Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 13

Sponsored Links

CINIKIN RAI….13
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>

*Trust me, you are the one,

whom my eyes seek, whom my

heart finds, whom my destiny

wants, whom my mind reminds

me of, whom my life ill sold,

whom I really depend on,

whom I wake up for each and

every morning, whom I love

more than anything, more than

anyone, and… I will do

whatever it takes to have you

in my arms forever…..*
<<<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>
Ware idanu Amjad yayi, yana son tayi suna ta shahara, yadda zai samu damar shigarta Kasuwancin Malik ba wai ta shahara da yan iska irinsa zasu na kawo mata farmaki ba, shi yadda zata hadu da Malik yayi koma. “And ina son ka saka idanu akanta, dole zan dawo” “Da ina ga kayi hakuri da bukatarka, ita ba a mata dole, domin.” Shako wuyar Amjad yayi yana zare masa idanu, “karya kake, yadda ta fito ta nunawa duniya ita karuwa ce, dole na tafi da ita, so nake naji ina nutsu a jikinta, don haka na gaya maka idan ba haka dole na sha jini da ruwa lokaci guda ” yana fadar haka ya ture Malik yayi tafiyarshi. Rike wuyar shi yayi yana kwashewa Akram Jafar Wazir albarka a zuciyarshi. Yana fita ya sauke ajiyar zuciya yana faÉ—in. “Tsinanne dan iska, ba zaka bata min dagiyata ba.”
★★★
A masife ta isa gida, shi yasa baki daya ta ki kula kowa, asalima bata kaunar magana. mika mata sako Abbas yayi ta amsa ta wuce.
,Wkakaasaj Har tayi gaba, sai kuma ta ce. “Sakon me?” “Ina son ki duba, ne iyayen Hibba Yin cYuue a tura me ake bukata” ya fada yana juye-juye. Kamar zata yi kuka ta ce mishi. “kana nufin sunce ka tura manyanka?” Gyada mata kai yayi yana rike rigarshi.
“Okay Angon Hibba!” Ta fada tana barin wurin, bata ce bata ji dadi ba, amma kuma zuciyarta yaki accepting din abin yake faruwa. Baki daya ta manta da wani dan iska can.
—–
Tsohon store, Zulfa ta shiga. Haska torchlight din tayi, a hankali ta fara buÉ—e wasu kwalayen. A hankali tayi ta sauke kwalayen tana faman bincike, tayi karatun nan ne domin fitar da gaskiyar da Hukumarsu ta kasa fito da shi, koda kuwa ace zata cilla rayuwarta cikin kasada ce, ta shirya haka domin baki É—aya rayuwarta akan wannan binciken zata kare shi. Buga mata kofa aka yi ta ce daga ciki. “Sajin kai ne?” “Eh Madam, wani aiki na kawo miki.” “Shigo” ta fada tana kallon kofar, a turo kofar yayi ya shigo ya sara mata, sannan ya mika mata wasu files, yana faÉ—in. ” Madam gashi a wani binciken da nayi, a tsohon Office din mu, don bana manta wannan case din,koda ban da cikakken tarihin faruwar abin amma lokaci zuwa lokaci ana yawan tadda case É—in domin a tattauna a akai similar kamar kisan prime minister.” Amsa tayi tana faÉ—in. “Ka kyauta min, amma ba a kan case din nake ba yanzu, sai dai kuma dole zan bibiyi case É—in. Daga baya”

“Tow Madam” ya ajiye ya fita, ta cigaba da binciken ta, har zuwa abin da take nima sai dai bata samu dukkan abinda take bukata ba, domin har lokacin sallah yayi, haka ta mike ta fita, sai bayan ta idar da sallah, ta tura aka kwaso mata binciken, ta cigaba da a cikin office É—inta, yadda zaka fahimci tasan aikinta, tana binciken tana rubutawa, kowani single words, tana adana shi, har ta gama binciken wasu file abu daya ta samu Malik Menk Jordan.

Tattara files din yayi ta ajiye su, me yasa sai shi sunansa yake fito mata, baki daya ta kasa fahimtar kome. Koda la’asar yayi, a Office É—inta tayi sallah tana idarwa IGP yana kiranta. Tura baki tayi faÉ—in ” Allah sai ya saka min sumbatar da kayi min” dauka tayi tare da daure fuskartar kamar yana gabanta. “Zulfa!” “Meye!” shiru yayi kafin ya ce mata. “Allah ya baki hakuri! Hmm ina kewarki” “Ji min gulma, ina ka bar Aunty Fannah?! Kaga idan baka da abin yi ina da shi sai an jima.” “Kinga don’t hanging my call,.” “Hmm!” Ta ce. “Ok me yasa baka tsorona?” “Saboda Idanuna yana hango min yar shekaru ashirin da bakwai a gabana, wacce ta manta yayi ta kara shekarun haihuwarta.” Dafe kai tai tana faÉ—in. “Allah na manta, dake!” “Dake kin sakawa kanki aikin da bana ki ba? Na gaya miki ni dake ki ajiye wannan case din ko?”

“Akhi!” Ta kira sunanshi a hankali, kafin ta ce mata. “Ni na gaya miki, ki ajiye saboda wasu dalilai, ni ma haka nayi ta wahala karshe, na hakura idan dai akan Malik ne ki ajiye domin akwai abubuwan da baki isa saninsu ba, dole sai anyi amfani da lokaci.”
Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, “amma me yasa kace na hakura, bayan akwai dubbanin al’ummar da suke zubda kwalla saboda su!” “Saboda shi ma akan daidai yake, a duk lokacin da kika fahimci waye shi, ba zaki zargi dalilin shi na kananainaye kome ba, sai ma tsoron Allah ya shige shi, Zulfa ki daina binciken nan haka, amadadin haka ki bada hadin kai, next month a daura auren sai a sha biki, kafin nan da wata hudu kina dauke da little!” “Zan kashe wayar fa!” “Tow doguwar mace me kayan marmari!” Katse wayar tayi, tun fil-azal Yasir bai da kunya inda kunya tabi bawan Allah nan bai bi ba, bata mantawa lokacin da dangin Mahaifinshi suka ce ya auri Fannah kiri kiri ya gaya musu. Fannah idan ta samu wuri kiba zata yi, kuma shi baya son macen da zata yi kiba. Shi Zulfa yake so domin ba zata yi kiba ba. Akayi ta rigima da shi kafin ya aure ta, ko bayan auren babu ruwan shi, ya ce ai sadakin shi ya biya, kuma zai more kayanshi, don haka ko da zaman yayi zama Allah bai albarkace su da haihuwa ba, amma shi yasan cewa matar da zata haihu mishi Zulfa ce, don haka yake ta bibiyarta dan rigima irinta shi. Duk wanda ya fito yana sonta koranshi yake yana fada mishi, ai matar shi ce bata tare ba ne, amm da aurensu.
Gyada kai take tana karawa, domin ta fara gajiya da halinshi. ‘ki fitar da miji kiyi aure’t tsaki tayi a fili, tana faÉ—in. “Mara mutunci ba barina zai yi nayi aure ba.”
★★★
Keivroto International airport.
Lalla Salmah ce tsaye da Maidah, wacce tayi sanyi, kamar ba ita ba. Baki daya bata son zuwa Demark. “Baby an gama kome, Allah ya tsare, kiyi kokarin niman number Malik. Ina bukatar shi urgent kuma saboda ke!” Gyada kai tayi har zata wuce ta dawo da baya ta ce mata. “Maama, me yasa baki da number shi?” Murmusawa mata tayi tana faÉ—in. “Malik yana da number mu, amma mu bamu da na shi, Malik yana tare damu amma zaku fahimta.” Gyada kai tayi tana faÉ—in. “Maama me yasa kike son na shiga rayuwar Malik” d’ago kai tayi tana kallon Maidah, “we need powerful! We need everything! We need Malik Menk Jordan!” Lumshe idanun yarinyar tayi sannan ta ce mata. “Zan samo miki Malik Menk Jordan!”
Sai da aka fara kiran fasinjoji, kafin ta juya ta tafi da gudu, tana d’agawa Uwarta hannu, murmushi uwar tayi tana faÉ—in. “Dole kiyi amfani da shekarunki da darajarki koda kuwa ta dare daya ce. Malik ya dawo hannun mu!” Daga airport din itama jiran jirgin da zai kaita *Gista* tayi har zuwa lokacin tashinsu, ta mike tare da barin wurin.
Jirginsu Maidah da ya tashi karfe tara na safe, bai isa ba sai karfe biyar na Yamma. Hajiya Jalilah ita ce ta je ta dauke ta, abokiyar harkan Lalla Salmah ce, don haka tana daukarta gidanta ta fara kaita, sai da ta huta, gidan kamar gidan Ƙaruwai da yan iska yake, domin babu Yaren da babu, kama daga bakakken fata, yan Afirka zuwa fararren fata yan Asia da birbishin turawa marasa galihu da suka fada harkan karuwanci da sauransu.
Idanun yan mata dayawa ya sauka akan Maidah, amma Hajiya Jalilah ta musu jan ido, tilas kowa ya É—auke kanshi.
Bayan ta huta taci abinci, tana zaune Hajiya Jalilah ta shigo sanye da shigar hausawa ta ce mata. “Yar Mama zo mu tafi maza!” Gyada kai tayi tana me mikewa, sanye take da riga da wando English wear, sai kanta da ta yane da mayafin shiffon.

“Kin fahimci abin da ya kawo ki ko? Naji labarin kamar Malik yana zuwa a duk bayan wata shida, wannan karon kuma zai zo ne domin maganar wani kamfanin da zasu bude da gwamnatin kasar nan, na kera waya, ki kula sosai!” Gyada kai tai tana faÉ—in. “in sha Allah zan yi iya kokari na” “Good girl!”
A hankali suke tafiya har suka isa wani unguwa mara yawan mutane, da tsirarrun gidaje. Sai da aka tambaye su ina zasu, suka fadi inda zasu, sannan aka bar su, suka wuce bayan sun kira Madam Qudussiyah, ita ke kula da Yaran kusan itace dangin Mahaifin Malik da tayi saura, dattijuwa ce da ta girma ainun. Amma yadda take samun kulawa ba zaka tab’a yarda cewa takai shekaru saba’in ba, hutu da kyakkyawar cimma me kyau.

Gata tana da addini ga ilimin addinin da na boko, ba laifi sai dai tafi karfi a kan addini. Har kofar apartment din suka isa, suka fito, sai da suka danna kararrawar bakin kofar, can aka zo aka bude musu, murmushi akan fuskar yar matashiyar budurwan da ba zata wuce sha bakwai ba, ta ce mata. “Maidah Sheikh!” Murmushi tayi itama ta ce mata. “Wahiba Malik Menk Jordan!” Girgiza kai tayi tana faÉ—in. “Wahida Malik Menk Jordan dai! Nafi Wahiba sake fuska. Muje ki gani da idanunki.” Bude musu kofar tayi tana faÉ—in. “Tadaaaaaa!” Juyowa yan matan suka yi baki daya, suna kallonta, ganin ta dan girme musu, yasa baki daya suka wani dauke kai. “Ashe bana gaya miki ba, wancan me sanye da. Armenia gown ita ce.Nadrah Shatima, gefenta Wahiba Malik Menk Jordan. Ga Jadda can tana fama da Mistih, sunan magenta ne da matar shi itama….”

“Radio me jini, a bar zubata haka, uwar masu surutun Keivroto!” Tura baki tayi tana faÉ—in.”Jadda kin ganta ko?” ” Ai matsalarki surutu, ki bar baki su shigo, barkan ku da zuwa, sannun da zuwa Maidah.” Gyada kai tayi, tana murmushi. Hajiya Jalilah ta ce mata, “Sayyadah Qudussiyah. Ya aka ji da jama’a.” Murmusawa tayi tana faÉ—in.”Alhamdulillahi, muna kan fama dasu, sai godiyar Ubangiji.” Gyada kai Hajiya Jalilah taii, bata ce bata da madubi ba, kafin ta fara harkan nan da take a boye,sai da ta zauna a Diana Menk Jordan, foundation. Asalin taimako suke bawa mabukata da yan gudun hijira, tare da yan cirani.

Dare daya ta gudu, kafin daga baya taji labarin an mai da shi, Salsabilah Menk Jordan, sunan mahaifiyar Menk Jordan, bayan rasuwarsu, ita ta dawo nan suka cigaba da kula da wurin, duk da tasha bakar wahala, ko da yake ai ba ita za a ce tasha bakar wahala ba, hatta Malik sai da yayi kamar ba zai tab’a samun kome ba, kafin Allah ya nufe shi da dawowa, masu ganin ba zai tab’a dawowa da abin da aka kwace mishi, tow kuwa sai da ya shafe musu hadda.
“Ina Lalla Salmah!” Murmusawa Maidah tayi tana faÉ—in. “Maama tana can tana fama da majalisa.” “Allah sarki Ubangiji ya dafa musu, aikin kenan idan kana raye dole ka tashi ka nima, idan baka nima ba kare sai ya fi daraja, duk da akwai mutanen da suke da Sa’a amma kuma niman na kai yana da fa’ida! Atikah?” Ta kwalawa wata mata kira. “Yes Ma!” Ta amsa cikin girmamawa. “Ga bakuwa nan ki kaita dakin da yake kusa da na Nadrah!” “Ok Ma!” Tazo ta amshi kayan me yi mata jagora har cikin gidan, “Baby zan tafi, Sayyadah Qudussiyah zan tafi! Yan mata Wahida ko! Zan tafi” “Allah sarki na zata zai zauna sai dare” “A’a ina da abu me muhimmanci!”

“Allah sarki, sai yaushe!” Satar kallon Jadda tayi taga hankalinta yana kan mage, sai Sayyadah Qudussiyah ta bukaci haka. “duk da tserewa tarbiyyar da kika yi, har yau dai gidanku ne nan, duk lokacin da kika so zaki iya zuwa ki dauke shi kamar gidanku” gyada kai tayi tana faÉ—in. “In sha Allah!” Sannan ta fita a gidan tana ajiyar zuciya. Wannan shi ne zuwanta na farko bayan barin Foundation din shekaru kusan sha takwas, hawaye ne ya zubo mata.

Su uku kamar yadda suka taso, kallon fuskar Wahiba tafi kamar da Nuratu kamar me, Wahida ce dai take kokarin hango fuskar waye tabbas tasan fuskar. Amma ta manta baki daya ta manta fuskar waye, lumshe idanun tayi tana jin dariyar Nuratu. Bude idanun tayi tana kallon gefen ta. _Idan har na samu Malik dole zai hakura da kiyayyar shi, ya bani abin da nake so._ kauda kai tayi hawaye na zuba mata. “Ku zama shaida idan na kuma ganin, Jalilah sai dai a maidani gidan kaso, amma tabbas sai kashe ta.” Hawaye ne ya zubo mata da gudu da gudu. Ta zauna zaman jiranshi amma aka samu tsinannen da ya shiga rayuwarsu ya lalata kome.

“Ku fita min da Æ™aruwar nan, ko na kashe ta” kuka tayi tayi tana kara kukanta, “Malik!!! Ka yarda da ni, ban san kome akan abin da ya faru ba, wallahi ba zan tab’a barin a cutar da Nuratu ba!”
Kuka take sosai har suka isa gida, rabonta da tayi kuka haka, ta manta. Tana shigowa gidanta. Kalamanshi masu zafi suka kara dawo mata. “Ke tsinanniya ce mara albarka, tsiya da lalacewa sune zasu ta bibiyar rayuwarki, kiji da kyau yadda kika bata rayuwar Nuratu Allah ya tsine Miki! Magajiyar Ƙaruwai!” Wani irin abu ne ya tsaya mata a makoshi. Tabbas Malik yayi gaskiya ita magajiyar Ƙaruwai ce, ga gidanta ta cika da karuwai, ita kanta bata taÉ“a tunanin maganar zai tabbata ba sai yau. Tara dukiyar take amma har yau ba zai yi albarka ba, domin da zina da wasu abubuwan aka same shi. Wucewa É—akinta tayi abin da ake fada akan Malik gaskiya ne, yawun shi da dukiyarshi Bala’i ne.

———
Tun bayan fitar ta, Sayyadah Qudussiyah ta Sunkuyar da kai, hawaye ne ya zubo mata. “Sayyadah wallahi ban san abin da ya faru ba, a daren ranar na san mun je gidan Lalla Salmah kuma mun ci abinci mun fito, daga nan muka tsaya muka a kofar gidan Lalla Salmah muka shiga Mota. Daga nan ban san kome ba, sai farkawa nayi na ganni a asibiti. Sayyadah wallahi ban san kome ba, taya zan dauki Nuratu da bata da wadatacen lafiya, na cutar da ita, Sayyadah meye amfanin rayuwata idan na lalata rayuwar Nuratu. Don Allah sayyadah kada Malik ya ce ya fasa aurena. Ban san ya zanyi!”

Tabbas nuratu ba ta da laifi, amma waye zai yarda da ita? Bayan an gama bincike an gano biyanta aka yi ta kai Nuratu aka yi lalata da ita. Bayan ta dawo da ita Keivroto tunda Malik yace matukar ya ganta zai kashe ta, yasa ta rufawa kanta asiri ta anan ta zauna daga baya tsangwama da take fuskata yasa ya gudu babu shiri.

Zare medical glass dinta taii, domin har aka gama Nuratu ta haihu ta rasu, Jalilah bata da labari, sai bayan wani lokaci ta hadu da Sayyadah Qudussiyah ta gaya mata mutuwar Nuratu, a ranar tayi kuka tare da cewa In sha Allah wanda yayi sanadin rabata da Malik da Kawarta sai Allah ya mishi, sama da abin da ya mata. Hakika an cutar da ita. Kuma gefe daya Malik ya kara kiyayyar shi da tsinuwar shi yayi tasiri, tasan darajar rashin ahali domin iyayenta hatsarin mota jirgin ruwa suka yi, ita kuma aka sace ta, aka kawo ta Demark, ta sarafa kafin ta fada hannun Alhaji Menk Jordan……
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:27 AM] Maman Sadiq Da Khadija

Leave a Reply

Back to top button