Gidan Haya Complete Hausa Novel

Gidan Haya 9-10

Sponsored Links

🛖GIDAN HAYA{A RETEND HOUSE }🔞

 

 

 

DAGA ALQALAMIN MARUBUCIYAR

WANI UBA

ACIYAU ACIGOBE

MABUQACI

DARE ƊAYA

 

 

 

 

Littafina na kuɗi ne akan Nera ɗari biyu ₦200 kacal ki biya ki karanta cikin salama, yar uwa idan kinaso kiji badaƙalar da ke cikin wannan littafi na GIDAN HAYA ki tuntuɓi wannan number 08143344386

Ko kiyi joining wannan group link domin karanta free pages👇🏻👇🏻👇🏻

 

 

https://chat.whatsapp.com/HC0P1YTc8CZJNyHiIEemJd

 

 

 

 

FREE PAGES 9️⃣&🔟

 

 

 

 

 

Koda suka tashi gaba ɗaya kafafuwanta sun kumbura sai cije lips dinta take kamar mai ciki wata tara tashi sukayi hostel suka nufah suna shiga Bushrah ta samu guri ta zauna muryarta na rawa take Ummi kinada ruwan zafi Girgiza mata kai tayi tana cewa Aa bara na ɗora miki a gas kunna gas tayi ta ɗora mata suka danyi ɗumi ta sauke ta jiuye a bucket har toilet ta kai mata Bushrah ta tashi ta shiga ta canza pad sosai bayan ta ke ciwo kamar ya tsage sai sannu ummi ke jera mata, ko 15mint bata yiba tace Ummi zanje gida a hankali tace zaki iya zuwa kuwa ɗaga mata kai tayi Alamar Ehh sbd ko magana batason yi, tashi tayi ta rakata har bakin gate ta jiuya zata koma sukayi kiciɓis da Akil murmushi ya sakar mata ita kuma ta gaishesa tana russunawa amsawa yayi yana cewa meke damun ƙawar ki? E’ena ta fara masa dama dama bayan ta ne ke ciwo sai kafafunta Hmmm amma Meyasa ba taje school clinick ba A hankali tace wlh nace mata muje amma tace A’a gida takeson zuwa okay Allah ya bata lafiya ya faɗa damuwa kwance a fuskarsa ji yake kamar ciwon ya dawo jikinsa fita yayi ita kuma ta jiuya ta koma hostel yana fita yaga bai ganta bah murmushi yayi yana cewa gaskiya aekin John na kyau masallaci ya wuce yayi sallar la’asar, Yana gama sallah direct GIDAN HAYA ya nufah kamar kullun ya tsaya yana ƙarewa unguwar kallo da yanda mutane ke shiga da fice cikin gidan babu control kowa shiga yake wasu da mini skirt wasu da Hijab har ƙasa wasu kuma da mayafi hardama marassa mayafi mata da maza shiru yayi yana tambayar kansa toh me takeyi wannan gidan? Nan ne gidansu? Idan ba gidansu neba me take zuwa yi cikin gidan Auzubillahi minal shaidan rajim yashiga maimaitawa cikin zuciyarsa saida ya natsu sosai kafin a hankali ya fito daga cikin motarsa ya nufi gurin Onyendu kamar kullum ya duƙa har ƙasa ya gaishesa amsawa yayi fuskantarsa dauke da murmushi yana kiran sunansa da gurɓatacciyar hausar sa da bata fita sosai Akil yakake ya aeki, A hankali ya ce alhamdulillahi kowa yayi shiru shima Akil yayi shiru amma sai gate din Gidan hayar yake kallo ji yake kamar ya shiga yaga me mutane keyi a ciki da tun fitowar rana har faɗuwar rana mutane basa dena shiga gidan bincike ma da yasa aka yi masa cewa akayi ba’a rufe gidan a buɗe yake kwana sbd masu yowar dare a waje gyaran murya Onyendu yayi yana cewa Akil lafiya ko kana neman wani ne naga kana kallon gidan sai nasa a kira maka shi girgiza kai yayi yana kallon mutane biyu da suke gefen Onyendu Ehh!! Ehh!! Ina tambaya ne idan ba damuwa kuma Inaso su bamu guri ya nuna faɗawan Onyendu da Igbo yayi musu magana gaba ɗaya suka watse suka koma gefe, A hankali yace dama akwai wata yarinya kullun daga nan gidan take fita kuma kullun anan gidan ake sauke ta toh idan ba damuwa Inaso nasan wacece kuma waye mahaifinta Hmm why? Murmushi Akil yayi kafin yace Inaso nasani Onyendu nayi bincike sosai ance mun kaine mai wannan gidan Hayar amma duk wanda na tambaya game da yarinyar wasu suna cemun basu santa ba wasu ma suna cemun babu wata yarinya a gidan wasu kuma suna littaso min yaran da ke gidan amma babu ta a ciki Hmm murmushi Onyendu yayi cike da dattako yace Yaro toh me yasa kakeso ka san wacece? Girgiza kai Akil yayi Sam baso ya gayawa Onyendu cewa son yarinyar yake amma kuma yaga alamun yanada taurin kai kuma ba gaya masa zanyi bah idan har bai gaya masa Meyasa yakeson jin wani abu game da yarinyar bah bubbuga sandar hannunsa Onyendu yayi yana cewa kayi shiru are you okay, firgigit Akil ya dawo daga duniyar tunanin daya faɗa yana cewa am in Love with her that’s why, hhhhhhhhhh Onyendu ya ƙyalƙyace da wata dariya gaba ɗaya saida faɗawan sa suka jiuyo suna mamakin dariyar miye Onyendu yake yi haka yajima baiyi kalar wannan dariyar bah zasuma iya cewa tun bayan da yasa yaransa baiƙara dariya bah saidai yayi murmushi, shiru Akil yayi yana kallonsa saida yayi dariya sosai ya tashi yayi rawa yana jijjiuyawa yana yarfa Cow tail dinda ke hannunsa alamun yana cikin tsantsar farin ciki, I know!!! I know!!! You are in Love with that girl sinces d day i see you!!! But  i want to hear it out from you !!! Sai rawa Onyendu yake yana jiuyi kamar ba tsoho bah kunsan dai yanda Igbo ke nuna jin dadi idan abun farin ciki ya same su, komawa Onyendu yayi ya zauna yana cewa Alhamdulillahi am so happy to hear it and am so happy that i reached thes day!!!!, Akil kuwa Onyendu zame masa yayi tamkar Tv sai kallonsa, murmushi Onyendu yayi yana cewa am the owner of this house yana nuna gidan hayar da cow tail dinda ke hannunsa murmushi Akil yayi na ƙarfin hali domin haryanzu baiji abunda yakeso yaji bah a hankali yace her Name is Bushrah Tajuddeen Ahmad also known as Ada sunan mahaifiyar ta Ayshat Ana kiranta da Nne nasan mahaifinta kuma tajuddeen Ahmad mahaifiyar ta Igbo ce mahaifinta kuma bahaushene haifaffen dan Kano ne da kasuwanci ya kawo sa Lagos Kaga wannan gidan Akil ya daga kansa ya kalli gidan hayar yace Ehh toh anan aka haifi Bushrah yanzu anan tayi wayau basa zuwa ko ina basusan kowa bah bayan mahaifiyarsu da mahaifinsu bata da yawan rigima and batason yawan magana tanada Nwanne guda biyu Bayyanat da Dinayah amma kasan me girgiza kai Akil a hankali Onyendu yace itace kawai take zuwa school a cikinsu amma bansan me yasa bah kuma bana shiga sabgarda babu ruwa na shiru Akil yayi yana tunani toh me yasa basa zuwa makaranta kamar daga sama yaji Onyendu yace karka tambaye ni nima ban sani bah, kuma idan Tajuddeen yabar gidan nan baya dawowa sai 10:00PM Hmmm Akil ya sauke ajiyar zuciya yana cewa toh yakuke da maifinta are you her granpa girgiza kai Onyendu yayi yana cewa bansan suba kawai Nne ta daukeni tamkar mahaifinta sbd na basu gurin zama a gida na gaba ɗaya Onyendu Yasa Akil a duhu yarasa gane me yake faɗa a hankali Akil yace Inaso zanyi magana da Baban Bushrah kuma idan Kanada number dinsa ka bani dan Allah murmushi Onyendu yayi bai kawo komi bah ya basa number Akil ya ciro kuɗi masu yawa ya ajiyewa Onyendu yana yi masa godiya yabar gun har an fara kiraye kirayen sallar magrif, bai ƙarasa gida bah sai bayan isha’i gaba ɗaya hankali mummy ya tashi sbd baya kaiwa isha’i bai dawo gida bah sallar magrif ma yana gida ake kiran salla sai yayi alwala ya fita tana zaune a falo tayi tagumi ya shigo ƙuri tayi da ido tana kallonsa batare data ammsa sallamarsa bah da sauri ya ƙaraso yana cewa am sorry mummy nabar wayana a office ne saida na fito daga Theater room naga miss calls dinki shiru mummy tayi tana ƙare masa kallo sosa ƙeyarsa yayi sbd daga ganin yanda Mummy ke kallonsa yasan ta gano ƙarya, a hankali ta kiran sunansa Akil daga ina kake dagowa yayi idanunsa suka sauka cikin na mummy da sauri ya sauke nasa ƙasa yana cewa Mummy zan gaya miki yanxu inajin yunwa mummy ta ƙara daure fuska zatayi magana Abba ya shigo da sauri Akil ya dashi daga gaban mummy inda ya duƙa kamar wani ƙaramin yaro da yayi laifi yana neman ayi masa afuwa, yana cewa Abba sannu da zuwa dama flight din dare zaka biyu da ido Abba ya bisa ba tare da yace komi sbd ya kira yawan sa sau uku bai daukaba saidai Ya kira Ishaq dake da mata yaje ya dauko sa miƙewa mummy tayi tana cewa sannu da Zuwa Alhaji yawwa sannu mummyn yara murmushi tayi ta karbi Jakarda ke hannunsa suna nufi upchairs Akil ya sauke ajiyar zuciya yana cewa na tsira daƙyar……. ✍🏻✍🏻

 

 

 

 

*WANNAN SHINE LAST FREE PAGE DINMU INSHA ALLAH*

 

*ZAKI IYA TUNTUƁATA TA WANNAN NUMBER 08143344386 IDAN KINASO KI SHIGA PAID GROUP NA* GIDAN HAYA🛖

Leave a Reply

Back to top button