Gidan Haya Complete Hausa Novel

Gidan Haya 7

Sponsored Links

🛖GIDAN HAYA{A RETEND HOUSE}

 

 

DAGA ALQALAMIN MARUBUCIYAR

WANI UBA

ACIYAU ACIGOBE

MABUQACI

DARE ƊAYA

 

 

 

 

Littafina na kuɗi ne akan Nera ɗari biyu ₦200 kacal ki biya ki karanta cikin salama, yar uwa idan kinaso kiji badaƙalar da ke cikin wannan littafi na GIDAN HAYA ki tuntuɓi wannan number 08143344386

Ko kiyi joining wannan group link domin karanta free pages👇🏻👇🏻👇🏻

 

 

https://chat.whatsapp.com/HC0P1YTc8CZJNyHiIEemJd

 

 

 

 

FREE PAGES 7️⃣

 

 

 

 

Tana gyara darningtable Hamidah ta fito tana hamma daga gani yunwa ce ta tashe ta yanda ta sauko kallo ɗaya zaka yi mata ka gane yunwa ta keji kuma kamar zataci babu Mummy dake busy shirya abinci akan darning taji Hamidah tace mummy!!!!!!! Daga mummy har Akil duka jiuyowa sukayi suna kallonta a hankali tace mummy yunwa nakeji murmushi mummy tayi saɓanin Akil daya haɗe fuskar zaiyi magana mummy tace yar albarka zo gashi kici tun ɗazu naso ki tashi kici abincin rana amma kiƙaki tashi zo kiji my baby girl murmushi tayi ta ƙaraso saida tayi huggin dinta kafin ta zauna mummy tayi serving dinta shinkafa da miya sai pepesoup a gefe ta fara ci mummy sai kallonta take tana murmushi cikin fushi Akil ya tashi ya bar falon a hankali mummy ta tashi ta bar darning din part din Akil ta nufa koda taje ya kifah ɗakin so dark a hankali tace Akil shiru yayi kamar baiji taba ƙara kisan sunansa tayi a hankali yace na’am ya tashi yaja remote ya kunna wutar ɗakin, a hankali mummy ta ƙarasa kan gadon Akil na’am mummy tashi muje kaima kaci abinci girgiza mata kai yayi Hmm nasan bakaci kome ba tashi muje kaji dan albarka murmushi yayi okay mummy zanzo tashi tayi tana cewa am waiting sai ka fito toilet ya shiga yayo wanka ya shirya cikin ƙananun kaya riga da wando sosai suka yi masa kyau Yafito sak buzu yanayin kalar fatarsa kuma sak yan Ethoipian ƙamshin sa ya fara isowa kafin shi a falon Hamidah sai raba ido take dan ko ɗazu data sauko bata gansa ba ƙamshin sa kawai taji yanzu kuma sai taji tana bala’in son ta gansa ya nufi darningtable din ta kasa daurewa tana dagowa suka haɗa ido ya dalla mata harara da sauri ta jiuyar da kanta tana turo baki har cikin ransa yaso yana kusa da ita take turo masa baki da babu abunda zai hanasa basa bakin bata iya komi bah sai baccin asara mtsww ya saki tsaki daidai yana ƙarasowa girgiza kai mummy tayi tana cewa Akil wai lafiyar ka 2 days kana abu kamar mai aljanu shiru yayi baice komi bah mummy kuma tasan ba magana zaiyi mata bah ta zuba masa abinci ta tura masa gabansa cire spoon din da tasa masa yayi ya ajiye gefe ya nufi wash hand base dake darning din ya wanko hannunsa ya dawo ya naɗe hannun rigar sa ya fara ci Murmushi mummy tayi Akil yana bala’in son cin abinci da hannu tun yana ƙaramin sa, har yanzu kuwa baya jin kunyar ko ina yaje aka basa abinci ya ajiye spoon ya wanko hannunsa ya fara ci abincinsa, saida yayi nisa da cin abincin sa kafin yace mummy wlh ke tadaban ce mummy haryanzu banci abincin da yayi daɗin naki ba mummy Nifah gani nake kece macen da tafi kowa iya girki a duniya Hamidah ta ƙalƙace da dariya Sam Akil bai damu bah saima ci gaba da yayi da surutun sa Mummy kisani a addu’arki nima soon zanyi aure finally na samu macen da ta dace dani kuma nake mafarkin samu a rayuwata mummy idan kika ganta kema nasan zaki sota, ƙwarewa Hamidah tayi da sauri mummy ta tashi ta zuba mata ruwa a cup tana cewa sannu gaba ɗaya idanunta suka fito waje sukayi jajajir da sauri ta tashi tabar darning din Akil kuwa shiru yayi yaci gaba da cin abincin sa mummy ta miƙe tana cewa ina zuwa tabi bayan Hamidah!! Hamidah kuwa tana shiga ɗaki toilet ta faɗa sbd yanda taji wani abu na taso mata so kawai take tayi kuka ko zata dena jin abunda keyi mata yawo a zuciya kunna Tap tayi ta fashe da kuka mummy na shigowa taji ƙarar ruwa a toilet sai kawai ta jiuya ta fita tana komawa falo nan ma har Akil ya gama ya tashi, gyra gurin tayi ta koma falo ta zauna shiru ita kadai tana tunanin maganar da Akil ya gaya mata just Now Alhamdulillah tayi ta maimaitawa a cikin ranta ga murmushi kwance a fuskarta daya kasa ɓoyuwa Akil ne da kansa yake cewa aure zaiyi kai amma naji daɗi sosai ya kamata Abba yaji wannan lbr mai daɗi wayar ta ta dauko zata kira yara suka turo ƙofar falon da gudu suna cewa granny su hudu duka maza sai mace ɗaya wacce itace ma ƙarama a cikinsu tayi mata 2 baby jalar gashin sai rawa take gaba ɗaya kan mummy sukayi duka su biyar saida kowa ya samu inda ya hau akan jikin mummy itama tana murmushi sosai tace welcome home my kids ya school gaba ɗaya suka haɗa baki gurin cewa Alhamdulillah!!!!!! Murmushi ta sakar musu tana cewa yanzu muje ayi wanka a canza kaya sai kuzo muci abinci, okay granny duka suka amsa saɓanin Afaff dake riƙe da hijab dinta idanunta cike da kwalla ƙiris take jira tayi kuka waroo idanu mummy tayi tana cewa Innalillahi!!!! taƙwara lfy aekuwa dama jiran take a tambayi ba’asi ta fashe da kuka tana cewa basu bane Big uncle yana tsayawa da mota duka suka fito suka bari a baya murmushi mummy tayi tana cewa gaskiya Haidar baku kyauta ba Meyasa kuka barta a baya duka suka haɗa baki gurin cewa Wlh mummy itace sai ta ringa tsayawa yi mana shakara shiyasa yau muka haɗa baki muka gudo muka barta a mota duka sukayi mata gwalo 😛 ta fashe da wani kukan kamar zata fasa falon Su kuma duka suka kwasa kayansu suka bar part din uku daga cikinsu suka shiga part ɗaya sai kuma Daya daga cikinsu ya shiga wani part daban yana shiga ya fara ƙwalawa mamansa kira Mami Mami haryakai ɗakin ta yana kiran Mami yana shiga tace Haidar wai Meyasa bakajin magana ne bana gaya maka ba ka dena yimin kiran mafarauta ko ban gaya maka bah shiru yayi ta ƙara da cewa lafiya Kake kirana?? Mami Afaff nacan tana kuka part din granny girgiza kai tayi tana cewa Allah ubangiji ya shiryamin Afaff tashi kaje kayi wanka sai kazo kaci abinci washe baki yayi yana cewa Laaaaa Mami ba kisan granny ta haɗa muna abinci bah yauma gurin ta Zamuyi dinner shiru Hafsa tayi a ranta tana mamakin mummy yanda Sam bata gajiya da girkawa yarannan abinci so tari suna cewa basai tayi abinci ba idan sukayi zasu kai mata amma sai tace A’a ta hutar dasu murmushi tayi tana cewa hala ma sbd Akil takeyin girkin sbd yaƙi yayi aure tashi, haka suma sauran yaran suna shiga suka fara kiran Umma Umma we are back gaba ɗaya suka shige dakinsu batare da sunje sun ga maman tasu ba bare su gaishe da ita itama Umman tasu daga ɗaki tace okay go an fresh off dama tasan banan zasuci abinci bah shiyasa yau bata mayi girki bah tunda haifinsu baya nan……… ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Leave a Reply

Back to top button