Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 2

Sponsored Links

War volume 2
“Koda wasa kada ku d’aga mata kafa, sai ta yi danasanin zuwa amsar kudina, idan ta samu lafiya ku farauci rayuwarta kamar ba zata kai ba, ku sakata a Ukubar da zata zo inda nake!”
“An gama Malik!” Ya fada, yana kashe wayar. Biyayyar da take tsakanin Malik da Elbashir biyayya ce me matukar tasiri da sadaukarwa. Har yau babu wanda yasan me ne a tsakaninsu sai Allah, amma dayawan mutane suna kiranshi da bindin Malik ko karen Malik, ko dan koran Malik. Duk abin da ka kira shi yana amsawa, gwargwadon yadda ka ɗauke shi.

Asibitin ya koma, ya tsaya har kusan awa uku kafin ta farfaɗo. Yana zaune. Kujeran da yake facing ɗinta. “Yaushe zamu samu kudin mu?”
Dafe kanta tayi, tana kallon shi kafin ta ce mishi. “Me ya faru n kare a nan?” Watsa mata kallon banza yayi sannan ya ce mata. “Kudinmu muke bukata! Ko kuma mu fara farautar rayuwarki ba dare ba rana, baki da ikon motsi ko kyakyawar numfashi. Daga wannan lokacin ki fara niman mafaka.” Yana kai aya, ya saka kai ya fita, dafe kanta tayi. Tana kara jin wani irin zafi, tabbas tayi kuskuren amsar kudin mutane da shi kanshi, Malik domin tasan ba zasu tab’a kyaleta ba.

Don haka ta sauka a gadon, duba wani drower tayi a dakin ta ga kayanta, ban daki ta shiga ta saka, ta ajiye musu kayansu a wurin, tana fitowa ya bude window ɗinkin, ta bar dakin. Abin mamaki babu wanda hankalinshi ya kai kanta, sai da ta tsare daga cikin dakin, suka zo bata magani me suna gane bata dakin. Ko kafin a cafkota yarinyar nan, ta ware abinta.

A lokacin da security din da suke kula da kofar dakinta,suka kira Elbashir suka gaya mishi, yana gaban Malik. Zufa ne uay karyo mishi ya d’ago kai zai gayawa Malik ya ce mishi. “Ta gudu ba?” Ya kura mishi idanu, gyada kai yayi yana me tsananin kunya da zafin rai. “Hmmm ai zata gudu!”
Shi dai kanshi yana kasa, ya gaza d’ago kan balle har ya iya kallon Malik. “Ba ka nasan me yasa na biye ta ba ne?”
Sake sunkuyar da kai yayi yana me kame hannunshi. “Kayi hakuri Malik!” Girgiza kai yayi yana faɗin. “Kasan waye ni?” Ya kara maganar a sanyayye. Jikin Elbashir ya kuma sanyi, yana me gyada kai. “Na sha gaya maka ita bakuwarmu ce, kasan me yasa.”
Gyada kai yayi yana jin ɓacin rai, matukar yayi idanu biyu da Zeenobia sai ya kusan kashe. Rabon Malik ya mishi irin wannan maganar tun shekaru goma sha uku, da wani abin da ya faru wanda yasan sakacin shi ne. “Kayi hakuri Malik!” Girgiza kai Malik yayi yana faɗin..
” Ba anan matsalar take ba, budewar da bakinta zai yi shi nake tunanin, don haka ba zan gaya maka yadda zaka yi, amma wajibi ne a farauce ta har sai ta gaji ta zo da ƙafarta.”
“An gama!”
“Zan tafi Demark.” “Allah ya dawo da kai lafiya!” “Amin Ya Allah!” Ya tura kekenshi zuwa dakinshi, domin yayi alola domin lokacin sallah isha ya karato.

Bayan fitar Elbashir ya tara security guard na gidan bakiɗaya, ajiye musu hoton Zeenobia. “Yallabai baya bukatar kwarzane a jikinta, duk abin da zata yi kada ku mata kome kawai ku sakata a gaba da farautar rayuwarta har sai ta zo nan da kafarta.” “Yes sir!”
★★★
Tunda ta bar asibitin, bata tsaya ko ina ba, sai Al’umma Charity House, zubewa tayi a gaban jama’n gidan ta ce musu.
“Ba zaka tab’a sanin muhimmancin rayuwa ba, sai igiyar ƙaddara tayi ninkaya da kai a kogin kaddarorri. Na fada wata masifar da mutukar ba Allah ba, babu me fidda ni.”. Ta fada tana me niman wuri ta zauna.

“Wai me ya faru?” Kurawa Innah Idanunta tayi, kafin ta kwace duk abin da ya faru ta gaya musu, sannan ta kara da cewa. “Ban san yadda zan yi ba!” Rasa me mara me mata magana aka yi, suka zuba mata ido. Can Ammyn Abbas ta ce mata.
“Kinyi kuskure!” “Ai nima abin da nake nufi kenan Ammyna, rashin binciken me yasa Amjad ya nime ni. Me yasa bai fuskanci Malik ba?” Kare mata kallo tayi, kafin ta ce mata. “Saboda akwai wani boyayyen al’amari da yake makale da ke, wanda bamu san shi ba, amma kuma Allah ya fimu sanin dai-dai!”
Juya kanta tayi cikin jin haushi ta ce. “Dake Malik tsohon banza ne, wai shi yake kokarin amfani da tab’a mishi kudi da nayi akan lallai sai na amshi tayin auren shi.”
“Allah ya miki tsari. Dan luwadin!” Kamar wacce aka gaya mata mutuwa bata san lokacin da ta ware idanun tayi cikin firgici.”Inna mugun abun yayi yawa, kuma abin haushi tsoho ne fa!”
“Ke tafi can, da ma tsohon Arziki ne, zan tsaya ayi kome,ai rufin asirinmu ne, amma tsohon banza tsohon najadu, ai bai dace da rayuwarki ba. Ki koma sama ki zauna zamu ce bakya nan, ina dalili ayi mutum da budurwan zuciya wato ya boye ta’asar da yake yasa zai auri yarinya danya jagab. ”
“Fisabilillai Innah taya ma za a kalle ni yar madara da ni, ace wai na auri wancan second hand din? Dube ni fa? Yo Allah na tuba dan shekarun talatin ma ai ya min tsofa, saidai ruwa daidai gari.” Ta fada tana tura minchi lips dinta. “Inna ki bar biyewa Zeenobia kuna rage mishi zunubi, amma maganar kudin mutane da Malik zamu tsaya a kai.”
“Kayya Uwarmijina, duka-duka nawa Abulle take? Ina laifin ya saka a hukuntatta a hukumance, sai ya ce zai aureta.”
“Inna cewa yayi na aure shi,zai biya bashin mutane, ni kuma ba zan iya auren tsoho irinshi ba gaskiya ko da kuwa bashin zai biya.”
. Rike kunnenta Ammy tayi tana faɗin, “Zainabia nasan halinki, kin nuna mishi halinki ne?” Gyada kai tayi tana faɗin. “Ammy sakarya sakatarenshi ya ce min fa, Ni kuwa na ja necktie ɗinsa na wani buga shi da kasa.”. “Kash!” Ammy ta fada tana dafe kanta tayi tana faɗin. “Kin ga irinta, ke da zaki bi kome a hankali!”. “Ammyna ni kaina, ban san lokacin da nake fusata ba.” Ta fada a hankali, *Harsashin kanta, ko ya ya nutsa to zata iya rasa hankalinta da tunaninta, Hajiya ku godewa Allah tana numfashi, amma da abin ya kassara lafiyarta babu yadda aka iya haka zaa kyaketa.*
“Zainabia! Fada da fusata ba naki bane, yana da kyau ki fahimci haka. Babu yakin da aka tab’a cin nasarar shi ba tare an zubda jini ba. Yana da kyau ki koyi hakuri rigima da Malik ba abin wasa ba ne. Maza da yawa sun mutu, wasu sun nakasa, akan dukiyar shi ran dan adam ba a bakin kome yake ba, shi abu daya ya sani dukiyarshi. Sannan kuma ganin kamar idan wani abu ya same ki ba zamu yi kuka ba ne? Ni ce a sawun farko da zan yi kuka. Don Allah ki tuna da dan uwanki Abbas idan wani abu ya faru, kece a gefenshi idan babu ke fa? Shi ya dace na barwa amanarki amma ke nake barwa Amanar shi.”

Tabbas kamar maganar ya shige ta, domin lokaci guda zaka iya hango rauninta, sannan zaka iya samun rashin kwarin gwiwa a tare da Idanunta, tsayayyun gashin Idanunta, sun yi luff.
“Ammyna, ba zan tsaya Malik yayi yadda yake so da ni ba.”
“Kuma gaskiya ta fada, a duba al’amarin!”
“Inna baby zancen duba lamarin, dukiyar al’umma aka salwantar ta sanadiyarta, idan muka goyi bayanta kamar mun hakka rami mun cillata ciki ne, mu bata kwarin gwiwar fuskarta matsalarta.”
“Kai ina Ammy ba zan auri tsoho irin Malik ba, gara na dauki raina kawai. Dan luwadi fa? Kuma mutumin da zai ajiye ni ne domin dukiyarshi da na tab’a. Sannan idan aurena yayi, zan kasance mara yanci, dan fitar da samari ke da yan matansu ba zan sani ba, yar kyautattan da saurayi yakewa Budurwa ban sani ba, babu romantic kawai rayuwata ce a kuntacce, na fara ban san kaina ba, na kare akan biyan albashn da ban san dalilin fadawa ta ciki ba, Ammyna ki duba al’amarin haka zan bada rayuwata domin farincikin wasu? Zan iya badawa domin naku.”

Kasa magana Ammy tai, domin tasan taurin kan Zeenobia bai zama dole ta fuskanci abin da take nufi ba, amma kuma zata cigaba da mata addu’a, amma kan Zeenobia tana bukatar du’a’i.

★★★
Khuldu Jahid Khan resident.
Babban estate ne, da ya amshi sunan estate domin ana kiran da billionaires Quarts, eh unguwar masu hannu da shuni ne, domin idan bakaci ka batse ba. Baka isa ka sayi gida a estate din ba.

Wuri unguwa ce da take dauke da kazaman yan siyasa, yan rashawa gwamnati, shafaffu da mai, killers da ake basu aikin na musamman, army robes da suke aikata miyagun laifuffuka wanda kowa yasan an saka hotonsu da sunan ana nimansu.

Daga cikin daya daga gidajen, Amjad Fahad Albagwi yake shi da iyalinsa. Kallon Salim yayi ya ce mishi.
“Yanzu kai Salim ba zaka dauki, 25% ba, ko Zeenobia da tayi aikin 1% muka bata domin bata san cewa hakkinta muka biya ta ba.”

Mikewa Salim yayi ya ce mishi.
“Ka haɗa da sauran ka rike, amma ni ba zan amshi 25% ba, wallahi gara na mutu ban ci.” Yana fadar haka, ya saka kai zai fita, da yasan haka zasu Mishi da ba makawa bai bada damar an shigar da Zeenobia ba.
Kuma ya san zasu nime kashe shi,, amma kafin ya mutu zai fara bayyanawa duniya gaskiya, musamman Malik Menk Jordan. Don haka bai bar gidan ba, ko da ya fito wurin motarshi zama yayi ya fara rubutu da yana gama rubutun ya ya saka a leda, ya hàdiye dakyar, kakari, haka ya saka kai ya fita, domin yana jin wani irin yanayi shi yasa yana tuki, ya shiga video recording, yana gamawa ya cire memory ɗin, ya hàdiye. Sannan ya karamin video ya bar shi kan wayar shi, yana faɗin. “Sakona zuwa ga Malik Menk Jordan!” Kyakyafta idanun shi yayi ya sannan ya kashe wayar.

Sai da ya bar unguwar, ya hau babban gadar da zata kai shi, cikin City, kawai wata babbar motar kaya, ta buge motar shi, sai da ya hantsila cikin kogin Keivroto, kuma yasan dama haka zai faru, kafin, koda yake al’amarin ya faru cikin dare ne, don haka babu wanda ya fahimci tashin hankalin, sai washi gari da aka kai labarin kai tsaye izuwa ga office din counciler, domin a kai al’amarin zuwa ga office din Mayor. Wato me gari.

Lokacin da labarin ya isa office din Mayor, hannun Elbashir ya fada, domin ana shirye shiryen barin Malik kasar ne, shiga babban dakin Malik yayi, ya same shi yana gyara link na hannun rigarshi.
“Morning Malik!”
“Hmmm! Anything else?”
“An hatsari aka yi daren jiya, kuma ana son sahalewan ka domin ciro motar da mamacin!”
“Waye shi?” “Salim Ghaddafi!” Murmushi yayi ya ce mishi. “Fansa yazo dauka kenan?”
“A sakon da na samu daga office din counciler, ya tabbatar min da yana tare da Amjad ga bayanin.”
“A ciro shi, a tabbatar da an kammala binciken kafin karfe biyu na sauya min lokacin tashi”
“Okay Malik” ya fada cikin sanyin murya.
Fita yayi daga dakin, shima Malik yana son tambayar shi ɗangane da Zeenobia amma sai ya share yana me mantawa da zancen ma baki daya.

Kamar yadda Malik ya saka aka Ciro motar da gawar aka fara binciken, ana ka gano abu a wurin ledar da memoryn suna hanjinshi, wayar shi an kai bangaren CID, criminal Investigation Department ne, anan aka shiga duba last sent din shi, last call ɗinshi, abubuwa yawa.
Suna gama tattara kome, suka tura office din Malik, Elbashir yana Office din ya karba, sannan ya wuce shi da sauran security guard suka nufi airport da Malik.
Ba karamin al’amari ba ne, rigima amma dake Malik bai yarda ya shirya rogima yanzu ba, kallon su yake ba yasa shi tattara ahirginsu a gefe guda. Mika mishi takardan yayi da kome da kome.

“Yaron ya turo maka sako, zaka gani amma al’amarinsa akwai daure kai. Hmmm a cikinmu akwai me farautar rayuwarka Malik!” Gyada kai yayi yana me gyara zaman agogonshi. “Zan duba! Yarinyar nan ka kama min ita kafin na dawo.”
“”An gama!”
“Ko kuma ka kyaleta. Ka bincika min meye take so, da shi zan kira ta.”
“An gama Malik!”
“Na yarda da kai, ban sani ba ko dan abin da na tara yana gabanka, idan shi ne ka da ka soke ni ta baya, ka soke ni ta gaba shine jarunta!”
Dukawa yayi yana me sunkuyar da kanshi a gaban Malik. “Duk ranar da ka kamani da cin amanarka, don Allah Malik ka kashe ni.” “Bashir shirunka yana bani tsoro.”
“Malik shiruna halittace ba dabi’a ba ce!” Gyada kai yayi, sannan Elbashir ya cigaba da cewa. “Dabi’a ana sauyata, amma halitta Allah ya tsara abinshi. Ban ce ka yarda da ni ba, amma ina son na gaya maka, rayuwata tana tare da naka, faduwarka faduwata, mutuwarka mutuwata. Malik i give you my words!”

……. “Allah ya maka jagora! Amma ya kake ganin shirin *Plan B* yayi?” Gyada kai yayi yana faɗin “Eh Malik amma last statement din ne bai min ba, don Allah kada haka ya shafi fansarka!”
“Wanda ya min daban, ka je zan duba lamarin!”
Fita Elbashir yayi, daga jirgin ya jira tashin private jet ɗin. .Malik yana barin kasar, aka kira Elbashir.
“Ka haɗa hannu da ni, zan biyaka kome kake so, zan baka duk abin da kake so. Zan maka kome idan kace na maka biyayya zan maka, amma so nake ka durkusa da Malik!”

“Kyautattawa Malik wajibi ne, cin amanar Malik halaka ce, ka fara gudu kafin Malik ya zakulo ka, yana sane da duk motsin kowa, duk inda kake tsammanin hatsabibi Malik ya wuce haka, ya dauke jai ne akan Yarinyar da kuka turo, kada ka manta yanzu haka Malik yana jin mu da kai. Kuma a can bangaren sadarwa ana gab da cimmaka domin IP dinka ya bada abin da ake bukata.

Ita kuma Yarinyar babu ruwana Malik zai ji da ita, da kun bar kome ya tafi yadda ake zaune, da na zaku kunce zakin da yake barci ba, ita kanta yarinyar bata san wacece ita ba, balle har ta iya tunkarar Malik hhhhhhh! Ba ku kuka nemo Malik ne ya nimo ku, ba kune kuka shiga tunanin shi ba, shi ya shiga naku ya tsara muku haka yakin da baku shirya ba, ku fara karbar shi ka gayawa shugabanka, maza bisa kanshi.

Ya turo akuya ramin mayunwacin zaki, ya fara takanshi kafin ya iso kanshi, sannan kace mishi ta yadda aka hau ta nan lissafin zai sauka.”

Daga haka ya kashe wayar, ya nufi wurin motarsu, ko gida bai isa ba aka fara haska labarin, matattan man fetur din kungiyar KJK groups ya kama da wuta. Murmusawa Elbashir yayi, domin akan hanyar Shatima ya kira shi a tsorace.
“Bashir wannan wani irin shirme nekuke aikatawa da Malik?”
“Khamis! Ka kira Malik ka tambaye shi me yake shirin aikatawa, kada ka kuma tambayata.” Ya kashe wayar abinshi.

Ko minti biyar ba ayi ba, Lalla Salmah ta kira shi, “Wai me yasa Malik yake haka ne? Me yasa ba zaka bashi shawara na gari ba?”
“Wai tsaya ni da kuka rena ne zaku gaya min maganar da ta muku?.ku kira Malik ku mishi irin wannan tambayar mana, ai wannan renin hankali ne!” Ya kashe wayar nan.
Sake kiran shi tai cikin burga ta ce mishi. “Amma a dokar kasa bai dace, Malik yayi haka ba, yana ina ne ma?” Zuciyar shi daya ya ce mata. “Yana hanyar Demark!”
“What! Yana hanyar kace?”
Tsaki yayi ya ce mata. “kije a miki wankin kunne!”
Daga haka ya katse kiran.
—-
Lalla Salmah
Mikewa tayi tana zaga falonta, sannan ta kira number Maidah tayi tana faɗin. “Malik zai zo kin sani kuwa?”
“Eh Maama, Nadrah da su Wahiba da Wahida suna ta aikin tarbanshi.”
“Kina ina?”
“Ina gidan Mama Jalilah!”
“Tasan Malik zai zo?”
“Eh nice na gaya maka mata!”
“Kai amma ke jakar ina ce? Wannan yakin neman kafa gwamnati ne ina ruwanki da gaya mata? Listn to me carefully, ki bar gidan yanzu, ki rufe maganar nan,like baki sani ba.”
A hankali ta kitsawa yarta kome sannan ra kashe wayar ta tura mata wani number, tana murmushin da ta barwa kanta sanin sanin ma’anar shi.

★★★
Yar kunama.
Cikin gidan Zulfa ta shiga, tare da mata yan sanda. “Ku duba daki-daki ku fito min da barauniyar nan yanzu!” Sanin halin yan sanda ba mutumci ne dasu ba yasa ta, fitowa tare da musu fyeduwa.
“Nace ba, uwar me za a duba dakin matan aure da tsofaffi? Ba dai nice na ci kudin mutane ba? Oya zoki kama ni!”
“Meye yasa kike ji da kanki?”
“A jini na yake, jin kai da tausayi. Shi kuma wnnan sa nake kimata nake karewa;” ta fada tana me saukowa daga sama!”
Har ta iso kasa, kwalar rigarta Zulfa ta kama! Black ya daki motar su. “Kai dan jagaliya! ” Kafin tayi wani magana, Dondurus ya ja rigar daya daga cikin yan sandan sai da ya b’alla botirin. Murmushi Zeeno tayi ta ce mata. “Kwalata ko mutuncin yar uwarki yar sanda!” A hankali ta sake rigar Zeeno, nufar gabanshi tayi ta ce mishi. “Kada ka kuma haka, kuskurerren lamari ne, cin zarafin macen da aiki ya kawo ta, amma kuma ta wani gefen yayi kyau ko babu kome ka nunawa yar sanda yadda ake ladtar da irinta.”
Shiga bayan motar tayi, suka bar gidan baki daya. “Ke baki da dangi ne?”
“Ina ce ku kuna da shi?” “Ke karamar Yar iskar! Me yawo da maza waye bai san karuwancin da kika yi ba?”
Lumshe idanunta Zulfa tayi, tana jin zafin kalaman da kurtun yar sanda take gayawa Zeeno!
“Madam kin zarafi ne, ki kiyayye kalamanki zata iya tuhumar ki da laifin keta alfarmarta.”
“An sorry Ma!”
“Ke kin san su waye suka tsaya min?”
Tana rufe baki, mutanen Malik suka dukar motar yan sandan.
“Officer! Wannan yaki ne da ake yin shi tsakanina da mutanen Malik wacece ke da zaki kama ni, duk kudaden da ake ihu akan shi naci banza………..😂😹
*Yasin ku tashi kaina da Comments ko na tafi sabon hutu*
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button