Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 15

Sponsored Links

Mamuhgee 15_
Akace Salati baya hana daukan rai hakama qaddara yashi ce ko an daunqulata bata dunquluwa,zuciyar Sumayyah batai shawara da ita ba acikin qanqanin lokaci ta saka bilal cikin kanta.

Har Benazir ta samu sauki kuma interval nata ya qare ta dawo suka ci gaba da exams bata fahimci ‘yar kusanci da shaquwan da Sumayyah ta samu da Ms aysha da Sir bilal ba sbd hankalinta gabaki daya akan jarabawarta ya koma sbd babu tsayawa yanzu saita gama duka exams din.

Sumayyah kuwa itama ba dan laifi Ms aysha na iya kokarinta akanta ga bilal yanzu da duk ranarda baizo ya ganta ba a wayar Ms aysha yake magana da ita.

Tin tana jin nauyin ms ayshan sosai harta dan sake da ita sbd a rayuwarsu basu taba samun kulawa,kauna ko tattali da sakewa daga wani ba wannan ne karan farko datake samun hakan daga Bilal da ms ayshan.

Koda suka gama exams suka fara zaman hutu daga bilal din har sumayyah jin sukeyi ba dadi musamman shi din.

Benazir Tinanin result da yanda wahalarsu ta qaru ba sauki yasata gaba,
Abincin dasuka saba dashi kuma na Kaantes H&S yanzu dasuke hutu ba daman cinsa sai suka taru sukai wata irin rama sbd yunwa kaman wainda ake dibansu ana girkin gidan dasu.
Yar lafiyar dasuka samu ta jiki sbd cimar dasike ci mai kyau da lfiya tini ta gagaresu sbd yanzu aiki ne kan aiki da yunwa kan yumwa duk sun sake ficewa hayyacinsu gasu yau lafiya gobe babu sbd marika da harbin qafa,Annensu kuwa tini Ababa ya haukatar da dodan kunnuwanta da marika dan haka yanzu kusan idan kana nesa da ita bata jinka sosai idan ba murya zaka dago ba.

Cikin ha ula’i da ukuba sikai hutun sika gama aka koma karatu,
Ranar dasuka koma mashin sika hau kaman yanda suke hawa a baya,
Sunje makaranta sun duba time table nasu kaman mayu suna cikin wainda basu qara ko kwana dayaba,

A gantale suka wuni makarantar sika dawo Ms aysha ma bata shigo ba ranar dan haka Sumayya jiki a sanyeye ta dawo gida.

Sallah sukai suka fito qarasa aikin da Anne bata gama ba suka shige bayan sinci Shinkafar da aka basu.

Washe gari suna fitowa suka ga sulaiman yana jiransu inda suka saba ba bata lokaci suka shige a yanzu dasuka fara ita boye abu kudinsu na makaranta sun dena bayarwa dika rabi suke boyewa suna sadakar rabin shiyasa harsun fara tara ‘yan kudaden da ko basu fada ba na guduwa da Annensu ne insha Allah.

Suna isa makaranta Sumayyah na kama hanyarta Ms aysha ta aiko kiranta dan haka itama cikin jin sanyi a ranta ta nufa office dinta.

Cikin kulawa da farin cikim ganinta sosai ms aysha ta tarbeta tareda cewa ta zauna
Nan ta fara tambayarta ya hutu da sauran abubuwan.

Bata wani jimaba ta tafi lectures saidai baa kira  Sir bilal ba yau din sukai magana.

Tana barin office din ms aysha ta kira Bilal ta sanar dashi irin ramar da Sumayyah din tayi sosai a dan lokacin hutun.

Suna fitowa da yamma maimakon sulaiman Bilal ne yazo daukansu cikin daya daga cikim motocinsa masu shigen daukan ido da hankaliz

Kaman marasa gaskia suka gaidasa ya amsa cikeda kulawa idanuwansa na kan sumayyah data kasa dagowa ta kallesa sbd kunya da farin cikin ganinsa.
Shiga motar sukayi suka bar makarantar tin kan wani ya gansu duka kama hanyar gida.

A motar Benazir kawai ya danyi magana da ita sumayyah kuwa da idamuwansa yake maganarsa da ita
Ita kuma bata iyaba bata ganewa duk sai neman rikicewa takeyi.

Suna isa a tare suka fice motar suka kama hanyar gida batareda Benazir ta taba tinani ko fahimtar wani abu na faruwa da Sir bilal ba da Yar uwarta.

Ayau abincinsu na musamman ne sbd da kansa ya karbo musu dan haka sina sallar magrib suka zauna sukaci suka koshi take Anne tafara amai sbd wunin ranar so daya taci abinci.

A boye tagama aman suka kwashe suka wanke sbd kada aga aman asan sunci wani abin bayan tuwon da akai gidan.
Da omo mai qamshi sika wanke koina dan haka dakin bayan qamshin omo babu abinday yakeyi baka cewa anyi amai.

Suna gamawa sallar ishai sukai kawai suka fito suka danyi wankin shago da baida yawa yau koda 9 tayi sun gama sun shige sun kwanta.

Washe gari ma Bilal ne yazo daukansu hakama a dawowa.

Saida suka share kusan sati da komawa Bilal ne yake kaisu da daukosu har saida tsarguwa da tsoron Benazir ya bayyana a fili tukuna Sumayyah ta rokesa ya dena zuwa din sulaiman yaci gaba da daukansu.

Koda result dinsu ya fiffito Benazir ta fadi Course daya Sumayyah kuwa a duka uku kawai taci suma da pass,

Dukan dasuka sha kuwa saida Sumayyah ta kwanta jinya sosai wadda ta qara mata shakuwa da kusanci da Bilal da ms Aysha dasuka fahimci babansu ne keda wani irin zafin dayake dukansu.

Kulawa da tattali sosai sumayyah ke samu daga ms aysha da bilal harma da benazir ana tattalinta saidai nata bai kai wanda sumayyahn take samu ba.

*******lokaci ya dan ja semister tayi nisa zuwa lokacin tafaru ta qare soyayya mai qarfin gaske ce a zuciyoyin Bilal da sumayyah wanda suke yinta boye batareda sanin kowaba sai ms aysha da benazir wadda ba qaramin shock ta shiga ba da Sumayyah din ta sanar mata amma kuma kirki da tsananin mutinci da girman kaunar da Sir Bilal ke musu yasata jin hope a ranta na akwai yiyuwar Allah ya kubutar dasu ta hanyar Bilal din kila.
Kuma ganin yanzu sumayyahn na gane karatu ba laifi yasata sake jin girman Sir bilal din da ms aysha cikin ranta,.

Tafiya tayi tafiya Ita kanta Benazir Ms aysha ta shaqu da ita sbd wani irin tsananin tausayinsu datake ji yasa mata kaunarsu sosai musamman Benazir wadda zuciyarta ke danqare da damuwa da quncin rayuwa fiyeda sumayyah sbd sumayyah yanzu Bilal shine sanyin dayake narkar da nauyi da quncin zuciyarta.

Sunyi hutun qarshen session din results dinsu yayi kyau Benazir bata fadi ko daya ba sumayyah ma kusan taci sosai dan iya biyu kawai ta fadi duka da sauran daqyar aka wucesu.

Zuwa lokacin boyayyar soyayyarta da Bilal tayi wani irin nisa da qarfi ta yanda aurenta yakeson yi matiqa saidai babban tashin hankalin daya fara tinkarosu shine mahaifinsa kai tsaye baiyi naam da maganar ba batareda yaji sauran bayanin ba yace sun riga sunyi magana da senate president ‘yarsa zai aura.

Sumayyah ma a nata bangaren yanatason yazo yayi magana da Ababa amma tsoro ya hanata barinsa sbd abinda bai saniba duk ranar da ababa yasan sun taba kallan wani namiji ba bare soyayya wlh zai iya konata bare yayi alqawarin fasa idanuwansu idan hakan ta faru.

Ta bangare daya kuma cimar dasuke ci mai kyau da lafiya tasa fatar jikinsu da jikin nasu sauyawa sosai tayi fresh da kyau alaman ana cin cima mai rai da lafiya.
Komai yana son siya musu sbd yanason ya sauya rayuwarsu zuwa rayuwar da basu taba tinanin zasu kai ba,
Yanason barar musu da dukiyar da basu taba tinanin akwai ba,
Yanason inganta rayuwarsu ingatawar da wasu yayan masu arzikin basu samu ba sbd Nasu arziki da dukiyar da Allah yabasu kaates tanada yawan da bazasu iya fadar adadinta ba.

A bangaren Ababa rayuwarsu bata taba canjawa ba da matsayinsu na kamar dabbobi gidan,
Dukansu da azabar da ake basu tana nan babu abinda ya sauya saima qaruwa sbd kullum karatunsu sake cin kudinsa yakeyi dan haka azabarsa akansu take qaruwa ga shagonsa na wanki ya sake bude wani sbd sosai kasuwancin wankin ke tafiya dan haka ya sake bude wani shagon kuma duk sune masu wanki da gugar kawai dai iyakaci yaran shagon su saka a leda ayi packaging kaman na kamfani a bawa me kaya idan yazo karba kuma yawanci manyan mutane sosai yanzu suke kawo wanki shagon dan haka manyan motoci matsu tsada ake aiko masu karban kayan wanki shima kansa Ababa tini ya tanadi mashin suka fara delivery din kayan da kansu idan an wanke.

Ms Aysha itace take taimaka musu sosai yanzu kusan itama a boye dan haka soyayyar Bilal da sumayyah taketa qara nisa da qarfi.

Sumayyah sun gama nasu karatun gyara ne kawai takeyi yanzu sabanin Benazir da yanzu karatunta yake qara nauyi sbd tana 300lvl gashi Accountancy take karanta.
Sosai hankalin Benazir ya duqufa kan karatunta sbd ganin sumayyah na gane kartu sosai dan haka ta dena damuwa da karatin sumayyahn ta kama nata.

Yanayin yanda karatin nasu ya hargitse yasa dole badan Ababa yaso ba a ringa raba musu kudin abin hawa sbd tsananta tsaronsa akansu duk wanda ya gama baya jiran daya ya dawo gida.

Nasir Ahmed wani dan kyakkyawan saurayi dayake final year dinsa a Accounting kuma kuma kusan shine guru din course mates dinsa tin Benazir na first year dinta Allah ya saka masa kaunarta amma bai taba tinkararta ba sbd yanda take kame kanta.

Ya dade yana bibiyarta amma ba fuska sai gashi Allah ya hadasu sanadiyar wani course da itace tafi kowa cinsa shine lecturer din ya hadata da Nasir yana qara mata haske akan course din sbd yanada matiqar wuyar gaske shiyasa malamin ya jinjina mata data cinye tana mace.

Karatu shine ya kawo mutunci da yar shaquwa a tsakaninsu amma sam babu sakewa sbd yanda take tsorace sosai da Muamalar tasu,

Shi kansa daya fahimci tsoro fa fargabar ganinsu da akeyi tare sai ya ringa sirrintawa yana samunta gurin zamansu da sumayyah inda ba mutane acan suke karatun.

Son Benazir yake sosai da gaske dan haka yake tsananin mutunta ta kuma ita kanta tana mutuntasa a zuciyarta saidai duk yanda zuciyarta taso saka mata wani abin daya zarce hakan saita hana kanta sbd idan suka bari wani abin ya shiga tsakaninsu to tabbas ita a bangarenta tasan suicide mission ne dan kuwa shi kansa Nasir din tasan saiya shiga tashin hankalin abinda zai biyo bayansa idan ubanta ya sani dan haka take dan baya baya da duk wani tinanin daban amma kuma zuciyarta ta basa matsayi mai mahimmanci amma bai zurfafa ba.
#MAMUH#
#BILLONAIREsROMANCE
#DD KAANTE
#BENAZIR ABABA
#CONTRACT
#insideLife#marriage#love#hotlove#Lover#Zafin kai#zafafa biyar#paidnovel#Mamuhgee#morepages@Arewabooks#

For more pages kuje arewabooks ko vip

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-FURAR DANKO
Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim

Send your Shedan biya Anan👇
09032345899

MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇
09033181070

Zafafa🫶🔥🔥

Leave a Reply

Back to top button