun mutum is he the only man on this earth? My dear clean your tears” goge hawayen ta Hadiza tayi tanajin karfi na zuwan mata wannan ne kalan shawarma dataso Anty Jams tabata amman bata bataba, sai shawaran dayasata cikin wahala kawai all this while.
Zeenah tace “Hadiza it seems you are lost kin manta waye ke lemme remind you girlfriend” Zeenah na kallonta tace “Hadiza you are a strong independent woman wacce ko da namiji ko ba namiji you can live your life and survive on your terms, you are a feminist Hadiza!” Wani karfi Hadiza taji yashiga jikinta, Zeenah tace “idan zaki mutu die of normal course badan namiji ba, a man is too small yabaki ciwon zuciya! Ke with ko without Nura you have you can have a better life, kinada booming business worth millions of naira, you have cars, kinada yara tell me mekike bukata awajen Nura da zai dinga marinki bayan yaci amanarki yana miki tinkaho”? Ahankali tace “babu! I can do everything for myself, I can live my life yanda naga dama, I have money to sponsor any desire na, inada gida dana siyama kaina a kano” Zeenah tace “good now kin soma dawowa, ke Nura ya auran miki yar aiki baki tadamai hankali ba kika cigaba da zama dasu ana cusa miki bakin ciki, yarinya na kada takashi agabanki left and right ba kunya ba tsoron Allah in your own house, gidanki fa Hadiza asiri Nura yamiki ko yamiki rufa ido da rufa baki ma duka? Ya taushe miki bakine da bakici kutumar buhun bura ubansu ba dagashi har yar aikin kihanasu kwana agidan” ahankali Hadiza tace “looking back wlh I’m regretting daban tadamai hankali ba, Zeenah banmasan meya shigeni ba those days, bansan wani kalan wayau Nura yamin ba kawai yadinga kwanciya dani yanamin some things that I can’t even explain, bansan wani kalan brainwash and mind wash yamin ba but anyi an gama, yashani kuma na warke, Is time to let him know know that I am still that Hadiza kuma daidai nake dashi, first and famous bari na samo yan aiki dan koni I hate dirty, zan dauki yan aiki guda hudu, 2Nanies masu kula da Aman da Amali, sai biyu masu gyaran gida da aiki, Nanies din su Aman inason yan Philippines dinnan irin yan shekaru 40 educated ones dazasu din tayasu yin homework, sai I want a chef mai girki yar tsohuwa hakanan sai mai shara da gyaran gida kuma yarinya age 12-15 haka kada tawuce 15yrs, I don’t care konawane salary su i will pay” dasauri Zeenah tace “lemme call my personal person goben nan zakiga tasamo miki” tace “kira nima I will call my lawyer I just have to sue Nura let’s settle this score, koda zanyi withdrawing lawsuit din daga baya but yagadai i can take action idan yataba lafiyan jikina sabida karya kara kuskure yace zai taba educated independent woman like me” ihuu Zeenah tayi tahau tafi tace “now you are talking, my friend is back kicima Nura kutumar babakeren uba, ke maza fa sunfi tsoron maicin ubansu” dasauri Hadiza tace “I believe you ai sanyin danayi kwana biyu yasa raini ya gitta tsakaninmu wai harda marina, ni Nura zai daga hannu ya mara, kinga snap my face i will use it as evidence” tabama Zeenah wayanta, karba Zeenah tayi tadauki hotunan fuskan Hadiza harda cemata “yi kaman wacce taci kuka takoshi” Hadiza tai haka tai clicking snap tabama Hadiza wayan, duba hotunan tayi ranta na kara baci sabida yanda yatsu biyar suka fito a fuskanta dodar dan da duka karfinshi na maza yamata marin saida taga duhu.
Mikewa tayi tace “kutashi muje lemme go nayi gyaran jiki and facials kafin hannunshi yazama permanent tabo a fuskana.
Tashi sukayi sai kawai ta rungume Zeenah tace “I love you best friend, you are better than my own blood sister, you just brought back light into my life” Zeenah tace “absolutely no man aduniyan nan ya isa yace zai takamu wlh, we know our right, mari fa ko a shari’a batada kyau, ai Nura deserves more, ki yarda wani stupid love who love help kuyi settling score yakoma yana tsoronki zakiga wlh zai shiga taitayinshi” Hadiza na murmushi tace “da ina cin ubanshi ma yafi sona, yanzu dana dena wai Nura ne yasamu liver daga hannu ya kodamin mari ni Hadiza, I will mess him up wlh”. Suka wuce suka fita daga gidan.

Jama’a like I said I just wanna portray the major issues dake kawo rabuwan aure a zamanin nan sabida ku gani kusan daga ina mistakes din ke zuwa, ta yanda zamu karanta mu gyara idan munayi dan believe me most of us munada one of two dabi’un Hadiza Allah dai ya kyauta yakuma shiryan damu.

But then I have a question, what do you think can change mata masu strong opinion din Feminism???

Note dukan mace baida kyau fa, please maza masuyi su dena, cus kahadu da macen datasan kanta she can ruin you completely da career ka so adena dukan Mata maza 🔊
Dukan mace ke jawo case din dambe between mata da miji, daganan kaga an kashe juna, ko mata ta kashe miji ko miji ya kashe mata, ko ajima juna rauni mai muni Allah ubangiji ya shirya damu.

Leave a Reply

Back to top button