Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 31

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣1️⃣

 

…….“A’a gaskiya, sai dai idan yanzu ta samesu”. Uncle Yousuf ya bata amsa. Iska Ammah ta ɗan furzar a hankali da cije lips sai dai ta kasa cewa komai. Duk yanda sukaso hasaso komai sun kasa, ga Smart yay masifar ɗaga hankalinsa da ƙyar su Abba suka baibayesa suna masa nasiha. Saurarensu kawai yake yi amma al’amarin na bashi matuƙar mamaki da tsoro. Wace irin masifa ce wannan suna ganin sun tsallake wancan siraɗin da ƙyar ace kuma ga wani abun daban dama yafi na baya muni. A wannan yini dai duk yanda akaso yin ɗan sauran shagalin da ya rage bai yiwu ba. Sai Daddy ne daya fita dan Ammah ta bada shawarar su wuce da Lulu Nigeria kawai. Sannan suka yanke shawarar a faɗama Baba Garko anga Lulu ɗin kamar yanda Smart ya bada shawara tun farko. Domin shi yana ganin Alh. Sulaiman ne yayo musu wani ƙullin kawai. Daddy da Uncle Yousuf da Abba ma tunaninsu kenan. Ammah ce dai keta wasi-wasi da tunani kala-kala sai dai batace wa kowa komai ba a zahiri. Ana tsaka da wannan cakwakiya kira ya samu Smart da Uncle Yousuf na gaggawa zuwa England akan harkar ƙwallonsa. Dole badan yaso ba suka wuce amma daka ganshi kasan hankalin ƴan mazan a tashe yake. Dan ma su Ammahn sun taru sun masa nasiha mai ratsa jiki da tabbatar masa matarsa na tare da shi in sha ALLAH. Nan da ƙanƙanin lokaci kuma zatazo ta samesa a inda yake. Hakan ya ɗan ƙarfafa masa gwiwa suka wuce….

Sanarma Baba Garko anga Lulu ya taimaka matuƙa. Dan cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa abinda Daddy ya fara a washe gari da daddare suka wuce Nigeria a private jet. Suma su Mommy an sanar musu, da su Aunty Bilkisu. dan haka ahalin uku suka shirya babbar tawagar tarba. An yanke shawarar wucewa da Lulu gidan Abba zata zauna a wajen Ammah. Dan haka aka rankaya can kowa bakinsa yaƙi rufuwa da farin cikin ganin Lulu da jaririn da basu san da cikinsa na sai haihuwarsa. Dan farin cikin wannan Surprise Baba Garko ranar har ƙyaututtuka yayi na musamman. Abin tashin hankali na biyu tunda aka shiga da Lulu gidan su Smart ta juyo da gudu baya sai da aka rirriƙeta. Wannan al’amari ya sake hargitsa su Daddy yayinda sauran da basu san mike faruwa ba hankalinsu ya tashi. Umma da ke a birkice tunda labarin ganin Lulu yazo musu a kunne faruwar wannan abun ya sakata faɗawa dakinta tana dariya dan daɗi ji take kamar ta ciza uwauwanta. Ana can ana haya-haya na al’amarin tana nan tana kiran Hajiya Naqiba suna kwasar dariya. Sai dai fa batun haihuwar Lulu da sai a yanzu suka sani ya taƙaita musu farin cikin nasu…

Dole aka koma da Lulu gidan Daddy ita da Babynta hankalin kowa a tashe musamman Ammah da Daddy da Abbah. Dan sun sake tabbatar da lallai akwai matsala. Aunty Bilkisu da aunty Amarya da abu yayma tsaye a rai basuyi ƙasa a gwiwa ba suka ja Ammah gefe game da zargin su akan Umma da abinda ya faru bayan tafiyarsu. Mamakin wannan al’amari ya kashe Ammah tama kasa cewa komai sai kallon su Aunty Bilkisu takeyi. Itako mitaima Umma da zafi haka a gidan nan take mata irin wannan ƙiyayyar, duk da basu tabbatar ita bace dole ko suna so ko basa so tana cikin zarginsu tunda tayi abubuwan zargin ciki harda wanda aka gani da ido. Gwaggo Sa’adah da ranta ya ɓaci ce tace zatayi magana ita kam sai dai ayi duk wacce za’ayi. Da sauri Ammah sarkin dattako ta dakatar da ita da faɗin, “A’a Sa’adah ai magana ba tamu bace yanzun. Domin yinta kamar mun fargar da itane ta sake shiri tunda zuciyarta ta riga ta mutu. Fara magance matsalar ya kamata muyi kafin mu ɗauki mataki. Yaran nan na bani tausayi matuƙa, auren kusan shekara ɗaya amma basu taɓa zaman cikakken wata ba a ƙarƙashin inuwa ɗaya gashi harda rabon haihuwa. Muyi ƙoƙarin ganin al’amarin su ya dai-daita sannan muje mataki na gaba dan ita ba komai bace face baiwa ta ALLAH shine zai mana maganinta ta inda batai zato ba.”
Badan Gwaggo Sa’adah ta so ba ta haƙura. Amma ta ɗauki alƙawarin sai ta wajiga rayuwar Ummah itama….

A wannan yanayin akai taron suna mai ƙayatarwa, dan a zahiri Lulu normal take tsakaninta da Smart da duk abinda ya shafesa ne aka nisanta su, hatta da ƴan uwansa komai normal. Dan yanda ta dinga haba-haba da su aunty Bilkisu da ma duk wanda ya ɗan uwa na Smart abin zai baka mamaki da birgeka. Bama ita ba, hatta ƴan uwanta babu wanda ya wulaƙanta mata dangin miji. Umma ce ma taso kawo gutsiri-tsoma a wajen da ƴaƴanta akan abinda bai ko taka kara ya karya ba. A take Adda Mairo ta taka mata birki da faɗin, “Sufa basa son fitina da ƙananun magana. Alkairi da farin cikine ya kawosu akan gudan jininsu. Dan haka ta kama kanta gaskiya, tunda iya ƙoƙari mutanen nan sunyi da su a wajen taron nan”. Wannan abu ya ƙonama Umma zuciya dan ba haka taso ba. Bata bari sun taho tare ba tayo gaba, babu wanda yabi takanta sai ƴaƴanta. Dan ko Mama cewa tai wlhy bazatama kanta mugunta ba sai anci komai da ita, duk da acan gida ma da suka baro wani taron za’ai.
Bayan an gama taron suna da ya girgiza sukatan su Umma da har ta fara tunanin abinda tai ɗin kamar yama warwarene ganin ɓarin kuɗin da Smart yayi, dan hatta anan gidan suma Ammah tayi taron suna sai ma kace anan maijego take, yanda aka yanka rago da sa acan gidan su Lulu anan ma ƙaton sa da ragon aka yanka, a cewar Smart basai sun damu dana can gidan su Lulu ba balle a samu masu ƙananun magana duk da yasan su Lulun bazasu ƙi kawowa ba. Alhmdllh mutanen arziƙi sun taru tako ina fiye da zato da tsammani. Yayinda komai ya tafi cikin farin ciki da bajinta dai-dai misalin da baza’a taɓa kallonsa a almabazaracci ba ko nuna fariyya….

________★

A washe garin gama taron suna Alh. Sulaiman ya iso Nigeria a hargitse. Dan a daren jiya labarin tabbatar da Lulu ta dawo Nigeria ya isa garesa. Kamar yanda mahaifinsa ya saka kuwa hakance ta faru, dan tun a filin jirgi jami’an tsaro sukai ram da shi. Wannan lamari ya girgiza zukatan Garko family sosai dama mutane da yawa da ke da alaƙa da uban da ɗan. Dan basu ɗauka Baba Garko bai haƙura ba tunda an samu Lulu. An saki Tajuddeen da ya share wata biyu a hannun jami’an tsaro yau, Baba Garko kuma yabar ƙasar sabgogin gabansa tamkar ba’ai komai ba. Ƴan ƙananun magana sun fara tashi kaɗan-kaɗan a tsakanin al’umma game da wannan cakwakiya tsakanin ɗa da ubansa. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa, tun ƴan jarida nayi a ƙumshe har dai zancen ya fara fita a bayyane. Sai dai kowa da abinda yake faɗa akan al’amarin. Wasu suce sace ƴar ƙanwarsa yay ya ɓoye, wasu suce harda azabtar da ita yay saboda bata auri ɗansa ba. wasu suce aure yaje aka ɗaura mata akan aure da ɗan nasa. Magana dai barkatai gata nan, har abin ya fara shan kan Garko family musamman da sukaji ana neman saka waswasi akan AA wai ba’a ma san ɗan mijin Lulu na farko bane kona Tajuddeen.
Wannan magana ita ta tayarma da Daddy hankali. Ga Uncle Yousuf na tare da Smart acan England. Smart ne ya kwantar masa da hankali ta waya da tabbatar masa ai dama hakan zata faru dole, amma yayma kowa banza sai sun gama cecekuce ɗin nasu sai su san gaskiya. Abinda ke faruwar a yanzu yana cikin shirinsa akan Sulaiman ɗin. Hankalin Daddy ya ɗan kwanta ya samu nutsuwa. Amma yana mamakin wannan wane irin shirine haka da Smart da atashin farko ya ɗauki hanyar tallata abinda ke a ɓoye bayan da kansa yace yaƙin sunƙuru za’ayi. Koda yake bari ya saka masa ido yaga minene manufarsa. ai karan bana shine maganin zomon bana daman…..

Ana tsaka da wannan dambarwa aka dawo da Dada gida Nigeria. Alhamdullah ta samu sauƙi sosai kamar ba itace aka fita da ita ƙasar raga-raga ba. Sai dai ta dawo ƙasarta da tagwayen al’amura biyu masu gogayya da juna zuwa uku. Na farko shine anga Lulu, sai dai tana baƙin ciki da haihuwarta da ɗan talakan nan dai, amma dai bata yarda ta furta ba gudun karta sake ƙullama kanta tsiya ga Baba Garko da tun a sibiti ƴaƴan keta faman kiransa suna bashi haƙuri ya maidata iddarta saura kwanaki ta cika amma yay biris da su. Abu na biyu shine fitowar Tajuddeen da kama Sulaiman kuma. Wannan al’amari ya sake ɗaga mata hankali. Ta kuma sake tabbatar da Baba Garko a shirye yake da kowa kenan, dan haka ta ƙara kama kanta.
Da ƙyar ta iya bari gari ya waye tasa Uncle Muneer ya kaita gidan su Lulu. Karo na biyu kenan da zata taka Jiƙamshi House a tsohon rayuwarta. Da ga lokacin rasuwar mahaifiyar Lulu sai yau saboda tsabar ƙiyayyar da takema Daddy a baya, koda yake har yanzu ma bawai ta barsa bane, kawai tana dannewa ne saboda Lulu ta nuna mata bazata ɗauki wannan ba ana zagar mata mahaifi. Duk da kasancewar gidane ginanne a tsaye, a kuma anguwar data amsa sunanta anguwa dan kosu da ke a kusa da gidan gwamna sun san a yanzu hotoro G.R.A ɗin ta basu baya. Amma haka tsohuwar nan ta dinga wani yamutse-yamutsen fuska har abin ya bama Uncle Muneer haushi da tabbatar da Dada fa bazata taɓa ta canja ba sai dai a barta da halinta kawai dan ya riga ya shiga jininta ne. Sun sami tarba tautuntawa da ga Daddy da Mommy. Duk da dai Dada na amsa musu gaisuwa sama-sama basu damu ba. Uncle Muneer ne dai ya ware abinsa sunata shan hira da Daddy cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. A haka su Amrah dake maƙale da AA akoda yaushe yanzu, ko makaranta sai anyi jan ido suke wucewa suka fito. Yana goye ne a bayan Afrah yana barci, yayinda Amrah ke jiran time ya cika ta kunto mashi dan dole aka koma sakama kowa lokaci har su Naseer da ake korawa makaranta da ƙyar. Dan yau Suhaib harda kukansa shi sai da AA zai tafi kamar wani ƙaramin yaro. Basu ba dake ƙanana hatta Mubeen wataran faɗa ake da shi akan ɗaukar AA. Hakan na saka Lulu farin ciki da jin ƙaunar ƴan ƙannen nata matuƙa. Su twins kansu kullum sukan kirata sama da sau uku suna tambayar ina son ɗinsu. Hotunansa kam ƙa’ida akai masa wanka sai an tura musu. Ra’is da Deen kam ai sun ma dawo nan gidan saboda AA. Mommy kanta na ƙoƙarin gyara kuskuranta akan AA ɗin, dan itace a tsaye kan kula da Lulu da yaronta duk da Iya Tabawa na iya ƙoƙarinta. Dan ana cewa za’a samo tsohuwar da zata kula da Lulu ta ce ita dai a bata dama ta maida alkairi a wannan karon. Duk da dai a tsorace take saboda sanin halin Lulu ɗin. Amma dai ganin kamar ta ɗanyi sauƙi yanzu yasata cewa a bata dama. Bako a samu wata matsalaba kasancewar a yanzu ma ga Ummita kuma, sannan da gaske al’amuran Lulun sunyi sauƙi kam, duk da idan ƴan masifar na kusa takanyi abinta………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button