Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 34

Sponsored Links

34- “Ka ji! Ka sahale min haka kawai zai saka na cika maka alƙawarinka” juyawa yayi ya zuba mata idanu, sannan ya taka har gabanta, ya rungume ta sosai. “naji zan sahale miki, zan baki iska, zan baki damar kiyi sabon rayuwa. Amma zan kare rayuwana ina jiran kiranki, zan jira kiranki har zuwa ranar mutuwata, zan jira ki zan jira zuwan kiranki, Zainaba zan yi kewarki zan yi kewarki zan yi kewarku da abin cikinki, ba zan daina kewarki ba” kuka take sosai tana kara tura kanta kirjinshi, tana jin wani irin kaunarshi, kamar ta janye bukatar ta na rabuwa da shi, amma ina idan ta tuna shi ne sanadin fadawarta dogon mantau sai ta ji dole ta rabu da shi.
“Idan har kana son na cika maka alƙawarinka, dole ka sahale min. Dole ka nisance mu, dole ka bamu damar mu rayu inda babu kazamar rayuwa, inda babu kazamar soyayya, inda babu haramtacciyar kasa, inda rayuwa da mutuwa ba a bakin kome ba ne, ka bamu damar tafiya can inda sai dai ka a ranka muna raye, amma ba zaka san me muke ba.”
“Zan baku kome zan baku damar kome, amma ki sani ba zan tab’a cire idanu akan ku ba, ko ƙarƙashin ƙasa kuke. Idanuna sa zuciyata tana tare da ku. Kune Duniya ta, kune rayuwata, farincikin da nake yana tare da ku ne, amma zan hakura da nawa farincikin na baku kuyi, na barku Ku rayu cikin aminci da salama, na san kinyi fushi ne idan kika yi sanyi zaki fahimce ni, Albashir zai kawo miki duk abin da kika bukata, duk abunda kike so akwai ki bukata kawai, sannan na amshi number Kawunki na can Maiduguri, zan saka a tura duk abinda zaki bukata na haihuwa. Zainaba don Allah, kada ki cusawa Yarona ko yarinya ta, kiyayyar da kike min. Don Allah na hadaki da shi.”
“Zan yi maka duk yadda kace, amma sai ka bani sarari.”
Idanun shi cike da kwalla, a hankali ya ce mata. “Daren yau zaku bar Keivroto, ki kula da kanki.”
Daga haka ya fice daga dakin, yana jin kamar ya fashe da kuka, zuciyarshi tayi nauyi, tunda ya saka kai ya fita ta rushe da kuka, kuka take yi na jin haushinsa da ita kanta. Me yasa ta dage sai sun rabu? Amma ai shi ya kashe mata iyaye. Shi ya kashe mata iyaye ba zata tab’a yafe mishi ba, gara da ta rabu da shi, domin ta haka ne kawai zata huce haushin da take ji, ta cusa mishi bakinciki da har ya mutu yana tunawa da ita,
Duk su Ammyn suna jinta, babu wanda ya iya kulata, asalima haushi ta basu suka zuba mata idanu. Har can yamma kafin Elbashir ya kawo mata wani karamin akwati, ya gaida su Ammyn sannan ya ajiye mata akan gadon.
“Ga wannan inji Malik ya ce na kawo miki, wannan kuma na baki!” Ya mika mata wata farar takarda, kasa amsa tayi ya ajiye yana nazarin yadda jikinta yake rawa.
“Ai ba zaki gane kuskure kika aikata ba, sai kin saka kafa kin bar garin nan zaki fahimci waye Malik menk Jordan, ba zaku tab’a danasanin rabuwa da shi ba, sai kin shiga kin ga yadda mata suke jiran samu karamin damar da kika wofatar.. wallahi da ina da ikon da ke, da tabbas ba zan tab’a barin ki rabu da malik ba. Domin duk inda ake bukata namiji ya kai, ko ni da nake tare dashi. Nasan illar kadaici da rayuwa da mutumin da kake so, Zainaba kina ganin zaki yi rayuwa cikin yanci da farincikin rayuwa ko? Tow wallahi ki ajiye zaki yi kuka ne, nan kaɗan da wani jimawa ba.
Zaki gane Allah da girma yake, idan kika ga Matan da suka fiki suna zaune aka wulakantasu, suna bibiyar namiji zaki fahimci yadda ake gudanar da rayuwa mara amfani. Kince Malik ya sake ki tow ki kwantar da hankalinki, zai sake ki. Ban da zuciya mara adalci taya mutumin da mata ke bin shi, ya aure su zai kare a tare dake? Kuma ki zauna kina gaya masa abin da ya miki, kuma ki zauna kina mishi danyen hali.
Allah yana gani idan Malik ya cutar dake sai ya saka miki idan kuma ke kika cutar da shi, ki san da cewa Allah ba azzalumin sarki ba ne, domin ba zai kyale ki ba, dole ya bi mishi hakkinsa. Sakarya wacce bata san kome ba sai rawan kai da yanke makauniyar hukuncin!”
Daga haka ya juya yayi tafiyarshi, a yau ya kara tabbatarwa kanshi Malik namiji ne na gaske, wanda babu me iya abinda yayi ya sadaukar da farincikinshi saboda yar karamar matsalar da zai magance da karfin tsiya. Ya dauke kai daga duk abinda yake ganin yafi karfinshi. A yau ya kara jin tsanar Hafcy ta kara fita kanshi.
Matukar Zeeno bata dawo rayuwar Malik ba, har abada ba zai taba yarda ta tare ba, Gara su kare rayuwarsu a haka. Koda yake bayan fitar Elbashir tayi kuka kamar ranta zai fita, har ta fara ganin duhu, a cikin asibitin kuwa, shige da ficce take. Ya kuma hana a mata magana yana son fahimtar zata iya tafiya ta bar shi ne? Ko zata iya zama ta ji me ya faru, har ga Allah. Dama daya tak yake nima ta ce zata ji daga gare shi. Shi kuma zai tsallake shingen rayuwa da mutuwa ya isa gare shi, idan bata nime shi ba, zai kare rayuwarshi yana jiranta.
Zai ta jiranta har ranar da zata kira shi, zai ta dakon da son ji daga gare ta, na don kome ba, sai don yasan bai da laifi. Yasan bai da hannu a kashe mahaifanta, ta yanke hukunci cikin sauri da fushi amma yasan daga ranar da gaskiya tayi halinta, daga ranar ne zata yi kuka, ina ma da yana tare da ita, ina ma da yana kusa da ita ya share mata hawaye, amma ina lokacin ya kure. Lokacin ya kure yadda ba zata daina kuka ba. Har karshen rayuwarta, baya fatan tayi kuka me yawa, hakan zai saka dansu ko yarsu suyi maraici.

Sai da aka hada su, da personal Dr da Nurse biyu, a daren ranar. Yana rike da jakarta, don ba zata iya dogon tafiya ba, dole a keken mara wheelchair aka turata, ya ɗan durkusa a gabanta. “Ba zaki ce min kome ba!” D’ago kai tayi tana kallonshi. Kafin ta ce mishi. “Me zance maka?” Murmushi yayi wanda kana gani kasan yake ne. “Ba kome!” Dauke kai tayi ta daina hango tashin hankalin yake cikin idanun shi. “Look at me?” “A’a ka kyale ni!” “Ba zan iya kyale ki ba!”
“Anya xan iya kyale ku kuwa?”
“Zaka iya mana, zaka iya mana, ko sai na gayawa duniya ka kashe min iyayena?” Yadda ta tsura mishi idanu yasa shi shiru.
“Ok haka ya miki?”
“Ko bai min ba, ka rabu da ni!”
“Zainab ina sonki yasa nake binki, ina girmanki saboda ina kaunarki. Zan kuma cigaba da ganin girmanki saboda dan da yake tsakanin mu.”
Hawaye ne sharr suka zubo mata, ta ce mishi. “Na tsane ka, bana son ganinka, da na dawo gare ka,gara kaji labarin mutuwata!” Yarrrrr yaji abu yana mishi yawo a tsakar kanshi. “Me nayi miki da zafi?”. “kai dodo ne, ka kashe min iyayena sai na.gaza jin zafin ka ? Ka raba da farincikina sai naji dadinka. Gara mutuwata zata zo maka lokacin da nace ba zan yafe maka ba, lokacin zaka gane cewa Allah yana tare da ni, idan har kai cikakken muslumi idan kana son Allah da Manzonsa, kada ka tako inda muke kamar yadda kace zaka jira sai na nime ka, zan nime ka. Lokacin da na sauke ajiyar da yake tare da ni, xan bukaci kazo kaga danka na hadaka da Allah, kada ka nime mu. Ka zauna a inda kake, idan ka sake ka bibiye mu. Daga ni har dan zamu mutu!”

Kallonta yake, yadda take maganar zaka fahimci, da gasken gaske gaskiya take gaya mishi. “Shi kenan! Allah ya tsare hanya, ki gaida gida ki ajiye a ranki ina sonku daga ke har abin cikinki.” Juyar da kai tayi tana me kifa kanta a kan cinyarta, kuka take, tana ganin bata mishi adalci ba. Ya dauki rabuwa da ita, gashi ta kuma raba shi da danshi ko yarshi. Da ita da shi waye azzalumi? Waye ya shiga tsakani? Ita kenan, itace azzalumar. Kuka take har cikin jirgin kuka take, gashi don gata privet jet dinshi ya basu, wanda xa a sauke ta a g1arin Jigawa, domin Dangin mahaifinsu sun bukaci haka. Kukan da take ya fara isar Zulfah ta ce. “Bana son iskanci, ke wata irin jaka ce? Kina sonshi kika watsar dashi. Ba ya sake ki ba?” Wani irin juyi cikinta yayi ya rike shi da sauri. “Kin bukaci ya sake ki ya sake ki uban me kuma ya rage? Shegiya me shegen kafiyar tsiya, wawuya idan kika mutu wutar su Fir’auna da Hammana zaki zauna jakar banza!”
Zaginta Zulfah take tana kara gaya mata magana marasa dad’i, har jikinsu ya tashi.
“Don Allah ki kyaleta!” Inji Ammyn, “Haba yarinya kamar aniyar, baki daya bata da mutuncin bata gaida mai mutunci ba, yar kika mara mutunci, wallahi ban da Malik ya roke ni nayi hakuri da naci ubanki haka mara hankali” kalmar jaka kuwa kamar a bakinta aka.fara kawo shi. Domin zagin tsamar miya takewa Zeenobia ita kuwa sai kuka take, tana jin kamar ta fita daga cikin jirgin ta fado ta mutu kowa ya huta, tunda ba a damu da ita.
“Madam ko zaki dan yi hakuri, domin condition dinta baya son tashin hankali.”
“Taya zan yi shiru yarinyar nan haushi take bani,kamar na rufeta da duka, don ubanta yar iska har akwai wanda zai min sanadin rabuwa da mijina ba a haifeta ba dan ubanta. Wallahi ko akan wata mace na ganshi ba zan hakura dashi ba. Balle don an gaya miki cewa mijinki ya kashe iyayenki, sau nawa ana haka? Sau nawa muna handling cases irin naki.”

Yadda take kuka ne, da haki yasa Dr ta mata allura, tare da saka mata ruwa barci ya ɗauke ta. “don Allah kuyi hakuri.” Nurse din ta faɗa, a takaice. Haka yayi ta barci.
★★
Shiru yayi yana kallon, sararin samaniya. Ba zai ce yaushe yayi danasanin fadawarshi duniyar fansa ba, amma a yau yana ji yana gani ya rasa wacce yake so, ya rasa matarshi da babynshi. Ta haramta mishi ganinsu, danne zuciyarshi yayi ya sake murmushi kamar babu abunda yake faruwa. “Hmm!” “Malik!”
“Elbashir me ba zaka Duba matarka ba?”
“Na hakura da ita dama ina son, idan kome ya lafa sai na sawwake mata.”
“A’a wallahi zata tare, ka je ka dawo da ita zan tafi China!”
“Malik!”
“Kayi abin da nace, bana son musu.” Ya faɗa yana kallon sama. “Malik kayi hakuri!” “Babu kome, ya wuce” Elbashir kamar zai yi kuka, ya ce. “Malik ka yafe mata, don Allah, wallahi ban san kome ba, kuma idan baka yafe mata ba zata iya zame min matsala.”
“Babu kome, jarabawa ce idan ban amshe shi ba ya kake tunanin al’amarin zai kasance? Ina ganin zuwa yanzu ya yaci ace ka gane cewa Zainaba ita ce tawa ƙaddaran, idan ban amshe ta ba zan iya butulcewa Ubangiji. Kayi hakuri ka amshi matarka hannu bibbiyu, don Allah ban da wulakanci. Don Allah kada ka mata kome wallahi Allah ya nufa haka zai faru ne.”
………
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

 

Leave a Reply

Back to top button