Matan Ko Mazan 2
đ« MATAN??? Ko MAZAN???đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ
Binsu da kallo Nura yayi yadan sauke ijiyan zuciya koba komi tayi shiru yanzu, komawa falo yayi yakunna wuta yazauna kan kujera, yadawo ko chanza kaya baiyiba, bai wanka ba ranshi yabaci, kunna tv yayi yana kallon news dudda hankalinshi bawai yana wajen bane dan damuwa ne cike fal aranshi. Yana zaune awajen Amal tafito da kanta rikeda karamin bowl da aka soya kwai mai kyau aciki tace âDaddyyyy Oumu Oumuâ tana nunamai bowl din, dan murmushi yayi tazo kusada shi daukanta yayi yazaunar da ita saman kujera kusadashi tahauci, ruwa Ummi tabiyota dashi a water bottle nata mai kyau ta ijiye agabanta takoma chan nesa dasu wajen dinning tazauna akasa duk atakure take dan batama saba ganin mai gidan ba, kusan 1yr tana aiki agidan itada yaran sukafi zama agidan nan, sai yau ne take ganinshi hakan yasa duk takejinta atakure. Dauke kanshi Nura yayi dagakan tv ya kalleta yanda tazauna akasa kaman wata mara daraja irin yar maulan nan dukta takure tana wasa da hannunta bini bini tana kallon Amal dakecin kwai abinta da hannu kusada shi yasa yadanji wani iri, he always hate yan aiki to be honest yaune rana ma na farko daya taba kallo fuskan yarinyar nan dake musu aiki agida kuma this is almost 1yr take gidan nan, ba yabo ba fallasa yace âjeki kwanta kiyi bacciâ kanta akasa cikeda respect tace âsaita gama cin abinci na wanke mata hannu na gyara wajen nasata bacci tukunna zan iya bacciâ dan jinjina kai yayi saikuma yayi shiru bai kara cewa komiba, yakai hannunshi yataba wuyan Amal din jikinta yadan rage zafi maybe sabida ruwan daya watsa mata neyamaida idanunshi kan TV, tass Amal tacinye kwan ta cillar da plate kasa tace âakoshiâ dasauri Ummi ta taho ta duka tadauki plate din da cokalin adan kunyace dan sheâs not comfortable yanda Baban ke wajen tamika mata hannu tace âzo aje a wanke hannuâ makemata kafada Amal tayi zata kama Babanta da hannun kwai dasauri ya matsa yace âje princess awanke miki hannuâ turo baki tayi takalli Ummi dake kallonta, cikeda dabara da iya wasa da yara tace âzomuje muyi wasa da pampoo akitchenâ wani kalan dirkowa Amal tayi abin harsaida yabama Baban mamaki tazo gaban Ummi da dugudu tace âruwaaa, pampooâ da sauri Ummi taduka ta dauketa tana murmushi tace âyauwa Amalulu na muje, idan Aman yatashi gobe shima mu soyamai Omu Omu koâ? Gyadamata kai Amal tayi sukatafi kitchen, dan ijiyan zuciya yasauke to some extend kam sheâs good with kids kawaidai shi bayason yan aiki ne and he donât trust hygiene dinsu, dan ijiyan zuciya kuma yasauke idan ba yan aikin ba yasan Hadiza ba aikin nan zatayi ba ko sama da kasa zata hade.
Tass ta wanke mata hannu ta share mata baki tare suka wanke plate da spoon din tace âyanzu sai bacci ko, nagoyakiâ? Gyadamata kai Amal tayi Ummi ta duka tace âyauwa babuuu Amalilyâ da gudu tahau bayanta tana murna dariya tayi bataso tasake fitowa daga kitchen din hakan yasa sai kawai tacire dankwalin kanta ta warware ta goyata dashi, wasu manya manyan kitson hannu ne akanta shiku ya tsufa sosai amman tanada bakin gashi mai kyau da santsi, zagaye kitchen din tashigayi da ita tana jijjigata tana mata waka ahankali. âAmal Amal yar gayu, Amal yar kyakkyawa, Amal yar fara saidai tana fitsari agadoâ dan ihu kadan Amal tayi tana hamma Ummi tai dariya tace âto nadaina Amal bata fitsari agado, Amal jaruma ce gimbiya mai kafafun zinare yi bacci toâ haka tadinga jijjigata tana zagaye katon kitchen din nan da ita dantai bacci. Gajiya yayi da zama afalo dan dama jira yake agama wanke mata hannu yadauketa suje sama gashi kusan 30min shiru basu fito daga kitchen ba, baki yabude zai kwalama Yarinyar kira yakasa, shi wlh ya manta sunanta kuma is somehow yakirata yar aiki, dan tsaki yayi yamike tareda kashe tv yatafi wajen kitchen din, kofan abude hangota yayi tana tafiya a kitchen din tana jijjiga Amal data fara bacci abayanta suna zagaye, ko kadan bata luradashi ba dan bekai gaban kitchen dinba, yanda yaga take zagaye take jijjiga Amal abayanta gently tapping her bombom ta saman zanin goyo tana mata wake haka sai kawai hakanan yaji yaji wani iri aranshi, he canât even understand idan guilt yakeji ko anger, wannan wani kalan rayuwane ace mahaifiyar Yarinyar na bacci anbar yar aiki da yarinya bata runtsaba tsakar dare, tun 9 yanzu kusan 3 idanunta biyu, is she not human being ita? Ko machine ce? Kowa fa deserves this sleep, dare mahutan bawa, koda aikinta ne thereâs nothing bad idan Maman yarinyar natare dasu to help her out, abin is really really somehow azuciyanshi, jiyayi ranshi yamai badadi dauke kai yayi tareda dan gyaran murya batare daya karasa kitchen dinba, dasauri Ummi tajuyo jin gyaran murya, batare daya kalli kitchen dinba yace âkawota taje ta kwantaâ dasauri Ummi tace âtoâ goyon tashiga kwancewa kafin ta sauketa tafara jan dan kwalinta ta jefa akanta sannan ta dauketa a hannu tariga tai bacci ta taho ahankali har zuwa gabanshi tamikamai ita tace âgata Alajiâ dan juyowa yayi yakalleta ahankali yasa hannunshi ya karbeta yace âsannu da kokari, jeki huta kemaâ âtoâ ta amsa tana tsaye awajen, wucewa yayi itama tawuce falo takashe wuta sannan takoma dakinta ko 1min bata karaba sai bacci.
**
Wuraren 5 yabude ido sabida zafin jikin Amal data kwana dakinshi, tashi yayi zaune yakai hannunshi yatabata yarinyar nan needs hospital wucewa yayi yashiga bayi ya watsa ruwa yafito daure da alwala yawuce yasauka kasa motsi dayaji a kitchen yasa yawuce kitchen yar aikin yagani tana sharara da goge goge jin knocking kofa yasa ta dago kanta dasauri ganinshi yasa ta duka tace âina kwana Alhajiâ juyawa yayi yace âlpy lau kibar aikin nan kije ki shirya Amal ina dawowa daga masallaci zamu kaita asibitiâ bai tsaya jiran amsanta ba yawuce, wanke hannunta tayi ta tafi sama azuciyanta tace Allah sarki Amal dina, dakinta taje ganin bata ciki yasa ta tafi dakin Aman yana baccin shi shikadai batanan to ko dakin Maman take bude dakin tayi da sallama bata wajen hakan yasa tai tunanin dakin Baban, idan da sabo tasaba shiga dan ita ke gyara dakin ta wanke bayi, bude kofa dakin tayi tadauki Amal dake bacci tawuce dakinta wanka tamata ta shiryata tsaf itama tai salla nan da nan tai parking jaka taje kitchen agurguje tamata air frying chips da sausage tasa mata a cute flask nata da ruwa tahada komi da yaro ke bukata, itama taje ta chanza kaya zuwa wani dan dogon Riga baki ba laifi yanada kyau but irin outdated one din nanne shima Anty tabata ta yana gyalen akai tazauna a falo rikeda Amal da yanzu bamata da karfi, shigowa yayi gidan ganinta zaune akasa afalo rikeda Amal data shiryata tsaf in this short time yasa yace âletâs goâ dan kallonshi tayi saikuma ta tashi da sauri, harya zauna agaban mota yaga tafito ta kinkimo Amal da katon jakan a hannu tana tafiya da kyar kaman zata fadi yasa kawai yafito yataho da sauri, tsayawa Ummi tayi gabanta nafaduwa ganin yanda ya dumfarota, hannunshi yamika mata yace âbani jakanâ bashi tayi yajuya itama tabishi bude bayan motan yayi ya ijiye jakan ya tsaya yana jiranta tana tahowa tashiga baya rikeda Amal saida tai settling down yamaida kofan yarufe yakoma gaba yashiga yatada motan yaja duk wani motsi da Amal zatayi saita tambayeta menene, ciwo, zafi, me kikeso, zakisha ruwa sannu ko Amal dina abinda baitaba ganin Mamanta tayiba.
Wani babban asibiti suka tafi wannan karan shiya sauko yabude musu baya da kanshi yadauki jakan yabar mata Amal dayaga tai lakur ajikinta suna shiga aka karbesu sukai ciki office na Dr suka shiga, wani baturen Dr ne yace âmeke damuntaâ? Kallon Ummi Nura yayi yace âmeke damuntaâ ahankali tace âzazzabi take tun kwana biyu bata iyacin abinci, but nafada ma Anty tadubata tace chanjin yanayi ne, jiya tanata tari sai zazzabi, kuma idan tashiga flowers na gidanmu jikinta na kaikayi, idanunta namata kaikayi shima, jiya batai bacci ba kagani kuma yanzu batada karfi ko kadanâ tanuna Amal dake jikinta kaman zatai kuka, sosai Nura ke kallonta saikuma yadauke kai yama Dr bayani da turenci Dr yace âzaâa basu gado cus tana running temprature da yawa kafin a debi jininta aga meke damunta, tashi yayi zai debi jininta da sabuwan alluran daya bude dasauri Ummi takalli alluran tadan kankame Amal ajikinta, ahankali Nura dake lurada ita yamika mata hannu yace âkawotaâ batai musu ba bashi Amal tayi Dr yadebi jininta hawaye taruwa yayi a idanunta yabda Amal ke kuka nan da nan aka kwantar dasu awani private room sai kuka Amal take tana mikama Ummi hannu, kasa zuwa Ummi tayi ganin Babanta natare da ita tashi Nura yayi yakalli Ummi yace âzo ketake nemaâ kaman jira take dasauri taje rungume Amal Ummi tayi tace âlikitan nan ko saimun kaishi wajen police yama Amal allura da zafiâ? Gyadamata kai Amal tayi a shagwabe, Ummi tace âsannu ko, zakisha Capri riâ? Dan yatsine fuska Nura yayi irin menene Capri ri kuma, Gyadamata kai Amal tayi, dasauri Ummi tabude jaka tadauko caprisone tace âtadaaaaaâ wani kalan murmushi Amal tayi dashi kanshi Nura saida yayi murmushin yadan tabe baki yaciro wayanshi aranshi yace âomelette Omu Omu, Caprisone kuma Capri ri ikon Allahâ tana cikin bata juice din wayanta dake pocket din jakan kayan Amal yashiga ringing da sauri tasa hannunta daya taciro wata screen touch Vivo ne dataji jiki sosai ganin Anty yasa ta amsa takai wayan kunnenta cikeda girmamawa tace âHello Anty ina kwanaâ daga ta dayan bangaren Hadiza tace âkina ina Aman yatashiâ? Cikin kwantacciyan murya tace âUhmm Anty munzo asibiti da Amal ne, jikinta ya rikiceâ Hadiza najin haka tasan mijinta ne yakawosu asibitin cikeda masifa tace âto yanzu wazai yima Aman brush da wanka yabashi breakfast eh? Ko nine danake shirin fita aiki yanzu zan tsaya nayi all of this, maza maza ki bar Amal wajen Babanta ki kira bolt yazo ya maidoki gida ai nakoya miki yanda ake yin bolt dan nasan nace kifita kije kibi mota along bacewa zakiyi babu inda kika sani, maza maza kira bolt and come back home kima Aman wanka kibashi breakfast ki shiryashi yatafi school kafin school bus yazo keko school bus yazo idan sun tafi ki kira bolt ki kaishi school din dakanki, kina jina tunda ke mahaukaciya ce dakikiya yar kauye dayace kizo kutafi asibiti bazaki iya gayamai zakiyi aiki ba kika bishi, nabaki 3min karki bari su cika ban ganki agidan nan ba, sabida jakanci da dakikanci irin na yan kauye ina biyanki danki kulamin da yara da gida akanme zaki wani asibiti bayan babanta natare da ita, idan kinsan kin gaji da aikin ne bazaki iyaba ki gayamin na sallameki wata tazo haâaa nida kudi na ko yan aiki guda dari nakeso zan samesu wlh yau yau din nan, zan koreki wlh kika batamin raiâ da sauri Ummi tace âkiyakuri AntâŠâŠâ dip ta katse wayan tashi Ummi tayi dasauri tace âina zuwa Amalâ tajuya dasauri hada ido tayi da Nura dake kallonta hakan yasa da sauri ta tsugunna daganan wajen gado tace âAlhaji zanje gida Anty tace nabar Amal awajenka zanje in shirya Aman yatafi schoolâ kai tsaye yace âkoma ki zauna bazaki baâ dasauri ta kalleshi ganin yacigaba da danna wayanshi yasa takoma ta zauna ahankali but gabanta sai faduwa yake kusan 4min da gama wayan wayanta yahau ruri hannu yamika mata yace âbani wayanâ daukan wayan tayi tazo har gabanshi ta duka tabashi wani iri wayan yamai a hannu screen din dukya faffashe wannan ai zai iya yagamai fatan kunne saida wayan yakatse yay dialing number ta da wayanshi yatashi tareda ijiye wayanta kan kujera yawuce yafita dan baiso wani yanajin wayanshi da ita waje yafita wajen parking space daidai ta amsa wayan kafinma yayi magana cikin fushi da ihu tace âsabida kaike biyan salary nata kahanata zuwa ko to daga this month kadaina nizan dinga biyan salary nata lemme be in charge of her nai controlling nata to my satisfaction Alhamdulillah inada kudina, but akan mema zaka hanata dawowa ga Aman ko brush baiyiba bai wanka ba yana kuka yunwa yakeji kuma kasan zan tafi shagona yanzun nan maisa kakemin haka? What kind of man are you? Why do u always look for opportunity to belittle me kanunama kowa banda power over anything in our house eh? What is your problem dani? Bakin ciki kake inada kudi kafison kullum ina kasanka ina rokonka do this for me do that for meâ? Shiru Nura yayi saikawai yaciro wayan daga kunnenshi ya katse wayan dan talking to Hadiza is impossible, ita ko kunya bataji ta haifi yara saidai wasu su tayata kula da yaran, gatada baki kaman reza talking to her is just too impossible dukan motanshi yayi ya jingina da motan yayi shiru is this how life zai cigaba da tafiyan mai? Bayagane gaba balle bayan Hadiza, ance communication is a key in Marraige but communicating da Hadiza is impossible kafin kayi magana daya tal tayi dari da hamsin, babu one single abu datakemai na mata, she doesnât take care for him, karma aje batun girki he canât even remember the last time da Hadiza tadau ruwa ruwan nan dai bottle water tabashi yasha, he canât even remember wen was the last time yaci abinci agidanshi, shi bayacin abincin yan aiki itakuma batayi saidai kullum yaci abinci awaje ko agidan abokai, tun yana korafi yan aiki na shigo mishi daki harya dena dan yagane idan basu gyaraba dakinshi bazaâa taba gyaramai ba, he canât remember the last time data gaidashi, is as if he doesnât exit awajenta whenever he tries to talk to her tace yafara fitina da balaâin da korafin da mita shi yabarta tagaji, sheâs not remorseful akan abubuwan datake she feels itadashi equal right sukedashi sabida tana matanshi he canât step and match her ko control her, sabida tana mace doesnât mean zata kwantarmai dakai thatâs just her mentality, Hadiza is very stubborn ga baki Ya Allah, wlh yagaji baison mata biyu dan ko daya bakar wahala take bashi aduniya, baison broken home dan yataso Mamanshi bata tare da babanshi he donât want that ma yaranshi, baison neman matan banza abinda baiyiba yana yaro shine yanzu zai fara when heâs approaching 50 haba bazai tabayiba but heâs just tired yarasa ta ina zaibi ya gyarama Hadiza zama ya gwada zama waje yakai 1-2 nadare amman ko ajikinta yadawo ma tai bacci abinta heâs just soo tired of everything heâs not happy in his home.
Wajajen 10 aka sallamesu da magunguna a hannu suka dawo tunkafin sukai gate na estate dinsu ya hango Aman dinshi kan kujeran security da pajamas ajikinshi da ledan popcorn idanunshi sunyi jaa, jiyayi zuciyanshi takama da wuta parking yayi yafito dasauri security dayake zaune kusada shi yace âYallabai barka da dawowa Madam ta ijiyeshi anan gashinan yanata kuka yace yunwa yakeji shine na saya mishi Popcorn yamai jikiâ? Sabida yanda ran Nura ke daci gyadamai kai yayi Aman yarike hannunshi yakalli fuskan Baban kaman zaiyi kuka gwanin ban tausayi, kaman dan maraya yace âDaddy whereâs Anty Ummi am hungry sheâs the only one that gives me food and play with me, Mommy never gives me food or play with meâ suppressing anger dinshi yayi yaduka ahankali ya shafa kan yaron yace âmuje Anty Ummi na bayan mota da princess donât cry again okayâmurmushi yayi yay bayan mota da gudu yabude yashige shikuma ya tsaya yama security godiya tareda bashi kudi sannan yazo yabude gaban mota yashiga ya zauna yaja mota ta glass na gaba yake kallonsu duka yaran sun kankame Ummi suna hira da ita, sai biye musu take kaman yarinya itama, wlh zaka dauka itane mahaifiyar yaran kawai dan ita black beauty ne yaran kuma fararene tas su kaman turawa amman kana ganinsu kaga strong affection tsakaninsu, sunma manta dashi a motan sai hira suke Aman yarike Ummi gam yanata zuba kaman bashi yayi kaman orphan dazuba, akofar gida yayi parking duk suka sauko tana rikeda Amal, Aman shima yarike mata hannu suka wuce ciki yabisu da kallo direct kitchen suka wuce zaunar dasu Ummi tayi kan kujerunsu dake kitchen din dake gaban island, tashiga yimusu girki agurguje dan Aman yunwa yakeji tana attending to them, ta dafa lafiyayyen taliya na manza fevorite dinsu da kaza ta zuzzuba musu a plate tajuye sauran kuma a kula mai kyau takai dinning ta ijiye sannan takoma kitchen tana bama Amal abaki dantaci da kyau, koda yashigo gidan dan tuntuni yana waya awaje kamshi ne yamai sallama wani kalan yunwa yaji yanaji dinning yaje yazauna kaman wanda ke tsoron wani abu bude kulan yayi daidai Ummi tafito da tray na ruwa da fresh juice a hannu dantaji zuwanshi ta ijiye kan dinning taduka tace âko adafa wani abune daban Alhajiâ girgixa mata kai yayi yace âaâa wannan yayiâ tashi tayi takoma kitchen, kaman mai tsoro yadau fork yasa yadebo kadan yakai bakinshi yatauna dadin dayaji wlh saida kunnenshi yayi siiiii, baisan sanda yadauki plate yadeba ba shi arayuwan shi yanason home made food rashi yasa almost few restaurants ne baisaniba a Abuja ba yaune rana na farko dayaci abincin yar aiki and wlh yamai dadi sosai tass yacinye yatashi ga mamakinshi rawa yaga tanama Amal tana kai abinci bakinta da wayau dantaci, ga magani dayaga ta fito dasu ta zuzzuba a marfi dan an fadamata yanda zata bata asibiti, shima Aman yataso yana tayata rawan sunama Amal rawa dukansu biyun tana dariya sosai fa tana karban abincin tabata maganin ta shanye tass ba gardama ko kakarin amai suna mata waka Aman na tafi kaman suna studio, jinshi kawai yayi yana murmushi ance some yan aiki suna faking love ko sabida parents na yaran but shi all he sees ana is genuine love, kuma yaran loves her suma dearly hakanan samin kanshi yayi yana kallon Ummi sosai, yarinyar black beauty ce tanada tsayi akalla zatai 23 ko 24, yar kauye ce from her dressing but sheâs kind and tanason yaran shi kuma her smile is contagious dan gashi shima yanata yi, sannan the way she dance is annoyingly cute, kaman Ummi taji ana kallonta juyowa tayi da fuskanta ta kallo falon karaf suka hada ido da Nura dake kallonta tana rawa ma Amal.
Wanna talk to me about something??? Chat me up anan;
wa.me/+2347012181461