Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 14

Sponsored Links

CINIKIN RAI….14
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Maniyyata sun fara payment! Jiran me kike?
<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>
“`Love looks not with the eyes, but with the mind, and therefore is winged cupid painted blind.“`
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>>
“Jadda ya dai?” Nadrah Khamis Shatima ta tambaye ta, tana kallon yadda ta shiga damuwa. “Ba kome, kawai wasu abubuwan ne idan ka tuna bayan baka da yadda ka iya sai kaji zafi a ranka.” Gyad’a kai tayi tana faÉ—in. “Haka ne, amma kome yayi zafi maganin shi Allah.” ” Na yarda da haka, sai dai a wata rayuwar, Allah yana sane yake barmu da mugayen halaya. Domin ya ga yadda zamu yi, barin mu a haka shi ne babban tashin hankali.”
Ganin yadda Nadrah ta makale tana son jin me ya faru, yasa ta basar da abin ta mike tare da barin falon. Idan ka zauna da Yaran zaka fahimci kowa da halinshi. Nadrah Khamis Shatima tana da masifar son jin kome, shi yasa kullum kafin kaji labari a bakin wani a bakinta zaka fara ji. Yayinda Wahida Malik Menk Jordan, ta kasance me yawan fara’a da son mutane, da surutun tsiya kamar Radio. Wahiba Malik Menk Jordan kuma sai ta kasance miskila mara son magana, ga dan banza reni da gani-gani. Sannan idan Ubanka ba wani ba ne, bata kula ka. Gashi tana da ilimi sosai, amma magana bai dame ta ba, bayan wannan halin Nadrah yarinyar tana da kirki sosai, domin ba kowa yake iya jure zama da Wahiba Malik Menk Jordan ba, domin kusan kullum sai ta mata rashin mutunci. Amma tana like da ita, tana hakuri hakan ne domin mahaifinta ya rarrasheta da tayi hakuri ta zauna da halin Yaran. Duk da babban damuwarta, shi ne ta samu kusanci da Malik kamar yadda uban ya ce, akwai wani abu daya da suke kokarin ganin sun cusawa yaransu, shi ne dole yaran su bayyana jikinsu ga Malik ta haka sha’awa zata saka ya ga ya bukaci yaran daga Khamis Shatima da Lalla Salmah wannan shine buÆ™atarsu da kuma kudirinsu.
Shirin su na rikito da Malik ba karami ba ne, sannan idan har akwai abin da suke hari tow dukiyar Malik ne, shi yasa duk abin da suke har kwanan gobe babu nasara, amma zasu cigaba da fafutukar ganin sun sami hakarsu ta cimma ruwa.
★
Amjad
Sintiti yake daga Office dinsa, zuwa bakin Office É—in. Baki daya hankalinshi a tashe yake, kai yafi ma ganin hankalin shi zaune take da gindinta, wayar shi ce tayi kara ya É—auka tare da sakawa a kunnenshi.
“Chairman gata nan ta shigo kamfanin!” Hadiye yawu yayi, bai taÉ“a kawowa a ranshi zata dawo yau ba, sai gashi ta dawo É—in. Sai da ya sauya kaya sannan ta wuce office dinshi domin Mss Mary ta gaya mata yana son ganinta.
A hankali ta tura kofar, yana zauna a kujeranshi, zuba mata ido yayi. “Ke kuma haka ake rayuwa?” Dauke kai tayi tana kallon waje, “Nasan bai kyauta ba, amma a madadin haka sai ki tsaya ki ji me zance miki, ba wai kiyi gaban kanki ba. Gashi nan zaki hadu da Elbashir, duk abinda zai faru, ya faru amma ka da ki sake baku hadi da Malik ba, shine kawai zai yarda da bukatarmu”

Gyada kai tayi tana faÉ—in. “Tow idan ban hadu da Malik din ba fa?” Murmushi yayi ya ce mata. “In sha Allah, zaku hadu ina jin hakan a jikina!” Gyada kai tayi a karo na biyu, sannan ta ce mishi. “A ina zan samu damar haduwa da shi?” Office dinsu yana kan titin sir Victor James black. Menk property management companies, ga wannan laptop din naki ne, mun tsara kome sannan na tura musu abin da zaki bukata, sannan sun amince da bukatar tattaunawa da ke, and ban sani ba ko zaki iya tafiyar da wasu abubuwan. Don Allah ku kula.”
“Tow!” Ta fada tana me daukar laptop din, ta fita murmusawa yayi yana hango yadda yayi nasarar kome, ya barta a cikin ruwa tsundum. Juya kujeranshi yayi yana faÉ—in. “Ina tausaya miki, domin kuwa nama na sakawa Zaki yadda zai fada yaci yana me shiga tarkona!”
Kamar yadda ya fada mata haka kuwa, ta isa kamfanin sai dai kuma tunda ta isa bata samu damar haduwa da kowa ba, asalima, kamar ba asan da zuwanta kamfanin ba, har yamma babu wani gamsashhen bayanin da zai bata kwarin gwiwa.
Haka ta tafi bayan an tashi gida ta nufa, tana isa wanka tayi ta kwanta domin tana hutun sallah. Don haka bata nemi abinci ba, sai dare. Washi gari da zata fita suka hadu da Abbas, nan yake tambayarta sun je gidan Hibba kuwa? Girgiza kai tayi tana faÉ—in. “Kawu Nura zai zo daga Kamaru, idan yazo zasu tafi da abokin Abba in sha Allah da baban Chu-chu.”

“Shi kenan. Ni dai ku tafi ku karbo min aure da Hibba!” “In sha Allah, kayi hakuri na makara.” Ta fita da sauri, tana hada step, a kasa suka hadu da Hafsy! “Xnoo!” “Babu lokaci, idan na dawo zan har É—akinki!” Ta bude motar da sauri ta fada, tna sauke ajiyar zuciya. Da gudu ta sa kai zata fita Dundurosu ya tare mata hanya, sake glass tayi tana sako kanta. “kai mataccen nama, sai na bi ta kanka ne?” “A’a amma yau za a biya kudin wuta da na ruwa, kuma mun je har É—akinki jiya kina barci. ” Bude jakarta tayi ta ciro katin banki ta cilla mishi. “kuyi kome kafin na dawo!”

“Har da sharholiya?” “Sai na kashe ka, idan kayi min wasa da kudi ” ta fisgi motar a guje, ya ce. “Sai mun yi wallahi!” Dukan sitiyerin motar tayi tana faÉ—in. “punk!” Ta kara wuta da gudun gaske, tafiyar da zai dauketa minti goma sha biyar, yar wutar ciki a cikin minti goma kacal ta isa harabar kamfanin, a hankali ta sauko kafarta wanda yake sanye da Hill na Vince brown sai jakar takalmin, sanye take da gown light brown, kanta sanye da yar dankwali ta daura shi baya, sai sunglass da ta saka shima brown. She look gorgeous and beautiful. Rufe motar tayi tana me takawa a hankali cikin nutsuwa, hannunta daya riÆ™e da jakarta da wayarta. Daya hannun ta soke shi a cikin aljuhun wandonta. Yau fuskar ba laifi hoda da kwali kawai ta dan goga, sai lipsglow.

Yadda take tafiya zaka iya cewa, wata macijiya ce, tsabar yauki da Yanga. Har ta shiga cikin kamfanin. Ma’aikatan kamfanin sake baki suka yi, suna kallonta domin ta share musu hadda, tana shiga ta nufi wurin matar jiya, ta tambaye ta shin Elbashir ya iso kuwa? Matar ta ce mata bai zo ba, kuma bata da sanin zai zo ko ba zai so ba. Shiru tayi tana sakawa da kuncewa.

A hankali ta d’ago idanu ta ce mata.
“Ko zan iya samun number shi!” “Kiyi hakuri Ma, tsarin aikin mu bai lamunci bawa Kowa number wani ba, domin akwai matsala idan aka fahimci haka!” Murmushi Zeenobia tayi tana faÉ—in. “Babu wanda zai fahimci haka, idan kin bani” “amma Ma!”
“Shi kenan na fahimta!” Ta juya a hankali, jikinta a mace, Office dinsu ta tafi, tun da ta isa ta bata tsaya a ko ina ba, sai a wurin Mr Amjad. Tana shiga ta watsa mishi files din. “Kasan baka sama min appointment na zama da shi ba, ka bar ni sai yawo nake?” “Kinga ba wani abu bane, amma don zama da shi na nima, wallahi ki duba laptop din.”

Shiru tayi kafin ta mike, “ina zaki?” “Gida!” Ta fada kai tsaye, tana me barin Office.
Wasa wasa tun daga lokacin, Zeenobia bata kuma gajiya da son ganin Malik ba, har sai da ta cika kwana talatin da bakwai, a ranar na bakwai tana isowa, Elbashir Jamal Arab, yana isowa a hankali ta bude motar dama, tana gabansu ne, dake an tura mishi sako akanta da kome da kome.

Har da number motarta, sai da tayi parking, ta fito a hankali yau sanye take da riga da skirt ta atamfar Super exclusive, wata yar karamar gyale ta rab’a a kafad’arta. Bakinta kuwa yaji lipstick alley, bakin kamar ba ita ba, gyara zaman glass dinta tayi, fari da shi. Sai da ta kwashe kome nata a motar, sannan ta wuce zuwa kamfanin duk da tasan shi ne amma duk kar a rena mata ajawali yasa baki daya ta tattara kome ta watsa a gefe, kamar bata san shi ba. Lokacin da ta isa cikin kamfanin dama sun santa suna ganinta suka tarbeta da hannu bibbiyu.

“Yau kam kin zo a sa’a, domin Oga ma ya zo!” Murmushi tayi tana faÉ—in. “Ayya ba damuwa!” Ta zauna tana kallon agogon hannunta, har suka shigo kamar bata ganshi ba, tana ganin yadda mutane suka mike domin girmama shi, amma ita tana zaune kamar wata sarauniya. Shi kanshi Elbashir sai da ya kalleta da wutsiyar ido, yarinya ce jagab, amma girman kan na meye? Koda ya shiga office dinsa, a hankali ya fara ganawa da bakinsa, kafin aka zo kanta. Tashi tayi ta nufi office É—insa. Ko da ta shiga ciki kallon juna suka yi, kafin ta ja kujera ta zauna. “Ina jinki me ke tafe dake?” Shiru tayi tana kallon office É—in, kafin ta ce. “Malik Menk Jordan!” Kura mata ido yayi kafin ya ce mata, “Idan baki da abin yi zaki iya fita!”

Dariya tayi tana fad’in, “Ni wurin Malik Menk Jordan nazo!” “Baki da lafiya, tashi kije dama tunda na ganki na san za ayi haka fita na saka a fitar min da ke!” “Ai kuwa ba zan tab’a barin nan ba, sai na fara ganin Malik” “ke mahaukaciyar ina ce?” Murmusawa mishi tayi sannan ta ce mishi. “Mahaukaciyar garin nan”

Daukar wayar Office din yayi ya ce.
“Security kuzo ku fitar min da ita;” murmushi tayi, tana fad’in. “Ba zan fita ba, sai na samu ganin Malik Menk Jordan!” Kwankwasa kofar aka yi ya ce a shigo.

Wasu irin kartin maza, shiga suka yi sannan suka sara mishi. “Kuyi min waje da wannan yarinyar!” Mikewa tayi tana faÉ—in. “Zan baka nan da kwana uku, ka haÉ—a ni da Malik kafin na binciko waye shi! Daga lokacin da na fahimci waye shi, da zaman lafiya ko da bala’i sai ka haÉ—a ni da shi. Ka ajiye kalmata.” Ta juya ta fita ba tare da ta kuma cewa cikanka ba. Baki sake yake kallonta tabbas yana ganin tsagera amma ita wannan uwar tsagerancin ce.
Tun daga ta fita taa sauke ajiyar zuciya, bata tsaya ba asalin cikin gari ta nufa. Unguwar Kauraye, tasan ba zasu rasa wanda yasan Malik ba. Don haka ta nufi gidan Basiru Kaura.

Zama tayi tana kallon shi, ba zata manta Nasiru Kaura ba a rayuwarta. “Kaura! Waye Malik Menk Jordan!” Ware idanu yayi tare da rufe mata baki, “shiii!” Juyawa yayi ya riko hannunta suka shige cikin daya daga cikin dakunan gidan. “Baki da hankali ne? Kin waye kike son sanin waye shi?” Kallon shi tayi sannan ta zauna tana faÉ—in. “Yau nake son sanin waye Malik ? Idan baka sani ba fine!” “Ba zan iya baki labarin Dodonmu ba, amma ki tafi unguwar kudu, wurin Boss me hannu daya, ya baki labarin artabon shi da Malik!”

“Tir!” Ta fada tana me mikewa, barin dakin. “Kaji da kyau sai na nimo, Malik Menk Jordan!” Daga haka ta bar gidan, gidan su ta wuce, tana me alkawarin shigar dare zata yiwa Unguwar kudu, tasan unguwar matattarar duk wani shaidanin marajin magana ne, don koda ta koma gida, ba wani damu ba, abincinta kawai ta ci ta nufi dakin da take ajiye wasu kayan fada. Tana ganin kiran Mr Amjad taki dauka, ai yasan abin da yasa shi hadata da Malik kuma yanzu zai addabeta da kira.

Sai da ta dauki kayanta, sannan ta koma dakin ta shirya cikin kwarewa, sannan ta saka bakakken kayanta, ta saka tare da nufar unguwar kudu, da mashin din Black ta nufi unguwar, da tambaya ta isa gidan Boss me hannu daya. Yana tsaye a wani shago wanda ake sayar da duk wani nau’in makami, amma babu bindiga.

“Boss me hannu daya, Nazo sanin waye Malik Menk Jordan?!” A mamakance kowa ya juya.yana kallonta…….
Kuncanki wacce drama zata fashe next page…..
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
*Idan na samu lokaci zan karo page 1 zuwa dare! In sha Allah*
[8/28, 2:44 AM] Maman Sadiq Da Khadijah:

Leave a Reply

Back to top button