Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 6

Sponsored Links

006
_Past_
A lokacin da suka zo ganin wurin dayawan su, sun yi fatan da sune suka kawata wurin domin ai sune yan kasa ba Nasr Hadejia da Aswad Yamini ba. Taya baƙin haure zasu zo su fi yan gari kawo cigaba har haka, wani abin ya tsaya a ransu. Matukar tsaya musu. Kuma ba iya shi ba, asalin su mutane ne masu matukar Kyashi da Hassada da wannan dalilin yasa suka buɗe iyakokin duk wani tubalin bakincikinsu, inda aka fara turo musu yan jagaliya suna yiwa mutanensu daukar amarya. Koda Alhaji Nasr Hadejia ya ga haka sai ya shigar da bukatar jami’an tsaro su shiga cikin al’amarin amma abin haushi sai aka yi rashin dace. Domin yan sanda bakinsu daya. Haka yasa jikinsu yayi wani zai ce me yasa suka nace da son suyi wurin shakatawa? Abin da mutum be gane ba, shi ne fisto yana cikin garuruwan da suke buƙatar a inganta su. Na farko zai samawa birnin cigaba, na biyu matasan garin da suke sana’ar daba da jagaliyanci zasu samu aikin yi, dattawan da suke sana’ar kamun kifi, zasu samu damar baje kolin sayar sa kifinsu. Sannan gari ne masu al’adar gargajiya. Wannan dalilin yasa baki daya mutane biyun nan saka zuciyarsu, akan lallai su kawo cigaba da garin.
A hankali kome ya fara kwace musu, domin a zahirin gaskiya yan daban sun dame su. Abubuwa biyu ya dame su, ga asarar dukiyarsu ga wasu daga cikin mutanensu a hannun yan garkuwa. Akwai wata rana da Alhaji Nasr Hadejia da Aswad Yamini suka hadu a gabbar tsibirin. Kowanen su, yana da damuwa amma dan samu kwarin gwiwa a tsakaninsu yasa suka sauke ajiyar zuciya a lokaci guda. “Hadejia ina ga ya kamata mu sake budar wurin Mayor Fahad Albagwi da wannan al’amarin, idan har muka yi haka tow ba makawa zamu samu adalci, kaf garin nan kansu a haɗe yake ba zasu sake mana mutanen mu ba.” kallon shi yayi sannan ya ce mishi. “Ni ma nayi tunanin haka, amma nasan Allah yana sane da al’amarin mu, Allah zai tsaya mana.”
“Ka saka mana lokaci mu tafi wurinsa, idan yaso sai mu shirya ba.” murmushi Alhaji Nasr Hadejia yayi ya ce mishi.
“Idan Allah ya kai mu gobe, sai mu tafi. Ina son na kira iyalina ne su zo da Yarana.”
Dariya suka saka ya ce mishi.
“ai ku yan Nigeria kuna da hakuri da juriya, ina zan iya wannan hakurin? Kawai malam ja sa Madam ta dawo nan, kafin nan karatunsu da kome nasu zai dai-daita.”

“Hmmmmm! Tow ya zamu yi? Kasan idan baka yi hakuri ba, ya zaka yi da hakkin Allah, shi Allah ya sauke hakkin mu da yake kansa, saura mu mu sauke wanda yake kanmu. Ina da Yara mata biyu, ina jin kunyar na bude idanu na kalle su bayan na sabawa Allah, sannan Allah ba zai kare mu ba. Sannan ba zai kare bayan mu ba, amma idan muka ƙare kanmu da iyalinmu Allah zai kare bayanmu bayan mutuwar mu.” jinjina kai Yamini yayi yana faɗin. “Na gamsu da bayaninka. Allah ya kare zuriarmu bayan mutuwarmu” “Allahumma Amin” da wannan suka ajiye zancen zasu tafi wurin Mayor Fahad Albagwi.

Washi gari kuwa Yamini shi da kansa ya taso ya dauki Alhaji Nasr Hadejia, izuwa farfajiyar gidan gwamnati. Sun taras da mutane, musamman manyan baƙi don haka suka tsaya su jira. Bayan kamar minti Talatin sai ga sakataren Fahad ya fito dake an isar mishi da yayi baƙin. Duk da kasancewar sun same mutane a wurin bai hana sakataren isowa wurinsu ba, ya ce musu.
“Ku iso ana kiranku.” mikewa suka yi, tare da bin bayanshi, a cikin ofishin Mayor. Cikin girmamawa da mutuntawa Mayor ya mike tare da tarbansu yana faɗin.
“Malik sune mutanen da suka zo da nufin raya garin Fiston, amma Shu’iba da Dulma sun hana su, har nan suka zo suka min kashedi. Malik na kira ka ne, domin ka taimakawa bayin Allah nan, suna san cigaban jahar nan ta fuskar Kasuwancinmu.” duk da basu ga fuskarshi ba, amma baki daya basu wani gamsu da shi ba, domin kuwa ba a niman taimakon dan daba akan yan daba yan uwanshi. Hadin kai ne dasu, d’ago hannunshi me dauke da zobban ya yi musu wani alama.
“Wai ku gabatar da sunanku?”
“Aswad Yamini, wannan abokina Alhaji Muhammad Nasr Hadejia.” a hankali ya juyar da kujeran ya zuba musu idanu, mutum ne mai tsannanin kwarjini da cikar halitta. Mutane da matukar ka kalle shi sau daya sai ka sunkuyar da kanka ƙasa. Domin yanayin zubinsa kamar zubin zaki ne, rintsa idanun Yamini yayi yana jin wani irin yanayi. Domin kallo daya yayiwa Malik ya hautsina mishi tunani, banbancin shi da Nasr Hadejia da ya kuma kallonsa ido ciki ido har sau biyu. Duk da wannan yanayin bai hana shi jin kamar ya zuru da gudu ba.

“Had’ejiya ta Jigawar Nigeria?” da sauri Alhaji Nasr ya d’ago suka kara kallon juna a karo na uku. Mikewa yayi yana me fashewa da dariya, Fahad Albagwi ka had’e ni da dan uwana dan kasar kakana. Ai ni na samu aboki waye ya isa ya ce ba zasu gina wurin shakatawa ba. A shelantawa duniya na tsaya musu. Ai ko don albarkacin dan kasata na tsaya musu. Yamini kai ma ɗan uwana ne, domin Mahaifiyata yar yankin jaziratul arab ne.” lallai sun taki sa’a kuma sun dace. Sai dai basu san cewa akwai ragon azanci a amincewa Malik. Musamman yadda tambarin shahararsa tasa ya fantsama yayi wanka da munanan ayyuka ba, mutum ne ya yayi wanka da zunubai babu iyaka.
Don haka suka bada yardansu tare da yarjejeniyar habbaka Kasuwancinsu. Amma ya boye musu makasudin amsar alaƙarsu.
“Batun ma’aikatanku da suke hannunsu, zan amso su kafin rana tayi tsakiya.” ya duba agogon hannunshi. Sannan ya juya yana kallon Fahad. “Albagwi alkawari.” gyada kai yayi, sannan ya fita. Bin bayanshi suka yi da idanu. “Mayor hankalina bai kwanta da Mutumin nan ba, idan abun nan ba zai yiwu ba, mu hakura ko Yamini?” murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Ni kuwa naji kamar alkhairi, koda kuwa akwai matsala ba zai gaggare mu ba. Kwantar da hankalinka.” haka suka amince da Malik domin kiri-kiri Alhaji Nasr Hadejia yaki karban Malik, ba don kome ba. Sai don sanin duk inda aka samu dan daba zai yiwu ya ki taimakawa yan uwansa.

Shu’iba da Dulma.
Malik ya jima yana nimansu, ba don kome ba sai don akwai tsohuwar gaba, wanda suka jima da shi a ransu, sai dai bai samu damar ramuwa ba, domin kuwa basu tab’a zama wuri guda. Asalima wasan boya suke da shi, shi kuma yayi alƙawarin duk wanda ya gaya mishi inda suke zai mishi kome, ana haka Fahad Albagwi ya tura mishi sakon ganinsu. Ana gab da zaben kasa.
Dulma dan uwan Shu’iba ne, kaninshi cikin su daya, a duniya babu abun da Shu’iba yake so sama da Dulma, domin ta kai, hatta matar da ya aura tunda Dulma ya ganta ya ce, yana sonta. Babu musu Shu’iba ya bar mishi ita. Karshe azaba da wahala ya kashe Yarinyar, tun daga lokacin Shu’iba ya samu damar auro mata Dulma ya shiga abin da yake so da su.

Hill and Tim town.
Ana kiran wurin nan haka ne, sakamakon duwatsun da suka kewaye wurin, kuma akwai ma’adinai irinsu kuza, ana hakarsa na fitar hankali. Ba ƙaramin samu suke ba. Sannan sun kwashe maza matasa da yan matasa,. Suke musu wannan aikin cikin azaba da wahala, dalilin wannan dukiyar da yake kasa yasa suka watsar da duk wani cigaba da ya dace su samu. Musamman a fuskar garin, domin idan suka gyara garin su waye zasu musu wannan aikin? Duk matasa zasu samu abin yi. Shi yasa wurin suka kawata shi da nauyin azaba kala-kala. Babu wanda ya isa ya gudu, akwai zakuna masu gadin mutanen, domin kuwa idan mutane suka ne gudu bude zakunan ake suyi fata-fata.
Koda Malik ya bar ofishin gwamnati, bude motarshi yayi, masu kula da lafiyar shi suka fito suna me niman take mishi baya, d’aga musu hannu yayi. Ya dauki wata local gun, sannan ya shiga motar bayan ya dauki wata glass na Prado ya saka a fuskarshi, fuskar shi a kame, na zaka ɗauka yana dariya ba.

Haka ya juya ya fita, a duk lokacin da yayi irin su wannan shirin, tabbas ba ƙaramin al’amari ba ne, jinjina kai Elbashir Jamal Arab yake, yana faɗin. “Allah ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, amma tabbas maza sun fita farauta.” Haka ya koma cikin motar ya zauna, tare da kunna wakar rosta.
Tafiyar kilomita bakwai ya kai shi, Hill and Tim town.
Tun kafin a bude mishi kofar shiga town din ya fara musu barna, har ya isa cikin sansanin, koda yake fushin sa ba a kan kowa yake saukewa ba, akan wadanda suka tab’a shi ne.

*present*
Koda yake kusan rabin ayyukan da tayi, bata jin akwai wanda ya kai na yau, shi yasa tayi kokarin ganin ta nime haduwa wani dan kasuwan da zai zuba jarinsa. Sai dai batayi nasarar haduwa da shi ba. A gajiye ta fito daga ginin ta fito inda Black yake jiranta, wurga jakarta tayi tana faɗin. “Wash Allah na!” Ta zauna a cikin motar tana mika. “Ina zamu?” Idanunta a lumshe ta ce. “Akwai inda yafi gida ne?” “Babu” ya bata amsa, sannan ya ja motar suka bar wurin.
“Chairman! Yarinyar nan ta kawo abin da bamu zata ba, mu kyaleta haka!” Murmushi Mr Amjad yayi ya ce mishi. “Ban gama gamsuwa ba, sai tayi min abin da3 zan barta. Amma ka sani duk kudaden da take samo mana, na hannun jari bai kai na babban kifi ba.” Shiru MD yayi ya ce mishi.
“Akwai matsala, idan har aka sake kifin ya sake ya zama me k’aya za a wahala.”

“Bana kwai na, sai da zakara don haka da ita zan amfana!”

A kan hanyarsu ta dawowa gida ne, suka tsaya a traffic jam. Yan sanda ne suke bincike, “Kai Xno ga mutuniyar!” Juya kanta tayi zuwa ga inda yake nuna mata, kafin ta tabe baki ta ce. “sun fito cin na goro!” Ta fada tana dauke kai, domin ta gama gajiya likis. Dama da gayya ita kanta Asp ta fito kan titin. Sake mutanen da suka tare take, kafin su Zeeno su iso ta saka an tare hanyar, dauke kai Zeeno tayi.
“Ina driving license din ku?” Banza suka mata. Ba ƙaramin kunya ta ji ba, domin ana ta wucewa da kafa, kuma ana kallonsu.
“Ina magana kin min banza!” Babu wanda ya d’ago kai ya kalleta, hannu ta kai da niyyar zata cire key din motar. Zeeno ya kai mata wani irin duka da bayan hannu, faduwa can tayi, kamar an cillata. Sauka daga motar Zeeno tayi tana me cire top din suit din jikinta, a hankali ta shiga nad’e hannun white shirt din jikinta tana faɗin.
“Kul ki ce zaki tab’a min mota ta, zan kyale ki ne domin kakin jikinki idan ba haka, kul ki kuma shiga harkata!” Mikewa Asp Zulfa tayi tana faɗin. “Kika saka hannunki a jikin Yar sanda.” Wani juyar da kai tayi tana faɗin. “Idan ta kama na zane ki zan yi ki tsaya a bakin aikin ki.”
“Da shi haka yana nufin duk wanda ya nime saita miki hanya, sai kin kashe shi dalilin da yasa kika kashe Asp Ayuba kenan?” Rintsa idanunta tayi, ta nufi Zulfa da wani irin sassarfa ta cukume ta. “Idan kika kara kiran sunan tsinannen can, sai ja tura ki idan na tura shi, ki bincike idan kin samu labarin wanda ya ga lokacin da na kashe shi, ki zo nan a gaban jama’a ki saka handcuffs.” Daga haka ta koma cikin motar ta zauna. Wani irin kallon banza Zeeno ta aikata mata, tana mata gargadi.
*Past*
“Kai ku sake mishi zakunan nan!” Haka suka sakar mishi dabobbin. Yarda bindigar yayi ya nufi zakunan da mugun gudu, kamar yadda suka nufe shi. Oho faduwar gaba asarar maza, a fusace Mayuntan zakunan nan suka nufe shi, aikuwa aka rungutsume akayi wata kazamar arangama, a duk inda aka raya fansa, tow zaka samu tsoro da fargaba bai cika samun matsuguni a wurin ba. Haka ce ta faru da Malik, domin a duk lokacin da ya dunfaru wani abun da ya shafi fansarsa. Haka suka hautsine da wani irin fada, me tashin hankali. Kafin wani lokaci,ya watsar da gawarsu, ya mike yana karkad’e jikinshi yana kallon inda Dulma yaƙe. Hannu ga saka a cikin aljuhun wandon shi ya dauko cigarette, ya kunna tare da zukar hayakin ya hura a sama…….
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI….
Beauty and the beast♡
Mai_Dambu

Leave a Reply

Back to top button