Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 33

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣

 

…….Alhmdllh sosai jego yayma Lulu ƙyau, ga Iya Tabawa na mata wani sirrintaccen gyara irin na mutanen da cikakke da ke zama a jikin mace duk da bada kanta ta haihu ba. Gefe kuma Aunty Saliha ta sake kawo wanda sukai mata gyaran aure na nasu suma yanzu. Mommy ma na nata ƙoƙarin. Sai ruwan addu’oi wajen Malam na Yakasai da ake amsowa Lulu na tsarin jikin da yanayin da take ciki game da Smart. Wannan ƙoƙarin Ammah ne da Abbah. Dan ita kanta Ammah kan zauna da kanta tai mata addu’oi a cikin ruwa da ma ruwan zam-zam shima AA ana bashi.
Sai Daddy da ya kawo mata malama har gida tana ɗora mata karatun addini saboda Ummita zataje ganin gida itama. Da yake Lulu tasa abun a ranta hatta Mubeen zaunarwa take ko su Amrah su ƙara mata karatun. Gefe guda kuma tana ta ciku-cikun yima ƙungiyarta rigester shima da taimakon Daddy da Uncle Khamil na Abuja da shima ya bata goyon baya. Koda wasa bata son tuna Smart, dan ko AA ta kalla babansa yazo mata a rai kanta ya dinga wani irin masifar ciwo kenan dake tayarma kowa na gidan hankali. Inda aka yankata Alhmdllh yana sake warkewa, Aunty Khadijah matar Coach ce ke zuwa dubata kullum babu fashi, idan abinda ya kama taje asibiti ne kuma sai ta shirya Mubeen ya kaita suje suga likitan su dawo. Da Ummita zata wuce shatara ta arziƙi Daddy ya haɗa mata, itama Lulun ba’a barta a baya ba, Uncle Khamil ne da yazo ya wuce da ita duk da dai jirgi sukabi zuwa Abuja tare, dan Lulu ta gargaɗeta zuwa ɓagwai saboda gudun mutanen Alh. Sulaiman kar su cutar da ita ko iyayyenta.

★A ɓangaren Ammah tsaye take wajen kaima UBANGIJI kukanta akan dai-daituwar zaman waɗan nan ma’auta. Tare da yawaita sadaka da azumi. Yaranta kaf basu zauna ba har ƴan uwanta kasancewar suna da haɗin kai. Yayinda itama Ummah ta kasa zaune ya kasa tsaye wajen sake lafto sabbin asirai kala da iri akan Ammah da Smart kai harma su Aunty Amaryar ba bari tayi ba. Dan a kwanakin nan da ƙyar suka samo kan Abba da aka nema juyarma da kai. Sai Alhmdllh al’amarin baiyi nisa ba ya sake shi, hakan ya tada hankalin Ummah kam sosai, dan ba ƙananun kuɗi ta kashe a aikin da akaima Abban ba, amma sai gashi ya tafi a banza cikin ƴan kwanaki ƙalilan….

*_UK LONDON_*

Hassada ga mai rabo taki ce, sannan duk abinda UBANGIJI ya ƙaddara shi a matsayin naka babu wani mahaluki a duniya da ya isa canja wannan ƙaddarar. Dan kuwa a lokacin da Ummah ke can tana faɗi tashi akan abinda bata iya jayayya da shi ba anan ƙasar England ƙaramin labari ne ke neman canja kansa akan Aliyu Mika’il Idris Mawashi, wato Smart Mawashi zuwa babban gaske gagarumi. Dan fa manyan clubs da ke zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa sun fara bayyana kansu a fili yanzu. Wannan yasa aketa faman kai kawo da dambarwa tun barowarsu Canada shi da Manager ɗinsa Uncle Yousuf. Sosai ake ta kai ruwa rana da bata kashi a tsakanin Coach’s ɗin mayan clubs ɗin. Shi dai Smart ya duƙufa gayama UBANGIJI da neman zaɓinsa. Dan bashi da wani zaɓi sai nashi. Yayi alƙawarin duk inda ya tsinta kansa zaiyi aiki tuƙuru in sha ALLAHU duk da a cikin zuciyarsa yana da club ɗin da yafi so da ƙauna kuma gashi a cikin masu zawarcin nasa. Amma sai bai Zafafa ba ya bar ma UBANGIJI komai sai su Uncle Yousuf da keta kaiwa da komowa shi da Coach ɗinsu na Queen City da duk manyan masu faɗa ajin club ɗin.
Sosai mahawara ta ɗauki zafi a tsakanin manyan clubs guda uku da suka riƙe wuta fiye da sauran, dan kowa ya gagara janyema kowa. Sannan duk sun zuba manyan kuɗaɗe akan Smart ɗin masu girgiza zuciya. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta sake zama babba. Dan manyan gidan jaridu na duniya musamman a fanin ƙwallon ƙafa sunyi ƙur da idanunsu akan wannan batu domin ganin wazai ɗauki wannan lu’u-lu’un a cikin juji. An buga an turza an kai matuƙar kai ruwa rana kowa yaƙi sakarma ɗan uwansa, dole aka tafi mataki na biyu wato jin ra’ayin Smart game da wane team yafi sha’awa shi a ransa. Tun farko Smart nada ra’ayinsa dama, amma ya zaɓi barma UBANGIJI zaɓinsa. Har a yau da aka kai wannan matakin na jin ra’ayinsa bai ji zuciyarsa ta canja da ga abinda ta ke so ba tun yana da ƙuruciya. Dan haka bai wani basu wahala ba ya faɗa musu zaɓinsa wato *_ARSENAL FC_*. hankalin sauran clubs biyun da sukai gogayya da Arsenal ɗin ya ɗaga, a take suka ƙara kuɗi akan wanda suka saka a farko, amma dai Smart nakan bakansa Arsenal ɗin dai, dole suka haƙura dan aikin gama ya gama Arsenal tayi nasarar siyensa da kuɗi kimanin dala Miliyan arba’in.
Duk wani masoyin Smart a wannan rana yana a cikin matuƙar farin ciki mara misali, Ammah duk dauriyarta sai da tai hawaye lokacin da Uncle Yousuf yay kiransu yake sanar musu al’amari fa ya kai girman da aka daɗe ana fata. Sai kuma addu’ar cigaba da samun nasarori ga Smart ɗin. Amma wannan tsanin kam an haye sama ƙololuwa.

Sun ɗanyi zaman meeting meeting da ƴan cike-cike na tsarabe-tsaraben da aka san ƙwallo da shi su da Manager ɗin sa Uncle Yousuf da shi kansa Smart ɗin. Kafin dai a ƙarƙare ya saka hannu a ƙarshe. Da ga haka akaje matakin duba lafiyarsa ciki da bai. Alhamdullah nan ma normal an samesa da cikakkiyar lafiyar jiki dama ta sassan jiki. Bayan kammala waɗan nan ya ziyarci Arsenal camp domin yin hotuna da gabatar da shi ga teammate ɗinsa. Ya samu tarba fiye da yanda yay zato da tsammani ga teammate ɗinsa. Dan tunda suka shiga cikin camp ɗin bakinsa bai bar ambaton ALLAH ba. Kwarjininsa da hasken musulunci ya sake ƙawatashi a garesu da girmama mutuncinsa. Sunyi hotuna da duk abinda ya dace a wannan ranar kafin a wuce mataki na gaba. Wato gabatar da Smart Mawashi ga fans.

Duk wani masoyin Arsenal ya halarci babban stadium ɗinsu da ke a cikin birnin London. Wasuma da ga ƙasashen ƙetare suka zo domin ganin sabon yaron na Arsenal da za’a gabatar saboda soyayyar da sukema club ɗin. An cika matuƙa da har sai da Smart ya dinga jin kansa na sara masa. Ga kuma masu kallo a television. Amma ya daure bakinsa na cikin ambaton ALLAH ya fuskanci masoya. Wani irin ihu da stadium ɗin ya ɗauka lokacin da yake shigowa fuskarsa ɗauke da sassanyan murmushi yana mai ɗaga musu hannayensa biyu yay dai-dai da wanda su Mubeen suka ɗauka suma a cikin falon gidansu da Lulu ce kawai babu tana can ɗakinta tana barci. Hatta AA na a hannun Daddy dan har shi ake wannan kallo. Fitowa tai a ruɗe, sai dai ganninsu duk suna kallon ƙwallo a tv kuma duka gidan ya sata tsayawa turus cikin dafe kai da jan tsaki. Babu ma wanda yasan tanayi dan hankalinsu bama ya wajen. Cikin jin haushi ta juya ta koma duk da tayi mamakin ganin harda Daddy da su Iya Tabawa wai ake kallon ƙwallo yau a gidan. Abu ne ita dai da bata taɓa gani ba. Ta dai san Mubeen nayi da su Hussain idan sun zo. Amma kosu Amrah ta sha jin suna faɗa da Mubeen idan zai kalla ƙwallo ya hanasu su kalla film. Amma wai yau sai gashi ƙwai da kwarkwatar gidan ta gani. Abinda ma Lulu bata lura da shi ba shine harda masu wanki duk suna a falon, dan suna da ga ƙasa ne zaune yasa bata gansu da ƙyau ba… Kamar yanda a gidan Daddy suke kallo a gidan su Smart ɗin ma hakane. Dan su Mubarak ne suka cika gidan da abokansu da samarin anguwa. Yayinda ba’a bar Abba a baya ba da ga shi har Ammah da sauran yaran gidan sun cika a falonsa danƙam dan shi yasa a tattaro kowa yazo. Ran Umma da Mama a mutuƙar ɓace yake. Zuciyar Umma bata nema fitowa ta baki ba sai da aka nuna Smart na shigowa cikin tsakkiyar tarin tawagar turawan nan yana ɗan wasa da ƙwallo, stadium ɗin ya ɗauki ihu kamar zai tsage. Sai kuma sanda aka ɗaga rigarsa mai lamba tara yanda suka ɗauki ihu mai jijjiga kunne ita zuciyarta suke jijjigawa, dan a bazata kawai sai ta fashe da kuka. Da farko babu ma wanda ya lura da ita sai da Huwaila ta ce, “Ummah ke kuwa miya sakaki kuka? Ko duk farin cikin ganin Yaya Hydar ɗinne?”.
Lokacinne hankalin kowa ya koma kan Umma. Sai dai kafin ma wani ya iya cewa wani abu ta miƙe cikin rangaji kamar wadda tasha tai marisa ta nufi ƙofar fita. Ƙayataccen murmushi Abba da Ammah suka saki kusan lokaci guda. Yaranta dama duk wanda ke wajen zasu ɗaga hankalinsu su bita Abbah ya ce kowa ya koma ya zauna, idan kuma wani ya bita sai ransa ya ɓaci. Dole sukabi umarninsa. Da ga baya ma abinda ke faruwa ya ɗauke hankalinsu kowa ya manta da batun wata Umma can….

Sosai Smart ke jin farin ciki a ransa mara misali dan harda hawayen farin ciki ganin yanda waɗan nan ɗunbin al’umma suka amshesa da taruwa domin shi. Bakajin komai sai ambaton sunansa a wajen, _Smart Mawashi, Smart Mawashi_ dai. Yanda ma suke ambaton Mawashi ɗin abin dariya. Abinda ya ƙara tabbatarwa da mutane Smart Mawashi ya amsu yanda a yinin ranar kawai an saida copy na rigar JC mai ɗauke da sunansa kawai ta kai kimanin dubu hamsin. Wannan al’amari ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da gidajen jaridu. Yayinda masu fashin baƙi akan harkar ƙwallon ƙafan keta nasu aiki. Gida Nigeria musamman arewaci kuma garin Kano sun shiga matuƙar alfahari da ganin ɗan su yau a wani mataki na rayuwa da sai ɗan baiwa mai Sa’a kawai ne ke takawa. Hatta da social media babu abinda ke kai kawo sai hotunan Smart Mawashi da tarihin rayuwarsa. Hatta da hotunan bikinsa ranar sai da suka dawo sabbi a yawon media. Sai a lokacin ne Lulu tasan wainar da ake toyawa. Ita kasa ma fassara al’amarin tayi sam. Cikin sauri ta shiga bincike-bincike a media. Sai ko gashi ta ga duk abinda take buƙatar. Tsabar yanda al’amarin ya dakar mata zuciya bata iya furta komai ba. Dan datace ma zata tsananta tunani ko maganar Smart ɗin matsanancin ciwon kai da tsanarsa da take ji ke dawo mata sabuwa. Dan ma Alhmdllh zuwa yanzu akwai ɗan sassauci a a al’amarin kasancewar addu’a da aka duƙufa yi babu dare babu rana. Yau ɗin ma dai ta yini da ciwon kan, dan har dare tana kwance tana fama har sai da Daddy ya shigo yay mata addu’oi….

Bayan Smart ya fito da ga stadium hirarsa da ƴan jarida ta zama abu na biyu da ya sake zama babban topic a kansa a wannan yini. Ya bada tarihin rayuwarsa da yay matuƙar taɓa zukatan mutane harda masu hawaye, dan ma ya ɓoye kaso tara cikin goma ya bayyana abinda yake da buƙatar duniya ta sani ne kawai. Ya bayyana irin yanda ya tashi da son ƙwallo a zuciyarsa da taimakon da Abdull-Hameed Coach yay masa a rayuwa da matsalolin da ya samu da ga baya. An masa tambaya akan dalilinsa na zaɓar team ɗin Arsenal duk da sauran clubs biyu da suka riƙe wuta a zawarcinsa sun sake ƙara kuɗi amma yace Arsenal ɗin dai. Sai yay murmushi da faɗin “Arsenal club ne da tun yana yaro yake matuƙar so, sannan club ne mai ɗunbin tarihi da kuma ya ajiye tarihi da tarin masoya a duniya, sannan club ne one of the best in the world. Sannan yana da ƴan wasan da yake matuƙar so da kallo a matsayin madubinsa a cikin club ɗin irinsu Terry Herry. Patrick Vieira da sauransu…….”✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button