Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan ko Mazan 21

Sponsored Links

💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPİSODE 2️⃣1️⃣
Ina mata masu sha’awar koyon sana’ar saƙar kwarashi ta zamani?
Ko kina da labarin Heart Stitches kuwa?
Zata fara online classes na koyarda sakar kwarashi nan bada jimawa ba.
Ita wannan saƙar idan kin iya ta, kina zaune gidanki zaki dinga yi kina saida abun da kika saƙa cikin sauki.
Gashi kuma tana saida haɗaɗɗun handmade bags.
Ki shiga group ɗinta domin ƙarin bayani ga link din 👇🏼

https://tinyurl.com/bagsstitcheshaven

Kiyi following page dinta kisha kallo.
https://www.instagram.com/heart_stitches77
Zakuma ku iya chatting nata up ta hanyar danna this link;
https://wa.me/2347034845999

21
Wajajen magrib suka shigo gidan as usual Meena direct dakinsu tawuce dan ranta amugun bace yake tun dazu darana duk wanda ya tambayeta meke damunta tace ciwon mara take, binta da kallo Hajiya tayi ta kwalama Ummi kira ganin bata afalo. “Ummi Ummi” tabe baki su Rabi sukayi suka wuce ciki Hajiya tace “hala salla take nima bari naje nai salla” mahaifiyar Hadiza tace “ina gani kam dan da yanzu tazo tamana sannu da zuwa” wucewa daki Hajiya tayi ganin Meena kan gado yasa tace “Waike lafiyanki kalau kiketa kumbure kumbure ke kadai” tana kwance kan gadon tace “cikina ke ciwo Hajiya” kanta Hajiya ta shafa tace “sannu to kinji Auta na” dan murmushi kadan Meena ta mata Hajiya tawuce tazaga bayan gida tayo alwala tayi salla tana zaune kan dadduma wanda dama haka take har akai ishai tayi tai yan addu’o’inta tashafa saikuma cikeda damuwa tace “Meena kinga je sama dan Allah ki dubomin Ummi bantaba shigowa gidan nan nakai war haka yarinyar nan batazo wajena ba, kinji muryan su Aman fa suma sai kwalamata kira suke, tashi dan Allah dubomin ita Allah sa lafiyanta kalau ba zazzabi bane ke damunta dan abinda zai hana Ummi saukowa gaisheni babban abune” daidai lokacin Anty Jams tabude kofan tace “Hajiya angama abinci kufito muci” anatse Hajiya tace “to bari Meena takiramini Ummi Jamila ganinan zuwa” tashi Meena tayi tawuce sama itama Hajiya tafito falon tasami waje ta zauna.
Dakin Ummi tashiga Meena tabi dakin da kallo yanda suka barajı dazu haka yake dasauri tace “Ummi” shirun yayi yawa hakan yasa tawuce wajen bayi tabude bayin but Ummi bata ciki dasauri tafito tashiga bude dakunan yaran ganin Aman adakinshi yasa tace “Aman have you seen Ummi”? Cikeda rashin jin dadi yace “no Aunt I can’t find Anty Ummi anywhere” dasauri dasauri Meena tafito tasauka kasa Hajiya data bita da kallo ganinta ita kadai tace “ina Ummi”? Dasauri tace “ina zuwa Hajiya” saita wuce kitchen tabude kofa taje backyard batanan dasauri tawuce wajen gateman dinsu tace “Yallabai dazu damuka fita Ummi ta dawo”? Dasauri yace “bata dawo ba babu wanda yazo gidan banda ku dakika dawo yanzu” Dasauri Meena tabude bolt na wayanta zuwa history nan taga Jabi akakai Ummi that means she changed the trip dudda haka takasa gasgatawa, part of zuciyanta nacemata Kodai bolt direban ya saceta ne nan da nan takira Number bolt driver yana dauka tamai explaining tace “ina sister na data biyoka”? Dasauri yace “Madam she was crying seriously in the car and asked me to take her to jabi garage Adamawa line” dasauri Meena hannunta da jikinta har rawa suke taciro number Ummi takira but wayanta akashe da gudu takoma cikin gidan Hajiya data kasa zaune takasa tsaye dan hakanan zuciyanta ke gayamata ba lafiya ganin Meena yasa tace “ina Ummi?” Sai kawai tafashe ma Hajiya da kuka tace “Hajiya wlh duk laifina ne” yanda gaban Hajiya ke faduwa batasan sanda tama Meena tsawa ba. “What happened what did you do Meena?” Kallon yan uwan Hadiza dake falon Meena tayi saikuma tace “Hajiya muje daki nagayamiki” ran Hajiya abace batajin zama ta iya moving kafafunta ba tace “tell me anan Meena, idan kin boye musu bazaki boyema Allah ba” Dan lumshe idanu Meena tayi tace “Hajiya naga how sad Ummi was akunshe adaki shine dazu da kuka kirani nakawo shayi naje na sameta tazo muje asibiti taki tace ba’ace tajeba shine nace kene kikace nazo da ita shine tabini………” tabama Hajiya daga farkon labarin har karshe zuwa wajen bolt Hajiya kawai ta daurama Meena mari! Saida kowa yazabura Maman Hadiza tace “assha, assha Hajiya dan Allah kiyakuri” Rabi da Hafsat zuciyanshi kaman an watsa ruwan sanyi sabida dadi, ran Hajiya yanaci bana wasaba kallon Anty Jamila tayi cikin kakkausan murya tace “tashi kitafi asibiti yanzu yanzun nan Jamila, kekuma kiramin Nura da wayanki” tama Meena dake share fuska magana azafaffe Maman Hadiza tace “Hajiya calm down bakida lafiya fushi haka baida kyau agareki” cikin tsananin fushi tace “I don’t care! Koda zan fadi na mutu awajen nan I don’t care! Kiramin shi nace!” Hajiya tafadi ranta abace kowa yaja bakinshi yayi gum babu wanda baisan labarin Hajiya ba batada kyau tai fushi Anty Jams ta tashi sun sun taje ta dauki key motan Hadiza tafice, ringing daya biyu Nura yadaga strictly Hajiya tace “kome kakeyi Nura a asibitin nan kabarshi kazo gida yanzun nan ga Jamila naturo asibiti tazo ta zauna da Hadiza” zaiyi magana Hajiya ta katse wayan takalli Meena tace “bacemin daga gani, kuma ku tashi ku kwashi abincin nan ku wuce kuje chan sama kuci” Hajiya tama su Hafsat tsawa duk suka tashi Falon yarage daga Mama sai Hajiya tazo gefen Hajiya tariketa cikin kwantar da murya tace “Nura bai kyauta ba dudda kuwa Hadiza diyata ce amman kiyakuri baya hayyacinshi kinsan ba kowa ne ya iya handling pressure ba, dan Allah kiyakuri Hajiya fushi nan baida kyau agareki” lumshe idanu Hajiya tayi sai kawai ta zauna Mama tazauna kusada ita tadauki ruwa ta bata Hajiya ta karba tasha.

Cikin 20min Nura yashigo gidan adan tsorace dan yadauka ciwon Hajiya ne yatashi yana shigowa falon suka hada ido wani kallo data mai saida gabanshi yafadi wlh dasauri Nura yazo wajenta yaduka yana kallonta yace “Hajiya menene? Wani abu yafaru ne? Jikinki ne? Mama meya sami Hajiya”? Yayi maganan cikeda so dakuma kulawa ga Mamanshi nuna kanta Hajiya tayi tace “Nura tunda kai aure yau shekara goma zuwa gomasha kenan nataba saka a hanya mara kyau?” Dasauri ya girgiza kai yace “a’a” tace “nataba cemaka ka bakanta ma Hadiza koka kuntata mata, kai nama taba gayamaka ga yanda zaka tafiyar da gidanka?” Dasauri yace “a’a Hajiya, Hajiya meya faru waya bata miki rai haka eh Mamana”? Bubbuga kirjinta Hajiya tayi tace “Nura ni uwa ce, na haifi mace na haifi namiji, nasan darajan yara, banda haka d’a nakowa ne, abinda bazanso ama nawa ba wlh bazan taba bari ama nawani ba” Mama tace “kwarai!” Hajiya tace “Nura Ummi ta daukeni matsayin uwar da batada shi, bamata min kallon maman mijinta sai mahaifiyarta, bata kyashi tashiga kitchen tadafamin abincin dazanci takuma dafa na gida, wlh wlh abinda Ummi kemini ko Meena diyar dana haifa da cikina batamin, tabani abinci, ta kwashe kayana takai washing machine ta wanke tazo ta goge, ta gyaramin wajen kwana ta kunna turare, idanba na kora Ummi ba ko nace tabarwa Meena wannan tayiba yarinyar nan ita kemin komi da murmushi kan fuskanta Nura yau karasa wanda zaka wulakanta sai Ummi?” Cikeda mamaki yake kallon Hajiya danshi ya manta yama Ummi wani abu dasauri yace “Hajiya mena mata kuma? Takikkirani tun shekaran jiya ban samu nakirata back ba ban mata reply message ba shinefa kuma ai ban natsu bane” sosai Hajiya ke kallon Nura jin yau kwana uku rabon dayamayi magana da yarinyar tanason tai magana Mama tace “Nura bakai magana da Matarka ba yau kwana uku tana matarka koma menene ai ka kirata kaji ta tashi lafiya tunda hakki ce agareka gaskiy……….” Hannu Hajiya tadagama Mama azuciye hakan yasa Mama tai shiru ganin yauwa ran Hajiya alalace yake, Hajiya na kallon Nura dake gabanta aduke tamike tace “Nura auren huce takaici ko auren sha’awa fadamin wanne kayi da Ummi?” Nura na kallon Hajiya yama kasa magana saikuma yace “kaman ya Hajiya”? Cikin fushi Hajiya tace “how dare you Nura baka kira yarinyar nan for 3days kaji yatake ba you think is okay, dazu Meena takawota asibiti da sunana kamata koran kare!” Mikewa tsaye dasauri Nura yayi yashafa kanshi zuwa fuska yakalli Hajiya yace “Hajiya wani irin koran kare? Cewa Meena nayi tawuce takomar da ita gida is not good Hadiza dake that condition taganta” cikin fushi Hajiya itama tace “wat do you mean by that Nura are you trying to say Ummi tasa Hadiza in that situation”? Cikida gajiya da maganan yace “Hajiya no bahaka nake nufiba amman dai ai aurenta danayi yasa Hadiza ke neman rasa ranta so I have to keep her away from Hadiza kada tazo takara samin heart attack, am just protecting Hadiza Hajiya” Sosai Hajiya kewani kalan kallon Nura the way he said everything da zuciya daya kai tsaye is as if Nura baida single feeling for Ummi aranshi all abinda ke ranshi ke kuma damunshi ayanzu is just Hadiza he sees nothing wrong a abinda yayi, jinjina kai Hajiya tayi irin na manya cikin wata kalan murya tace “ai shikenan Nura tunda aurenta shine dalilin dayasa Hadiza ke neman rasa ranta saisa ka wulakantata baka daukan wayanta, tazo asibiti kuma kamata kiran wulakanci dacin mutunci Ummi ta tafi garinsu! Tabarmaka gidanka!” Dawani kalan sauri yakalli Hajiya sake jinjina matakai Hajiya tayi yanzu damuka dawo mun nemata sama da kasa bata, Meena ta duba bolt taga ta chanza location ta tafi jabi takira mai bolt wai yakaita Adamawa line” kusan shiru falon yayi na kusan minti biyu duka abinda yafaru dazu a asibiti na dawowa Nura jiyayi ranshi yabacı matuka, cikeda bacin rai yace “yanzu sabida dan maganan danayi wanda da Meena ma nayi magana bada itaba shine ita mai zuciya tawuce ta tafi garinsu”? Sosai Hajiya ke kallonshi cikin tsantsan bacin rai yace “ai shikenan Allah kiyaye, nina tafi asibiti” yajuya fuuu zai fita haryakai kofa Hajiya takirashi tace “Nura!” Juyowa yayi idanunshi sunyi jazur yakalli Hajiya tace “Nura kasani abin nan dakayi nikamawa” cikin fushi sosai Nura yace “Hajiya wai mekike cewa haka? Idanma ita nama fadan menene ba matata bace? Bazan iya ma matata fada ba? Niba mijinta bane? Itane sarkin zuciya takama ta tafi bazata iya fahimtan wat am trying to do ba, inbar Hadiza tamutu sabida Ummi? Inbar Ummi tashiga dakin sabida banso nabata mata rai eh? Things are not done like that Hajiya? Taje bazan kirata ba bazan bitaba idan tagaji da zama tasan hanya tadawo Abuja inba hakaba tayi zamant……” Tass! Hajiya ta daura mai mari abinda bata tabayiba, yadafe kubcinshi yana kallon Hajiya, dakuwa Hajiya tamai tace “kaci mai garinku Nura kaji u are very stupid, how dare you call yarinyar dake kula da mamanka all this sort of names Nura kasan bakason yarinyar nan why did you marry her? Ubanme yakaika ka aureta eh? Naga ba ita tace tana sonka ba, kotace lallai saika aureta kaika nemeta, kaiharka isa kayi magana haka akan Ummi data taimakeka da gidanka da yaranka dani uwarka, kazaci zaman ka nake agidan nan shashasha dakai zaman Ummi nake wlh agidan ma right from day one danazo itane komiba, yarinyar dake kula maka da gida da yara, tarbiyan su waye ajikin Aman da Amal Ummi, how dare u say such things about my precious daughter ina tarbiya ka da hankalin yaje eh, Nima da izinin Allah gobe zan barmaka gidan kome kaga dama kayi kuma kasani ba Ummi ka wulakanta ba ni mahaifiyar ka ka wulakanta dan yarinyar nan tadaukeni amatsayin mahaifiya, the poor thing tariga taga baka sonta baka bukatanta gwara ta koma garinsu kafin kamata kora da hali, kaji kunya Nura girmanka bai amfaneka da komiba indai wannan ne kalan rayuwan daka daukama kanka mayaudari kawai, innocent yarinya marainiyan Allah kawulakanta haka sabida burinka yacika yanzu shikenan kaje kada ka nemeta bazance kayi ba Ummi ko’ina kike Allah tsare ai Meena nada number kakarta zan kira naji kaje kayı duk abinda kakeso just know this wlh gobe zan bar gidanka kaji na rantse maka” tajuya fuuuu zata wuce dasauri Nura yataho gabanta yasha yayi kneeling tareda rike kafanta yace “Hajiya dan Allah ki yakuri baki fahimceni bane, dan Allah kada kiyi fushi dani Hajiya dan Allah dan Allah Hajiya kiyakuri” hankade kafanshi Hajiya tayi tawuce dakinta tarufe kofa tana kallon Meena dake kuka.

Ahankali Mama tace “Nura baka kyautaba a gaskiya bahaka ake zama da mata biyu ba, nasan Hadiza batada lafiya kuma i get you are doing everything possible kaga tasami lafiya kar hakan yasa ka tauye hakkın Ummi wacce itama matace agareka, hakkine akanka kaje ka ga lafiyanta akullum ranan duniya which bakayiba, ita dutse ce kwana uku bata daura ka a idoba, batai magana dakaiba tazo asibiti ai ka kaita gefe kamata magana mai dadi ba kamata koran wulakanci ba kodako da Meena kake magana ai agabanta ne, kazaci bazataji ba dadi bace mahaifiyar ka na maka fada kuma kana kiranta sarkin zuciya, Allah kiyaye, tagaji da zama zata dawo, haba Nura fisabillahi fa? Haka ake magana? Kanada kanni kuma Kanada diya mace kaima Nura haba” shafa kanshi yayi yayi huci mezafi yace “Mama gida nawa akeso naraba kaina tsakani ga Allah eh? Ga Hadiza ga Ummi yanzu kuma Hajiya eh Mama”? Cikeda tausayi tace “yanzu tunda Jamila na wajen Hadiza, jekabi sahun Ummi kaga, ka kuma gwara kiranta awaya ko Allah zaisa kasameta ni zanji da mahaifiyar ka”.

Wucewa yayi kawai yajuya yafita su Rabi dake sama wani tsalle sukai suka rungume juna zokaji dadi kaman zasu zare.
Mota Nura yabude yashiga yaja motan yayi nisa yana tuki sannan ya gangara yayi parking tareda punching car steering da hannu yana wani huci gabaki daya ranshi ya dagule ranshi abace yake sosai bana wasaba, hannu yasa a aljihu yaciro wayanshi yayi dialing number wayan Ummi yakai kunne wayan akashe cire wayan yayi daga kunne ya jefar yasake punching car steering kaman shine yamai laifi yace “damn it” ya fuzar da iska chan yace “ni zaki gwadama zuciya? What? Can’t you just be a little Patient dani Ummi sabida kin kirani ban amsaba, what me kikeso? So kuke ku kasheni? Ku rabani biyu kowa yadauki part daya nabar Hadiza ta mutu sabida ke? Ke mai zuciya kin kama kin tafi kina kashe waya ai sai kije Allah kiyaye I will not look for you nor follow you” yayi maganan ranshi a bala’in bace kaman ba Nura ba abun yamai mugun ciwo, tada motan yayi yajuya yayi nisa sai kuma yakara daukan kwana yatafi jabi har Adamawa line yafito kawai ya tsaya yana kallon wajen that looks empty motoci duk sun tafi tsaki yayi yace “kin kyauta” yakoma cikin mota yatada motan yatafi gida yakoma yayi parking ya tsani arayuwanshi Hajiya na fushi dashi parking yayi yafito yashiga gidan direct dakin Hajiya yawuce kofan yabude Meena yagani tana bacci Hajiya kuma zaune tayi shiru kana ganinta kaga damuwa akan fuskanta ga wayanta a hannunta kallo daya tama Nura tadauke kai ahankali zuwa yayi yazauna ahankali agabanta yakama hannunta murya Chan kasa yace “Hajiyah” kallonshi Hajiya tayi duk yanda tadaure saiga hawaye tace “Nura I know baka batamin rai kasafai amman yau ka matukar batamin rai, Nura nasan kanka yayi zafi but no matter what you are going through bai kamata kama yarinyar nan ihu kamata koran kare batare daka tsaya kun gaisa ba bayan bata ganka ba ko saka a ido ba na kwana uku haba Nura yarinya mai hankali haka, ranan da abin nan yafaru agabana naji tace ka manta damu anan ka kula da Hadiza ita zata kula damu, Ummi musulma ce kowa yaje yaduba Hadiza banda ita bamu gayamata komiba batasan me akace game da Hadiza ba atleast daka ganka the least you could have done was ka kirata gefe kamata bayani gashi gashi ka rakasu su tafi amman kamata haka haka akeyi? Ka nuna baka damu da ita ba, Ummi ba zamana takeba zamanka take kaine mijinta she must have felt baka bukatanta yanzu baka sonta saisa kamata haka ta tafi tabaka sararin dakakeso are you happy yanzu kalli wayana” tanunama Nura wayan hannunta tace “nakira number yafi sau goma baya shiga na kakanta ma haka idan wani abu yaje yasami yarinyar nan ahanya fa Adamawa ba kano ba chan gari da nisa eh, Nura baka kyautaba koma menene kaci mutuncin Ummi, ka masifan bakantamin rai Nura” Hajiya tashiga matsan hawaye cikeda bakinciki Nura was just feeling bad badan Ummi danshi baiga abinda yamata ba but sabida kukan da mahaifiyarshi keyi, hannunshi yadaura kan fuskanta yana share hawayen yace “Hajiya dan Allah kiyakuri nayi kuskure bazan karaba kuma İn sha Allah zatakai gida lpy bari ana sallamalı Hadiza ta dawo gida zanje na daukota dakaina kinji Hajiya” gyadamai kai tayi tace “amman nidai gobe zanbar gidan nan kamana booking jirgi” dasauri Nura yace “appointment dinki next week fa” cikin kuka Hajiya tace “wlh nahakura da appointment, ina bukatan fresh air, Nura banson rayuwan dakakeyi da kasan bazaka iya adalci ba dabaka auro Ummi ba in the first place, bace wa nake son dakakema Hadiza kuskure bane a’a shi soyayya Allah ke daurawa mutum amman Nura ka kyautatama mai kyautata maka, ka farantama mai farantamaka, Nura Ummi has been there for you for yaranka thanks to that girl gidannan is running smooth amman bakomi kayi duk yanda kaga dama” kusan har asuba da Nura da Hajiya na zaune lallashin Hajiya yake taki bini bini saita kira number Ummi kona Gwaggo saima yazo yana tausayin Hajiyan hakanan ba yanda ya iya yamata booking jirgi sukama su Mama sallama da kanshi yakaisu har airport wajajen 8 dan jirgi su 9 ne.

Leave a Reply

Back to top button