TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 41

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA P🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣1️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Bamu hadu da mommy
ba har wajajen goman dare kafin naji muryoyin su kaf diyan dakin su suna magana
akan abinda ya shafi rayuwan su.

   Saidai zancen ya
shafi wani rikicin daya tasone a tsakanin su lokacin bukin uwartake kolatin
sasanta tsakanin su a lokacin.

   Saidai duk laifin
akan mommy suka dorashi inda ita kuma bata yarda da hakan ba inda nake jin
muryan mommy na fada da karfi da alama bata yarda da korafinsu a kanta bane.

   Kafin naji wace ke
biwa babban yar nasu ta sako zancen na a cikin maganan su tana fadin irin
abubuwan da mommy din tayi ta nuna mata rashin jin dadin hakan da tayi.

   Nan ta sake daga
murya garesu tana fadin ina dai wanan kuma ba matsalan daya shafeku bane ko
kuma ita din ma zaku saka min idone a kanta yanzu kuma.

    Duk abinda nakeyi
sai a zauna ana sakawa mutum ido  don
kawai ayi mashi sheri ace ga abinda mutum yayi in bashi ba meya kawo zancen yar
mijina a bakim ku yanzu ko ita ta fada maku hakan kum ?

   Bata fada muna
komaiba wallshi uaarsu ta fada sai naji tace kada tayi mana ni dama ai don
ibanta nake son na taimaka mata tunda taki ai shike nan gata ga fakirin nata da
take so ai sai tayi ta kaya.

   Daga haka na daina
jin muryan su ina nan wurin ina tunane har barci yazo ya daukeni na manta da
zancensu .

    Komai nasa ya gama
hadawa a lokacin ya shirya tsab don gari yake jira ya waye yayi sallama da masu
gidan yatafi don alkawari ya daukarwa kanshi cewa ba zai kara kwana wanan garin
ba kuma.

   Haka kuma yayi
alkawarin cewa bai kara waiwayo wanan garin na mambilla a rayuwan shi ya
sadakar da zancen zai kara haduwa da mahaifinshi.

    Yasan cewa babu
zancen shi a zuciyan wanan mutumin yanzu duba ga yadda yaji labarin harda da
wanda sukai kama dashi sosai yadda mutane suke fada din kuma suke ganin kamar
tasu.

    Yana jin kiran
sallah ya fito yayi alwala don har ya riga malam musa tashi shidake tayar dasu
a kulun suyi sallah jam,i sai gashi yau shi ya riga dattijon tashi.

   Daga nan daki ya
koma ya fara gabatar da nafila bai dade da tayar da sallah ba yaji fitowan
tsohon daga dakinsu shima har ya gama abinda zaiyi yana jin motsin shi kafin
yazo yana bugamai kofa yayi gyaran murya dake nuna yana falke a lokacin shima.

    Tare sukaje sallah
sun dan dade basu dawo gidan ba kafin su dauki hanya su dawo gida bayan su gama
zikirin safe kamar yadda suka sabayi din.

    Sai bayan sun
dawone ya dibi ruwa da sanyin nan yaje bandaki ya watsa ya fito ya shiga
dakinshi ya shirya tsab ya fito a cikin shirin shi ya samu shattu na kashe kuna
shi kuma malam musa yana zaune a dan rufar shi yana tulawa.

   Shattun ya fara
gaiyarwa kafin ta dago  kai ta sauke ido
a kanshi yana rataye da yar jakarshi ta tafiya da yazo dashi garin.

    Kallon mamaki take
mashi ta amsa ya mike zuwa wurin malam musa ya duka yana masa ina kwana ya dago
kai yana amsawa tare da fadin yau ba zaka zauna tulawan ba ke nan ?

  Sai idon shi yai
arba da jakar tafiyan shi a bayanshi don haka ya kasa boye mamakinshi a lokacin
saboda tuhumar da zuciyan shi ya fara mai zai tafi ke nan kome matashin yake
nufi dayin hakan.

    Ya naganka haka
dattijon ya tambayeshi ba tare daya iya amsa gaisuwan daya fara mashi ba tare
da kura mai ido cikin son jin amsan da zai bashi din.

   Baba zan tafi
gidane yau din nan insha Allahu don yanzu kuma hankalina gaba daya ya koma gun
kakata dana baro gida saboda nasan tana can cikin wani hali na rashin sanin
idan na shiga a yan kwanakin nan.

   Nasan kuma zamana a
wanan gari a yanzu haka zai iya haifar da barazana a gareni a yadda na fahinta
don haka nake son inyi gagawan barin garin nan a yau din nan.

    Amadu ya kira
sunan shi na yanka kamar yadda ya fada mai din sunan shi tun farko yace nasan
kana da ilimin addini dana boko.

   Don haka zaka iya
hango abinda ni ban hango makashi ba a yanzu to amma dai komawan nakane a yanzu
tun kan ai wani abu gameda mahaifinka din shine ya daure min kai a yanzu.

   Babu komai baba
saidai zuciyana ta kasu biyu a kan matsayina a zuciyar shine don bansan a wani
rukinin nake a wurin shi har in bai fadawa yan uwanshi komai game dani ba kaga
hakan zai iya haifar da wani matsala mai karfi kuma a tsakanin mu.

   Don haka gara in
bar garin nan kasan masu kudi yadda suke a yanzu zai iya gano gidan nan ya turo
a halakani ko ai maku wani abin da bai dace ba.

   Indon wanan ne zaka
tafi kayi kuskure kuwa koma me zaiyi maka yayi din ka dai tabbata a dansa har
in mun zauna dashi din nake gani.

    Kayi hakkuri baba
ka barni in tafi a yau din don nasan daga baya zaka fahinci manufata da abinda
yasa na yankewa kaina wanan hukuncin a yanzu.

   Saidai taimako daya
da nake son kai min baba shine duk sanda na tashi nunawa wani ahalina zan
nemoka a matsayin dan uwan mahaifina din don girman Allah.

    Shiru dan dattijon
yayi na dan lokaci kafin yace wanan yafi komai a wurina yanzu da zaka yardama
ni har gida sai in kai ka amma ko yanzu ma hakan bai baci ba garemu zanyi
kokari nan gaba inzo har garin naku na ganka a matsayin dan uwa a gareka ni da
wasu.

   Godiya sosai ya karawa dattijon  kafin shatu ta iso wurin da kwanon kunnunta
tana fadi a cikin yarensu naga kamar yaron mu zai tafi ko ?

   Mijin yace haka ya
kuduratawa zuciyan shi duk da banji dadin hakan ba don baso ya tafi hakan cikin
bacin raiba gashi ni kaina bai fada min komai game da haduwan nasu da mutumin
wanda yake zaton mahaifinshine shiba mu sani.

    Ban rike sunan
shiba nadai san cewa shidinne ta maganan dana fada mai duk da bai ban amsana
daga bakin shi ba amma yanayinshi gaba daya ya gama nuna min shi din ne.

   Duk yadda malam
musa uaso ya dakatar da matashin yaki yarda da hakan karshe dai malam musa din
yace ba zaka bi hanya ba batare daka karya kumallo a gida ba .

   Wanan ya dan tsayar
dashi ya tsaya yasha kunun sama sama malam musa din ya kalloshi yace kana da
guzurin da zai kaika har gidane ya dago kai yace insha Allah kudin dake wurina
zasu kaini har gida baba.

   Bayan ya dan kara
kurba kunun ya mike yana masu godiya ya sallami shatu ta nuna mai damuwanta a
fili kan rabuwan su dashi a lokacin.

   Tare suka fito da
malam musa din sai dai ba mutane don safiyane sosai kowa na gidanshi lokacin
yana rage hantsin safe da iyalanshi agida.

   Malam musa din
baiyi aune ba yaga ya nufi wurin garken shi ya dan tsaya kadan kafin ya juyo su
kama hanya saiga mai mashin suka tare yayi jinga ya kaishi tasha nan malam musa
din ya mikowa Ahmed din wasu kudi masu yawa yana fadin ka karbi wanan ka kara
kayi amfani dashi .

   Ahmed din ya
durkusa kasa yana kada kai alaman bazai karba yace ashe baka daukeni ubaba a
wurin ka ka karba kuma ina rokon ka idan kaje ka kirani muji saukan ka yace
insha Allahu baba.

    Ya mike yana dan
goge hawaye a fuskanshi ya tafi yana dagawa malam musa din dake jin wani abu a
cikin zuciyar shi game dasshi lokacin hannu.

    Yayi sa,a yana
zuwa mota mota mutum daya ake jira ys biya ya shiga ba bata lokaci suka bar
garin mambilla din suka dauki hanya bin garin yake da kallo kafin ya mayar da
idanunshi ya lumshesu.

  Fada takeyi sosai a
wayan kafin ta mike tana fadin gida zata koma mambilla don maigidanta baida
lafiya hankalin kowa ya tashi da jin haka.

   Anzo dadi dadi ana
buki gashi yanzu kuma mumunan sako ya risketa kowa da abinda yake fada a wurin
ita kan jinsu takeyi kawai don ita kadai tasan abinda take ji a zuciyar ta
lokacin.

    Don hankalinta
yayi kololuwar tashi sosai ga abinda yaronta aminta kuma hadimin maigidan nata
ya fada mata a safiyan ranan suna kama hanya tadauko wayan ta daga cikin jakar
ta tana neman wani layi.

    Ba adauka ba saida
ta kara kira aka dauka yaren su takeyi na mambillawa tana fadin su hadu da mai
wayan gata nan ta kamo hanya zata dawo mambilla din yanzu .

   Ta dan jima tana
waya da wace ta kira din a wayan kafin ta kashe wayan tana han tsuki duk a
zatonta driver su din baya jin me take fada don bata taba sanin ya iya yaren
nasu ba saboda bai taba yi a gabanta ba taji.

    Tafiya sukayi
sosai a ranan karfe daya suna cikkn garin mambilla din suka karasa gida direct
part din mijin nasu ta nufa tana son sanin halinda yake ciki.

    Zaune ta sameshi
shi kadai yana tunane gabantane ya fadi ras ras don dan canjin yanayin data
ganshi a ciki don a cikin kwana daya ya fada yayi dan duhu sosai a lokacin.

    Jin an shigo yasa
shi dago kai yana kallon kofan itace ta shigo yake binta da kallo kamar yana
son ya tuno da wani abu lokacin amma ya kasa hakan.

   Kofan aka sake
turuwa lokacin  duk suka juya don ganin
ko waye ya shigo dayan kishiyar tace tashigo dauke da kayan abinci a hannunta
tana sallama.

   Saidai tana ganin
ta tadan shiga rudu tana fadin au ashe kun dawo sannuku da zuwa ta dan tsuke
fuska kafin ta amsa tana fadin eh mun dawo yanzun nan.

   Abincin ta aje tana
kokarin jerawa a gabanta take fadin barshi kawai aiba yanzum ne zaici ba ko
tace cikin murmushi shiya umurceni na kawo mashi yaci yanzun din.

    Kallon mamaki ta
jefi kishiyan dashi na yadda ta bude baki ta iya bata amsa kai tsaye ga mijin a
zaune bai iya furta komai ba a lokacin don yanayin da yake ciki.

    Meke faruwa da
kaine haka Alh ta mayar da tambayanta kan maigidan nasu dake zaune saye da
doguwar jallabiya a jikinshi ya zauna ya mike kafafunshi duk da yana cikin wani
hali hakan bai hanashi kamshi turare ba sai dan karamin tasbaha daya rike yana
ja a cikin zuciyarshi lokacin.

    Kai ya dago ya
kalleta kafin ya daga mata hannu yana fadi da kyar kije ki huta zaifi ke kuma
aje min abincin idan na tashi yanzu zanci.

   To matar ta biyu ta
amsa dashi kafin ta kwantar da murya tana fadin Dan baro na waje yana sallama
dakai shida jabbi a kofan falo OK har sun iso ke nan ya fada yana mikewa da sauri
kamar bashi ba a lokacin.

    Kowa part dinshi
ya nufa zuciyar shi cike da zargi akan halinda mijin nasu ke ciki a lokacin na
tashin hankalin da yaki fadawa ko dan dama ita hjy Indo dake gari abin ya faru.

    Amma ita hajiya
Ni,ima da take wurin tafiyan bata san komai ba a yanzu sai zargin abubuwa da
dama da takeyi a zuciyan ta lokacin.

   Tunane take waye
wanan din da Alh ke tunane akansa haka kardai zancen sanda ya zamo ba daidai ba
gareta Alh ya sadu da danshine wurin sakaci irin nasu har hakan ya faru ?

   In ko hakane ashe
kashinta ya bushe a gidan nan ke nan don tasanda abubuwa da dama zasu iya
faruwa a cikin lamarinta ke nan a yanzu tunda anfada mata ka idan abin kuma ta
yarda da hakan .

  Sam bata taba tunane
ko zaton cewa maigidan zai iya sake wanan yaron nasa a ido ba kuma duba ga irin
shekarun da aka kwashe babu wanan zancen .

  Don har diyansu sun
taso sun zama wani abu yanzu a cikin rayuwa tana ganin cewa lokaci yayi da zata
gaje gidan ita da yayanta da yan uwanta da suka tsaya mata komai ya tafi
daidai.

  Amma yanzu zuciyarta
yana bata cewa duk wanan abubuwan suna kokarin wuceta idan ba Allah ne ya gyara
lamarin nata ba kam.

   Alh munyi iya
bincken mu mun kasa gano waye wanan yaron kuma daga ina yake wanda ma ya sanshi
ko yasan a inda yake zaune bamu sameshi ba gaskiya.

   Murmushin kasaita
mai kama dana takaici ya sake lokaci guda yana fadin amma Jabbi kasan dai yaron
nan dana gani ba aljani bane da zakuce ya bata a cikin garin nan.

    Ba haka nake nufi
ba Alh Jabbi din ya fada a ladabce yana sone kai kasa yace muna dai kan
binciken hakan in sha Allahu zamu gano komai a kanshi da yardan Allah.

    Shiru sukayi na
dan lokaci kafin Alh ya fara mikewa tsaye saida yaba da baya kamar zai shige
ciki yace ina mamaki da jiya zuwa yau za a ce an kasa gano inda wanan yaron
yake a cikin garin nan.

    Daga haka yasa kai
ya shige ciki ya barsu nan a zaune suna mamakin sauyin da suka gani wurin
aminin nasu kuma maigidansu abokinsu tuna tasowa da har yanzun basu yada junan
su ba suna tare.

   Saidai sun san cewa
shidin ba mai fushi bane irin haka alama ya nuna ke nan zancem wanan yaron yana
da muhinmanci sosai a wurin maigidan nasu.

    Nan suka mike kowa
ya nufi inda yake tsamanin samun labari akan yaron da sukayi siri da maigidan
nasu kan a nemo masa shi kota halin kaka a kawo maishi a gabanshi. 

    Kukan da akuyoyin
keyine ya sa Dijen fitowa daga daki don ta dubasu saidai tsoro da tashin
hankalin abinda ta gani yasa ta ja baya da sauri tana fito da ido waje tace .

  Uwar garke kene a
gidan nan kuma ni Dije naga abinda ya tsoratani akuya kamar mutum saiki tafi
sai lokacin da kikaga dama mu ganki kwatsam kin fado muna gida.

   Uwar garken da
kanta ke done a cikin kaskon da ake zuba masu ruwanshan su tana zukan ruwa
zakace tayi tafiyan mai nisa don yadda take durawa cikinta ruwa a lokacin.

   Kururuwa zatayi ko
sulalewa zatayi a cikin gidan taje neman taimako a makwabtansu azo a gane mata
abin mamakin datake shirin  gani kota
gani a gidan.

   Akuyan da tayi wata
nawa bata gidan  Amadi kafin shima ya
bace yayi neman akuyan bai ganta ba haka ya hakkura da nemanta har shima tashi
ibtila,in yazo ya sameshi daga baya.

    Tasowan ta ke nan
kwana biyun nan ta dan fara jin karfin jikinta har tana da  fitowa tsakar gidan nata tadanyi wani abu don
rashim jikin nata har damuwan hakan takaita kwance a gidan.

     Wazata kira ta
sheda mai yanzu malam tanimune da kunnuwanta ba wani ya tsegunta mata zancen
shi ba akan jikan nata da yake sakewa a bayan idonta ita da kantane Allah
kawota ta tsurashi yana fadin maganganun da basu dace ba ga jikin nata lokacin.

  Don haka kuma sai
taga ai gara taja bakinta tayi shiru kada kuma a kara chamfa masu sabon zargi
bayan wanda take fama acikinsa na batan jikan nata yanzu kuma.

    Tuna shawaran
makwanciyanta tayi kan ba komai ake fadawa mutane ba yanzu don mutane basu da
tabbas a yanzu lalaikan ta sheda hakan ita don bata taba zaton cewa Tanimu zai
iya sukan ahalinta a wani wajen ba ai.

    Tun safe muka kama
hanya kamar yadda mukazo garin iya mu muka dauki hanya nasamu nayi sallama da
maryam munyi musayan lamba da ita.

   Nan Allah ya
taimakeni dana tafi bamu karbi layin juna ba don ba wanda yasan da cewa zamu
koma a ranan zaune nake kawai a cikin motan ina tunanen abubuwan da suka faru
wanda a yanzu na sani aka  mommy din da
bansan dasu ba a baya.

   Tabbas dakan bata
san waye wanan matar ba amma yanzu zuwa gidan su yasa ta kara fahintar cewa
bata shigo gidansu da zuciya daya ba ashe.

    Ita kan a gobe
zata koma gusau wurin mahaifiyata ba zata yarda ta kara wasu kwanaki ba a
gidansu na Abuja din kuma.

   Ba wanda yai mata
magana a motan don kusan duk sun sharetane ma za ace don ba wanda ya nuna ma
kulawanshi a kanta kamar yadda itama din suke mata kallon karamar yar iska mai
shegen wayau da jin kai da nuna isa da gadara don hakan da take masu sai ya
saka wani dan shakunta a zuciyar su.

  Don da watace tayi
masu wanan iskancin dasun nuna mata cewa bata isa ba amma yanzu a matsayin
makami take a wurin su don suna sonyin amfani da daman su yagi mahaifinta ta
hanyar ta.

    Wai har yanzu Zahra
fushin ake da mommy ne kome hjy karima ta fada acan gaban motan inda take zaune
din don ta kawar da komai dake tsakaninsu kada su isa Abujan haka da ita.

    A bazata zancen
yazowa zahran har ta dan juyo tana fadin lah fushi kuma mommy ni bana fushi da
kowa wallahi .

    Kina fushi mana
zahra son tun jiya baki sake jikin ki ba kina faman daure fuska ta dan murmusa
tace a,a mommy kawai dai gajiyace yasa kika gani haka don ban faye shiga mutane
ba ni haka nake ko a gida.

   Jin hakan yasa ta
dan kama janta da hira ita kuma zahra din tana da  biyewa tana bata amsa bayan kar take kallonta
da mamakin halaiyanta fam a zuciyar ta.

  Ko ta mata da cewa
ya mace tun tana kankanuwa take fara fahintar wasu halaiya na zamantakewa oho.

   A haka har suka isa
gida inda suka samu cewa yaran Alh sunzo maza daga kasan waje hakan sai yaiwa
zahra din dadi sosai ganin yayyen ta musa da Jafar a garin har su biyu.

Leave a Reply

Back to top button