TUMFAFIYA 12
Safara da marwa ta
fara yi a cikin daki lokaci guda abu ya taru ya zama biyu a kanta lokaci daya
ga mamakin hjy Salma ga kuma na Abba da yanzu ya barta dashi.
Meke shirin faruwa
danine a yanzu mama ta tambayi kanta
kafin ta wani juyo tana fadin wallahi karyan ki salma ko zan tafi ba komai a
gidan nan kinyi karya ki hau kaina a gidan nan kun tabbata a bayan mu har abada
keda zurian ki a gidan nan.
Mama kinga har an
fara min magana wai anga zarah ta faso gari yau kowa sai zancen motar ta yakeyi
garin nan Aisha yar kwalisan gidan mu ta fada daga kofa.
Jin hakan yasa
uwar juyowa tana fuskantar diyar nata don jin abinda take fadi din ta faso gari
tafi wa a cikkn ku don wanan motar data shiga shine finku da tayi ko me ?
To mama su mutane
suna iya ganewane sai su dauka ita wata abuce a cikin gidan nan tunda gashi har
su samira na fadi a group wai da motar da ita sun zama celibirty a garin nan ko
ina sai zancen ta akeyi yau.
Ana tura photunan
ta da motar haba dai mama saida nace kada ki bari ta shiga motar nan yanzu ga
abinda hakan yaja muna kaskanci a idon jama,a da komawa baya.
Aisha zaki barni
naji da abinda nakeji yanzu ko sai kin kara bata min rai zaki fice yanzun nan
da kika ganni nan mun gama waya da baban kune yake fada min wai shi yabada kudi
aka saya mata motar ashe ba baba ya sayaba shine ya saya nasan dai baban yaje
mashi da zancen .
Shine tunda saida
ya fara zancen dake anan kafin ya tafi shine dayaje gun abba yayi zancen da
Abba din Aisha ke fadin hakan a hasale.
Rukkaiyace ta turo
kofan ta shigo lokacin tana fadin wai kinji yan iskan nan har kirana sukayi
suna min sheri wai sun san idan zamu fasso gari tamu tafi wanan ke nan.
Ina ruwan su yan sa
ido da gulma ni mutane na ban mamaki ga sa ido kan abinda bai shafesu ba wanan
ai tsaban gulmane da munafunci dama ai haka ake son gani a wurin mu ko yaushe.
To mama meyasa Abba
zai yi muna haka yasaiwa zarah din ita kadai muya ware mu bai saya muna ba
gaskiya ki tambaya muna muji dalilin shi nayin hakan ?
Ke Aisha ki fita min ido ki barni inji da abinda ke
damuna a yanzu ko kin fini sanin abinda ya dace inyi ne kan hakan yanzu ?
Ganin ta dauki waya
ta fara magana da yar uwarta yasa suka fice a dakin ransu bace har lokacin suna
ci gaba da zancen wai ashe Abbane ya saya ma zarah mota bama ya musa ba yadda
suke zato .
Don haka dolene suma
Abban ya canza masu mota wanan lokacin wace tafi nawa idan yazo zasu sameshi da
zancen hakan tunda basu gane kan mama ba lokacin.
Bai koma gida ba
sai bayan sallah isha,i lokacin hankalin Dije ya tashi don bai saba yin haka ba
ya kai wani lokaci yana waje duk ritsi magariba a gida take mashi.
Sai gashi yau din
har yakai karfe tara saura yana waje yana shigo sukayi kicibis da Dije data
yafa zani a kai zata fita neman shi suka hade da ita a kofan su mai dan guntun
katanga a wurin.
A,a Amadi yau
lafiya haka ka tayar min da hankalina kaida uwar garke dataki ci abinci ko ruwan gidan nan taki ci tunda ta
dawo gidan nan.
Wai ina kashiga
haka tun sallah asuba da kafita kabar gidan nan baka dawo ba har wanan lokacin
haba Dije kin manta dani na mijine ?
Ban fita ba saidana
fada maki cewa yau asubanci zanyi naje kasuwa daga can kuma na wuce zuwa school
muna fitow na bazama cikin gari ina tallata kayana gashi kuma har Allah ya
taimaka an kwashe don haka wana somawa
akayi indai kaiwa darene ai yanzu.
Meya samu uwar
garke din kuma wai ana nufin har yanzu mutumin nan bai biyo bayanta bane ko me
abin ya fara daure min kai wallahi gashi kuma ban san gidan shi ba balle nabi
sawun shi na mayar mashi da ita ai.
Yana magana yake
kaiwa duke gaban uwar garke dake kwance tana tuka kamar wace tayi kiwo mai
tsayi tana hadiyewa a cikinta.
Hannu ya kai ya
shafa bayan ta a hankali yana magana da ita kamar da mutum dan uwanshi yake
zance yace haba uwar garke ko fushi kike da mune wai ?
Kiyi hakkuri muma
dole yasa muka badake ga wani gashi kuma da rabon mu sake zama dake Allah ya
nufa kin dawo garemu kuma kiyi hakkuri kici abinci ko ruwane kada kisamu illa a
jikin ki.
Kici don Allah ko
kisha ruwan yana kokarin mika mata ruwa a bakinta tare da shafan bayanta a
hankali tayi dan kuka lokaci guda tana mikewa tsaye ta wani girgiza jikinta
lokaci guda.
Zagayen shi ta
farayi kamar tana sunsunan jikin shi kafin ta dan tura kafanta na gaba ta kada
kwanon ruwan da ake zuba masu ruwan shansu ciki sai kuma ta dona kai a ruwan
tana sha har lokacin hannun shi na saman bayanta yana shafanta a hankali.
Ikon Allah yanzu
uwar garke haka zaki mani kiyi fushi dani kike karban abincin hannuna saina
Amadi, kinyi fushi ke nan dani ko me ?
Dan murmushi
Amadin yayi yana dagowa daga duken da yake yana fadin tayi fushi mana Dije
tunda ke kikaba da shawaran sayar da ita.
Dana bada shawaran
wa yakaita kasuwa ya sayar kawai dai har dabbobi sun san kitihi yanzu baiyi
magana ba ya dan tara yayin kara yaje murhun dije ya debo rushin wuta tazo ya
saka masu ya dan gyara wurin .
Hannayen shi ya
dauraye yayin da Dije ta juya zuwa cikin dakinta bai shigo dakin kai tsaye ba
saida ya kai kayan gwajon shi ya aje dakinshi kafin ya nufo wurin dije din yayi
sallama ya shiga.
Tana gaban fitilan
kwai donsu har lokacin basu da wuta a gidan su sai hasken na makwata dake dan
shigo masu kasancewan ginan su yayi kasa sosai a cikin shiya.
Yayi sallama ya
shiga yana fadin Dije yaya gidan ta amsa da gida lafiya Amadi ya kasuwan kace
ka taba ciniki a yau din ya amsa da wallahi Dije ni har abin ya bani mamaki
sosai wallahi.
Na dauka ai ba
zasu shiga ba sai gashi mutane na yaba min wurin zaben kaya haka masu kyau ashe
sana,a dadi gareshi Dije yau din nan da farawa kinga abinda na samu yana fito
mata da kudin tare da fadin ba wani riba sosai na dora sama ba.
Don maishi yace min
har in ina son naci riban abin kada na cika kudi da yawa a sana,a na zanfi gane
kan abin da sauri gashi ko nabi shawaran shi naga alheri a cikin harkan.
Ya baka shawaran
kwarai sosai gara daka bi shawaran nasa Allah ya umfana muna abin baki daya,
kudin ya jawo gaban shi ya kirga ya ware wasu yana fadin.
Wanan Dije a sai
abinci mu dinga girka abinci muma a gidan nan kamar gidan kowa sau uku yanzu a
rana don Allah kada ki matse kanki da yunwa kuma Dije.
Yaro ke nan banda
abinka Amadi farawa da iyawa saimu zauna mu kurmushe uwar kudin a cikin mu kuma
tun yanzu.
A, a Dije ba zamu
kurmushesu ba da yardan ubangiji Allah ne fa yai muna mafita ga hakan dama
tuntuni nabi shawaran ki da ban tsaya aiki da madam kan dan kudin da take ban
bai ko isa biyan kudin karatu na balle kuma muci daga ciki.
Datuntuni wanan
sana,an nakeyi mu huta zama a cikin kunci irin hakan ki dauka ki sayo kayan
abinci ko nan cikin unguwane kafin naje kasuwa idan na samu lokaci nasayo muna
.
Amadi kudin nan
yayi yawa ka rage don bakin mu mu kadai ko dari uku na saya muna abinda zamuci
ba tare da riya ba in sha Allahu.
To Dije yadda
kikace din ya mayar da sauran kudin nasa cikin aljihun shi yayi shiru na dan
lokaci zancen karatun yaran nan ne ya fado mai a rai lokaci guda yaja tsuki don
yana ganin zasu ja mashi cikas a cikin sana,anshi kan wanan karatun nasu .
Shiya rasa yadda
akayi ma har ya bari sabo da shakuwa ya shiga tsakanjn shi da wani wani ma macen kuma yar mai kudi irin haka da zasu
moreshi a banza.
Taimakone ai
taimako taimako kuma baka san inda za a rama makashi ba gashi dai shine mai
taimakon nasu har yanzu dai.
Washe gari kamar
jiya ya fita amma bai yarda ya bar gida ba saida ya duba uwar gareke ya gyara
masu wuri ya aje abinci ya dan shafa bayanta yana fadin kiyi kiwo ki koshi
kinji uwar garke don Allah.
Yana fita masalaci
yaje yabi jam,i daga nan ya fito kasuwa ya nufa ya samu babu mutane sosai ya
zabi irin kayan daya kula ana so da ake tambayan shi.
Ya baro kasuwa zuwa
school ya kasance jumma,a don haka daga masallaci ya shiga yawata kayan shi a
cikin gari ya samu ya taba ciniki sosai a rana .
Yana ganin abubuwan
amfani irin su kayan miya yana dan tsunta a gari har su alaihu da shinkafa don
yasan Dije ba zata sayo ba tunda ba wasu kudi masu yawa a hannunta .
Wanan sayayyan da
yayi sashi shawaran komawa gida da wuri ya sake biyawa kasuwa ya kara zaban
kaya gredi daya samu an bude a lokacin.
Daga nan yayo gida
ya samu Dije a bakin murhu tana hada miya don har ta kwashe tuwon garin masara
data sayo a cikin unguwa miya ya rage ta hada.
Sallaman shi yasata
juyawa tana amsa mashi sallaman tare da fadin yau an dawo da wuri ke nan yace
to kinyi fadan dare jiya Dije.
Kayan da ya dauko
niki niki ya aje a gefen ta bau tsaya ba ya nufi garke ya duba yar amanan shi
uwargarke tana tsaye tana kiwo ya kara mata abinci ya kara gyaran wurin.
Dije data gama
duban ledan tace kai dan nan har shinkafa ka sayo muna yau gidan tana mamaki
Allah ne ya bamu sa, a ya nufemu da cinta a yau.
Nikan na riga dana
tuka tuwon masara ga miyan yakuwa dana tsunko gidan malam Tanimu nan ina muna
miya dashi yanzu muci.
Dan guntun murmushi
ya sake a fuskanshi yana fadin ai bai baci ba Dije Allah ya kaimu gobe lafiya
sai a girka a ci naman daine sai an gyara shi yau kada ya lalace.
Har nama ka sayo
kace yau take sallah a wurin mu ke nan yau din nan nama kan dole a gyarashi
kada ya lalace kafin gobe.
Tana magana tare
da jawo ledan zuwa gabanta kaikai Amadi wanan ai kudi ya wahala a nan Allah
yasa albarka sai ayi a hankali kada mu murkushe kudin mu koma zaune kuma.
Dan murmushin
gefen baki yayi daga inda yake zaune dirsha a kasa yana kallonta kafin ya mika
hannunshi zuwa wajen butan dake gefenshi
ruwa ya gunda a baki ya kurkure bakin kafin ya zauna da kyau ya fara alwala..
Na dawo a gajiye
Rukkaiya muka fara haduwa da ita daga irin kallon data watsa min na gane akwai
wata a kasa ke nan don ko dan tsayawa ko mu gaisa irin yadda muka saba a ranan
bamu yishi ba a tsakanin mu.
Sai ta wuce na
wuce kowa yaja iska a tsakanin mu ya wuce dan uwa naga karfin halina ga yin
hakan na shige part din ranan kanne na basu da lesson sun dawo gida da wuri duk
suna falo.
Na yaye gyalen
dana yafa a kaina nan suka shiga gaidani da dawowa ina amsa masu na nufi
bedroom din mahaifiyar mu don in gaida ita .
Tana zaune bakin
gado tana waya da hjy maryam kawar ta dake Abuja har yanzun da zama ita da
mijinta da yaranta.
Zan iya cewa hjy
maryam ce makwaciyar da tun zuwan ummah Abuja suke tare sun koma kamar yan uwa
a yadda naji suna maganan zuciyana ya bani wani abu mai muhinmanci ya faru
tsakanin mama da ummah ko Abbah.
Ganin hankalita
naga wayan yasa nayi mata sannu ummah ya gida ta gyada min kai na juya na tafi
na barta yadda na sameta zaune din hankalin ta a kan wayan.
Kamar yaddana saba
ina shiga na wurgar da jakkana saman gado ban daki na shiga na gyaro jikina
tsab ta hanyar rage wanke matse matsina da sabulu mai kamshi tare da dan tsane
jikina na da tawul na fito na kwabe kayan jikina na saka na zaman gida.
Yunwa nake ji don
haka na nufi falo don in samu abinda naciwa cikina lokacin abincina yana ajiye
kamar kullun.
Zama karamin kanin
mu ya taso shima zaici nan sauran suka nufo suma macen na tura ta dauko masu
spoon muka zauna tare dasu munaci a haka ummah ta fito ta samemu.
Salati ta saka
kafin ta nufo su tana masu fada don me ba zasu barni naci hankali kwance ba
suka zauna min ga abinci ?
Ummah idan inaci
dasu nafi cin abincin da yawa wani
kallona ke kika sani ta watsa min nayi murmushi har takai kofan fita zuwa
kitchen ta juyo tana fadin.
Ina kika aje key
din motar taki tana tambaya take kallona taji amsan da zan bata na gyarawa
kanina dake saman jikina zama nake fadin yana cikin jakata na aje.
Ki kula kada wani
ya dauko ko idan kin dawo ki rika ajeshi a dakina don mutanen nan sherinsu yawa
gareshi tunda ban bata key din da girma da arziki ba yadda taso.
Don haka ki kula
sosai da tuki da kuma kanki a yanzu komai da kikeyi idon mutane yana kanki
yanzu don komai ya canza yadda kuka sanshi a baya gidan nan.
Abban kuma yace
naje maki kunne da kikula kada samun motan nan ya canza maki rayuwan ki a yanzu
kici gaba da dabi,un daya sanki dasu abaya kinayi.
In sha Allahu ummah
na fada a sanyaye tare da dukar da kaina kasa kafin na dago tashige ciki ta
barni da kannena surutu suke min amma ban fahintar me suke fadi a lokacin.
Tunda na shige
dakin kwanana ban sake fitowa falon ba na kwanta iya tunane nayishi a lokacin narasa
gano dalilin sauyawan gidan mu yanzu cikin dan kankanin lokacin komai ya dagule
a tsakanin iyayyen kuma.
Wace ta haifi
mahaifin mu tana raye a duniya gidan mu baida nisa sosai da inda take don inda
iyayyen mu suka fara zama da farko yanzu itace ciki zaune don kamar a family
house din mu suke.
Don haka ganin ba
school da safe na na kwashi yan kannena mukaje gida mu gaida ita kusan duk sati haka muke zuwa
gidan duk da har na fahinci ba wani sin mu takeyi sosai kamar yadda take son su
Aisha ba amma ban bari wanan yayi tasiri a zuciyana ba game da ita.
Da sabon motan
muka fita zuwa gidan muna zuwa naga motan mama pack a kofan gidan kafin mu fito
muka hangosu suna fitowa daga cikin gida ina kallon suna nuna mata motan namu.
Kafin su karaso sun
tsaya magana muka nufi wurin iyayyen mu maza muka fara gaidasu don suna kofan
gida suna shan hantsi a lokacin.
Har suka wuce bamu
shiga wurin kakan tamu ba muna can muna gaisawa da mutanen arziki lokacin a
cikkn gida don gidan namua babban gidane sosai.
Mun fito mun samu
sun tafi kai tsaye wurin kaka tamu muka
nufa sallama nakeyi amma muryan tsohuwa yana tashi a cikin hausan mutanen
zamfara tana fadin .
Ni za a kawowa iya
shege da raina ka fara nuna bambanci a tsakanin diyan ka dame ita takwaran nawa
tafi yan uwanta da zai saya mata mota ya kyale sauran.
Sallama na karayi
cikin daga murya sai lokacin aka amsa muna muka shiga tana fadin watace mune
hjy na bude labule na shiga don tun ban shiga ba na fahinci a taikace kara mama
da yaranta suka kawo wurin hjy ke nan .
Au jikokin gal ne
haba mama wata gwaggon dake zaune tare da ita ta fada cikin bacin rai kafin ta
dora da fadin haba hjy bai kamata ba hakan nan don Allah.
Kamar ban fahinci
me suke zancen ba na aje mata ledan da muka saba zo mata dashi a gefe nakai
zaune gefenta ina fadin tsohuwa mai ran karfe kin tashi lafiya ?
Har lokacin akwai
sauran bacin rai a fuskanta ta amsa min kadaran kada ham tana fadin kema kin
tashi lafiya yaya uwar taku ?
Tana lafiya tace mu
gaida dake ga wanan tace a kawo maku nan muka gaida gwaggon namu muna dan hira
sama sama tsohuwar ta fuske damu.
Can nace hjy akwai
fura a fridge din ki ban sayaba uban naki bai aiko min da kudin saya ba tunda
yanzu ya fara mikawa yara kanana kaddarorin miliyoyi suyi yadda ransu keso
dashi.
A, a hjy badai
Abbamu ba kan idan bashi ba wane zai dinga wullakanta kudi haka ke wanan motar
da kike shige yanzu bai isheki ba sai
kun tursasashi ya sayo maki wani ?