Gidan Haya 3
🛖GIDAN HAYA{A RETEND HOUSE}
DAGA ALQALAMIN MARUBUCIYAR
WANI UBA
ACIYAU ACIGOBE
MABUQACI
DARE ƊAYA
PAGE 3️⃣
Bacci mai nauyi yayi awon gaba dasu Asuba ta gari, kiran sallar fari Bushrah ta farka duda ba wani bacci mai nauyi tayi ba idanunta sun kumbura sunyi luhu luhu sbd kuka yar ƙaramar wayar da ke hannunta ta kunna gaba ɗaya ɗakin yayi haske kunsan rakani toilet akwai haske da sauri ta danne hasken wayar gaban ta na wani mugun bugawa da ƙarfi sbd abunda idanuwanta suka gane mata hannu tasa ta ringa lalabe har ta kai jikin ƙofa ta cire key a hankali ta buɗe ƙofar ta fita, tana zaune ajiyar zuciya toilet ta nufah bakinta dauke da addu’a saida tayi fitsari ta fito ta debo ruwa a rijiya ta koma tayi wanka ta dauro alwala lokacin mutane sun dan fara tashi Mustafa na tsaye yana jiran wanda ke cikin toilet ya fito shikuma ya shiga yana ganin Bushrah ya washe baki yana cewa matar da nasan kece a ciki danazo na taya ki wani banzan kallo ta watsa masa tana cewa Allah ya kiyaye ta zubar da yawu ta wuce, da ido ya bita yana cewa dama ae taimakawa iyayen ki zanyi naga kin gama gandarewa a gabansu ba mashin shini banza tayi dashi ta shige dakinsu lokacin Dianyi da Nne Sun tashi harsun gyara kwanciyar su shima ya haɗa kayan shiga wanka gaishe su tayi Dianyi ya amsa cikin farin cikin ita kuma tayi gefen da kayansu yake ta nemi kaya, tana ƙokarin sawa Dianyi ya fita Nne na biye dashi kamar raƙumi da akala girgiza kai Bushrah tayi ta kammala shirin ta tsaff tayi sallah ta zauna tana lazimi karfe 7:00 daidai ta tashi ta fita zuwa dakin Maman Humaira a can take wuni cin abinci kawai sai bacci ke dawo da ita gurin iyayen ta, Zaune ta tadda mmn Humaira kan carpet din sallah tana duba littafai islamiyya a hankali tace ina wuni mmn Humaira lafiya ƙalau Bushrah an tashi lfy, tace lfy qlw Bushrah lfy idokin ke ciwo ne girgiza kai tayi tace A’a to meke damunki Bushrah ki dena sawa kanki damuwa kinji kada ciwon zuciya ya kamamin my Ada murmushi tayi tace ina Humaira yanzun nan ta fita kinsan yau babu school taje ta siyo ƙosai yanzu na dama koko ki gansa ta dauko tana cewa bara na zuba miki kisha girgiza kai tayi tace na ƙoshi mmn Humaira Hmmm bansan me yasa ba Bushrah bakyason cin abinci na ko ni ƙazama ce Aa wlh bakomi kawai na ƙoshi ne to me kikace da zakice kin ƙoshi, murmushi tayi tace nidai dan Allah ki dauko littafin ki muyi karatu murmushi maman Humaira tayi tana janyo Jakarta nan suka shiga duba littafai islamiyya, Dianyi da Nne tare suka shiga wanka da suka fito Dianyi cikin ɗaki yayi sallah yana gamawa ya fito da kuɗi dubu goma ya bawa Nne suyi cefane, yace zai tafi sai 10:00 zai dawo a hankali yace Bayyanat Dinayah je ku kiramin Bushrah a hankali Bayyanat ta miƙe ta tafi bata wani jima ba ta dawo tace tace tana zuwa shigowa tayi bakinta dauke da sallama murmushi Dianyi yayi yana amsa mata sallama kudi ya ciro dubu biyu ya bata yace gashi idan kina bukatar wani abu ki siya girgiza kai tayi tana cewa aa bana buƙatar komi Nna hararanta yayi yana cewa karɓa ansa tayi tana cewa nagode, Nne ta karɓi jakar Dianyi suka fita su Shema’u da Maimuna har sun shinfiɗa tabarma ƙarƙashin bishiya aka fara zunde ana nuna su da baki, Nne tayi kamar bata gansu ba ta raka Mijinta har bakin ƙofa tana yi masa addu’a Allah ya kiyaye ya dawo da shi lfy shikuma sai wasar baki yake, dawowa tayi cikin gida Shema’u ta fara magana, A haifi ɗa da samu yafi a mutu a bar masa gado maimuna tace Hmm kedai bari abun nayi ne an biya wa zawara hajji mutun yana da ganda memiyar budurwa a cikin ɗaki yace ihu da dare gaba ɗaya gurin akayi kwa da dariya daidai Bushrah ta fito daga dakinsu zata shiga dakin maman Humaira da sauri ta shige tana goge hawaye da bayan hannunta murmushi maman Humaira tayi tana cewa Bushrah ki dena sawa kanki damuwa kinji a hankali tace maman Humaira na gaji da zaman gidan nan miyasa mutane basusan destiny ba nima bada son raina nake zaune banyi aure bah miyasa basa iya gani su ƙyale fashewa tayi da kuka a hankali maman Humaira ta rungume ta tana shafa bayanta tana bata haƙuri harta samu tayi shiru suka ci gaba da firar su, a hankali tace yanzu idan Bahaushe yace yana sonki yaki sosa da sauri ta girgizawa maman Humaira kai tana cewa Aa Hausawa basason yare bare Igbo muda suke gani kamar ba musulmi bah girgiza kai maman Humaira tayi tana cewa aeba duka muka taru muka zama daya ba Hausawa akwai masu kirki wadannan da kike gani basason zaman lafiya ne shiyasa amma karki damu wata rana sai labari kinga mahaifiyar ki komi ta samu ke take tarawa sbd idan auren ki ya fito ta fita kunya sbd ta aure Bahaushe anaso taga yanda zatayi ranar auren ki, Nne da Dianyi sunada kudi amma sunƙi siyen gida sbd idan auren ki ya tashi su kashe miki kudi su fita kunya……. ✍🏻
littafina na kudi ne ban tsaurara ba ₦200 ne ki siya ki karanta hankali kwance ki tuntuɓi wannan number 08143344386 plz masu yimin magana domin siyen littafi dakunce Hey ko aslm ku fadi abunda kuke so bana buƙatar doguwar gaisuwa 🙏🏻🫱🏼🫲🏼