Muna Gabatar da HausaNew Sabon Shafin Littafan Hausa Novels
Duk cikin ma’abota gudanar da shafukan Hausa Novels babu wanda ya ke iya iyawarsa wurin ganin an samu saukin samun wadannan irin litattafai fiye da Shuraihu Usman.
Wannan karon ma ya zo mana da sabon shafi mai suna Hausa New. Kuma tsurar littafan soyayya, yake-yake, nishadi da sauransu ya ke wallafawa a shafin.
Kai kafin wannan lokaci ma, Shuraihu shi ne makirkiri kuma mawallafin shadin DLHausaNovels, wannan shahararren shafin na litattafan Hausa.
Zan dan fadada wannan rubutu nawa domin tsarge wa tare da warware muku yadda tsarin shafin nan yake.
An Kirkireshi da Saftuwayar WordPress
Babu fiye da wannan software da wordpress in dai fannin kirkire-kirkiren kowanne irin shafi ne na yanar gizo, tun daga kan Blogs, Websites, Portals, Forums, E-commerce sites da sauransu.
Kazalika shafin na tafiya yadda ya kamata.
An Girkeshi a NameCheap
Kwarai ko me za mu ce game da girkar shafi to ba za mu yi wawan tsalle mu haye namecheap ba, domin itan ta daban ce.
An girke shafin HausaNew ne a domains and hosting provider ta NameCheap domin tabbatar da kowanne lokaci kuna da dammar ziyarta tare da shiga cikin shafin.
Yana Da Kawataccen Saukakakken Design
Kwarai, ko tantama babu, design din shafin HausaNew na da matukar saukin tsari.
Ko bako ne kai a intanit to za ka iya karade shafin cikin ‘dan kankanin lokaci ba tare da yin karo da wata gargada ba.
Saukin Download
Sauke littafi daga shafin HausaNew matukar sauki gareshi fiye da yadda ka ke tsammani.
Ba wani tada hankali, ba redirects, ba pop-up ko kuma wani misleading ads a kan shafin, cikin sauke za ku samu damar sauke duk irin abin da ku ke bukata daga HausaNew.
A Karshe
Ina yi wa daukacin masoyan Hausa Novels da ma shi kansa Shuraihu Usman fatan Alkhairi kwarai-kwaira, fatan Allah ya bar zumunci da kauna.