Gidan Haya Complete Hausa Novel

Gidan Haya 4

Sponsored Links

 

🛖GIDAN HAYA {A RETEND HOUSE}

 

 

DAGA ALQALAMIN MARUBUCIYAR

WANI UBA

ACIYAU ACIGOBE

MABUQACI

DARE ƊAYA

 

 

FREE PAGES ya kusa ƙarewa ki hanzarta ki mallaki naki akan nera 200 kacal zaki iya tuntubar wannan number domin ƙarin bayani 08143344386

 

 

 

FREE PAGES 4️⃣

 

 

 

Hmmm mmn Humaira idan wanda zan aura yana sona, babu ruwan sa da abunda iyayena zasu kaimin saidai idan dama can ba sona yake bah toh shikenan yanzu ba wannan bah ya school dinkuh kwana biyu bakya zuwa islamiyya kuma naga bakya zuwa makarantar boko din Lfy? Lafiya ƙalau boko sun bamu break be kafin mu fara zuwa hospital masha Allah toh Allah ya taimaka amma kici gaba da zuwa islamiyya gaskiya ilimi shine mace konace ilimi shine mutun babu inda ilimi baya kai mutun zakiga maluman mu yanzu riba biyu suke ci sune ake bawa ministoci kuma sune ake kira suyi karatu su samu lada sannan a dauki maƙudan kuɗi a basu kinga sun samu duniya kuma suna neman lahirar su, murmushi Bushrah tayi tana cewa Insha Allah mmn Humaira zan koma yauma Insha Allah zanje yawwa ko kefa bara na tashi na dora muna abincin rana toh sai anji kinji nagode Murmushi tayi ta fita, babu kowa a tsakar gidan yanzu sbd rana tayi babu inuwa sosai da sauri ta shige dakinsu Nne na zaune itada su Dayyanat sunacin abinci Nne ta watsa mata hara tana cewa daga gidan ubanwa kike shiru tayi kamar zatayi kuka tace Nne ina cikin gidan fah babu inda naje, banza tayi mata ita kuma ta samu gu ta zauna can daga gefe Nne tace zanje kasuwa yanzu nan idan na gama nasan bazan dawo da wuri bah ki ɗaura girkin dare kinji ko ehh Nne naji amma Inaso naje islamiyya wani banzan kallo ta watsa mata tana cewa yauma bazaki je bah aenazaci an yayeki daga islamiyyar ne naga kwana biyu bakya zuwa Shiru Bushrah tayi sbd tasan batada gaskiya ƙwafa Nne tayi jin tayi shiru bata amsa taba, hayaniya sukaji daga watse ihuuuu ƙwato da rana tsaka wooooo kowa ya fito Nne jiki na rawa ta miƙe tsaye tana cewa kar wanda ya fito kun ji gaba ɗaya suka amsa mata da toh!!! ita kuma ta fita Mustafa ne tsaye da wandonsa a hannu sai gumi yake yana girgiza wa Maimuna kai alamun ta dena karta tara masa mutane Uwar daba ta fito tana cewa dama inaji a jikina idan na shiga wanka kamar akwai mai lefewa yana leƙena ashe kaine ƙaton banza ƙwarto ga gulma cike da duwawu nanfah mata suka fara ihu sai ga mai gidan ya shigo *onye_ndu* ya shigo haka suke kiransa sbd shine leader kuma kowa najin maganar sa kowa yayi shiru Maimuna dake riƙe da rigar Mustafa daya cire ya ajiye gefe ta saki rigar kowa ya kama kansa gyaran murya yayi kafin ya fara tambayar ba’asi nan aka shiga shaida masa yace za’a yiwa Mustafa bulala 20 shine hukuncin sa kuma ancisa tarar dubu 30k domin a gyaran gidan a kuma inganta toilets din da ke gidan shiru kowa yayi Onye_ndu ya ƙara da cewa ko akwai mai magana kowa ya girgiza kai shikuma ya jiuya ya fita mutane biyu na biye dashi kamar dogarai/fadawa ajiyar zuciya Nne ta sauke cikin gurɓatacciyar hausar ta da bata fita sosai tace Allah ya kyauta, Ehh lalle abun da yawa mutuwa taje kazuwa hardasu kaza a cikin giwaye kowa ya kasa da ita bare ta kwasa girgiza kai Nne tayi ta koma ɗaki sbd tasan da ita suke ita kuma batada lokacin su Mmn Humaira kuwa dama daga bakin ƙofar dakin ta take tsaye ta saki labule ta koma dama itace kadai sai Nne basa shiga harkar mutanen gidan idanma anayi aka gansu shiru ake yi wai muna fukaine su tunda yarene ba Hausawa bah😂, Mustafa yana ganin su Uwar daba sun gama wata sabgar ya zame jiki ya gudu kada su dawo kansa direct gurin onye_ndu ya wuce yana zuwa har jikinsa ke rawa ya faɗi a gabansa yana ina yeman afuwa a yimin afuwa a gafar ceni ayimin sassauci hukuncin da aka yanke min yayimin yawa da hannu yayi masa alamar ya tashi har jiki ke rawa ya miƙe yana karkaɗe jikinsa guri Onye_ndu ya nuna masa alamar ya zauna aekuwa ya samu guri ya zauna gyaran murya onye_ndu yayi kafin yace Mustafa wannan shine na biyu ana kamata kana lafewa a jikin toilet kana leƙen mutane ƙasan Nne ta kawo ƙararka amma na yafema sbd yan gidan sunce ƙarya take ko? Toh yanzu sune da kansu suka kama ka ya zakace shiru Mustafa yayi saidai yasa hannunsa cikin aljihu ya zaro dubu 35k jiki na rawa ya miƙawa onye_ndu yana cewa nidai yanzu ina neman afuwa kar a yimin bulala amma ga wannan Insha Allahu hakan bazai ƙara faruwa bah karɓa

Bana Allah ya isa akan Littafi amma ki siya idan dai bakyason kici da hakkina domin gumi nane kike ci ba tare dakin biya ba ₦200 kacal Onye_ndu yayi yana cewa amma sai an yima koda bulala 5 ne sbd suga shaidar cewa an dake ka, karsu dauke ni a matsayin shugaban marar adalci Mustafa ji yayi kamar yayi ihu amma babu yanda ya iya haka ya kwanta aka ringa auna masa bulala a baya har saida aka yi masa guda biyar aka kawo wasu ruwa a ƙwarya aka yayyafa masa aekuwa ya saki wani uban ihuuuu sbd an fasa masa baya…… ✍🏻

Leave a Reply

Back to top button