Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 21

Sponsored Links

21
Taka tsantsan suka hau yi da duk wani abin da zai saka a fahimci halinda sike ciki komai qanqantar kuskure kiyayesa sukeyi,
Sumayyar ita kanta dole ta ringa tilasta kanta tana nemo kuzari da qarfin hali tana fitowa wasu ayyukan sbd saka idon Hande akansu yayi yawa.

Benazir ma datake zuwa makaranta tini sukaiwa kansu fada komai na Alh bilal harma dana ms aysha sun dena karba duk tsananin yunwa da rashin lafiya sun dena karban abincinsa da maganin dasuke fitowa daga garesa duk da bak dawo din ba kawo musu akeyi makaranta amma sam Benazir ta dena karba.

Saida suka share sati kusan uku suna fama da jikin Sumayyahn kafin ta fara fita makaranta.

Annensu duk suka fita harsu dawo hankalinta baya jikinta sai taga dawowarsu sbd yanzu tsoron mutanen waje ma takeyi,
Benazir yanzu takeji duk da tasan ita tanada kame kai da hankali fiyeda yayarta Sumayyah din duk da ba dubararka bace tsarewar Allah ce.

Ita kanta Sumayyah tinda ta dawo makarantar take cikin damuwa da tsarguwa tareda kunyar dagowa ta kalli mutane sbd kunyar abinda yake jikin nata ganin takeyi kaman zaa ganeta.

Dan haka rayuwar makarantar ta zamar mata kaman wani sabon qunci da damuwa dan kuwa gabaki daya a muzance take cikin mutane,

Mummunan hali ta samu kanta aciki wanda ya saka rayuwar makarantar da karatun ficewa kanta gaba daya,
Tamkar mujiya haka ta koma acikin mutane,
Tin tana daurewa har takasa damuwa da qunci yayi mata yawa dole ta dena shiga mutane kwata kwata sbd itama ciwonta dake neman dawowa.

Hankalin Benazir tashi yayi ya rabu biyu akan karatunta da kuma Sumayyah din musamman yanzu dayake tana daukeda lalurar juna biyu.

Daga ita har sumayyar karatun acikin kwanaki kalilan neman lalace musu yakeyi ga jikin Sumayyah din ciwo yau gobe lafiya tin suna iya controlling abin suna boyewa har hande tagane sumayyah dai dale akwai abinda yake damunta bayan malaria da sukace.

Ana cikin wannan matsuwar da tashin hankalin sukai exam wadda daga Benazir din har sumayyahn babu wanda ya iya karatu bare rubuta abin arziki.

Ranar da suka gama exams wani babban tashin hankali ya samesu na rasuwar mijin Ms ayshansu wadda a ranar ta bar garin zuwa jos garin mijinta inda acan zaayi janaizarsa.

Wannan babban sabon tashin hankalin yasanya jikin Sumayyah rikicewa gabaki daya sbd ms aysha itace gata da mafitarsu dasuke gani itama ta tafi ta barsu.

A ranar sabon tashin hankalin kwanan zaune sukai duka su ukun babu wanda ya rintsa sbd a yanzu kam babu mafita sai wadda ubangiji zai sake aiko musu kokuwa dai qaddarar ce dai ahakan tazo musu.

Wannan karan kukan da Benazir tayi yafi na kowannensu tashin hankali da taba zuciya sbd itace take iya hango kowannensu ciwonsa dap yake da tashi wanda tasan suna juyewa shikenan ita kadai zaa bari da dawainiya da wannan quncin da radadin wanda daqyar itama wannan karan idan bata samu mental problem dinba,
Ya zasuyi da cikin sumyayyah?
Zatayi da babyn idan aka haifa?
Me zata fadawa ababa?
Me duniya zata fada akan babyn?
Tayaya takeda tabbacin Alh bilal zai waiwayesu?
Innalillahi wainna ilayhi rajiun.

Kuka tayi sosai wanda ya saka jikin Sumayyah da Anne sanyi dan kuwa sunsan ko a gurin azabar idan zasusha nata zai fi yawa sbd itace mai lafiyar da zatafisu jin radadi da ciwo tareda qunci mai yawa.

Sai dataji hawayenta har sun qafe idanuwanta ko buduwa basayi sosai ta dena kukan ta kallesu cikin tausayawa sbd a yanzu ta rungumi qaddarar cikin lafiyarsu da abinda zai samesu idan suka rasa hankalinsu take ji yana cin zuciyarta.

Tausayin tausayi akeyi tsakaninsu
Su suna tausayinta ita kuma tana tausayinsu da babyn da zaa haifa wanda zai taso cikin uquba da masifar da uwarsu ta taso aciki suma suka taso aciki.

Abincin dare ta fito ta dora tana gamawa tayi sallah ta fito ta hau wankin hande.

Sai goma da mintina hamshin ta shigo dakin ta tadda Annensu zaune tayi shiru tareda nisa cikin tinani idanuwanta na kan sumayyah wadda baccin wahala da dole ya fizgeta.

Qarasowa tayi ta zauna gefen Anne tareda zamewa ta kwanta tana yiwa Annen saida safe cikin dasashiyar murya.

Har kusan asuba Annensu bata rintsa ba tana zaune cikin nisa a tinaninda batama san me take tinanawarba,
Ita kanta Benazir har kusan asubar batai bacci ba sai daga baya ya dan dauketa bata jimawa akai kiran asuba ta farka ta fito.

Tare sukai sallar asuba dukkaninsu
Suna gamawa Anne da Benazir suka fito
Itama sumayyar daga baya biyosu tayi suka fara aikin gaba dayansu.

Sai 11 suka dan samu saukin aiki suka zauna suka ci abinci
Ko tashi gurin basu yiba amai ya subucewa Sumayyah mai qarfi sbd cikinta daya kasa karban abincin da suka cin.

Amai takeyi mai qarfi da sauti wanda yasa dukkaninsu miqewa suna rarraba ido,
Hande kuwa da sauri tayo dakin tana tambayarsu aman lafiya ne kuwa?

Shiru sukai tayita maganarta ta gaji ta tafi kafin Anne ta wuce da sumayyan dan tayata wanke jiki
Benazir kuwa gyaran gurin tahau yi ta kwashe ta wanke gurin fes da omo me qamshin ta goge.

Acan koda Anne ta wanke jikin Sumayyahn zazzabi da ciwon ciki mai qarfi ya rufeta saida Benazir tazo suka kamata suka kai daki
Take ta juye cikin ciwo mai tsanan koina nata jijjiga yakeyi.

Anne ta zauna da ita Benazir ta fita ta qarasa aikin tareda girkin rana tana gamawa suka zauna kan sumayyar wadda take cire rai da rayuwa.

Haka suka wuni da ita a daki cikin damuwa da mutuwar jiki
Haka kuma suka kwana da ita.

Washe gari ma haka suka kima wuni da ita jikin ba dadi sam sai addua ba wanda ya kulasu
Hande ma ido ta kawo ta saka musu sbd tasan ko zasu mutu Ababa bazai saka kudinsa yakaita asibiti ba dan haka ba ruwanta tinda ba lafiyar zata basu ba bazata iya yawon sanni ba.

********acikin sati biyu sumayyah gabaki daya ta koma kaman mai ciwon qanjamau sbd rama da rashin kuzari,
Ciwonta yaqi sauki sam kullum haka suke fama da ita,

Benazir da Anne ma kaman masu qanjamau din suma dan itace take ciwon amma ramar da zabgewar dukansu ne sukai babu me dubuwa acikinsu banbancinsu da ita kawai ita cikin ne yake ajikinta amma duk damuwa da kuncin daidai yake a zikatansu.

Har lokacin babu labarin ms aysha hakama ba na Alh bilal,
A kullum yanzu sallamar ababa da tarinsa tashin hankalin na fits hayyaci yake sakasu sbd sunsan yau da gobe bata barin komai.

Babban sabon tashin hankalin dasuka shiga shine fara bullowar cikin,
Ciki dai ya bullo bazai boyu ba,
Fitowa tsakar gida yanzu kam ya gagari sumayyah indai da rana tsaka ne sbd kada hande tagani ta sanar da ababa.

Idan sun lissafa daidai watan cikin uku kenan ake magana.

Ajiyar zuciya tareda numfashi mai zafi Anne ta sake tana kallan sumayyah da benazir ke cirewa farce sbd tsayi da sukayi da wata tsohuwar rezarsu da suka siyo kwanaki a hanyar makaranta.

Sanyi jikin Annen ya sake dauka suma sanyi jikinsu yayi ganin irin kallan da Anne ke musu cikin sarewa da sadaqarwa.

Ajiye rezar hannunta benazir tayi tana dafa hannun sumayyah daya dauki rawa ganin Annensu datake sake tsinkar dasu.

A hankali anne ta bude baki cikin sanyi tace

“Ya zamuyi da cikin nan na sumayyah daya fara bayyana?”
Kunsan cewan daga wannan watan cikin nan bazai taba boyuwaba,
Tayaya zaa hana hande da Ababa ganinsa,innalillahi wainna ilayhi rajiun”  tafada cikin fidda rai daba dukkanin sauki.

Sunyi kukan har hawayensu ya dena fita dan haka idanuwansu sukai jajir Benazir ta dago ta kalli Anne zatayi magana idanuwanta ya sauka kan hande dake gefen dakinsu tsaye tayi mutuwar tsaye tsaban tashin hankali da firgicin abinda kunnuwanta suka jiyo mata
“Ciki a jikin sumayyah kuma”?

Miqewa tsaye dukkaninsu sukayi cikin firgici da tashin hankali mai girma suna kallan handen.

Sai data share mintina kusan shifa a qame kafin ta iya motsawa ta rufe idanuwanta ta bude ta sake taba kirjinta taji zuciyarta na bugawa daidai bata sume ba,

Tsikar jikinta je suka miqe gabaki daya sbd tsoro dan kuwa ita kanta tsoron maganar shigarta tayi tinanin idan ababa kawai yaji zancen.

Babu wanda ya motsa acikinsu tsaban tashin hankali da tsoron yau ranar da suke tsoro tazo.

Qafafuwan hande na rawa ta qaraso cikin dakin tana kallan sumayyah da cikinta yake bayyane dan qarami a jikinta
Bakinta ya dauki rawa da yankewar kalma tace

“Cikin haihuwa a jikin sumayyah,
Ciki dai ciki dai na ‘dan mutum,Qalu innalillahi wainna ilayhi rajiun,
Benazir,Benazir yanzu daman cikin mutum ne ajikin sumayyah kuke boyo?
Meya kaiku?
Wace qaddarar ce wannan?
Uban waye yayi mata cikin?
A in?
Aljanun hauka ne suka shigeku duk ku dukan ko me?
Cabdijam,babbar magana,attt.

Babu wanda ya iya magana acikinsu sbd dai rana ta riga ta baci ba gyara.

Janyo sumayyah hande tayi da qarfi tana qara kallanta cikin kunya da baqin ciki da takaici tareda mamakinsu.

Numfashi ga koma saukewa sbd bata da bakin magana lamarin ya shallake tinaninta.

Fitowa tayi dakin a rikice ta zube tsakar gida tana sake sauke numfashi a jere sbd ita kanta kwatanta tashin hankalin da zaayi a gidan kawai tayar mata da tsikan jiki yakeyi.

Duk bayan sakanni sai ta sauke numfashi mai zafi tana kallan kofar dakin nasu dasuka kasa fitowa kaman yanda kowannensu wuta ta dauke masa babu me iya magana.

Kaman masu jiran sakamako haka suka kasa ko zaunawa dukkaninsu suna a tsaye har akai magrib sukai sallah babu wanda zuciyarsa ke harbawa daidai har handen itama ranar tana idar da Sallah ta fito tsakar gidan ta dasa kejera ta zauna jiran dawowar ababa.
#MAMUH#
#MARRIAGE#
#LOVE#HOT#LITTLE BENAZIR AMNAH KAANTE#DD KAANTE#ZAFIN KAI

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-FURAR DANKO
Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim

Send your Shedan biya Anan👇
09032345899

MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇
09033181070

Yan Nijar kuma ga inda zaku biya👇👇👇

+22799643131

Zafafa🫶🔥🔥

Leave a Reply

Back to top button