Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan ko Mazan 27

Sponsored Links

@💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣7️⃣
KUJE AGUJE🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️ KU KOYI HARKAN KITCHEN🏃🏻‍♂️🏃🏻‍♂️

Great news for the people outside jos who are eagerly want to become pastry chefs and bakers.
BAKE N’ FROST
is bringing you it’s first online class and the class will come with alot of benefits. 🥰🥰🥰
Make sure you join us today. 🤩
Believe me, you won’t regret it because we will be teaching you everything from scratch 💃🏽
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Hs8bU0RnXpLA5Lvr1o4qDe

Hadiza tajuya nan tajuya chan takasa bacci hakan yasa ta mike tawuce bayi ta tsaya gaban mirror ta wanke fuskanta tana kallon kanta idanunta sunyi jazur, takasa wrapping head nata around abinda Zeenah ta mata, wani kalan daura hannayen ta biyu tayi akan bakinta tafashe da kuka da kyar ta lallashi kanta tafito tadawo daki, wayanta tadauka takira Barakah amman harya katse bata dauka ba hakura tayi ta ijiye wayan ta lumshe idanunta, da ace Zeenah bata ambato zancen court ba da batasa Nuri a kotu ba wlh dudda tasan saitayi bura’uba dashi dan bai isa ya mareta bane ta hakura ba but bazata taba tunanin kotu ba. Zama tayi ta gaban gado tayi shiruu tanaji kaman an daura mata dutse akirji saikuma ta mike tsaye taje gaban wardobe tabude she’s feeling so angry da kanta, duk wacce tace zata iya maka bayanın the feeling after been divorce daga mijinka is just lying dan the feeling is just unexplainable, she’s having different emotions, She’s angry da abu biyu yanda Nura yasaketa yakuma mata iyaka da gidanshi and his life gabaki daya, yanzu fa idan tashiga rayuwanshi yanada hujjan yimata kome yaga dama dakuma abinda Zeenah tamata, takasa gathering courage na kiran gidansu dudda taga kiran Anty Jams takasa dauka takasa kiranta she don’t even know what she’s doing, all abinda tasani is zataci durun uban da uwar Zeenah gobe before she even think of anything dan idan bataci uban Zeena ba bazata sami kwanciyan hankali ba.

Komawa gado tayi ta kwanta tasake daga wayanta batasan metake ba but kawai samin kanta tayi da shiga gallery taciro hoton Nura yana sanye da suit da cake agabanshi ranan dayay lunching real esatate company nashi na a Abuja tamai hoton yana murmushi sosai yayi kyau da fararen hakoranshi, Nura is very very handsome, dudda shekaru sun ja but few furfura gareshi kodan yanada kudi ne kuma yana kula da kanshi ga yawan shan fruits but he’s super cute, kuma he’s still very fit bai ijiye wannan pot belly ba. Kuka Hadiza takejinyi tana kallon hoton but tahana kanta yi takasa yardanma kanta tayi kuka sabida wani yasaketa da sauri cikin karfin hali tana kallon hoton nashi cikin wani kalan murya da kasan she’s so hurt tace “ni zaka saka Nuri har kanace amaka shamaki dani who do you think you are? Kana tunanin zanyi kuka ne or I will be hurt sabida kamın haka to nima I don’t want you” tana maganan kuka yazo mata wuya tarike kukan gam tasa yatsanta ta nunashi tace “yesss I said nima I don’t want you, nima amin shamaki dakai, I don’t wanna ever see you” tai maza tai shiru jin kuka na neman kufcemata chan tace “I don’t even know why nake wani tunaka what’s so special about you Nura akwai thousands of men that are way cooler than you’re, sun fika kyau, sun fika kudi sun fika komi so why am I sad? With or without you Nura I will always be Hadiza Mangal Haruna! Babana yabani sunan nan and I will always be that, I have my money, I can give kaina anything danakeso and sponsor any trip danakeso naje so barina dakayi baida any effect akaina kuma kadade baka sakeni ba kaine kai rashi, i promise you bazaka taba samin mata as Preety as I am ba, as loving as I am ba, kuma bazaka taba samin wacce zata baka yara kyawawa kaman wanda na haifamaka ba and lastly Nura saikayi nadaman sakk…….” Kuka ne ya kufcemata da sauri ta ijiye wayan ta daura duka hannayen ta kan fuskanta tace “why am I crying now I hate you Nura I hate you, mugu azzalumi narasa meyake ma mace dayake sa so much effects on her, get out of my heart Nura, get the f*ck outtt already” tafashe da kuka sosai ita kanta batasan why takema Nura wani cool so, he’s just so adorable ne, gentle and cool guys has always been her spec, she loves Nura cus he’s so gently da ita, despite abubuwan dazatamai he will always treat her with so much love and affection kaman batamai komi ba Nura ko is just something else ne kawai a maza, bata taba ganin forgiving man like him ba, baida bakin ciki sannan zai iya sadaukar da rayuwanshi just to see you happy, dudda tanamai iskancin datakemai bata taba fatan ya chanza ba saisa bazatai karya ba daya saketa yau ta girgiza! Bata taba sanin zancen kotun nan zaisa ya saketa ba, abinda yafi jinjigata shamakin daya musu, wato yakai karshe yanzu he’s done with her ohhh no no her heart arching in agony wlh batasan sanda bacci yayi awon gaba da itaba.

Wuraren 7 ta farka tashi tayi ahankali tawuce bayi wanka tayi tayo alwala tazo ta maida kayanta tai salla sannan tai order abinci shima tsakura kawai tayi tasake dannama Baraka kira wajajen 8, Baraka na dauka Hadiza tashiga koramata abinda yafaru Baraka tace “mu hadu a shagon ki zan kira Zeenah sai a maida maganan” sukai sallama tashi Hadiza tayi ta shirya wajajen 8:30 tabar hotel room din tana kallon Anty Jams da Mama duk sun kirata taki dauka but taki dauka still hada handbag nata tayi tafito tai checking out ta tafi wajen motarta tabar hotel din zuwa shagonta da har sales girl dinta tabude amsa gaisuwansu tayi ta tsaya ta zabi abaya daya mai shegen kyau tawuce sama office nata dashi tana zuwa ta shirya tsaf ta zauna bata wani dade da zamaba saiga Baraka ta shigo tace “Hadiza” tashi Hadiza tayi cikin fushi tace “ni Zeenah zata yaudara” da sauri Baraka tace “kinga daina ihu Hadiza staff naki na nan” cikin fushi tace “bura’uban staff” fuuuu tawuce kofa tafita tasami yammatan guda biyu tace “kutafi gida nabaku off today” cikeda mamaki suka kalleta ganin da gaske take yasa suka tafi bayan sun mata godiya takoma sama, Baraka tace “Hadiza calm down explain it to me Zeenah tana hanya kinga baban yaran nan nafita nafito nima wlh sabida banma gane maganan dakikemin ba ta waya” Hadiza na kallonta tace “Baraka kinsan halina, ke da Zeenah are my only two close friends duk duniya, Baraka kinsan banda gulma arayuwana tunda nake dake nabata kawo miki maganan wata ko wani?” Baraka tace “a’a zan shaideki awannan Hadiza bakida time din nan” Hadiza tace “bana karya, sannan bana munafuntan mutum wlh yanda abu yake araina haka nake juyeta da bakina, bantaba samin wani naje nabada labarin ki ba, Baraka you and Zeenah are the closest associates danake da shi aduniyan nan banda family na akan me Zeenah zata yaudareni ta ha’inceni” daidai ana bude kofan Zeenah na shigowa tai shigan alfarma tace “kaman ya na yaudareki ko na ha’inceki”? Azuciye Hadiza tajuyo tashi Baraka tayi tace “dan Allah dukanku biyun calm down ku tsaya bari naje na kulle shagon kar customers suzo bamu sani ba” Baraka ta fice da sauri Hadiza da Zeenah sukahau kallon kallo Zeenah ko dar babu tattare da ita saima cingum datake tauna wa Baraka ta dawo ciki kai tsaye Zeenah tace “Baraka kinsan ina mugun ganin mutuncin ki saisa nazo wlh wlh dan banga abinda zai fito dani yau ba dan yau ake zuwa mini full body massage har gida, so why did you call me”? Anatse Baraka tace “Zeenah zauna” takama hannunta ta zaunar da ita akan kujera, Hadiza kuma taja kujeran gaban desk nata ta zaunar da ita tace “Hadiza you too sit please” itama ta zauna Zeena ta zauna kan center table more like tana tsakiyansu tace “we three are friends tun secondary school days namu a college munada n fadan mu da hargowa na yarinta but so far so good tunda mukai aure mukai hankali bamu kara tada ba, please what is happening, Zeenah Hadiza takirani this morning akan kin yaudareta kin ha’inceta, kin kuma cuceta meya faru? Talk to me Zeenah” wani kalan karkada kafa Zeenah tayi ta kalli Hadiza tace “Hadiza ni ne na yaudareki na ha’inceki how? Yan fashi ko kidnappers na kawo aka kwashe kayan shagonki ko me namiki tell me? Ko maganan ki nakai waje? Ni ban kira Baraka nakai karanki ba nida na taimaka miki mijinki ya koraki daga gida nakaiki nawa gidan ki kwana kikahau zagan mini miji saikene keda bakin kice na ha’inceki na cuceki ke babydoll ko, to uwar uban yaya na cuceki ko yaudaranki?” Sosai Hadiza ke kallon Zeenah adah Hadiza feels duk duniya bataga wanda yakaita baki da tsiwa ba, she can stand anywhere and defend herself but yau saitaga batada bakin Zeenah tafita cus for a moment saita rasa mezata fadi na cewa Zeenah ta cuceta ta ha’inceta, tarasa how she will put it in words ayanda takeji azuciyanta sai chan zuciya ya bala’in zo mata wuya amman tadaure tace “Zeenah lied to us she’s not abinda take fada mana she’s, she lied about tanada yan aiki, even vacation din datace taje for her birthday is not like taje din da gaske Zeenah is a crook lier and a deceit, she kept on telling us she’s a feminist ita kaza kaza kaza ce agidan mijinta, she’s lying karya take mijinta treat her kaman garbage, fasa plates agabanta without tsoron kada yaje yajimata ciwo, she’s just so full of lies mayaudariyan mata irin ta, taje tasa na maka mijina a kotu abanza a wofi makira annamimiya la’ananniya kawai, agunguma, wlh Zeenatu ta girmi shedan cus jiya saiya yamata salute din raba aure” jakan dake hannun Zeenah ta ijiye gefenta tana kallon Hadiza tace “ai kinga halin nata bantaba ganin yarinyar mara tarbiya irinki ba Hadiza saisa mijinki ya auro miki yar aikin ki!” zabura Hadiza tayi tamike danji tayi kaman Zeenah ta watsamata garwashin wuta, itama Zeenah ta zabura da sauri Baraka ta tashi tsaye tace “me haka kukeyi, wai ku yarane? Kuna abu kaman masu fama da tashin balaga”? Zeenah tace “Baraka dalla tashi agabana kinada 4kids I don’t wanna injure you for them akan me this stupid girl zatazo tana shararamin zagi ubanme namata, sabida she’s a fool ta dauka because nace ni feminist ce dole sai na dinga zagin mijina kaman yanda takeyi is that what makes me a feminist? Or ta dauka sai na iya ihu da shakemai wuya ina hauka danadenade shine feminist? Muna haduwa and talk about feminism but ban taba cemiki ni ina zagin mijina kuma bana ganin darajan shi kaman yanda kikema Nura ba ko nataba fadin haka Baraka”? Dasauri Baraka tace “a’a” Hadiza tace “amman kina fadamana baki daukan shit din namiji kema kina bashi hot hot, zaman fire for fire kikeyi” dasauri Zeenah tace “Hadiza dakata listen fa kalle ni da kyau ni Zeenatu ce ba Nura ba, stop talking kaman nine nafara saki zama feminist bayan kin rigani zuwa abujan nan ma, dakika dawo garin nan lokacin ina kano ina battling da tsohon mijina kan saki, nadawo Abuja nasameki ayanda kike we just flow together cus we were friends back then and bamu yarda maza su takamu ba so what are you saying?” Hadiza tace “eh amman ke kika zugani nasa Nura a kotu, ke kika sakani daukan that action against him kika kara harda molesting dina yake bayan bantaba gayamiki ba, you are so evil, black witch” Zeenah dake tafarfasa ganin yanda Hadiza ke wanke ta da zagi daban daban tace “you are very stupid for calling me evil and black witch kinji, Hadiza did I hold you at gun point nace saikin sa Nura a kotu eh?” Zeenah tai ihu ahaukace tace “nadauki bindiga na daura akanki nace dole kisa Nura a kotu keda ko maganan Uwarki bakiji wayeni dazakiji magana ta? Kuma molesting bake kika gayamana daya auro Ummi haka yake daddanneki yaciki bakiso ba”cikin tsananin fushi Hadiza na ture Baraka tace “uwata kika zaga?” Cikin fushi Zeenah tace “ke baki zagin uwar wasu”? Bangaje Baraka Hadiza tayi ta taho ahaukace zata damke Zeenah Baraka tasake riketa tana nishi tace “Dan Allah wai me haka ku yarane” Zeenah tace “ko amafarki kada ki kara cewa nina zugaki cus ko uwarki bata isa tazugaki ba balle Zeenatu, bansa gun akanki ba nace kai Nura kotu, dakika bani waya nayi snapping fuskanki as evidence shima nine nasaki? Stupid big for nothing girl kawai, an danna miki saki due to your stupidity yanzu u are looking for who to blame wai I deceive you how? My dear carry your cross kowama yadauki nashi, wawiya kawai da babu abinda tasani banda neman kudi da iya zagin mutane sai kace bamagujiya, ke wlh abin kunyace ga jinsin mu mata cus u are not woman enough tunda kina gidanki har mijinki zai iya yaga yar aikin ki yar kauye yaji yana sonta kin kasa cin bura’uban yar aikin, nine yanzu zakizo with your running mouth kinama hayagaga, if u even try that nonsense with me I will beat nonsense commit for your body niba Nura bane” Baraka tace “wai me haka Zeenah Hadiza kikema magana haka why are you so bitter kawarmu ce fa” Hadiza da Baraka tarike tace “yar bakin ciki dai ba kawar mu bace, bakin ciki take dani wulakantacciyan, gani tayi dudda tana matan minister nafito komi, gida, interiors, kudi, yara and everything” maganan tama Zeenah zafi ainun tace “eh naji but dai tell me cikin abubuwan dakika lissafo wanne yarage yanzu? Yaranki sunfison yar aiki sama dake uwarsu! Same with mijinki ya zabi yar aiki sama dake! Hakama yan uwan mijinki, Shammmmmmeeeee on you Hadiza!” wani kalan zabura da Hadiza tayi tai wulli da Baraka tawani daka tsalle ta zubama Zeenah nushi abaki sai jini, suka shiga dambe ana chakume chakume, ashedai Hadizan mu nada karfi, yau ta haukace tatas ihu kawai take sosai tana kaima Zeenah duka kota ina tace “Shegiyar shedaniya, azzalamu zalumamma, annamimiya miya miya, yar bakin cikin ciniki, ahaka zaki kare, wlh Hadiza namiki fincinkau, celebrate my down fall today your own is coming tommorow” zokaga fadan manyan mata dayake unexpected adiza ta farmata yasa tasami upper hand sai zubama Zeenah nushi dake da kyar Zeenah ta samu ta gannama Hadiza cizo kan breziya saida taji takamo kan nonon Hadiza ta saketa da gudu ta koma baya takama boobs nata tace “vampire witch kawai, Nigerian zombie” zasu koma kan juna Baraka ta shiga tsakiya tace “wlh zan bar shagon nan bazaku kashe juna agabana ba police su kamani” azuciye Zeenah ta tashi ta shiga maida dankwali ta tana share bakinta dake jini da bayan hannu sai haki take tace “kuma Alhamdulillah naji dadi da Nura ya sakeki yakuma miki shamaki dashi dan mace kalanki don’t deserve miji irin Nura, iyayenki ba kowan kowana ya daukoki ya rufamiki asiri ya aureki kinamai iskanci kin dauka bamusan shine yasiyama Babanki mota ba, ya gyara muku gida, sannan ya nemawa mijin yayanki Jamila contract yasami kudi daba hakaba ai a gidanku ke kadai kikadan auri miji me kudi su Rabi ai duk maneji suke agidan auren dan haka yanzu zakisan me rayuwa dan ubanki, business din nan dakike takama dashi saki dinga ciyarda kanki agidanku dan yanzu me ciyarda ku ya sakeki kuma Allah ya kara naji dadi yanda ya sakeki wawiya kawai and welcome to zawarci” tashi Hadiza tayi zatai kanta Baraka ta tareta tace “Zeenah tafi” Zeenah tace “kobaki fadi ba shagon ma ubangiji Allah yasa alhakin Nura ya sauka akai ya lalace, kullum kina mana tunkaho yau acahnxa wannan motan gobe achan a wanchan, Nuri kaza kaza kaza kaman ke kadai ce me miji aduniya you will loose everything banziya kawai karya” cikin wani kalan fushi Hadiza tace “Baraka wlh zan kashe matar nan in batabar min shagoba” da sauri Baraka taja hannun Zeenah itama ta sunkuci jakanta ta fitarda ita daga shagon.
Oya registration for shiga matan aure class dina dazai fara November yafara, payment is 2k.
Chat me up idan kinaso wa.me/+2347012181461🥰

Hadiza zubewa tayi akasa tasa hannunta aka ta runtse idanunta wacce all her life tadauka as her best friend turns out to be her best enemy, wani irin kuka take mai tsumarai wayanta ke ringing cikin wani kalan muryan kuka tace “Nuri” dasauri ta dauki wayan ganin Babanta ke kira saida gabanta yayi mummunan faduwa, share fuskanta tayi da sauri ta dauka, strictly yace “kada dare tamiki baki shigo gidana ba akano Khadija!” Dip ya katse wayan.
Oya registration for shiga matan aure class dina dazai fara November yafara, payment is 2k.
Chat me up idan kinaso wa.me/+2347012181461🥰

Wayyyo Hadiza betrayal is painful guys💔💔

Kuna ganin Hadiza ita tajama kanta all this calamity ko ba ita bane??💔

Menene matsalan Hadiza guda daya dakuka lura tanadashi??? Yimata fada akai??

Lemme go first; Hadiza I think kinada yawan zagi, and zagi ba shine solution ba😎

Oya yau mutaru mu mata fada cus ciwon diya mace na y’a mace ne, kufito muma Hadiza fada today 🤗

Leave a Reply

Back to top button