Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 27

Sponsored Links

Page 🖤27🖤

 

 

Bayan shekara biyu………….

 

Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama.
Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa.
Tayi kaman sa’a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata.
Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah tana maida numfashi sama sama.
Duk da rigar wuyanta nada ɗan sama,amma kasantuwar tsallan data sha nakusan awa guda,yasa wuyan rigatata yin kasa,da yanda mutum na iya kallon saman fararen albarkatun ƙirjinta.
Jan rigar tata tayi tagyara,har sannan bata daina fidda nimfashi ba sama sama.
Nufar wajenda ta ajiye kayanta tayi tareda ɗaukar gorar ruwa takafa a bakinta.
Da yawa tasha ruwan kafin tasaki ajiyar zuciya nauyayya..
Shuru ta ɗanyi kaɗan jin wani motsi yana nufo inda take,idonta ta buɗe a wajen da kunnenta yajiyo mata motsin..
Kasantuwar girman tafara suma idanuwannata sun samu damar ƙara yin dara dara farare tass,ƙwayar idonta kuma yanzu tasake yin wani shuɗi mai sheƙi sosai,Motsi shuɗin cikin idon yake yi,daga ƙarami yakoma babba daga babba yakoma ƙarami,sakamakon daidaita hasken ranar dayake haskawa zuwa cikinsa,wanda ganyen bishiya yake mata inuwa kuma yana karkaɗawa.
Dan shi kansa ganinta saidayi training sosai akai,yanda zata saita kallonta da rana da kuma dare.
Motsin datake jine yafara yawa kana kuma yana matsowa kusada ita..
Cikin zafin nama ta cafki kwari da bakarta tareda saita wajen da idonta ya tsaya akai.
Sauke kwari dabakar tayi tana kallon wani ɗan matashin yaro dabazai wuce shekarunta ba wato sha biyar.
Ɗaga hannu yayi sama alamar yayi sarranda lokacin data nunashi da kwarinnata,sai kuma yayi murmushi tareda jingina a jikin bishiyar da take kusada shi.
“Waye kai?”
Bombee tafaɗa cikin tsare fuska,alamar babu wasa a gameda tambayar datayi masa.
Takowa yafarayi a hankali har zuwa kusada itah,kana yasaka hannunsa yana shafa jikin kibau ɗim dake kan kwarin.
Har zuwa lokacin murmushin dayake kan fuskarsa bai bace ba.
“Shin zaki ajiye kwarin idan nace ni aljani ne?”
“Bana san shashanci ka faɗamin kai waye,ko kuma duk abinda nayi maka karka ga laifina akai”
“Ba shanshanci bane nima tambaya nayi miki,amma karki ɗau da zafi,sunana Aliyu,amma ana ƙirana da haidar,ina so muyi abota ne dake,shin zaki yarda dahakan”
Sake daure fuska Bombee tayi jin maganar wanda yakira da kansa haidar ɗin ya bafaɗa.
Harara ta gallamasa tareda sauƙe kwarinta tayi wajen da ta ajiye kayanta.
Ɗauka tayi ta saƙala a kafaɗarta tareda yin hanyar inda zata fitar da ita daga cikin dajin.
Binta yake a baya yana magana,amma ko waiwayowa batayi ba ballanta na ta kulashi.
Hakanne yasa ya dakata da binta,tareda yin dariyar gefen baki,shareshin datayi karon farko na haduwar ta dashi sai yaji ya burgeshi.
Tun sati daya dayayi yana yimata la’be yana ganin mai takeyi dama yayi tunanin hakan daga gareta.
Tunda yake bai taba haɗuwa da macen data burgeshi kamarta,ta yarda da kanta,sanann kuma bata kunyar nuna jarumtarta,duk da kasancewarta kuwa ƴa mace.
“Zamu sake haɗuwa Bombee dole sai na miki abinda zaki kulani”
Daga haka ya juya yayi wata hanyar daban yana jijjiga kai.
Itama Bombee a nata bangaren mamakin yaron data hadu dashi take,shin anya kuwa mutum ne,bata taba haɗuwa da wanda yakalleta batareda tsoron halittarta ba sai yau,idan tacire goje wanda shi bata sakashi cikin jerin mutane.
In mutum ne mai yakeyi a cikin jeji…..kai itama ai mutumce kuma take zuwa jejin,mutum ne ma dam bataji wani yarr a jikinta ba,irin wanda take ji idan mai aljanu ko kuma wajen da aljanu suka wulga ba.
Yanda taga shigar kayansa da kuma yanayinta,su kansu basuyi mata kamada irin na mutanen yankin su ba.
“Haiiidarrr???,koma waye kai bai shafeni ba,inka shiga gona ta ba raga maka zanyi ba”
Tafaɗa cikin ƙwarin gwiwa(confidence).
Gidan inno ta nufah,saida taci abinci tayi sallahr azahar kafin ta nufi gidansu.
Ko salama batayiba ta shiga gidan,babu kowa a tsakar gidan,dan haka ɗakinsu ta wuce kai tsaye.
Innayi ce a kwance kan gadonta ta tsuga mata sayi na baccin rana,dan dama ita tana fitsarin kwance.
Kallonta take tareda kama kunkumi tana kallon innayin,babu abinda yake tasomata a zuciya sai takaici.
Gashi dama babu wuyah sai ranta yabaci,ita kanta tana mamakin yanda koyaushe sanzawa take daga yanda take a baya.
Wani lokacin bata ganin laifin mutane idan suna aibatata,dan tasan tanayi musu abin muzgunawar ba bayanda zasuyi,saidia itama babu yanda zatayi,in anyi mata laifin daya bata ramaba ji take kaman zatayi hauka,muryar datake zugata a cikin kanta bazata taba barta tayi bacci cikin salama ba.
Dawo da tunanin ta tayi kan innayi wacce take jagab cikin fitsarin datayi mata kan gado.
“Yau zakici bantan innarki laari a gidannan innayi,dama ina taraki da gulamar dakikeyimin a cikin gari,shegiyar yarinya kai”
Takarisa magana tareda ficewa daga ɗakin tana cijan baki.
Fitowar inna laari daga ɗakinta taga wucewar Bombee cikin ɗakinsu ta bulali a hannunta dogaye guda biyu tana yimusu tuka.
Zaro ido tayi dan tafi kowa sanin mai Bombee zatayi dasu.
“Keeee Bombee wazaki daka da wannan bulalin haka?”
“Ki zuba ido kiga wa zan daka dasu mana,miye kike wani gaggawa”
Ta ƙarisa maganar tana watsawa inna laarin harara.
Tana shigewa ɗakin ta rufo ƙofar kirif,ko minti biyu ba’ayiba ƙarar dukan bulala ya jiyarci kunnenta,da kuma kukan ƴar tata wacce take har ƙasan maƙoshinta.
“Wayyo ku ceceni zata kasheni wayyo,innata innata ki taimakeni innaaaa”
Ganin inna laari bazata jure ihun ƴar tata ba yasa ta nufi ɗakin Daneji wacce itama take bacci,ga kwanannnan laulayin ciki take mai wahala,har ya yi wata biyar amma wahalar sa taƙi barinta ta huta.
“Daneji bakyajin Bombee ne zata kashe ƴar uwarta a ɗaki”
Zabura Daneji tayi ta tashi dakyar tareda nufar ɗakin su Bombee,wacce bakajin komai sai ƙarar bulalin dakuma ihun innayi wanda yafara dushewa.
“Ke Bombee ki buɗe ɗakinnan nagayamiki,wai meyake damunki nene kam a gidannan,anya kuwa kanki daya,ki bude dakinnan kafin raina ya baci inagaya miki”
Buɗe ƙofar tayi tana huci kaman sunyi dambe da bijimi,kanta a ƙasa bata bari sun hada ido da Daneji ba,wacce in kallo yana huda mutum daya hudata a lokacin.
“Mai tayi miki kika mata wannan mummunan dukan?”
“Fitsari tayimin akan gado,bayan tasan na hanata hawa min gado”
“Yanxu dan kawai rayi miki wannan lafin shine kika yi mata duka haka,”
“Faɗamata dai,anyi mata aure ta kasheshi da baƙin halinta,ta dawo gida ita ba auruwa zatayi ba tana musgunawa ƴan gidan.akan fitsari shine zakiyimata wannan dukan dan baƙin hali,nasan ma ba iya akan fitsari bane akwai wani mugun nufinki dai daban”
“Ehh akwai mungun nufin,tunda take zuwa tana munafurcina ko kuma takemin raini kin taba hanata ne,shine danna ɗau mataki za’a ga laifina,in kinji haushi ki rama mata mana,kiga in ban kasheta a gidannan ba muss har lahira kum……….”
Fasss bata gama kaiwa ayah a maganar tata ba taji Daneji ta wanketa da wani zazzafan mari a kumatunta,kafin ta juyo tasake daɗa mata a ɗayah kuncin.
Idonta har kanƙancewa yakeyi jikinta yana rawa saboda bacin rai,nuna Bombee tayi da yatsa tareda cewa.
“Bombee……..yanzu har kinyi girman da a gidannan zaki buɗi baki ki faɗawa addah laari haka,ehh lallai yau na tabbatar da baka haihuwar ɗa kuma ka haifi halinsa,kin nuna min iyakata tabbas,kuma naji daɗi da nunamin wanann halin da kikayi kinji”
Kecewa da kuka inna laari tayi jin abinda Bombee tafaɗa mata akan idonta,wanda suna cikin hakanne mlm Ahmadu shima ya shigo gidan.
Tambayar mai yake faruwa yayi,amma babu wanda ya tanka masa,ita Daneji tana faman yiwa Bombee faɗa,yayinda ita kuma inna laari take aikin share hawayen idonta da gefen zaninta,itakuwa wacce tafi dakuwa kukanta yafi na kowa yawa a gidan.
Larai kuma taga kan katanga tana sallallamin jin abinda Bombee tayi ɗin,dan tun ihun innayi na biyu take kan katangar.
Shi mlm Ahmadu dayake ta faman tambayar mai yake faruwa,bai samu sanin hakan ba daga wajen su,sai a wajen inna larai wacce take kan katanga tana kwararo masa bayani kaman recorder.
Tun kafin tagama faɗamasa mai yake faruwa ya zari igiyar awakai dake gefensa ya hau Bombee da duka,wacce take tsaye ƙinkam yana dukannta.
Tun yana dukannata da igiyar har saida ta yayyage ta baje a hannunsa,amma Bombee tana tsaye ta rufe idonta,sai ya zabga mata bulalar taɗan runtse ido kaɗan.
Shatu ce itama dake kan katangar tasamu damar faɗin
“Yanzu Bombee bazaki gudu ba irin wannan duka da ake miki”
Bayan ita babu wanda yayi magana,kowa baki ya buɗe yana kallon Bombee,yayinda shikuma mlm Ahmadu duk bayan duka ɗayah sai zuciyarsa ta ƙara tafasa.
Jefar da igiyar yayi yasake tsinkar tashanyar su ya cigaba da dukan Bombee da ita.
Wanda ita kuma a nata bangaren ba dukanne yake wahalar da ita ba,illah ƙoƙarin datake wajen cin galaba akan muryar datake yimata amo a cikin kanta.
Ba abinda take umartarta dashi illah tarama dukan da mahaifinta yake yi mata a lokacin,wanda har abada bata fatan taga hannuwanta sun aikata hakan.
Salatin dataji su inna laari sunayine yasakata buɗe idanuwanta da sauri,ba komai ta hanga ba sai mahaifinta kwance a ƙasa yana dafe da zuciyarsa,wanda tasan ko tantama bazatayi ba ta sanadiyyartane hakan ta faru.
Abin haushin kuma duk yadda taso ƙwakwalwarta tasaka zuciyarta jin haushinta abin ya faskara,saima haushin mahaifinnata daya turnuƙeta.
Tsugunnawa tayi a hankali zatakai hannunta kansa,caraff taji an rike mata hannu.
“Karki kuskura ki taba shi,wlh bakida wannan damar,ki bacemin daga gani yanzunnan”
Daneji ce tayi maganar wacce idonta yayi jajur ta tsanar halin Bombeen.

Ohhhh nagaji……i hope dai yana sugar littafin koh????

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button