Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 2

Sponsored Links

Mai_Dambu
BOOK ONE
002
Tsam tayi da ranta tana kallonsu, kafin ta mike tana faɗin. “Zanje nayi nazari amma yanzu kan ba zan yanke hukunci kai tsaye ba.” Kallon juna suka yi, ai ba haka Mr Amjad ya gaya musu ba, ya gaya musu rauninta ne al’umma da Abbas, amma bai gaya musu cewa tana da kafiya da ra’ayinkanta ba. Har ta fita a cikin office ɗin, babu wanda ya samu arzikin ce mata cikanki domin baki daya yanayinta ya sauya. Tana fita daga office ɗin, kiran Mr Amjad MD na kamfanin yayi ya ce masa. “Yarinyar nan bata yarda da matsayin da muka bata ba, asalima taki amsa fa, sannan nayi amfani da rauninta na gaya mata amma yarinyar taki amincewa sai tayi tunani.” Ajiyar zuciya ya sauke na cikin wayar ya ce. _Ka da ka damu, haka take zan ji da kome!_ gyara zama MD yayi ya ce mishi. “Kuma dole sai ita ne? Babu wasu yan matan ne?” _Itace kawai zata mana yadda muke so, ita ce zata iya daukar wasu abubuwan, kasan me? Ita din zamu yi amfani domin cimma manufar a yanzu gani muna tattaunawa da wasu kamfanoni amma babu alamar zasu amince, don haka ka lallabata domin zata mana amfani!_ “ok Sir!” Ya kashe wayar da sauri ya dauki wayar landline na kamfanin yayi kirà da shi. “ku kira min yarinyar nan!” A lokacin da kiransa ya isa office din Mss Mary da sauri ta fito ta fara niman Zeenobia. Kiran dakin tsaro tayi ta ce musu. “Ku duba min Zeenobia ta fita ne?” “Ok ma” kamar minti uku suka ce mata, “tana cikin elevator nan minti goma zata iso” “okay” ta nufi kofar elevator ɗin ta tsaya, sai kallon agogon hannunta take, tana jin kamar har lokacin zai wuce Zeenobia bata iso ba. Minti goma ciccib kofar yana budewa. Ajiyar zuciya ta sauke. “Zeenobia inji yallabai wai ki koma, tuntuni nake jiranki.” “Amma ai mun gama magana da shi me kuma yake bukata?” “Please muje.” Haka ta koma cikin elevator ɗin.
***
Daga cikin yan majalisu da suke karkashin jam’iyyar PKO, power Keivroto Own, tare da yan jam’iyyar CDL, civilian democrats labor, sai wasu manyan masu ɗauke da kamfanonin ƙasar musamman yankin Keivroto, gefe guda kuma wasu dattijai ne na musamman da suke zaune cikin shigar alfarma. Tare da wani dattijo da ya haura shekaru hamsin da wani abu a duniya. Shiru dakin ya dauka, sai kallon juna ake cikin fushi da fusata. “Dake an mai samu sakarkaru, babu wani labari daga ɓangarensu fisabilillahi a haka za a zauna lafiya? Tuntuni Khuldu Jahid Khan yake nan zaune, a ƙalla a girmama shekarunsa taron bunkasa tattalin arzikin Keivroto zai tafi amma aka dakwafar da shi a nan, anya akwai adalci cikin lamarin ku? Nace akwai adalci? Gaskiya duk wanda ya shirya wannan taron, ya shirya taron shan shayi ne domin Malik…” Bude kofar da aka yi yasa bakisaya suka mai da hankalinsu kan kofar, haka yasa shi kansa azagwaigwaidu da yake magana yayi shiru, ajiyar zuciya wasu daga cikin mutanen da suke wurin suka dauke, cikin girmamawa suka mike. Hatta masu hayaniyar da jami’iyyar adawa ta CDL su kansu mikewa suka yi, ban da Khuldu Jahid Khan da yake zaune fuskarsa bata yi na’am da zuwan mutumin ba, dauke kai yayi yana rike da sandar dogarawa. Dauke kai yayi yana kallon gefe har mutumin da ya shigo ya samu wuri ya zauna, sannan ya ce. “Ayi min afwa kusan dukkan mu, babu wanda zai so b’atawa wani lokaci. On be half of Khalquz Zaman muna bada hakuri.” “Yallabai Elbashir Jamal Arab mun yi hakuri, me yafi haka a gayawa Mayor muna jiransa an shirya mishi shagali ba musamman.” Murmusawa yayi ya ce. “Ayi hakuri Mayor ba zai samu halatta ba….” “Taya zai samu halartar taron da kowa da kafarsa zai zo? Shi kuma a keken guragu?” Inji mutumin ɗazun da yake ta b’ab’atu. Murmushi Elbashir Jamal Arab yayi sannan ya ce. “Da alamu ba karamin shan kaye kuka yi ba, da har yau baka manta rad’d’in da ya same ku, al’ummar Keivroto sun tsaya ka’in da na’in sun zabi abin da zai gina su ne, ta fuskar Kasuwancinmu, don haka abin da ya kawo mu nan shi ne, a tattauna a wuce wurin ina da trip to China!” Zuciyar Khuldu Jahid Khan ya buga, ‘ba dai wani abu Malik Menk Jordan zai kuma kullawa da gwamnatin kasar China?’ wannan wani irin mutum ne? Wani irin sa’a gare shi? Dole na ga karshen Malik Menk Jordan.
“Prime minister, ka saka baki Malik Menk Jordan ya barwa wasu daga cikin yan kasuwa damar yin kayayyakinsu a kasar nan, Malik Menk Jordan bafa dan kasa ba ne; kowa yasan cewa bakon haure ne, sannan Shugabana Khuldu Jahid Khan yana da shaidun gani da idanun da suka tabbatar Malik Menk Jordan dan ta’adda ne da yake, amfani da dukiyarsa yana kashe mutane, tare da tilasta musu karban bashin da zasu kasa biya.” Mutumin da aka kira da prime minister ya zubawa Elbashir Jamal Arab idanu ya ce. “Elbashir Jamal Arab ya haka? Abin da yake faruwa kenan?” Murmusawa mishi yayi sannan ya ce. “Mr prime minister dayawansu a nan, sun san Malik Menk Jordan, shima kuma yasan su, wasu kuma sun yarda da shi. Shima ya yarda da su. Malik yana da goyon bayan yan majalisu kusan 108, yana da sahalewan yan jam’iyyar PKO, sannan yana da hadin gwiwa da kwamishinonnin jahar nan, uwa Uba ta fuskar Kasuwancinmu muna da kyakkyawan alaka da wasu ƙasashen idan ayi dubi da yadda garin Keivroto city yake gabbatar ruwa. Mr prime idan har aka ce za a fito da abin da suke bukata, ai Malik bai yiwa mutanen da suka yi nominations dinsa izuwa matakin Mayor ba, taya zai yarda da muradunsu bayan shima yana da tasa muradun?” Mikewa Azagwaigwaidu yayi cikin fushi ya ce. “Prime minister a sake kidayan kuri’a Yallabai Khuldu Jahid Khan ya ci ba Malik Menk Jordan ba, mutumin banza kawai, dan luwadi waye bai sani ba, kaf gidansa babu Y’a Mace, wanda kowa yasan cewa Yallabai Khuldu Jahid Khan gidansa mata uku ne, Yara mata babu wanda yasan adadinsu, ka gayawa maigidanka kar yayi asarar kwayayyensa a ta baya, ya nimo ko karuwa ce, ta haifa mishi hana gori.” Gyara zaman tie dinsa Elbashir yayi ya zuba masa idanu, kafin ya ce mishi. “Na maka uzuri ni tarbiyyar Malik Menk Jordan ne, ya haramta min cin zarafin kowa.” Jin haka mutumin ya buɗe baki zai magana, Mr Khuldu Jahid Khan ya ce mishi. “kul!” Shiru yayi sannan ya cigaba da cewa. “Me yasa Malik ba zai yi show up ba?” Gyara zama Elbashir yayi ya ce mishi. “Meye matsakarka da show up dinsa, kome yana tafiya yadda yake, Kasuwancinmu da siyasar mu, tow kai me kake bukata anan?” “Wadancan mutanen!” Ya nuna mishi mutanen kusan su goma a zaune. Tabbas sun zo kwanaki uku da suka wuce, akan Mayor Malik Menk Jordan ya saka hannun jari a kamfanoninsu, sannan zasu mishi biyayya. Wato da suka ki amsar buƙatarsu shi ne, bari su dawo nan. Dariya yayi ya ce mishi. “Khuldu Jahid Khan!” Rintsa idanun yayi. “Amma Elbashir baka da kunya shugaban mu kake kira kamar, abin wasan ka?” “Kai kare bada kai nake ba, da ubangidanka nake, idan ka sake na kuma jin tashin muryanka sai na datse harshenka” juyawa Elbashir yayi ya cigaba da cewa. “Saura kiris da kunyi kuskuren amsar, dukiyar Mayor Malik Menk Jordan, da sai kun yi danasani, a yanzu ma ba kyale ku zamu yi ba, zaku biya zunubanku. Sannan shi wanda kuka daura yarda akansa bai gaya muku karon battarsa da Mayor ba ne? Ya gaya muku sanadin da yake dogarawa da sanda, Mr prime minister na gama jawabi, babu wani dan kasuwan da zai bude wani kamfani matukar Mayor Malik Menk Jordan yana numfashi ba zai lamunci haka gasa ba.” Yana mikewa, yan majalisunsa suka mike suma suna masu taka mishi baya, dayawan basu san Malik ba, kuma duk matsayin da suke da taimakon sunan Malik suka isa wurin, Idan aka ce maka Mayor Malik Menk Jordan tow, hantar sadaukan maza bari take. Domin tsaf dattijan Keivroto ba karamin tsoronsa suke ba, uwa uba ka tab’a mishi dukiyarsa sunanka shekakke.
Haka suka fito tare da raka Elbashir Jamal Arab airport, sai da ya haura jirgi sannan suka juya, wannan shi ke kira Powerful. Domin iya Elbashir yana taka muhimmiyar rawa koda Malik baya wuri.
Bayan fitar Elbashir. Jifa da kome na dakin taron Mr Khuldu Jahid Khan yayi, yana faɗin. “Sai na kashe shi, shekaru arba’in da shida kenan ina niman hanyar da zan kashe dan shegiya bakon haure, ɗan cirani!” “Yallabai wannan al’amarin, kasan cewa babu wanda ya isa karya Malik, kuma koda kuwa za a hada sama da kasa ne, babu wanda zai iya karya shi. Sannan idan kace zukatan al’umma zaka saya, ba zaka tab’a sayan tsoron da yake cikinsu ba, su ba zaban Malik suka yi ba, labarin abin da yayi kawai suke dubawa. Idan har akwai hanyar da zaka bi dole ka bi. Sannan rigimarka da Malik kar ya shafi Kasuwancin wadannan bayin Allah domin basu ji ba, basu gani ba.” Tsamo tsamo Mr Amjad yayi kutumar Uba, wato labarin Malik da yake ji, ba kome bane sai da Elbashir yazo yasan waye Malik shi baya tare su, amma anyi mishi abin da yake bukata. “kuma da ace Malik ne yazo da kansa, kana tsammanin ba wanka zai yi da jinin Daylam Yunis ba, kai ya dace ka koyawa mutanenka girmama kai, su daina zakewa. Bani manta shige asirin baya idan Malik yazo da yaron nan, baya tab’a yin tari matukar ba Malik ne ya bashi iznin yin haka ba, kai kuma saboda dalilinka kasa kowa ya zama me damar magana, kai idan har baka yi a hankali ba, sai ka ɗaure kanka. Kayi kokarin niman hanyar da zaka kadda Malik ni kuma zan tsaya maka har sai ka kadda shi. ” “Shi kenan.” Ya fada yana kurban ruwan zafi. Fita prime minister yayi, kiran wayarshi aka yi, p.a dinsa ya mika mishi. Jikinsa ne ya dauki mugun rawa, ya kasa dauka ji yake kamar zai fadi. Har suka kusan isa motarsa sai da ya shiga cikin motar ya dauki kiran. “Ranka ya dade.” _Kayi kuskure Prime minister, sauka lafiya_ kashe kiran aka yi, wasu mutane da ba asan daga ina suke ba, suna zuwa suka budewa janye p.a da driven, suka budewa motar prime minister wuta, sai da suka tabbatar da ya kama da wuta, sannan suka wuce a babur dinsu.
Lokacin dasu Mr Amjad suka fito, ganin motar prime minister duk da jami’an tsarosa bai hana a kashe shi, an tashi motar da wuta ba, take duk suka juya kowa ya cikawa bujensa iska, wannan tashin hankalin ba karamin firgita Mr Amjad yayi ba dole tasa ya koma kamfanin S digital art. Yana shiga bai tsaya parking me kyau ba, ya nufi cikin kamfanin, a firgice yana ji kamar ya tsula fitsari a jikinsa. Kai tsaye elevator ya shiga, sai da ta ganshi cikin ya tabbatarwa ya tsira, ya sake ajiyar zuciya. “Wannan wacce irin masifa ce, taron dangi akan Mayor Malik Menk Jordan ba shi ne mafita ba, tabbas.” Wayarshi ce ta yi gunji, sai da ya zabura, kamar zai gudu kafin ya tuna ai wayar shi ce take tsiwa domin da zasu shiga taron ya sakata a gunji. Dauka yayi yana faɗin. “Hello!” _Kada ka karya da abin da ya faru, ai dama ba iya nan ne shirin ba. Ka fahimta ko_ “Ni wallahi da zaka cire ni a cikin wannan lamarin da naji dad’i, Tunda aka iya kashe babban minista akan idanunmu, bamu iya me kake tunanin zai faru? Ku shafa min lafiya” ya kashe wayar, yana isa floor 9 ya bude kofar, jikinsa yana rawa ya nufi office din MD, kamar wanda aka koro shi ya isa office din, “ku bani ruwa ina jin ƙishirwa ne” mika mishi ruwan Salim yayi, sai da ya shanye ruwan tass, ya nime kari. “Sir lafiya?” Ajiye goran yayi ya ja kujera ya zauna, duk suka zuba masa idanu. “Zeeno baki tafi ba ne?” Mikewa tayi tana faɗin. “Eh Yallabai Amjad. ” Sauke numfashi yayi ya ce. “Hussain wani matsayi take bukata ma?” “Security service!” “Ya miki haka?” “Eh yallabai!” Kallonta yayi ya ce mata. “Zeeno naso na baki matsayin da zaki na, nimo mana manyan mutane suna saka hannun jira ni a kamfaninmu, na sha gaya miki ke kyanki shine jarinkie, akwai mata dayawa da suke niman matsayin da kika taka, Zeenobia idan har kika amshi security service, harajin da gwamnatin jahar Keivroto take amsa a hannunku duk wata ba zai kai ba, zaki cigaba da bangar siyasa ne? Shekarunki nawa?” Sunkuyar da kai tayi kasa ta ce mishi. “Ashirin nake!” “You see! Kiyi amfani da damarki, akwai Mss Mary zata hadaki da Dauduwa, ta kware a fannin sauya salon mutum da fasalinsa, albashinki dala dubu dari uku, kudin US. A cikinsa zaki samu dala dubu hamsin ki biya kudin haraji, me ya fi miki.” Juya idanu ta yi, ta ce mishi. “I,m satifai, idan har zaku bani dis moni, I kan do anitin!” “Yes good gurl yanzu ya yarda zaki iya, tunda kika yi magana da turanci, Hussain bani list na sunayen nan!” Ciro mishi kundin yayi ya mika mishi, a hankali ya bude yana kallon shi. “Ikon Allah kace har ka tura baki daua saura daya ne kawai ya rage?” “Yes Chairman na tura baki daya, wanda ya rage na Mayor Malik Menk Jordan ne!” Sarawa kanta yayi, ta dafe da karfi. “Lafiya!” Suka tambaye ta, “lafiya lau! Zan tafi.” Mai da kundin yayi ya ce mishi. “Ajiye akwai dayan fa na baka, bani na bata!” Bude drower din yayi ya dauko mishi wani kundin. “yawwa Dauduwa zata gayyace ki, ga wannan su zaki fara jaraba sa’arki akansu.” Juya Idanunta tayi ta ce mishi. “Wancan na farkon fa da ka mayar da shi?” A razane ya ce mata. “Wancan ai konawa zamu yi, kai Salim dauka ka je ka kona, kunna mana tv ta ji abin da yake faruwa, sunan da yake jikin wannan kundin bala’in duniya ne da tashin hankali ke yarinya ce, da babu ruwanki. Kada ki tsoma ranki da zuciyarki cikin wannan lamarin. ” Murmushi ta yi ta ce mishi. “Tow amma kada ka kona, bari na ga yadda zan ji da wadannan zan dawo kansa.” “Anya zaki iya?” Kunna tv aka yi ta juya tana jin labarin. _A yau garin Keivroto city ya tashi da mummunan al’amari da rabon a fuskanci haka tun shekaru talatin da suka wuce, lokacin kashe Mr Jahid Khan mahaifi ga Mr Khuldu Jahid Khan, me manyan kamfanonin hakkar ma’adinai, kuma Uba ga jami’iyyar adawa ta CDL civilian democrats labor, bayan nan ba a kuma samun tashin bom haka ba, sai dai shaidun gani da idanu sun ce wasu matasa hudu suka gani da babura, inda suka sauka suka idda mugun nufinsu, tare da kashe Mai girma Prime minister, a halin yanzu ana danganta mutuwar da Shahararren attajirin ɗan kasuwa, mai girma Mayor Malik Menk Jordan, wanda aka tabbatar da cewa anyi taron nan ne domin a kawo karshen mulkinsa inji wata majiya. Idan baku manta ba, Mayor Malik Menk Jordan shine mutum na farko da yake da kashi casa’in a na kamfanonin a garin Keivroto city, sannan yana da sahalewan shuwagabannin Kananan Hukumomin ɗari da shida, bayan nan dan kasuwa ne da ake zarginsa da hamdama da babakere, ga abin da wani ganau yake fada_ sako wani murya suka yi. _Gaskiya idan ka cigaba da barin Mayor Malik Menk Jordan yana abin da ya gadama, wata rana Keivroto city zata zama makabartan binne mutane amma ace babu wanda ya isa taka mishi burki sai abin da yaso, fisabilillahi taya za a rayu?”_
Kashe tv Salim yayi ya ce. “Da ina jin labarin Mayor daga nesa ne amma yau da naji ya kashe prime minister na yarda mutumin nan shaidani ne, Zeenobia Kinji ko?” Kallonsu tayi tana faɗin. “Ya naga kun razana, shi ne ya baku tsoro? Ni kuma gani nake ba kome ba ne.” “Ke ki raba kanki da masifa Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne……
Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Top-notch
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI……*
Beauty and the beast♡

Mai_Dambu

Leave a Reply

Back to top button