Cinikin Rai Book 2

Cinikin Rai Book 2 Page 19

Sponsored Links

Volume:19 guest.
Tun daga kanta har zuwa kirjinta, yake haukata, kamar zai cinye ta. Wani zazzabin karfi da muradi yake ji na kara taso mishi, bai san lokacin da ya damketa ba, domin yana jin kamar wani abu yana yawo a kanshi. Kanshi ya daura a tsakanin kirjinta, ya shiga murza kowani na shanun. Ita kan ba zata iya tantacce me take ji ba, abu ne da yake sabo a wurinta, ko wancan karon da ya faru na shanunta ne yayi ta azabtar da ita da ciwo, yau kan da alamu, sun dauki sakon Malik, domin ita kanta bata san lokacin da ta biye mishi ba, suka shiga haukata junansu da wani irin zazzafar kauna, ita kanta bata san lokacin da take biye mishi ba, sai dai wannan karon kamar farkon faruwar kome, domin sai da ya kai yana jin motsin lafiyarshi, amma kuma yana zame wandonshi, yaji kome ya tsaya cak.
Da sauri ya mai da wandon, amma ina wannan karon ma babu wani respon domin taki daukar wuta balle chaji, ita dai yarinyar da ya d’agowa hankali ita ya samu yayi ta, murzata yana kara matseta, sai da ya ga jikinta yana rawa, ya kyaleta. Yana rungume da ita, a bangaren Zeeno kuwa gani take ai iya wannan shi ne auren, kwantar da ita yayi a kirjinshi tana sauke ajiyar zuciya, kanta na daidai kirjinshi. Tana jin yadda zuciyar shi yake bugawa, lumshe idanun tayi tana jin abin har tsakiyar kanta. D’ago ta yayi a hankali ya kalli fuskarta, a hankali ya kama fatar bakinta yana tsotsa. Ba zai ce ga yadda yake ji ba, amma abin da daure kai. Haka yana lura da ita har barci yayi gaba da ita. Sannan ya ajiye ta, ya nufi ban daki wanka yayi ya fito ya shirya, ya nufi ban daki.

Bata farka ba sai wurin karfe biyu. Wanka tayi ta nufi dakinta. Da hanzarinta ta bar gidan. Tare da nufar cikin gari. Tsabar ta samu sake bata dawo gidan ba sai bayan isha. Ta tawo da Chu-chu, dakin Malik ta leka ta ga baya nan, sai ta wuce na ta, bata yi tunanin kiranshi ba.

Har wurin karfe goma tana zaune, Chu-chu tana barci, ganin ba zai dawo ba yasa ta shiga ban daki tayi wanka, ta kwanta. Tare da tunanin dama haka yake baya dawowa da wuri ko kuma yau ne bai dawo ba. Har barci ya ɗauke ta bata san kome ba, kuma tun bayan fitar ta Elbashir ya zo aka ce mishi basu nan. Ya tambaya yaushe ta fita aka gaya mishi, Malik fa? Suka ce ai yakai sati idan ya fita baya dawowa Sai dare, wani bin asuba. Shiru Elbashir yayi, ya koma da isha da ya dawo aka ce tana ciki, ya ce Malik fa suka ce bak dawo ba, don haka koma bai shiga ba, yayi parking ya zubawa Sarautar Allah ido. Yana son ga da gaske ne Malik baya dawowa gida sai tsakiyar daren.

Abin mamaki yana wurin zaune a cikin motar har karfe biyu da arba’in da tara, Malik ya dawo. Bude motar shi yayi ya nufi motar Malik. Don ranshi yayi mugun b’aci, budewa yayi ya shiga suna kallon juna. “Ai kai ba yaro ba ne, don haka gobe xan zo muyi magana;” ya bude motar ya fita, Malik bai kawo kome a ranshi ba, suka shiga cikin gidan.
Yau kan yana son ya kwanta a jikinta, don haka yana shiga cikin gidan. Dakinta ya wuce sai dai kash, ganinta dauke da Yarinya yasa shi juyawa ya koma dakinshi.
Da safe, tana idar da sallah asuba. Ta fita tare da hado kayan tea ta ajiyewa Chu-chu. Tana idar da sallah ta haɗa mata abin karyawan ta sha, sannan ta koma suka kwanta.
*01:30am*
“Na gaya maka Malik, duk abin da ya fito bakina zan gaya maka, ai na san dole zan iso wannan matakin amma ba zan tab’a lamuntar ka zalunci Mareniya ba, me ta maka? Akan me zaka na tsalleke matarka kana zuwa zaman jinyar Yarinyar da Uwarta take son ganin bayanka?”
“Bashir ina ruwanka da ni? Gidana ne i have right da zan tafi ko yaushe na dawo ko yaushe. Ina ruwanka da ni?”
“Ok shi yasa kake dawowa tsakiyar dare ko da asuba? Shi yasa kake yadda kaso don tana gidanka? Aurenta kayi ko alfarma ka mata? Gata nan aurenta kayi ko alfarma ce kayi mata? Batun Maidah ta dawo gidan nan bai taso ba”
“Gida na ne, ina da ikon kawo duk wanda ya min, kuma ka fita daga cikin harkan gidana!” Daga haka ya nufi hanyar waje. Bata san meke faruwa amma ganinsu kowannensu ya dauki zafi yasa bata iya cewa kome ba. “Zan ajiye maka aikinka zan koma wurin ahalina! Domin na gaji da makotaka da zububinka ba zan iya daukar zunubin marainiyar da bata san wacece ita ba;” daga haka ya ajiye mishi takardun a tsakiyar center table. Ya juya ga Zeenobia. “Kiyi hakuri!”
Daga haka y bar gidan, akan idanun Malik ya wuce abinshi. Sai da yaji ran shi ya b’aci, taya Elbashir zai bishi da kafar shi zai dawo. Tun daga ranar bai kuma jin duriyar Elbashir ba. Da gasken gaske Elbashir yayi fushi.

Kwana uku tsakani aka sallame Maidah, kai tsaye gidanshi Lalla Salmah ta kawo ta. Kafin wannan ranar, tana kwance ta ji ana ta buge buge dake ta maida Chu-chu gida. Fitowar da tayi ta ga dakin da yake kusa da na Malik ake buge bugen. Bata kawo kome ba, ta leka gyara ake a dakin don haka ta juya, da safe da suka hadu tunda zuwa yanzu ta fahimci baya kwana a gidan, a hankali ta koma daki ta cigaba da kwanciyarta. Haka a cikin kwanakin aikin. Ranar da zasu zo gidan da safe ya biyo ta dakinta ya ke gaya mata. “An jima Maidah zasu zo, ita da Uwarta wancan dakin da yake gaban nawa zata zauna.”
Cikanka bata ce mishi ba, ya gama maganar shi zai fita ta ce mishi. “Amma kasan ma gaji da zaman jiran maka gidanka? Zan koma rayuwata ta baya, idan tazo sai ta cigaba da kula da kai.”
Kallonta yayi ya ce mata. “Kishina kike?” Dariya yayi sannan ta ce mishi. “Allah ya kiyayye nayi kishinka, yadda ban sonka ba bana fatan na soka”

Wannan abin ya bashi haushi, don haka ya zuba mata idanu. Izuwa yau da su Maidah suka zo gidan, tana zaune a falo suka shigo suna hirar su, alamar farin ciki da jin dadi. Ganin Zeenobia yasa su shan jinin jikinsu. “Sannunku!” Ta faɗa rai a sake. “Yawwa!” Lalla Salmah ta amsa mata, rai a b’ce domin ta tsani ganin Zeenobia.
Daki suka wuce dake ya gaya musu. Suna shiga uwar ta cewa Yar. “Zama ba naki ba ne, dole ki shiga jikin Malik. Ki nutsu ki fahimci yadda zaki kwace shi kada ki dake ta fahimci kinyi nisa sai an fara maganar aure na gaya miki. Ina son ki mishi yadda zaki raba su.”
Ita kan Baiwar Allah bata san kome va, haka suka gama kulle kullensu. Suka fito suna kallonta a wulakance.
Koda Maidah ta dawo, shiga kitchen tayi ta shiga bada umarnin abin da za a girka a kaiwa Malik office, domin ta shirya tsaf zata kore Zeenobia. Ita kam Zeeno bata wani damu ba, domin Malik din ba damunta yayi ba, balle har ta saka a kanta.
Wannan yasa baki daya ta bar falon ta koma dakinta, wurin karfe biyu na rana aka kaiwa Malik abinci, bayan Maidah ta tabbatar da inda yake, bata yarda ta ce mishi ita ta saka ba, domin da ta kira shi a shagwabe ta ce mishi. “Dadi kana iya?” “Ina office!” “Ok dama na kira naji lafiyarka ne. Kuma za a kawo maka abinci!” Bata bari yayi magana ba ta kashe wayar.
Ana kai mishi abincin, abokan shi da suke tattauanawa suka zata abincin amarya ne, don haka ko sakawa a bakinshi bai yi ba, suka cinye abincin.
Kafin ya dawo an mishi tuwon shinkafa miyar ugusi da yaji nama da ganda, stockfish, dryfishi. Da zallar namar rago. Tunda Zeeno ta fito ta ga a tare suke aikin da Chef bata ce kome ba, ta koma gefe ta hada tea da Cookies, ta fita sam bai dame ta ba, har bayan isha da ya shigo gidan ya same tana zaune. Ta sha kwalliya kamar me zuwa party. “Sannu da zuwa dadi! Ya aiki?” A ranshi bai yi na’am da ita ba, amma don ya saka Zeeno ta zo gare shi ya ga ya samu opportunity da zai ga yadda zata dauki sabon relationship dinsa da Maidah.
Sai dai a wannan gaɓɓar ya fadi, domin Zeenobia bata cikin mutanen da suka bar matsalar su har wani ya sani, shi yasa koda ya wuce bai ganta a falon ba, sam bai yi tunanin kiranta ba, ya amshi jakarshi ua shige dakinshi. Yana watsa ruwa ya fito ya nufi wurin abinci. Maidah ta zuba mishi, ya tunda ya saka abincin a gaba Zeeno yake son gani bata fito ba,haka yayi ya hadiye abincin kamar yana cin guba, sai da ya kusan gamawa ta fito tana, latsa wayarta tana sanye da 3qrts. Kanta babu dankwali, kitson da tayi kalaba ce, ya sauka har bayanta. Daya ta mishi ta sake yar murmushi ta ce mishi. “Kawo ya aiki?” Daga haka ta wuce kitchen. Ta hado tea ta dawo falon ta zauna, baki daya tunda ya ganta ya susuce. Cire hannunshi yayi cikin abincin ya wanke, sai da ya goge sannan ya nufi dakin karatu da yake falon. “Dadi inzo na tayaka hira ne?” “No ga Auntynki kuyi da ita.” Ya saci kallon Zeeno a ranshi yana mamakin halinta.

Haka suka zauna bayan ya bar falon, Zeeno ta kira Hafsy suka shiga hira. “Ke akwai abinda zan kawo miki, na je wani gida kwalliya ake hirar abin shi ne na saya miki zaki sha ko?” “Eh tow bari na gani ko!” “Ke ance na jin dadin aure ne, ina son ko gwada ne ko dagaske!”
“Ke!!!” Ta mike tare da nufar dakinta, ta lailayo asharia ta ruga mata, ta ce mata. “Bana son iskanci ba zan iya bawa wannan tsohon jikina ba, na gaya miki!”
“Wallahi sai na gayawa Ammyn idan ta dawo ”
“Ke wasa nake miki!”
“Yaushe kika fara wasa ban sani ba?”
“Kinga wallahi wasa nake, don Allah kada ki hada ni da ita zata ga kamar ba biyayya na mata ba, sannan ki fahimta wallahi ba zan iya bashi kaina ba ne. Da kunya na bashi kome daga gare Ni! Don Allah kada ki gaya mata.”
“Ban tab’a sanin ke wawuya ba ce sai yanzu, Zeenobia wallahi baki da hankali baki daya, hakkin aurenshi kike hana shi. Lallai Allah sai ya kama ki, kuma kika mutu a wannan yanayin wuta zaki wuce.”
“Hafsy!”
“Dalla yi min shiru, kamar tasan Allah zan zo ki gaya min illar abin da yake jikinshi? Shugaba ne guda, wallahi idan nice ke mike kafa zanyi nayi ta haihuwa da shi.”
“Amma ya zanyi?”
“Ki tafi wurinshi, hala ma a dakinki kike kwana?”
“Hmm!”
“Na shiga uku, Zeenobia baki tunanin wata ya kwace miki shi?” “Tow ance miki Ina sonshi ne da haka zai dame ni?”
“Sakarya kawai, sai kiyi ai!” Ta kashe wayarta don haushi. Duk da Maidah tana bakin kofar, ta saka kunnenta. Murmushin mugunta tayi, “Mu zuba mu gani waye zai yi nasarar mallakar Malik Menk Jordan!….
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button