Hausa NovelsTabarmar Kashi Book 2

Tabarmar Kashi Book 2 Page 18

Sponsored Links

TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 18

Hawaye sosai takeyi tana shafa labban nata da suke mata zugi, anya ba baki afifa tayi mata ba? ‚idan ba haka ba me yasa yake mata kwarjini har haka?
“Martabar aure” amsar da zucivarta ta sake nanata mata kenan kamar yadda afifa ta gaya mata. Motsin fadee ne ya sanyata saurin share fuskarta da daidaita kanta. Ai tana hada idanu da sãahar din ta wantsalo gaba daya daga saman gadon ta qanqameta tana kiran

“Anty N,good morning” rungumeta itama tayi sosai cikin jikinta,a hankali takejin wani farinciki, bacin ran dake lullube a zuciyarta ya dinga zagwanyewa. Sun jima a haka sannan ta dagata tana kallonta

“Chubby fadeela ina wanka?” Kai ta langabe a shagwabe

“Sai kinzo ke zakiyimin” dariya tadan saki

“Kin fara girma fa,muje na gani” sai ta riqe hannunta suka wuce toilet din.

Sanda suka fito tana tsane mata jikinta aka tura gofar aka shigo. Baaba ramatu ce suna hada ido da sãahar ta tambayeta

“Ya akayi baaba” dab da ita ta iso, ta dan waiwaya ta kalli bakin gofa ta tabbatar a rufe take sannan ta warware bakin zaninta, wata leda ta ciro tayi saurin migawa sahar,sai sãahar din tasa hannu ta karba tana jinjina kai

“Kome ya tafi dai dai, tun bayan tafiyarki wannan magungunan take sha, ina lissafawa a cikin wadancan ina cirewa ina zubarwa kamar vadda kika kwatanta min, amma an samu matsala daga dawowar hajiya” baaba ramatu ta fada fuskarta tana canzawa, tadan sharce gumi, sãahar ta zuba mata ido gabanta yana faduwa

“Matsalar me baaba?”

“Daga dawowar matar nan da kanta take sanya fadeela a gaba da magungunan nan,yau kwana biyu nata take bata tana sha,duk wata hanya da zanbi na kauda afkuwar hakan wallahi nayi amma baiyuwu ba” baaba ramatu ta fada hawaye yana cika mata ido, tana jin bacin rai har cikin ranta na vadda tsahon shekaru tana zaune ana wasu abubuwan amma rashin ilimin zamani yasa bata fahimta. Sosai säahar taji hankalinta yayi mugun tashi,ta dinga jinjina kai tana jin tsohon bacin ranta yana motsawa, a lokacin ta’addancin da adam yayi mata sa qwayoyin magani ne suka dinga dawo mata, ba zata bari ba kuwa haka ya faru tare da innocent fadeela ba

“Zan yiwa tufkar hanci” ta fada a sarari, cikin zuciyarta tana jin zatayi amfani da nata power din da take dashi a yanzu na matar uban fadeela, duk da bawai tana tutiya da wannan matsayin bane.

Kwanaki biyun da maji ta qara cikin gidan säahar gurinta take wuni, tun daga ranar basu kuma haduwa da toufeeq ba saidai a wajen maji,idan ya shigo din ba wani dogon zama yakeyi ba,sosai ta fuskanci abubuwa da yawa,kamar rashin sabo da sakewa tsakaninsa da maji din,duk majin tana bakin qoqarin gain ta jashi a jikinta amma wasu abubuwan basu yiwuwa. Gurinsu maji take yini tare da fadee dinta ga nadeeya,rana ta uku majin ta gama shirin tafiyarta,a safiyar da zasu wuce
airport, dukkansu suna gaban motar da zasu wuce da
rakiyar nadeeya fadeela da toufeeq.

Su libril ke shirya komai,toufeeq din yana sassansa
bai kammala fitowa ba,suna tsaye dukkansu gaban
motar cikin alhinin tafiyar maji,ji sukeyi kamar su hanata
tafiyar, säahar a cikin jiki da zuciyarta takejin babu dadi
qwarai. Hannun säahar maii ta kamo tana murmushi

“Karki damu d’iyata,bazan dauki dogon lokaci ba zan
dawo, dawowar da nake kyautata zaton zan jima ban
koma Algeria ba,akwai kasuwancin da na fara
processing nasa a nan, bana tunanin zan wuce wata uku
ko biyu ma ban dawo ba” wannan albishir din shi yafi
komai faranta ran säahar, ta rige hannun maji sosai tana
murmushi dai dai lokacin da yake takowa zuwa gurin.
Sanye yake da wani baby cashmere da aka yiwa
lafiyayyen dinki wanda yabi jikinsa ya dace da
yanayinsa, ya kuma fitar da structure dinsa sosai yau din
ya saka hula saman kanshi, abinda sãahar din bata taba
gani ba kenan,hakan sai ya sake canza fuskanshi,ya fito
a cikakken shuwa dinsa ya tashi daga launin larabawan
Algeria. Ido suka hada,sai ta janye daga kallonsa tana
hade rai,can gasan ransa ya murmusa a karon farko
bayan da ya karanci wani abu saman fuskarta. Ta kalleshi
ne ba tare da kowa ya tilasta mata ba,amma kuma bayan ya ganta tana kallon nasa sai ranta ya baci tana tuhumar
kanta da kanta. Yau kwana biyu cur bai ganta ba,baisan
a wanne bigire zai sakata ba, amma tuni ya fara karantar
wasu halayen nata,bayan tsiwar da ya samu ya rage mata run randa ya yuwa labbanta wawan kamu,ya fahimci tana kafiya taurin kai da tsaiwa akan ra’ayinta.
Zarmewa idanunsa sukayi da kallon labbanta,sun koma normal,wasu irin soft and tiny lips, masu wani irin pinky color me dan duhu. Idonsa yayi hanzarin daukewa yana lumshe idanunsa tare da budewa duka lokaci guda cikin kaucewa gamuwar idanunsu, kada taga yana kallonta ta rainashi.

Isowarsa gurin ya dawo da hankalin maji kansa,ta saki garamin murmushi lokacin da yake duqawa har qasa saman gafafunsa yana gaidata,abinda ya sanyawa guard dinsa saurin juyawa suka basu baya. Ido itama sãahar ta dauke tana jin wani abu yana ratsa zuciyarta,karon farko da bataji feeling na rashin burgeta ba tattare dashi.

Dabi’arsa guda daya da zata iya zanawa tace me kyau ce,daga kan maji har dr jarma ba zatace ga lokacin da taga ya gaidasu a tsaye ba. Fadeela ce ta matso tayl kissing kumatunsa dake da wani kwantacciyar qasumba me laushi wadda bata cika yawa ba,tana ta fitar d qamshin hair mist da kuma qyallin mayukan da tasha gyara dasu,sai ta zame ta tsugunna tana gaidashi kamar yadda taga ya yiwa maji,dama kusan tun bayan zuwan sãahar gidan ta dorata akan hakan

“Barka da asuba abby” ta fada da salon da sahar din keyin gaisuwa, murmushi ya saja yana dan jan kumatunta

“Barka da asuba abby, a ina kika canza yadda aje gaisuwa?” Tana dariya ta kalli sahar da sam tagi tsaida idanunta a sashen

“Aunty N ce, haka take gaida mutane” basarwa yayi kamar bashi ya tambayu fadeela ba. Hannunsa maii ta kama ta migar dashi, tasa daya hannun ta kamo hannun sãahar,rigota din da tayi shine ya sanyata waiwayowa tana duban maji din. Hade hannayen nasu tayi guri daya,lallausan tafin hannunsa ya sauka cikin nata tafin hannun me wani irin taushi da dumi. A take tsigar jikinsa ta zuba wani irin dumin hannun yana ratsa jikinsa da wani gudu kamar gudun jini a kowanne sashe na jiki.

Itama motsa hannun nata tayi saidai ba damar ta janye saboda maji ta lullube nata hannayen da nasu tana duban idanun kowannensu

“Na baki amanar d’ana da jilkata na baki amana” sai ta waiwaya ga toufeed

“Na baka amanar diyata, ka kula da ita ka kula da mutuncinta, ka tsare mata dukka
buqatunta,mutuncinta naka ne, amanar Allah ce a wajenka daga gurin iyayenta kamar yadda abbanka ya gaya maka”. Dukkansu babu wanda baiji ta dora masa wani nauyi ba,ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba a cikinsu. Karo na biyu hannuwansu suka sake gamuwa wajen qoqarin da kowa keyi tsakanin shi da ita na budewa maji qofar mota, sahar dince ta fara janye hannu kamar wadda wuta ta jata, tayi gefe da hannun tana yarfarwa,ya ganta amma sai yayi kamar bai ganta ba,saida maji ta shiga ya sakewa nadeeva gofar suka shiga ita da fadeela. Da hannu ya yiwa elyas magana, sai gashi ya matso da sauri ya bashi key din motar,ya shiga seat din driver duk sai sukaja baya,don haka yana nuna musu da kansa zai tuga mamarsa
kenan.

“Yayi wuri ki fara fita diyata,da sai nace kema ki shigo.” maji ta fada tana murmushi, cikin alkunya sãahar tayi qasa da kanta taja baya tana daga musu hannu sanda motar ta fara fita a gidan.

Ana kammala rufe makeken gate din gidan ta juya cikin jin kewa,muryar daya daga cikin masu aikin gidan taji a bayanta

“Madam hajiya garama tana kira” da mamaki ta waiwayo tana kallonta,mamakin kiran da take mata na meye? batajin zata iya taka sassan matar bare ta saurareta,gaba daya babu wata daraja tata data rage mata yanzun a idanunta sai ‘yar kadan, ita dinma ta dosaneta ne a dalilin martabar dr jarma

“Kice mata zan shigo” kawai iya abinda ta fadi kenan ta wuce sassan su fadeela tana juya kiran a ranta.

Gyaran dakin fadeela ta soma,wanda ya tsaye mata a
rai,tun lokacin takeson gyarawar, amma nauyin maii bazai
barta ta sake ta gyara din ba.

Ta kammala gyara komai tana goge dressing table na
fadeela tare da kwashe hoodie towels dinta na wanka taji
an buda gofar,a nutse ta waiwaya, idonta ya sauka kan
hajiya qarama,sai ta ajjiye dukka towels din dake
hannuta ta juyo tana goye hannunta a qirjinta tana
dubanta kamar vadda itama take kallon nata. Tunda take
bata taba jin qwarin gwiwa akan kowanne mutum ba
kamar yadda takeji yanzu akan hajiya qaraman ba,daga
sanda ta fahimei magungunan bogi take baiwa fadeela
taji tayi mata wata muguwar tsana,sai take mata kallon
kamar wata jini ko ‘yaruwa ga adam, amma har yau tana
cike da mamakin dalilin da yasa take bawa fadeela
magungunan da ba likitanta bane ya rubutasu ba, meye a
cikin ranta? me vasa take yiwa yarinyar da take qaunarta
haka?,a zahiri kowa.yana yaba yadda fadeela ke
sonta kowa kuma vana yaba yadda itama take nuna
damuwarta da kulawarta akan yarinyar.
“Fada da aliani fa ba dadi……Ina kyautata zaton baki taba
sanin wacece ni ba ko?” Tsaf tayi karatun fuskarta na
wasu ‘yan mintuna
“‘Me sanin hakan zai amfana min?” Ta maida mata amsa
kai tsaye, a yanzun bata jin zata qyale duk wani wanda
baisan darajarta ya takata ba. Wani shu’umin murmushi

hajiya qarama ta saki
“Yaro baisan wuta ba sai ya taka,sanin ni wacece bazai miki dadi ba sam,abu daya zan zaya miki,ki samawa kanki lafiya da salama,ki watsar da dukka wata huduba da uwar mijinki tayi miki muddin kinason ki qarasa kwanakinki da suka rage miki a gidan nan lafiya lau” murmushi sãahar ta sakar mata ta juya tana ci gaba da aikinta,zatonta da zarginta akan matar yana sake qarfafa,dukka wani haushi nata dake tattare da adam tana jin a yanzu ta samu damar saukeshi akan hajiya qaraman ne,tayi imanin idan akwai banbanci tsakanin hajiya garama da adam to na jinsi ne kawai ,komai nata ya gama bayyana a idanunta,a yanzun tana jin zargi me garfi da rashin yarda da matar yana shigarta

“Duk wannan ba matsalata bace, matsalata daya kibar rayuwar fadeela ta samu salama,ki daina ci gaba da birkita kwanyar da take neman ta rayu da cikakken hankali da bawa gangar jikin data mallaketa kariya da ingatacciyar rayuwa” Wani mugun shock hajya qarama taji

“What!” Ta furta a rude tana duban fuskar säahar. Kallon tsakiyar idanu sãahar din tayi mata tana gyada mata kai

“Basai kince min eh kinayi ko a’ah ba haka bane, umarni

dava ne zan bayar, a matsayina na matar ubanta…wadda a yanzu take a mazaunin uwa a gareta,daga yau kula da lafiyarta da alhakin shan magungunanta yana wuyana,ban yarda ba ban lamunce kowa va sake baiwa fadeela magani ba, koda uban da ya haifeta ne!” Ta fada da kakkausar murya. Kamar ba zatayi respond ba saita saki murmushi tana duban saahar
“Kada ki qirqiri game din da bazaki iya kai qarshenta ba”

“Ba game nakeyi ba,ba kuma maganarta nakeyi ba, saboda ni din ba ‘yar wasa bace, ina gaya miki magana ne ta zahiri” ta sake jaddadawa hajiya qaraman ba tare data dubeta ba bata kuma fasa aikin da takeyi ba

“Idan kina ganin abune me sauqi yin hakan ki gwada aikatawa” hajiya qarama ta fada tana juyawa ta fita a dakin,don dukka kalaman bakinta sun gama qarewa,abu daya ta sani ya zame mata dole ta fara gamawa da saahar. Sai a yanzu ta fuskanci ba qaramar barazana bace a gareta, ita din wata babbar barazana ce da zata iya wargaza shirinta na shekara da shekaru. Abinda ta yita gudu kenan,ta sake tsanantawa wajen gain toufeeq bai rabi kowacce mace ba sai d’iyarta MEENAL AJI.

Dogon tsaki säahar ta sauke bayan fitar hajiya qaraman, gefan kanta ya saara tadan dafeshi kadan,a duk sanda zata tuna abinda ya shafu rayuwarta a baya saita shiga yanayi,ashe har yanzu akwai ragowar

azzaluman mutane irin adam a duniya? bama cikin jinsin maza ba kawai harda wai mace?,macen da aka santa da rauni? waishin meye dalilin hajiya qarama ne?, me take shiryawa?.

_tambayoyin dani kaina bansan amsarsu ba,saidai lokaci zai bayyana mana komai
[18/09, 7:21 pm] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_*

Leave a Reply

Back to top button