Hausa NovelsM SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan ko Mazan 13

Sponsored Links

đŸ’«MATAN?? Ko MAZAN??đŸ’«

âœđŸ»M SHAKUR

EPISODE 1ïžâƒŁ4ïžâƒŁ

Wai yan uwa yau magana ake ta kayan dadi da shan dadi, kun gane irin juice dinnan mai kaloli daban daban, kiga juice din kaman duka tattalin arzikin Nigeria ne aciki?? To ku tsaya kuji labari yau nakawo muku MOCTAILSBYTEEHA indai magana ake ta harkan Mocktails, milkshakes, frozen Mocktails and fresh juice đŸ„€ babu part two dinsu akap yanar gizo, zaki dan hada wata liyafa? Kirasu sumiki handling harkan abubuwan jika makoshi, for weddings, naming ceremonies, dinners, birthdays, graduations e.t.c name it zasu miki chat them up now ta hanyar clicking on this linkđŸ‘‡đŸŒ karkuji tsoro service dinsu is affordable
wa.me/+2348168045600
Idan kinason kiga hotunan kalolin juice dasukeyi da sauransu check them out a IG AND FOLLOW THEM❀
Instagram handle @mocktailsbyteeha
14
Juyawa Hadiza tayi jin atmosphere na gidan has become so unbearable for her tawuce dakinta, gyale tadauko da wayanta tafito idanunta sunyi jazur kaman tayi wata daya tana kuka, kasa tasauka tadauki car key nata tawuce tabude kofa tafice ta shiga mota ko kallon gateman dinsu dake gaisheta batayiba tawuce ta tafi.

Gudu kawai take shararawa akan titi, tayi nisa sosai ta gangara gefen hanya tai parking tadaga wayanta Anty Jamila takira tana bubbuga kirjinta dayake mata kaman an daura zuma rock akai, ringing biyu Anty Jamila tadaga duk karfin halin Hadiza kasa magana tayi, ita datagama cewa bazata kara kiran Anty Jams kan matsalolinta ba gashi yau tasake kira, kunya ma sai yasa takasa cewa komi kawai tahau kuka, shiruuuu Anty Jamila tayi tana jinta saikuma chan tace “gani nan cikin motan da mijinki yaturamin a airport za’a kawoni gidanki” dasauri Hadiza tace “eh”? Dan batagane tana hanyar zuwa gidan ta ba, dan jim Anty Jams tayi tace “mijinki dake bala’in sonki dakin kasa gani cus you’ve gone blind, dakanshi yakirani tareda Baban su Waleeda yarokeshi da cewa you need me right now nazo abuja, dakanshi yamin booking flight to and fro, yaturamin ticket ta WhatsApp, gobe zan koma kano dasafe, gani a mota, yanzu dai kina ina dan naji karan motoci”? Cikin kuka Hadiza tadago kanta bamatasan inda takeba hakan yasa tace “kizo shagona” katse wayan tayi Hadiza tasake tada mota taja kusan atare daga ita har jams sukakai shagonta, Babba ce Anty Jamila dan akalla zatakai 42yrs itace first born dinsu, Hadiza na ganin yayarta bata damu da suna plaza ba da gudu tai wajen kawai ta rungume Yayanta bakaramin tausayinta Anty Jamila tajiba, duktai zuru zuru, idanunta sun kumbure, fuskanta duk yakoma ja sabida kuka gashi yau kodan makeup da gayun data saba batayiba sabida damuwa, dagota Anty Jams tayi tace “ja gyalenki kirufe fuskanki muje ciki” yanda yayarta tafadi haka tayi suka shiga cikin babban shagonta staff din Hadiza na gaidasu Anty Jamila ce ta amsa suka wuce sama Hadiza tabude office nata suka shiga tana maida kofan tarufe sai kawai tayi wajen Anty Jamila data sami waje kan kujera tazauna.

Zama Hadiza tayi dirshan akasa takifa kanta akan cinyan Anty Jamila sai kawai tahau kuka. “Anty Jams na shiga uku, wlh na shiga uku na lalace, Nura ya cuceni, ya ci amanata ya yaudareni, Nura ya cuceni yakuma wulakantani” dudda yanda kanwar tata tabata tausayi but Hadiza needs to hear the bitter truth, da dan zafi Anty Jams tace “wlhy Hadiza kene kika cuci kanki, kika wulakanta kanki, kika yaudari kanki, u did all of this to yourself” Dasauri Hadiza takalli yayarta takai hannu tana share fuskanta tace “Anty Jams is it a crime kanada yar aiki? Laifi ne daukan yar aiki? Yarda danayi nakuma aminta da mijina cus zanma Nuri shaidan nan har ranan gobe kiyama shi ba dan iska bane kuma ba manemin mata bane, hasalima irin mazan nanne da mata basu damesu ba, Anty jams kiduba kiga this big shago i mange everything dakaina, am a business woman, an entrepreneur da aka san dani, I need to maintain level na integrity da face na business dina, niba housewife bace and I have kids so dole na dauko yar aiki dazata dinga managing mini gida da yarana, but shine Nuri zaibi bayana ya auremini yar aiki? Kinsan yanda nakeji azuciyana kuwa? Yar aiki ta fa? Yarinyar dana dauka tanamin bauta zai auro mini, Anty Jams jinake kaman na mutu kawai nahuta yafimin, naji na tsani kaina nagaji ma dakomi” takara kai hannunta ta share hawayen dasuka zubo mata saikuma takama bakin gyalenta tadaura kan idanunta, sosai Anty Jamila ke kallonta yanda Hadiza is looking this humble, ta zauna dabas akasa gabanta kaman mai daukan karatu tana kuka yasa saitaji kaman itama ta tayata kukan but dole ita ta daure, mikewa tayi zuwa table tadauko kwalin tissue tazo wajen tazaro daya ahankali takai kan fuskan Hadiza tashaga sharemata hawayen cikin fada irin ta manya tana goge mata fuskan tace “kinga abinda I’ve been telling you ko all this while but kikai kunnen uwar shegu dani, Hadiza kalli yau yanda kike kuka wiwi kaman bakeba, Allah yasa hakan yazama darasi agareki Hadiza, Allah kuma ya shiryeki ya ganar dake gaskiya yacire miki bakin akidan nan dakika dauka kika daurama kanki dayay landing naki in this situation, Hadiza ina ganin nafiki jin bakin ciki da Nura yakirani dakanshi dazun dasafe nida Baban Batool yana fadamana gashi gashi yayi aure, Ya aure Ummi and u don’t look okay plssss Baban Batool yabanni nazo naganki just for today gobe nakoma” Anty Jams taidan shiru tareda ijiye tissue daya gama jikewa tanunama Hadiza dake kallonta da jajayen idanu kirjinta tace “I was deeply hurt wlh danaji maganan but then again koda murya zan chanzawa Nura wanda zai nuna labarin baimin dadi ba nima nazama butulu kaman ki dan nasan kanwata ce caused everything and Nura has been annoyingly patient dake, cus hakurinshi ma at a point haushi yake bani yanda baitaba daddaura miki mari ba yafasa miki bakin dakikemai rashin kunya sannan yakado ki gida” Anty Jams tayi shiru tana kallon yanda Hadiza ke silent kuka tana shesheka tace “babu the most bitter punishment da zakama matarka irin ka auromata yar aikin ta, Hadiza yar aikin ki fa dababu abinda bata saniba dake faruwa agidanki ba, yarinyar dake zama cikin gidanki safe, rana , yamma, dare dakuma another safiya har na tsawon close to a year, rana daya mijinki ya aurota a matsayin kishiya Ya Allah! Allahumma Ajirni fi musabati!” Saikawai Hadiza tarushe da kuka Anty Jams ta girgizakai tace “I was deeply hurt but I couldn’t say a word sabida kin riga kin sani a position din dabazan ma iya bude baki nacema Nura haba Nura maisa zakawa Hadiza wannan sakkayan, but nakasa dan Hadiza ni kaina wani zubin idan kikai wani abun jinake kaman kada na sake kiranki har abada but then again bazan iyaba jini yariga yayi bounding dina dake for life, ni kenan balle kuma Nura dashine kikafi yima kashi aka, atleast ni kinadan shakka na kina ragamin, but still last time damukai magana cewa kikayi bazaki kara kirana ki gayamin matsalanki ba cus blaming naki nake now have u seen abinda nake fadamiki?” Hannu Hadiza tasa tajawo tissue tadaura kan idanunta Anty Jams tace “bangaya miki halin dakikema Nura zai iya pushing nashi waje ba? Ban gayamiki ba”? Gyadama Anty Jams kai tayi tana goge kwalla, shiru Anty Jams tayi tana kallonta tace “kinason mijinki amman haukanki yasa aurenki gabaki daya is shaking Hadiza, look at abinda kikama kanki, look, Nura ya auro miki mai miki aiki, wani cin zarafi yakai haka have u seen inda I know my right, nida mijina are equal, feminism, rayuwan Abuja, bla, bla,
bla yayi landing naki? Kinga result din yanzu? Have you seen the outcome”? Anty Jams tayi maganan da fada sounding so pained irin fadan babban yaya da karaman kanwarta dinnan, yanda Hadiza kema yayarta kuka yasa itama Anty Jams taja tissue tadaura kan idanunta dan takasa rike hawayen cikin kuka tone tace “kin kashe kanki abanza a wofi da bakin halin dakika samo Hadiza, miji mai kirki, mai hali irin Nura, gidanmu babu wanda Nura bai taimaka ba, Mama idan tai rashin lafiya kudin dayake turowa harsai na mai fada, yamana renovating gida, nan nan saida yayi shiga yayi fita yasaman ma Babban Batool contract na titin nan akano, eh? Kinada mijin arziki, mijin kwarai mai hankali, mara mako, hannun Nura abude yake koda yaushe, gashi yana sonki, wani zubin nakance Badadan nasan baki harkan malamai ba danace mallakeshi kikayi tsabagen yanda yake sonki, kimai wulakanci da cin mutuncin duniya but still yana tareda ke, har uwarshi kika daukoma dan sanda ranan ne yafara sakinki wanda shima washe gari yadawo dake maza nawa ne zasu iya haka? Wani kika zagi mahaifiyarsa ko kije extend na daukoma familysa police that’s the end of the Marraige koda jikin gwal gareki kuwa, but still Nura yacigaba da zama dake and u still won, cus ai kince bazasu zauna agidan ba kuma basu zaunan ba sun barmiki gidan, so akanmene yanzu idan yakirani yacemini yayi aure ya auri yar aikin ki zan iya cewa wani abu bayan nasan abinda kanwata tayi iyye? Waye aduniyan nan zaiji abubuwan dakikama Nura bazaiyi supporting kishiyan dayamiki da yar aikin ki ba eh? Hadiza bakanki kadai kika cutaba har mu nan gabaki daya kika cutar” kawai Anty Jams tahau kuka dan abin namata zafi arai cikinsu babu mai lallashin wani.

Da kyar Anty Jams tayi shiru takalli Hadiza dake kuka har lokacin tace “bawai baki nake miki ba but ace yau Nura yarabu dake wlh harki mutu Hadiza bazaki kara samin miji kaman shi ba, kuma idan zakiyi aure dari haka za’a dinga sakoki cus bakene matsalan ba halinki konace sabon halinki ne matsalan, namiji da mace ba daya bane, a man and a woman are not equal stop believing in that stupid theory! A house belongs to a man, gidanshi ne, shiya auroki shiya saki aciki, bakida right or whatsoever kice saida permission naki baki zasu shigo Hadiza, dafa abinci is traditional da globally mata aka barma wannan tradition na girki agida, tundaga upbringing ba’ayin rainon maza to be entering kitchen mata akema wannan training din so akanme zakice shiya shiga kitchen? Ya iya girkin ne? Kula da yara aikin mace ne idan mijinki yatayaki is fine idan baitayaki ba kada kice dole saiyayi dan shine ke fita kullum cikin rana yaje yanemo muku abinda dagake har yaran zasuci, Hadiza dan mijinki yace tashi bani kaza, yimin kaza, zonan, zauna, matsa, baya nufin ya rainaki bane No ya isa ne saisa yabaki umarnin kuma dole kibi, idan bazaki iyabiba idan u can’t subject kanki to follow umarnin mijinki maisa kika aureshi to??? Eh” cikin kuka Hadiza tace “wlh Anty Jams zan chanza nagayamai zan chanza amman yasaki Ummi mucigaba da rayuwan mu mukadai” dan murmushi Anty Jams tayi tace “Hadiza kenan u can’t eat your cake and still have it! Yanzu ace Nura yashigo nan kifadamai maganan nan agaban idanunki zance Nura kada ka saki Ummi” Hadiza nawani kalan kallon Anty Jams tana kuka mai tauna zuciya, Anty Jams tace “Hadiza a rayuwa one cannot always win, tunda kikai aure yau shekara goma going to 11 you’ve been winning akomi nakeda Nura, yanda kikeso haka ke faruwa agidan ki, kika fitini bawan Allah he let u have it ur way, wannan ma ishara ce Allah ya gwada miki dan trust me, Allah ne ya kwadaita ma Nura son ya auri yarinyar nan Nura da bayama kallon mata, rana daya yaga Ummi yaje har kauyensu ya aurota, inaso nagaya miki is too late for you amman I can’t because is not too late for you” Anty Jams tadanyi shiru tace “is too late for you cus Nura yariga ya auri Yarinyar nan ba gudu ba jadabaya, so kike yakoma karamin mutum ya auri yarinya sabida ke da bakimai biyayya ba yasaketa angayamiki batada iyayene? Wasu iyayene zasuso su aurar da Yarinyar su asakota bayan kwana biyu so maganan Nura yasaki Ummi ki manta dashi kawai” taushe bakinta Hadiza tayi dan ihu ne yakeso ya kufcema bakinta, ijiyan zuciya Anty Jamila tasauke tace “abinda nake Nufi is not too late for you shine Nura har yanzu yana sonki sosai, cus namijin dake tsananin sonka ne zaiga halin dakake ciki yabukaci wata yar uwanka tazo just for your comfort, Hadiza har yanzu Kece keda ragaman zuciyan Nura forget ya auro wata Ummi koda tanada wani abu axuciyanshi to akalan zuciyan ne, bazaka iyajan akala abu ya motsa ba amman mai ragama shine keda ikon komi, so Hadiza idan zaki gyara halinki from today ki koma asalin Hadiza da Nura falls for deeply lokacin nan kowa yasan labarin soyayyan ku a kano ki koma i assure u, u will come me to tell me wonders, is not too late for you Hadiza” Hadiza na kuka tace “to mezanyi? Yanzu haka zan zauna yadinga yanda yaga dama dani?” Yayarta na kallon kwayar idanunta tace “kwarai idanma takaki zaiyi yayi ke har kinada baki mutumin daya miki komi, the journey might be tough on you but inhar kika dage mijinki nakine Hadiza” sosai take kallon yayarta, ahankali tanuna zuciyanta tace “anty Jams inaso na tsani Nura so bad sabida auromin Ummin nan dayayi amman nakasa sai kace yamin asiri yanzu nema naji wani kalan sabuwar soyayyanshi nakamani danaga ya auro wata ina masifan jin zafi da kunci ko dakinta da dazu yashiga agabana wlh kaman ana yankani alive mesa nakeji haka? Maisa nakasa fushi namabar shi da yar aikin gabaki daya afterall bana bukatanshi inada kudina dazan iya kula da kaina aduniya, why why why maisa yanzu ne nakejin sabon soyayyanshi araina da inji na tsaneshi?” Anty Jams tace “sabida yanzu ne kikasan menene kikai loosing kokuma nace menene kika bari ya kufcemiki a hannu, all this while ai ina fadamiki kina mugun son mijinki amman kaman bake nake fadamawa ba sai yanzu dayay aure kikejin kina sonshi kawai da hankalinki da karatun ki kin cuci kanki abanza a wofi Hadiza, Hadiza Allah yabaki perfect husband, kinsan maza nawa kenan aduniyan nan da basa ciyar da matayensu sabida sunga matan na sana’a? Kinsan maza nawa ke bama matansu 200 kullum kudin cefane and matan su karba and fix something with it? Kinsan mata nawane da sunma manta when was d last time mazajensu suka musu dinki tun na akwati? Hadiza kinsan maza nawane a zamanin nan da bama su damu da yaran cikinsu da suka haifaba sun barma matayensu yaran sune cinsu, shansu, suturansu harma school feees nasu mazan na nan kuma bawai sun rasa kudin biya bane, Hadiza kinsan mata nawane yanzu that are going through domestic violence, bullying, torture damuwa da rashin sukuni agidan mazajensu from both mijin da yan uwan shi? And all this matan despite everything suna zaune agidan mazajensu despite ba sabulun wanki bana wanka, ba kudin kitso ba kudin kayan salla but ke kinsami everything, banda doraki dayayi akan business yasan kinada kudi baitaba kallon kudinki ba, for once baitaba cewa kuyi sharing bill ba, baitaba kin sayo wani abu ba, yan uwanshi ko mahaifiyarshi basu taba takura mikiba saina girmamawan Matan yayansu dasuke miki not until ranan da kika zagi mahaifiyarsu agaban Meena ta dauki action which I support dan banabin karya, kinsan mata nawa ke neman wannan jindadin dakika samu agidan mijinki? Kinsan how many women out there are dying to be in this position u are?Hadiza jibi rahama da baiwa daban daban da Allah yamiki, which of the favors of Allah can you deny??”Hadiza tai shiru tana goge idanu, Anty Jams tace “all abinda Nura ever wanted from you is just care, care for him care for his kids, attend to him and attend to his kids yataba demanding for more than this?” Girgizamata kai Hadiza tayi tana kuka komi nadawo mata fresh tundaga farko rayuwansu, ijiyan zuciya Anty Jams ta sauke tace “like I said is not too late for you cus Nura namiki wani special so azuciyanshi maybe sabida kene first love dinshi dan haka maza maza ki gyara before u lost him for good kısan inda dare tamiki and I will tell you this again kishiya fa yarıga yamiki, kidauki hakan amatsayin kaddara dakuma hukunci da Allah yamiki abisa laifinki Hadiza ki tuba taubatan nasuha kikuma chanza inba hakaba kindaisan haka nake gaya miki gaskiya baki yarda saiya kwabe miki, inba hakaba Hadiza wlh wlh zaki rasa Nura for life” dasauri Hadiza takalli Anty Jams idanunta sun nuna asalin fear gabanta nafaduwa, Anty Jams tace “kuma ki kara rubutawa ki ijiye again bazaki taba samun mijin dazaici kashinki kaman yanda Nura yaciba, idan zakiyi aure sau 1000 zaki fito so 1000 cus akidarki dabi’unki ne matsalan, beauty bashi ke keeping aure ba, being classy bashi ke keeping husband ba, having money ko business ko wayewa bashi ke keeping mijiba u of all people can tell people this yau bagashi Nura ya auro miki wacce batai makaranta ba, yar asalin kaune, Hadiza abinda namiji keso shine yasami mace dazatamai abinda yakeso which bakiyiba” daura hannunta Hadiza tayi akan idanunta sai kawai tahau wani kuka kai Anty Jams bata tabajin Hadiza tabata kalan tausayin data batayau ba tunda suka girma, ahankali tace “zonan Hadiza, come here” jawo Hadizan tayi tadaura kanta kan cinyanta tashiga shafa kanta ahankali tace “kidena kuka haka, ya isa ki yarda da kaddaran ki we all are humans, and yin mistakes yana kara tabbatar da yes mu fa yan adam ne we are bound to make mistakes, but what makes us special and unique is wannan ability na gyara mistake naka, trust me Hadiza is not too late u can amend all the broken relationships starting from Nura, apologize and become the good wife daya dade yana kwadayi yagani awajenki and zakiga Nuran ki zai dawo miki A man is like a little baby idan kika lallasheshi yana lallasuwa, yaranki ki karbesu, kin dauki cikin yaran nan for nine whole months, kika haifosu bar ganin baki gabansu as far as jininki ne su wlh wlh babu wanda ya isa ya chanza haka all it takes is kawai kijasu jikinsu, hug them that duminki dasuka dade basuji ba let them feel it, take them with u to kitchen cook for them and feed them da hannunki, bath them take them out to any park suje suyi wasa spend quality time da yaranki Hadiza and see idan sun kara kallon Ummi and last but not least Hajiya!” Anty Jams tadanyi shiru sanman tace “kinma Hajiya Babban laifi ta hanyar zaginta dakikayi da dauko musu police but Hajiyan dana sani is just like Nura, she’s a wise woman data haifi yara mata da yawa she knows how brain namu operate, she’s a mother trust me kikaje kika bata hakuri koda ta wayane wallahi she will forgive you and life goes on, Hadiza respect is earned baka demanding dinshi by fire by force, idan kika kama kanki kika sauke all duties naki as a wife wallahi Nura babu abinda bazai miki ba the, forget al’adun yan garin nan bakiji karin maganan nan ba idan wani yazo kasuwa yayi rawa yasami kudi wani yazo yayi duka zaici and this is exactly abinda yafaru dake, akidan wasu dakika dauka dakikaga works for them ke yajamiki saki dakuma kishiya, Hadiza u are educated I believe the only wanda ya chanchanci kayı pleasing aduniyan nan is Allah bawani ba ki manta da kawayenki and be you and win ur husband kinji” Gyadamata kai Hadiza tayi ahankali, Anty Jams tace “as for Ummi kada ki sake ki bata hurimin ta rainaki ki kama kanki babu abinda ya shafeki da ita ko harkanki trust me idan kikai haka bata isa tamiki maganan banza ba ke koma tayi gigin yi Nura zai taka mata burki I trust him kinji Hadiza” Gyadamata kai tayi, Anty Jams na shafa kanta tace “nasan da ciwo but kikai zuciyanki nesa and amend your path okay “ sake Gyadamata kai Hadiza tayi, sosai Anty Jams ke shafa mata kai tun tanajin sheshekan kukanta har wani baccin damuwa yayi awon gaba da ita ahaka.
**

Kusan awanshi daya da rabi da fita Ummi tayi dialing number shi, wayan na gab da katsewa ya daga yace “Hajiya Ummi” har cikin ranta Ummi taji yanda yakirata sai zuciyanta ya narke tana kara addu’a Allah karyabawa Hadiza ikon rabata da mijinta, cikeda danne damuwanta tace “dama nakira naji yaya kunkai asibitin ya jikin Hajiya kuma?” Dan shiru Nura yayi wallahi bazai iya kwatanta yanda this small small things da Ummi keyi counts in his heart ba, this has been abinda he desperately wants Hadiza tamai, murmushi yamata yace “eh munkai asibiti, jikinta kuma dasauki tagama ganin Dr dake managing ciwon suganta yanzu tana ganin likitan dake managing hawan jininta” ijiyan zuciya Ummi tasauke in a very caring way tace “amman akwai cigaba sosai ko?” Cikeda tsananin jin dadi yace “akwai Allhamdulillah” ahankali Ummi tace “naji dadi, Allah yabata lafiya gabaki daya ta warke tass tass” wannan karan murmushin dayayi saida Ummi taji yace “Ameen thank you Matata” yanaso ya tambayeta ko Hadiza ta dameta but baiso yabata room to think ill of Hadiza hakan yasa yace “kinci abincin dana kawomiki”? Dasauri tace “eh nacinye tass sabida abinci yayi dadi sosai” ahankali yace “ai kin iya girki saisa” cikeda so Ummi tace “a’a bahaka bane sabida kaika kawomin abincin saisa yakara dadi Allah kuwan” murmushi yayi ya jingina da mota tareda lumshe idanu ahankali yace “nayi kewanki sosai Ummi kaman nayi shekara bana taredake haka nakeji” lumshe idanu tayi ahankali tace “jiya gabaki daya nakasa baccin kirki, duk inda najuya bayamin dadi kaman ina kan icce nasaba da jikinka” cikeda so yace “gobe in sha Allah muna tare kinji Abu” dan dariya tayi ashagwabe tace “ni banson ana kirana Abu” dan hade kafanshi yayi dasauri yace “to to naji nadaina tuba nake” murmushi tayi saikuma murya chan ciki tace “I lobe you my Noor” lumshe idanu yayi wannan karan saida yakai hannunshi yadaura kan gabanshi dayaji ya harba, cikin wata kwantacciyan murya yace “kinaso nabar Hajiya nagudo gidane”? Shiru Ummi tayi itama tana lumshe ido wlh 2days dinnan kaman shekara mugun kewanshi dakuma sha’awanshi takeji kasa magana tayi ta girgizamai kai alamun aa, murya chan ciki Nura yace “I love you Hajiya Ummi na” murmushi tayi tana kokarin kauda maganan jin muryanshi yayi sanyi gashi yana asibiti tace “uhmmmmm” anatse paying close attention to her yace “menene da wani abu ne”? Cikin kwantacciyan murya tace “ahmmm dama inaso namaka magana ne kan Hajiya tadawo nan umm” tadanyi shiru saikuma dasauri tace “kaga gamu mubiyu anan ba dadi Hajiya na wani gidan daban zaune, koda Baffan baice komiba but abin zaiyi kaman bamujin maganan ka, dan Allah kadawo da Hajiya nan gida namaka alkawari zamu kula da ita da kyau” Shiru yayi kawai, yadade bai hadu da yarinya mai wayau kaman Ummi ba gabaki dayan statement nata bata aibanta Hadiza ba rather maganan tayi as per subiyu atare zasu kula da Hajiya tama Hadiza kara dudda tasan Hadiza baza tayi ba, kuma gaskiyanta ne it looks somehow matanshi har biyu amman mahaifiyarshi na zaune a gidan Baffan shi koda basuce komiba is somehow but Hajiya yake tunani da kyar inta yarda yarıga yamata maganan tanuna a’a, dan ijiyan zuciya yasauke yace “Hajiya bazata yarda tadawo ba Ummi” dasauri Ummi tace “kabani izini nakira Hajiya dakaina na mata maganan”? Batare daya musa ba yace “eh ki kira muji” murmushi Ummi tayi tace “nagode Baban Amanu” ahankali Nura yace “nagode nima Maman Amanu Hajiya taji dadin tuwon dakika mata duka gidan har Baffa da ni shi mukayi kari dashi, Matan Baffa na tace nagaya miki keda itane kinsa abincin data dafa yayi kwantai” dariya Ummi tayi tace “ahh ah ahh nayi babban laifi, katayani bada hakuri kuwa”? Dariya yayi yace “ni ina ruwana” kaman zata rushe da kuka tace “kai dan Allah Baban Amali” dariya sosai Nura yayi harya manta damuwan Hadiza daya addabi zuciyanshi yace “nabada wasa nake miki” murmushi tayi tace “godiya nake ka koma wajen Hajiya ka gaidamin da ita kaji saika dawo” Gyadamata kai yayi yace “in sha Allah” ya katse wayan feeling so happy.

Ummi na gama wayan wani kira yashigo wayanta dasauri ta kalli wayan number ne but ba irin na Nigeria ba bata saba ganin kalan number ba dauka tayi kafin tayi sallama taji muryan wata mace dayadan manyanta ba chanchan ba. “Ummi, Aisha ce, kanwar Ya Nura dake Egypt” dasauri Ummi tazaro idanu ganewa datayı itane maibin Nura cikeda kunya da bala’in girmamawa tace “laaa Ya Aisha ina yini, ya aiki ya yara da Babansu” murmushi Aisha tayi tace “Alhamdulillah Ummi, musamman nakira wlh Hajiya tasanar dani yanda kike dawainiya da ita, tace yau kene kika aikomata da karin kumallo sannu da kokari Ummi angode angode, ina zuwa dan Allah dakata kadan nakira Asma’u da Rukayya muyi conference call suma sunaso daman su kiraki” kafin Ummi tayi magana harta shiga kira nan da nan sukahau conference call sai godema Ummi sukeyi akunyace Ummi tace “dan Allah kudaina godemin haka, Hajiya mahaifiyata ce banga dalilin godiya dan nama mahaifiyata abuba, nima sonake nasami albarkan dakuke samu, bantaba sanın zan sami wacce zata maye gurbin mahaifiyata aduniyan nan ba bayan tarasu sai Hajiya, Hajiya Itace mutum nafarko tunda nafara aaikatau dudda tana mahaifiyar mai gida bata kyamaceni kaman yanda akeyi agarin nan ba takirani tasa na sauna mukaci abinci tare sannan tasaka Meena ta tayani aiki, itane mutum na farko da bata tabamin kallon yar aiki ba sai diyarta kuma tabani tukuicin girki da babu sanda yataba bani, Hajiya dabance araina kudenamin godiya kan wani abu ban mata komiba Mamana dana rasa Allah yabani a Hajiya” tai maganan muryanta nadan rawa yau ta tuna da mahaifiyarta kannin Nura jisukayi sun kamu da son Ummi atare sukace “kidaina kuka Ummi Allah ya Jikan iyayenki da rahama” ahankali tace “Ameen nagode” saikuma suka shiga hira tana tambayan su sunayen yaransu, yaran Aisha Hudu, Yaran Asma’u biyu, yaron Rukayya daya Ummi harda magana da yaran tana wasa dasu yaran najin dadi kusan 30min suna hira kaman sun saba, suna shirin sallama Ummi tace “Ya Aisha, Ya Asma’u and Ya Ruky dan Allah ku tsaya inaso nayi wata yar magana daku” dasauri giving her full attention sukace “okay Ummi muna jinki” anatse Ummi tace “dama inaso Hajiya tadawo nan nayi magana da Baban Amali yace Hajiya bazata yardaba saidai ni nayi to inaso anjima suka koma gıda zan kirata dakaina, amman dan Allah inaso kudan tayani sa baki ku lallaba Hajiya ta yarda tadawo nan zamu kula da ita wlh baza’a samu mata sala ba” kamin Ya Aisha tai magana Asma’u tace “Ummi kinga basaikin kare Hadiza ba kinga idan Hajiya tadawo gidan nan Hadiza ta kara zagin mini uwa wlh zanbar nan Port harcourt ne nazo harnan Abuja na nuna mata idan batada tarbiya zan bata sabo” dasauri Ruky tace “Meena kadai ta isheta ai basai munzo ba, amman nima nafison Hajiya na nan gidan Ya Nura da gidan Baffan mu gaskiya dudda Matan Baffa batada matsala but Ya Aisha me kikace?” Anatse Aisha tace “bari zan kira Hajiya namata magana but Meena tagayamin Hadiza bata sonsu agidan ne Ummi Hajiya nada hawan jini banso tana ganin tashin hankali kwata kwata” dasauri Ummi tace “laa wlh Anty bahaka takeba, lokacin nan kaman tanada dan matsala ne saisa hakan yafaru amman Anty nada kirki kuma tana kaunar Hajiya ba kadan ba, kada ku damu zamu kula da ita sosai wlh” murmushi Aisha tayi badan komiba saidan yanda taga hankali da dabaru irin na mata na Ummi dudda tasan Hadiza bawai chanxawa tayi ba but for the sake of Ummi dakeson Hajiya tadawo gidan harma she’s putting it in request yasa tace “shikenan Ummi zan ma Hajiya magana” cikeda farinciki Ummi tace “yauwaaa nagode sosai Ya Aishan muuu” su Rukayyah duk dariya sukayi Aisha tace “menene tsawon dogon riganki Ummi”? Ahankali Ummi tace “hamsin da takwas” cikeda so tace “zan saya miki dogayen riguna na aiko miki ta airport sai Ya Nura ya karbo miki” cikeda murna Ummi tace “Ya Aisha nagode nagode Allah yabiyaki yama yaranki Albarka” duk dariya sisters din sukayi cikeda son Ummi ganin Nura ya auri mata mai hankali yanzu sukai sallama suka katse Ummi sai dadi takeji.

Sun gama komi a asibiti suna hanyan komawa gida Aisha da kannenta suka kira Hajiya a conference call, Nura yana jinsu suna cewa Ummi ta aikosu cus wayan Hajiya is always on speaking suna lallaba Hajiya takoma gidan Nura, Nura sai mamaki yake shi baimasan Ummi nada number kanninshi ba dudda dai Hajiya bata yardaba cemusu ma tayi su daina damunta suna kaiwa gıda ta zauna adakinta Meena takawo mata ruwa saiga kiran Ummi wayan Hajiya tadauka tanunama Nura dake gefenta yana danna waya tace “wato yaran nan nan hada baki sukai” wayan ta dauka kafin tayi magana Ummi tace “Hajiya ina yini, ya karfin jiki kun dawo”? Hajiya na murmushi tace “lafiya lau Ummi jiki kuma Alhamdulillah nasami lafiya sosai an bani magani na sati daya daganan nakoma likita ya ganni sai kano in sha Allah” ahankali cikeda rage murya Ummi tace “Hajiya dudda ance Anty na fushi dani yau amman muna kishin ladan ki da addu’anki datake samu ita kadai kullum, Hajiya dan Allah kidawo gidanki muma musami ladan nan da addu’anki kinji Hajiyanmu”

Wlh Nura tunda yake baitabajin wani sabon soyayya da respect na Ummi dake shiga zuciyanshi irin na yau ba, just look at yanda tai putting maganan mind blowing! Ita kanta Hajiya jitayi kanta yayi girma saita kama baki tace “auuu hakane bari Karime tajiki keda itane” dan dariya Ummi tayi adan shagwabe tace “Hajiya dan Allah kidawo kinji har Auta Meena bazan bari tana damunki ba” Meena dake wajen tana murmushi tace “inajinki” dariya Ummi tayi tace “Meena please tayani lallaba Mamana tadawo gıdanta kinji” harga Allah ita kanta Hajiya tafison gidan danta da nan ba yanda ta iyane batason taxama silan haddasa fıtina agidan danta saisa tadawo nan din, ahankali takalli Nura daya lumshe idanu kaman baya jinsu Meena tace “Hajiya please mu koma chan kinji bahayaniya agidan Ya Nura kaman nan” dasauri Ummi dakejin komi tace “Hajiya dan Allah kidawo kinji babu wanda zai tadamiki da hankali ko damunki sabida ke Anty har shopping tafita yi yanzun nan ma” Sosai Nura ke mamakin Ummi, murmushi irin na manya Hajiya tayi tace “tunda dai kun taru kunmin chaaa aka hardasu Aisha kike aikomin sabida nacema mijin naki a’a dayamin magana ai shikenan, anfi karfina anmin taron dangi, gobe da safe nadawo koda rana in Allah yakaimu” daga Ummi har Meena dake wajen ihu sukayi Nura yadago yakalli Meena dasauri ta taushe bakinta cikeda farin ciki tana dan dariya, Ummi tace “Wayyoo dadi Mamana zata dawo gida gobe, mezan dafa miki eh Hajiya na gobe” har cikin zuciyanta Hajiya kejin dadin yanda Ummi ke nan-nan da ita ahankali tace “kome kika dafamin zanci Ummi Allah yamiki albarka, Allah ya farantamiki kema, Allah yakara daidaita zamanku dake da Hadiza, nagode ko Ummi” cikeda murna Ummi tace “Ameen Hajiya kinga harmun fara samun albarkanki tun yanzu” dariya Hajiya tayi sosan gaske irin na manya tace “Allah kara miki Albaraka to” kyalkyacewa Ummi tayi awaya tana dariya tana Ameen shima Nura yayi dariya sosai feeling so happy and satisfied a zuciyanshi yace “Ameen” he’s really happy with the way Ummi made his mom felt just now, from voice din Hajiya kadai she’s feeling soo pleased and special Alhamdulillah for the first time tunda yayi aure matanshi made his Mom his happy, just look at yanda Ummi tayi magana ki dawo GIDANKI!!! Murmushi yayi sai kawai yaciro wayanshi he don’t care ko zata gane ko bazata gane ba dudda yasan ta iya karatu but he just typed. “I love you Ummi na” yamata sending❀.

Like I said duk zafin challenge da kika facing agidan aurenki there’s always a simple solution to it, all it takes is the willingness and zeal naki gyara but kuna ganin Hadiza zata iya gyarawa??? Nura kam na son Hadiza so ma ba kadan ba, mutum da zaije to the extend yabiyama sister ki ticket just to come and be there for you ai karshe ne, kuna ganin zata iya bawa Nura that love, care and affection dayake nema awajenta kuwa ido rufe??? My question still stand can Hadiza change kuna ganin zata iya??

Now bari mu leka Ummimyn kauye.
Kunsan akwai ilimi that’s knowledge sannan kuma akwai Wisdom shine hikima ko a hausance? Rayuwanmu ayau akwai mutane dayawa masu ilimi but basu da wisdom if u ask me zan iya cewa Hadiza is one, she’s educated but she lacks wisdom, bata iya siyasa da kirsa da kisisina da iya siyan mutane ba, zero pretending and kara, batason abu tanuna maka karara. Believe me idan nace Ummi might be uneducated but yarinyar tanada wisdom and I will give it for Gwaggon ta zama da tsofaffi nakoyamaka dabarun zaman duniya da dama.

Now akwai wani magana da iyayenmu keyi akace “idan ka auri miji ka auri all the family” yanzu kuna ganin misali nan gaba idan Nura yayi kokarin sakin Ummi kanninshi da mahaifiyarshi zasu yarda yasaketa?? Aganin ku maisa bazasu bari ba? The logic is simple always pick on this small small abubuwan and keys danake samuku a novel din nan, ina kawo muku bangaren both Ummi da Hadiza sabida masu ilimi susan sunada chance arayuwa, marasa ilimin kimiyya suma susan sunada chance arayuwa to attain success all it takes is iya xama da mutane, magana mai dadi, nabarku lafiya yan uwana makaranta littafin nan makesure kun shiga class dina danakeyi na matan aure with just 2k you can bring your wife, sister, cousin, friend koma waye dakukaga tana bukatan karatuna, idan kinason magana dani M Shakur kuma chat me up a whatsapp wa.me/+2347012181461
Zaku iya samuna kuma a Instagram @mshakur_world hakama a TikTok mshakurworld.
I see the love dakukema this book and inada gagarumin albishir dazan muku gobe in Allah yakaimu, Thank you and Godbless❀

Leave a Reply

Back to top button