Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 16

Sponsored Links

ArewaBooks@Mamuhgee_
16
Annensu yanayin manyanci da wahala ga kunnenta da bataji yanzu sosai yanda ya kamata yasa jikinta da lafiya suka fara yimata qaranci yau da gobe wasu ayyukan bata iya yinsu da kyau dan haka sune suka karbe mata duk wani aiki saidai idan suna makaranta a bata wani aikin shima suna dawowa zasu karban mata hande tayi ta fada amma karba sukeyi saidai wata ran susha marika gurin Ababa akan sun fara Rena hande.

Sbd Anne yasa Benazir takoma gaggawa takewa karantunta ana tashi take dawowa bata batar da lokaci ko qanqani Shiyasa basa dawowa tare da sumayyah kusan tafiyarsu yanzu tare ta rage sosai,

Sumayyah tafara IT dinta a wata makarantar kusa da anguwarsu dan haka Ababa ya dena bata kudin mashin ita da qafa take zuwa ta dawo da qafa dan haka take rigan Benazir fita tinda safe.

Bilal ne da kansa yake kaita lokuta da dama kuma ya daukota ita kuma Benazir Sulaiman ne yaci gaba da kaita kuma abincinta babu wanda aka fasa kawo mata makaranta kaman yanda itama sumayyah acan ake kai mata nata.

IT din sumayyah ya sake kusancinta da Bilal kwatsam saiga maganar aurenta da wanda yayi alqawarin bawa yana karban kudinsa akan karatunta ta taso sbd karatun nata yazo karshe dan haka maganar aure ta taso take gadan gadan ba daukan lokaci.

Maganar auren ta rusa duk wani kwanciyar hankalin Bilal ita kuma dukkanin hope din data samu ya wargaje sbd tasan maganar Ababa bamai fasuwa bace ko gardamawa,ko mahaukacin kare ya cijeta bazata iya ko dagowa ta kalli Hukuncin Ababan ba bare gardamawa.

Abinda ya dagawa bilal hankali kenan wato sarewarta da kasa iya cewa komai akan hakan sbd shi anasa bangaren yaso ta basa hadin kai da goyan baya ya sakewa Ababan Nera ba yar kadan ba dan ya hanawa kowa aurenta ya basa ita sbd a hankali ya fahimci irin asalin rayuwar rashin gata da yancin dasukeyi hannunsa dan hakan ne ma yakejin idan bai karbesu su dakan daga hannun Ababan ba kaman zai iya shiga wani halin sbd zai iya komai dan ya rabasu da gidan dan haka auren Sumayyah din yake jin tabbas ba fashi garesa da yardar Allah.

Benazir tayi nisa a karatunta batasan tashin hankalin da suke cikiba saida Yaje daukanta da kansa ranar yake sanar da ita irin yanda yakeson daukesu daga gidan suyi rayuwarsu kaman kowa.
Haka kuma a shirye yake da auren Sumayyah ta roketa tabarsa yaje gurin Ababan dan yana qin zuwan ne sbd baisan kalan azabar da zai janyo musu ba shiyasa yaketa kiyayewa.

Ita kanta Benazir jin hakan saida takusa shidewar mintina sbd firgitaccen tashin hankalin wucin gadin data shiga sbd zuwansa gurin Ababa koda motar kudi zai ake masa wlh saiya kusa aikasu lahira kafin ya amsa kudin sbd sun take qaqqarfan doka da sharadinsa akansu na kula kowane irin namiji.

Cikin rashin boye masa tashin hankali da tsoronta taqi amincewa zuwansa itama,

Anne ma dataji da sauri ta hanasu qarasa zancen sbd kusan da hannu suka kwatanta mata rabin zancen tinda bataji sosai sai an dan daga murya gashi zancen bana a daga murya bane wani yaji Alqiyamarsu ta tsaya.

Wanna maganar tasa ta sanya kwata kwata suka fara qaurace masa ga tsananin Ababa akansu ta qaru dan kusan yanzu dabiar kai musu ziyarar ba zata ya dauko dan haka suka shiga taitayinsu ba shiri
Ko hanya suke tafiya basa dagowa.

Kusan sati biyu Bilal yayi bai saka daga Sumayyah har benazir a idanuwansa ba dan haka ya shiga damuwa da tashin hankali sosai sbd kar Ababa fa yayiwa Sumayyah aure bai saniba.

Ita kanta sumayyah tana cikin damuwa da qunci ga dukan da yanzu kusan kullum sai tasha sbd tinani ya hanata nutsuwa ta aikin data saba kullum saita qona manyan kayan mutane gurin guga dan haka a cikin qanqanin lokaci ciwonta yafara kokarin dawowa na kai,
Benazir na ganin haka tafara kokarin kada Ababan ya gane ciwon Sumayyah saidai kuma kusan abin gaba gaba yafara sbd da asarar datake ja masa tayi yawa sai ya hanata fita kwata kwata makarantar datake IT din bayan wahala da duka babu abinda take samu kullum a gurinsa.

Ganin lamarin yafara yawa tsoron Benazir sai qaruwa yakeyi ga Anne itama yau lafiya gobe ciwo sai abin yawa Benazir yawa tafara skipping lectures itama sbd lalura da ayyukan da karatun.

Daqyar da Addua Ababan yabar sumayyah tafara fita takoma makaranta bayan ta share kusan sati uku ko kofar gida bata isa ta leqa ba.

Koda tafara fita batada lafiya sosai dan haka suna isa makaranta Ms aysha ta dauketa da kanta a motarta sukai asibiti ita kuma Benazir tanada test a ranar dan haka ms aysha tace tayi zamanta.

A asibitin ba bata lokaci Bilal da ms aysha ta kira ya iso cikin mummunar damuwar halinda sumayyah din take ciki ta rame sosai ta sauya gabaki daya kaman wadda tai jinyar shekara guda kwance.

Ruwa da magani aka hau dara mata
Ko minti uku basuyi da fara shiga ba ta hau zubo amai mai qarfi.
Sosai ta bata jikinta dan haka ms Aysha ta kamata bayan ta gama suka shiga toilet tayo wanka akai mata ordern kayan ba jimawa mai delivery ya kawo Bilal dinne ya karba ya miqa mata ta kofar toilet din sbd Ms aysha ta wuce ankirata da gaggawa Mijinta ya dan samu accident.

Sauya kayan tayi jiki ba qwari ta fito jiri na dibanta daqyar ta dawo da kanta gadon ta zube take aka sake maida mata ruwan wani wahalallan bacci ya dauketa.

Baccin awa hudu tayi ta farka,
Abinci yafara bata taci ba laifi kafin taje toilet da qyar tayo fitsari da Alwala ta dawo tayi sallar a zaune sbd bazata iya tsayuwaba,

Tana idarwa ya karban musu sauran maganinta yace gida zasu sbd kayanta dayakeson suje a wanke a shanya su bushe in time ta mayar dan yasan ko tsautsayi bazaisa sumayyahn taje gida da wasu kayan ba wanda ta fito dasu ba kuma gashi doguwar riga ce mara nauyi har qasa amma ta kwanta jikinta tayi mata kyau sosai duk da tana cikin hali na ciwo.

Kai tsaye wata anguwar dake zagaye kaman ta masu qasa ya nufa da ita wadda ta sanyata jin zazzabinta na sakinta sbd kusan duka gidajen anguwar ba tsarin ginin Nigeria bane,
Anguwa ce mai tsarin gine ginen Turawa masu tsada na asalin masu abun Hannu na gasken,
Tin daga babban gate din shigowa anguwar baka shiga saika fada inda kazo ka kuma nuna id card din kowane iri hakama commercial abubuwan hawa basa shiga anguwar kwata kwata,
Manyan samudawan Securities ne wani kamfanin securities mai zaman kansa suke gadin Anguwar da bazaa kirata da estate ba sbd ba estates din bace amma   Tamafi estate tsari.

Id card dinsa ya fiddar suka duba suka scanning motarsa yafada gidan wanda zashi saida ya fada private security code na gidan da zashi din wanda kowane gida akwai private security code da ake basa duk wanda zaizo gidanka sai fada masa code din ya fada a gate abarsa ya shigo.

Wangale masa manyan kofofin gari guda akai ya shigo da motarsa tareda miqewa kai tsaye zuwa gidan DD kaante wanda kaf gidan shine ya zabi zama wata anguwar daban ba acikin babban kaantes ba,

Shi kadai ya zabi rayuwarsa daban sbd yinta yanda yake so da buqata,ba damuwa,ba hayaniya,ba takura haka zalika rayuwarsa da zafin kansa dake hanasa jituwa da Mutane musamman Dad kaante wato mahaifinsa daya kasa gane haka Allah yayisa.

Duk matsi da takura tareda fadan Dad kaante da dd babba wato kakansu sunyi sun hakura amma bazai iya zama a can cikin family ba,
Baya son kusanci da gidane sbd rayuwarsa bayason duk abinda yake amfani dasu na daily life dinsa ya zama mutane na kusanta,
Idan har yana gida yasan umminsa da sister dinsa da brothern nasa da dad kaante harma da wasu baqin wata rana duk zasu ringa shigar masa ana muamalantar abubuwansa dan haka ya zabi zama a gidansa a anguwar datake da iya tsaro,tsafta,tsari da dokikin dayake so na rashin hayadan ko horn baayi aciki idan ka shigo.

Isarsu kofar gidan yasa Jikin sumayyah sake daukan rawa sbd kusan ko a hanya dasuke wucewa a anguwanni hanyarsu zuwa makaranta bata ganin irin wainnan gidajen dan haka jikinta yayi sanyi ta qara rasa kuzarinta.

Codes na bude kofar qaramin gate din gidan ya saka gidan ya bude suka shige ya sake saka na kofar shiga asalin cikin gidan kofar ta bude ya saka kai ciki kai tsaye yana janye da hannunta sbd batada karfin tsayuwa da kyau.

Dummm kirjinta yayi na kokarin rage jan numfashi sbd wani Ni’imtaccen qamshi daya shiga hancinta duk da gidan tsawon lokaci sosai ba kowa amma qamshinsa daya gama kama komai da koina na gidan ya kasa fita hakama komai na gidan tamkar kullum ana shigowa ana gyarawa komai nasa daban ne.

A rayuwar DD kaante daga black sai fari iya sune kalolinsa sai ta kama cancan ga gansa da wasu kalolin da bazasu wuce milk,ash,navy blue shikenan suma dan suna yanayi da kalolin nasa ne wato black and white,dan haka gidan nasa ya zama kusan komai na cikinsa iya wainnan kalolin ne dan haka komai yake unique na masu dala,
Luxuries kawai ta ko ina daga dala sai dala babu abinda bana Waje waje ba.

Zaunar da ita Bilal yayi yaje ya kunno switch na wutar gidan take ta kawo koina ya dauki wani irin Haske su Ac daman duk a kunne suke switch dinne aka kashe na wutar gidan kai tsaye dan haka take suka fara aiki.

Dayake harda bra dinta ne a kayan shiyasa bai bawa wani ya wanke ba yazo yayi da kansa tinda Benazir na makaranta gashi ko sumayyah bazataso a hanata test dinta ba haka shima a yanzu dayake jin Benazir din tamkar Aleeya qanwarsa ta jini bayajin zai taba bari karatunta ya ringa samun tangarda.

Abinci da magani ya bata tanasha bacci mai qarfi ya dauketa ya kaita dayan dakin dake gidan bayan na DD sbd yasan ko DD bayanan wani ya hau masa gado zai gane sbd hancinsa dayake daukan qamshi ko sabaninsa nan take koman qanqantarsa yasan halinsa dan haka baiko kwatanta kaita dakik DD dinba wanda babu ma wanda ya taba shigar masa harshi Bilal din da baida tamkarsa.

Gyara mata kwanciya yayi ya rufeta ya rage Ac dayayi mata yawa sbd yanda ta dan takure duk da sanyi na wahala sun saba dashi.

Toilet yaje ya nade kayansa ya wanke mata kayan fes duk da bai wani iyaba sbd rayuwarsa kaf bai taba wanki ba sai ranar sbd undies dinsama a machine yake sakawa bawai wankin hannu ba suma mafi yawan lokuta mai aikinsa jamil ke wanke masa.
Bayan ya gama duk ya jiqa kayansa sbd rashin iyawar toilet dinma duk ya jiqa koina,
#MAMUH#
#DD KAANTE#
#BENAZIR ABABA#
#LOVER#ROMANCE#MARRIAGE#Sisters#Little Benazir Amnah kaante
#Billonaireromance

Leave a Reply

Back to top button