Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan Ko Mazan 20

Sponsored Links

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣0️⃣

@TRENDYOUTNET Modest fashion world ne inda zaki samu professional kayan zuwa office masu kayatarwa, kyawawa, masu suturta jiki da mutuntawa, idanma casual kaya kike nema na sakawa yau da gobe duka tanada sunadashi all you have to do is chat them up ta wannan number
wa.me/+2349093300112
Kokuma zaki iya zuwa shagonsu dake nan Shop C22C 2nd floor Platinum Mega Mall opposite Ultra Modern Market Behind Next Cash and Carry Jahi, Katampe Road Abuja
And u can also check shagonsu a IG @trendyoutnet don’t forget to follow them🔥 cus anayi baki😅

20
Saida tayi kuka ta koshi sannan tadago kanta taciro wayanta daga jaka tareda mikewa tabar wajen taje chan wajen wata bishi ya ta duka awajen, duk duniyan nan batada kowa banda kakanta duk wani abu data iya yau aduniya kakarta ta koyamata, Kakarta is her everything.
Dialing number ta tayi yana ringing ta daga tace “Yar Albarka kinganni nan fa tundazu nake jinki araina amman Shatu nake jira tadawo tazo ta tayani kiranki amman ina tanachan tana buga yar gala gala, ya kike yar Albarka ya mijin naki da kowa da kowa”? Kungane feeling dinnan da yaro yakeji idan yana cikin damuwa yaji muryan iyayenshi kawai sai Ummi ta rushe ma Gwaggo da kuka, hankali tashe Gwaggo tace “ke! Meya faru kike kuka haka? Waya tabamin jikata iyye? Rabonda naga kinyi kuka haka tun zamanin azzalumin nan Mudi, meya faru kike kuka Ummi? Ya isa, ya isa, bagani ba, da raina fa Ummi kike kuka haka sokike Mamanki tayi fushi dani bayan tabani amanan ku, dena kuka kinji komeme ina nan fa, da raina kuma oya ya isa, zan iya saida raina naga bakuda matsala arayuwan nan, ishuru Zainabu ishiru kinji, wayataba mini yarinyata mai hakuri da kawaici da kunya? Wayatabamin jikana?” Cikin wani kalan kuka Ummi tana shesheka tace “Nura!” Salati Gwaggo tayi da sallallami tace “Nuran ne yasamin ke kuka haka? Mutumin danaganshi tsofai tsofai dashi zai iya haifanki sau biyar shine zai sakamin jika kuka haka? Shi baisan badan naganashi tsoho babban mutum mai hankali daban yarda nabashi ke ya aure ba, wato yagama tsotse kuruciyanki zai fara miki tijara, meya miki? Share hawayenki fadamin meya faru, fadamin daga tushe zuwa reshe share hawayen ki imaza, inajinki” share fuskanta Ummi tayi kaman yar baby tana kuka ahaka dai tabama Gwaggo labarin komi dake faruwa gabaki daya bata boyemata komiba har zancen kannin Hadiza, Gwaggo tace “amman mijinki yabani kunya Ummi, sabida shi tijararre ne katon banza, da girmanshi da tsufanshi bai amfaneshi ni zaizo har gidana ya auremini ke, wato auren huce takaici yayi, yazo ya chusama jikana soyayyan shi a zuciya haka sannan ya wulakanta mini diya? Jibi yanda jikana ke kuka a tasha gaban dubbannin mutane sabida shashashan Nura” Gwaggo tayi shiru tana karajin yanda Ummi ke kuka ko ba’a fada mata ba taji tsananin soyayyan Nura atattare da Ummi, wannan karan ne yatta tafada soyayya bata taba son wani ba Ummi, lokacin da akamata auren Mudi bamatasan menenen soyayya ba, da ace Ummi batason Nuran datace mata tadawo gida dan dudda tana yar kauye tasan darajan jikokinta, lokacin da Mudi ke kirbama Ummi duka tasan taje ta dauko jikanta tadawo da ita gida, tayi shige da fice akauyen nan maigari da manyan gari tasa aka raba auren, dudda Mudi nashigowa har gida yadakesu still batasa Ummi takomamai ba saidai tasan yanda tayi tafitar da Ummi daga kauyen, ina bata yarda awulakanta jikokinta ba. Ijiyan zuciya tasauke ahankali tace “Zainabu” ahankali Ummi tace “na’am Gwaggo” Gwaggo tace “Ummi dudda mu yan kauye ne ba yan binni ba Ummi nabaki tarbiya nakoya miki dabarun zaman duniya ke Ummi ko birnin sin aka kaiki zaki iya zama cikin mutanen yan boko sannan ki samama kanki lafiyayyen waje dan haka share fuskanka, Alhamdulillah ina raye ban mutu ba, Nura ne dai ko wlh sai yasan yayi rashi dan jikata daban take acikin jikoki dubun dabara!” Gwaggo tace “dudda za’ace kinyi gajen hakuri dakika taho ai aure ya gaji yau ayi fada yau ashirya but ni kakarki nayi na’am da tahowan ki Ummi idan Mata da Miji natare inhar akwai soyayya to ka tsaya koma wace ukubace zaka iya jajircewa ka maganceta amman in babu soyayya a auren gwara kayi gaba, abinda Nura yamiki ya nuna kaman dama chan baitaba sonki ba yakawai aureki sabida ya farkan da sumammiyan matanshi Hadiza ne yanzu kuma data farka baida bukatanki dan haka saurareni nan Ummi kibawa Nura tazara harsaiyasan amfanin ki, ke koda baya sonki ke wlh ma yayi karya yace baya sonki, Ummi nabaki tarbiya da dabarun zaman duniya duk wanda yazauna dake saiyaji yana sonki Nura na sonki kawai bairiga yasan dahaka bane amman yanzu zai sani, kalleni nan bazaki dawo adamawan nan ba, sabida zai biyoki nan barni dashi yazo nemanki wlh wlh daina mishi wankin bargo zan solleshi tas, saizan yarana nada daraja kuma babu abinda bazan iyaba akanku ku ukun nan, kinsan mezakiyi yanzu?” Dasauri Ummi tace “a’a” tace “kowa yariga yasan ke yarinyace mai tarbiya da hankali ce baikamata kitashi farat daya kibar gidanba yakamata ki sanar da wani babba yanzu Hajiya na asibiti kada ki kirata dubama da bawani lafiya gareta ba kira kanwar Nura dakika gayamin kwana kin baya kunyi waya wacce bata kasan kiraya maza maza ki gayamata cikin hikima kinji” Gyadamata kai Ummi tayi Gwaggo tace “koyaya kukayi ki kirani kisake sanar dani wayata na hannuna”.

@TRENDYOUTNET Modest fashion world ne inda zaki samu professional kayan zuwa office masu kayatarwa, kyawawa, masu suturta jiki da mutuntawa, idanma casual kaya kike nema na sakawa yau da gobe duka tanada sunadashi all you have to do is chat them up ta wannan number
wa.me/+2349093300112
Kokuma zaki iya zuwa shagonsu dake nan Shop C22C 2nd floor Platinum Mega Mall opposite Ultra Modern Market Behind Next Cash and Carry Jahi, Katampe Road Abuja
And u can also check shagonsu a IG @trendyoutnet don’t forget to follow them🔥 cus anayi baki😅

Kiran Ya Aisha tayi ringing daya Ya Aisha ta katse wayan takira Unmi back kafinma Ummi tayi magana tace “Ummi ai dama ina shirin kiranki yau nace kwana biyu bamu gaisa ba, to ya kike” cikin muryan Ummi da baya fita sosai tace “lafiya l…..” “Ummi, meya sameki kikai kuka haka har muryanki ya chanza”? Ya Aisha tai tambayan da sauri Ummi tarasa mesa aka tambayeta sai tahau kuka da kyar tace “Ya Aisha kiyakuri kada kiyi fushi dani saisa nakiraki inaso ki lallashi Hajiya itama kada suyi fushi dani amman zan tafi kauyenmu wajen Gwaggona gani nan atasha” dasauri Ya Aisha tace “mene! Ummi! Mesa zaki tafi? Meya faru? Fadamin kinsa gabana nafaduwa menene”? Ahankali Ummi ta rairamata komi daga AzuwaZ Ya Aisha zuciyanta yafara tafarfasa sosai tace “sabida yar gwal dinshi zai wulakanta ki? Ai wlh Ya Nura kaman na dakeshi wani zubin bantaba ganin kalan mutum mai zuciyanshi ba Mata tazagi mahaifiyar ka ka kasa komi haba” tayi shiru tana sauraron yanda Ummi ke kuka tace “Ummi kema saiki tashi kitafi mesa baki fadama Hajiya ba? Hajiya bazata taba bari Nura ya wulakanta kiba wlh yayi kadan yayi irin abin nan agabanta ai shi yasan waye Hajiya idan tai fushi ko duka kano zasu hadi ba’a iya lallaso ta kuma wlh bazakije Adamawa ba zai gane yamiki laifi yaje har garinku ya auroki marainiya dake shine yanzu zai fara wulakantaki wa zaki kalla kiji dadi? Zaman wa kike? Yan uwan Hadiza sumiki kinyi shiru sunzo gıda sun gaje kitchen though nagane dalilin dayasa Hajiya bata musu magana ba amman dudda haka gwara dakika barmai gidanshi dan suka dawo ma wulakancin saiyafi nada….” Ya Aisha tahau surfafa masifa kafin chan tace “Ummi kiyakuri kinji amman dan Allah kada ki rabu da Yayana but na yarda yanzu kada ki koma gidan kiyi fushi dashi amman dai kada kirabu dashi wlh zai koma gidan jiya kin tsamoshi daga kangin dayake ciki kin maidashi mutum kin rufamai asiri kuma ke Ummi kinma Ya Nura komi fan Allah kada kiyi fushi dashi yanzu kinsan mezamuyi zan kira wani kanın Mijina yazı ya daukeki ya kaiki gida zanyi arranging komi amiki international passport da visa da sauransu Mijina duk yanada hanyan da za’amiki fast saikizo wajena Ummi zan gyaraki wlh sai Nura yamiki kuka kafin ki koma wajenshi kinji dan Allah Ummi kada ki koma garinku” Ahankali Ummi tace “Gwaggo na bazata yardaba nariga nagaya mata zan dawo gida” dasauri Ya Aisha tace “kira Gwaggo hadamu conference call kin iya hada conference call”? Ahankali Ummi tace “a’a” Dasauri Ya Aisha tace “turamin number ta” tura mata number Gwaggo tayi sunyi waya mai tsaye sannan Aisha tasake kiranta tace “Gwaggo tace takirata” kiran Gwaggo Ummi tayi tana dauka Gwaggo tace “kije wajen kanwar nan nashi Alhamdulillah yan Yan uwan shi duka suna sonki, kidena kuka zamuyi magana idan kinkai gidan kanin mijinta ki kashe wayanki but kullum kidinga kunnawa kina kırana sau daya muna magana inji lafiyanki kuma nagayamata kada tafada ma kowa kina wajenta tace haba bazata fadi ba, bari Nura yadawo daidai zai gane yayi rashi, jikata daya ce tak acikin mata miliyan” katse wayan tayi Ya Aisha takira tace “me Gwaggo tace”? Ahankali Ummi tace “tace naje wajenki” murmushi Ya Aisha tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah kina tashan jabi ko” Gyadamata kai Ummi tayi tace “um” nan da nan ta katse wayan kafin chan tasake kiranta tace “gashinan zuwa nabashi number ki kada ki kara kuka Ummi, kinga maza wlh halin maza saisu saisa wasu ke cewa gwara kaci ubansu dan sunfison matan dake basu wahala suke basu kashi ada ban yarda da maganan ba but wlh yanzu akan yayana uwa daya uba daya na yarda, idanma tunani yake baki da gata wlh baiyi tunanin da kyau ba Ummi nadade banga Kakan dakeson jikokinta kaman Gwaggon ki ba ko ita kadai ta ishi ya Nura ai zaije kauye nemanki wlh saitaci mishi mutunci, butulu kawai gwara da kika bar musu gidan indai Hadiza ne gashi ga ita ai hali zanen dutse mai hali baya fasa halinsa ayi soyayya agama yanzu idanunshi zasu budene ya nemeki”.
Sosai Ya Aisha take mata hira awaya just to ensure bata kara kuka ba har Faisal yazo ganin call waiting na shigowa wayanta yasa Ummi tace “wani number nakirana Ya Aisha” dasauri Ya Aisha tace “shine dauka” katse wayanta tayi tadauka suka gaisa yace “ina gaban yola line kina ina”? Tashi tayi ta taho wajen harta ganshi suka gaisa yabude mata baya tashiga tazauna yabata ruwan gora mai sanyi ta karba tamai godiya suka tafi gidansu mai kyau babba ne matanshi dakeda tsohon ciki tama Ummi sannu da zuwa suka kaita daki lafiyayye matan tazauna da Ummi sannan tafita takawoma Ummi abinci da drinks da kayan sawa da yawa tasamata a sip Ummi tamata godiya.

Leave a Reply

Back to top button