Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 22

Sponsored Links

Page 🖤22🖤

 

Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje.
Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan.
“Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?”
Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko sallama.
Inna Daayi ce a zaune akan tabarmar datayi sallah tana cin tuwon da indo ƙanwar goje ta kawo mata gabanta.
Ɗaga kai tayi cikin bazata ta kalli yarinya a kanta,yatsine fuska tayi kafin ta ɗora cewa.
“Ke lafiya yarinya kika shigo ko sallama babu,kufah yaran zamaninnan haka kuke,gabaɗa kaman an saka ku a kwano an raba,ba’a jin daɗinku sam.
Idan cukui kikazo siya babu saina kaɗa gobe in allah ya kaimu”
Duk surutunna da take Bombee batace kanjil ba,hannunta riƙe a kunkuminta tana nazartarta.
Saida ta gama kafin ta zauna a kujera ƴar tsugunno dake tsakar gidan.
“Uhhh in kingama surutun inna dama wajenki nazo,tambayarki zanyi,kina amsamin zan tafi…..amma kafin sannann dan Allah zanyi sallah,kuma yunwa nakeji,ƙanshin miyarki yasa cikina yayi kuka yana neman abinda zai haɗiya.”
Kamar wanda akayiwa asirin wucin gadi,haka inna daayi tabawa Bombee buta tayi alwala,ta ɗau hijabin inna daayi tayi sallah,sannan indo ta zubo mata tuwon taci tayi nakk.
“Yawwa Alhamdulillah ciki ya ɗauka,ki faɗa yar ki ta iya abinci,da alama baza’aji kunya ba”
“Ke yarinya wai daga ina kikene,hala ba batan hanya kikayi ba?”
“Babu wani batan hanya,ina kece Daayi matar jauro uwar Goje”
Ɗaga kai inna daayi tayi,duk da taji haushin rashin kunyar Bombee na ƙiran sunna su ba sakayawa.
“Na shigo garinnnan ne saboda naji waye goje,mai yake taƙama dashi da har yake shirin shiga min hanci da ƙudundune,to wlh kijawa ɗanki kunne hawainiyarsa takiyayi ramata,tun muna shaida juna nida shi,idan ba haka ba kuwa dagake harshi zakuji babu daɗi,dan kun tabo marar daɗin.
Naji ance taƙadari ne,to duk tsiyarsa na fishi aradu,karya ganshi zabgege ya gannni kaman itace karmami yanemi ya rainani,shaidar ɗan maciji da kyansa tamm”
Duk magana tanayi ne idonta ɗaya a kanne,yatsa ɗaya kuma tana nuna idon inna daayi bako tsoro.
Saida tagama tass kafin tamiƙe tayi hanyar waje tana faɗin.
“To nina tafi badan dare yayimin ba saidan kar inna ta nemeni,hhhhhhhh wai amaryar daza’a saka lalle wani satin tana yawo”
Ita kanta saida abin yabata dariya,ƙarin mamakin ta ma wai ta yarda ayi auren.
“Yarinya wai wacece ke,sannan menene ma’anar wannan gargaɗin dakikayi,kina cikin wadda goje yayi wa fyaɗe ne? Inma kina ciki ina faɗamiki tun wuri kisan me kike,dan bazaki iya ja dashi ba,kuma shi aure ma zayyi wani satin.
Inso kike ya aureki ma tun dare bai miki ba kima wani hannun”
“Fyaɗe???? Tabbb ya isa ma dan ubansa,yama fara mana…….so kike kisan wacece ni? Sunana Bombee ƴar gidan mlm Ahmadu kuma wacce Goje zai aura nan da wani satin.
Nasan dole dama kunyi mamakin meyasa babana ya yarda da auren koh,bayan yasan tantirancin goje,. Saboda kar tasan kar ce,niba banida daɗi ra’ayina nake bi naci karena babu babbaka,tunda ɗan ki kuma yaɗau kasadar son shiga rayuwata bismillah.
Ni nayi nan sai mun haɗu wani satin kuma Su…..ruuuukkaata DAAYI hhhhhhhhh.
Wai ikon Allah Bombee da suruka kaman mafarki”
Ita kaɗai bayan tagama tujarar tafara tambayar kanta na shaƙiyanci tana bada amsa.
Buta ce a gefen ƙofar gidan,da alama ta jauro ce an cikata da ruwa.
Kallon butar tayi tareda yin bolll da itah ta wajen saitin inda daayi take zaune.
Da sauri kuwa ta matsa ruwan ta zube akan tabarmar,bayan butar ta fashe.
“Karbi wannan kafin nazo ki dunga tunawa karki barshi ya goge innar mijina”
Tana gama faɗin haka tajuya ta bar gidan.
A hanyar fita sukayi kicibis da jauro zai shiga gidan.
Ko kallo na biyu bata sake masa tunda tayimasa na biyu,dan dama ba wajensa taxo ba.
Kai tsaye ta tasamma dajin dayake gabanta babu koh ɗar bare alamar fargaba.
Bujen wandonta ta naɗe zuwa ƙwanji kafin ta nausa da gudu cikin jekin kaman lokacin rana,abin ya haɗu mata biyu,ga sanin jejin ga kuma ganin idonta daya ƙaramata taimakon gani a cikin duhun daren.

“Ahh ke Daayi inata magana nadawo kinyi shuru,sannan wannan yarinya ƴar inace marar ɗa’a,munyi karo da ita amma ko sannu batayiminba ta fita.
Ke indo miƙomin buta nan na wanke hannu”
“Ga nan butar a kusana”
Daayi tafaɗa tana haska masa butarsa wacce Bombee tafasa,duk ruwan yajiƙa tabarmar daayin”
“Ahah wannan kumafah,ko indoce ta jefar ta”
“Hmm surukarka ce ta ta cankofa tun daga hnayar mashiga,itace wacce kake cewa kun haɗu bata kulaka ba”
Nan take Inna daayi ta kwashe abinda Bombee tayimata ta faɗawa jauro.
Jijjiga kai kawai yayi,saidaga baya yayi magana bayan yagama gajeren tunani.
“Hoɗaan wato goje yagamu da gamonsa kenan!”
“Oh hakama zakace jauro,to aradu kuwa tunda tazo tayimin wannan ɗanyen aikin saita zama abin tausayi a cikin gidannan,da nayi niyyar nuna mata soyayya saboda tana matar goje,amma yanzu na fasa,saina koyamata hankali”
“Ahh to ga fili nan kuma gamai dokinnan saura sukuwa muke jira mu kallah,ni bari kiga nayi masallaci kar ayi sallah bandani,da ina faɗamiki ki daina yiwa yarannan riƙon sakainar kashi amma ƙinƙi ji,yanzu gashinan goje ya zame mana Ciwon ido sai haƙuri,sai yanzu da muke son maganin abin kuma Alƙalami ya riga ya bushe.
Sai muzuba sarautar Allah ido kawai mu basu waje muga wacce wainar za’a toya,danni kam dama bani cikin sha’anin zaman sa da wannan yarinya,kece sai yau kikaji labarin ta,ni dama naji labarinta tun ranar da mlm Ahmadu yace wai ya amince ƴarsa ta auri goje,na tabbatar akwai lauje cikin naɗi,dan ruwa baya tsami banza”
“Toh Allah ya kyauta wai rago yasha ƙida”

Cikin sanɗa ta shigo gidan siƙaff siƙaf,har takai bakin ɗakinsu zata shiga taji murya a bayanta.
“Daga ina kike,bana hanaki fitaba tun wancan satin,wai kekam wacce irin yarinyah ce ne,daba dama a faɗamiki abu kiji,kullum idan bakiyi wata tsiyar ba bakyajin daɗine”
Sauke ajiyar zuciya tayi irin ta faru ta ƙare dinnan tunda an kamata,jefar da takalmanta tayi wanda take rikeda su a hannunta.
“Yi haƙuri bazan sake fitaba daga yau shikenan,”
“Baki amsa min tambaya ta ba,daga ina kike a wannan tsohom daren,tukunna ma kinyi sallahr magriba da isha,bata zancen la’asar da azahar ma akeba,wanda bana tunanin kinyi su”
“Wai inna nace miki ina sallah,dukkansu nayi su,isha da magriba ma sukam ƙasaru nayi…..”
Tana faɗan hakan tayi saurin rufe bakinta tana zaro ido,ganin su’butar bakin da tayi.
“Ƙasaru wanne gari kikaje da ƙasaru takama ki,kiyimin bayani naji”
“Uh….uhm rugar su goje naje,acan nayi sallah harma naci abinci”
“Rugar su goje,ni ɗiyar nan mai kikaje yi a rugar su goje da wannan daren,kai kai wai nikam mai kikeso ki jawomin ne a wannan rayuwar Bombee,zo nan biyoni yanzu nan,maganar bata waje bace,saikin faɗamin wane halin kikaje kika nuna a gidan surukan ki uhmmm”
Daneji taƙarisa maganar tana tafa hannaye cikin kiɗima da abinda taji Bombee ta faɗa.
“Babu fah abinda nayi,kawai zuwa nayi naji waye shi a wajen innarsa”
“Kuma yanzu dan zakiji waye shi ki rasa mai faɗamiki waye shi sai innarsa Bombee,wannan tsaurin ido damai yayi kama haka?”
Fincikar Bombee Daneji tayi cikin bacin rai suka shiga ɗakinta,jangwabata tayi akan gado da ƙarfi kafin ta zauna a bakin kujera suna kallon juna.
“Gobe za’a fara sha’anin bikinki,kuma daga goben gidannan zai fara samun mutane,banida lokacin yimiki wata muhimmiyar magana,shiyasa dama na yanke yau zan miki. Amma saboda rashin hankali irinnaki tun safe bakya gidannan sai yanzu kika dawo,abinda kikeyi ko na miji bayayin irinsa,ki fice sanda kikaga dama,ki dawo sanda kika dama saikace shikan wawa.
To ki buɗe kunnenki kijini da kyau,Aure ba abin wasa bane,karki ga yanzu kinada ƴan cinki,idan akayi aure komai naki yakoma ƙarƙashin mijinki.
Yi nayi bari nabari,banda musu kuma ƙorafi ko kuma ƙiwuyah. Sannan kiyiwa uwar mijinki biyayya tamkar ita tahaifeki,ki rungumi ƴan uwan mijinki ki nuna musu soyayya,banda shashanci Bombee ina faɗa miki……”
“Inna dare yayi yakamata ki kwanta,ba’ayi aurenba tukunna kike wanann zancen,ina auren kawai akace nayi to zanyi,amma gaskiya sauran abubuwa kuma banyi alƙawarin zanyi yadda akeso ba,yanda nakeso zanyi su.
So ake yayimin abu na ƙyaleshi,shima fah ba mutuncin ne dashi ba,sai a dameni ƙadai,komai ni”
Cikin bacin rai tagama maganar,Daneji tana ganin hakan tace.
“Tashi ki tafi mukwan lafiyah,Allah ya shiryeki”
“Ameen”
Babu buƙatar sake magana bayan abinda ta faɗamata,dan tasan ko tsafi take da baƙar jaba bazatayin ba tunda tace haka.
Abinda aka sakawa lokaci bashida wuyar zuwa,Auren Bombee ya kam kama ka’in da na’in da angonta goje.
Duk da rashin abin hannu da kuma rashin ƴan uwa a kusa na Daneji,hakan bai hanata taka rawar gani wajen gyara ƴar tata ba.
Tun ana sauran ƙwana uku da aure aka farayi mata wankan madarar shanu,sannan kuma takoma ruwan shanta.
Bata zuwa ko ina koyaushe tana ɗaki,abinka da fata dama haka take. Nan da nan tayi wani haske fatarta tana sul’bi da sheƙi.
Ranar Asabar aka ɗaura auren Bombee da goje a masallacin ƙofar gidansu,kan sadaki Dubu talatin lakaɗan ba Ajalan ba.
Babu laifi kuwa ya tara ɗumbin mutane masu shaiɗa daurin auren,kasancewar shima mlm Ahmadu ba baya ba wajen mutane.

To an ɗaura Auren Bombee da goje,sai muce Allah ya basu zaman lafiya…..😀😀😀….

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button