Cinikin Rai Book 2 Page 44
44-Tayi laushi sosai, don haka komawa jikinshi tayi tana wasa da gashin kirjinshi. Da suke kwance luf-luf. Janyota yayi kirjinshi ya kwantar da ita, yana wasa da gashinta. “Kin ga Kanwata Rahmah?” Gabanta ne ya fadi, ta d’ago kai tana kokarin kallon fuskar shi. “An bani aurenta, tun zuwan da nayi bayan rasuwar Iyayenku. Amma ban amsa ba, saboda bana tunanin haka ta sauki.” Gyaran murya yayi, sannan ya cigaba da cewa.
“Mahaifinta tun kafin na tafi ya bani auren yarshi, amma ban amsa ba domin ina tunanin gobenta. Ashe yarinyar ta saka haka a ranta, taki kula kowa sai ni. Don haka koda nazo akan su tafi min bikonki. Suka taso da maganar Rahmah. Ba xan iya kin musu ba, shi yasa na amince da zancenta. Saboda naga kamar baki da ra’ayina.” Tashi tayi zaune, ya kalle ta ganin take ƙoƙarin danne kukanta yasa shi juyawa, zai sauka a gadon. “Kuma aurenta zaka yi?” Murmushi yayi a ranshi ya ce. “Eh ai da mahaifiyarta da Mahaifina abokan wasa ne, Sayyada Quddisiya ta auri Wan Babanta, kin ga kenan duk lamarin daya ne, Babanta kakansu daya da Abbana.”
Ya faɗa yana me daukar towel ya daura akan idanunta. Kallonshi take daga sama har kasa, wani irin kuka ne ya kwace mata.
“Tow meye na kuka?” Ya tambayeta, bayan ya wuce banɗaki, yana wanka ta shigo itama. Tana kuka tana wanka, tana gamawa ta fito ta nufi wurin kayanta. Ta wanda zata kwanta, wani abin mamaki shi ne barci ua kaurace mata baki daya, babu al’amarin barci a idanunta. Shima aikin shi yake a laptop yana lura da juyinta, har ya gama bata rintsa ba, yana gamawa ya haura gadon. Ya janyota jikinshi yayi mata wani irin runguma da dole ta kwanta a jikinshi. Domin tana rigimar ba zata kwanta ba ne a jikinshi. A hankali ya take sauke ajiyar zuciya. A haka barci yayi gaba da ita. Wurin asuba, tunda ya sakata a gaba da fitina sai da taji a ranta kamar ba zata iya ba, domin al’amarin babba ne a gare ta, sai da tayi kuka kafin ya kyaleta, yana kyaleta ana fitowa sallah asuba. Ban daki ya shiga ya tara mata ruwan wanka, ya zo ya dauke ta cak, ya je ya sakata, sannan ya shiga suka yi tare, suna fitowa Abin sallah ya shimfida musu, sannan ya jasu sallah. Barci sosai tayi bayan sun idar. Wurin karfe daya tana barci tayi ta jin maganarshi sama-sama, saka kunne tayi ta ji yana dariya sosai. Dakyar ta shiga ban daki ta gasa jikinta, riga da skirt ta saka tare da hula ta fito falon, fuskarta iya kwalli ta zizara, sai man baki amma babu laifi ta zuba turare a jikinta.
Takowa yayi har bayanshi, Video call suke da rahama, tana nuna mishi Yaranshi da draman da suke, shine yake dariya, itama rahamar ta dage sai biye musu take. Mace kenan ya faɗa a ranshi, domin ta fahimci yadda yake son walwala. Sumbatar kumatun Malik Zeeno tayi tana faɗin. “Kanwata ya kike?” Ta faɗa tana dariya itama, bata rai Rahmah tayi. “Hi Babys ya kuke?” Yuuu suka yi kan wayar suka fara mata gwaranci. Sannan ta biye musu. A hankali ta kwace wayar bayanta dawo kan cibiyar shi ta zauna, a hankali ya rungumeta, yana shafa bayanta. Kashe wayar tayi, ta ajiye a kan center table ta ce mishi. “Yunwa nake ji!” Sumbatar kanta yayi yana jin kamshinta yana fisgar shi.
“Nima yunwa nake ji.” Ya faɗa yana ciwon kunnenta. “Ai kaci rabonka, ni gaskiya ina jin yunwa.” Landline phone service na dakin ya dauka da yake gefensu, yayi odar kome, sannan ya ajiye yana mata wani shu’umin kallo. “Ni yanzu yunwa nake ji, don Allah a bar ni na karya.”
Murmushi yayi ya cigaba da jagwalgwalata, har aka kawo abincin ya amso, dakyar ya barta ta ci abincinta. Tana gamawa ya ce mata. “Nawa ne kudin kwalliyar nan? Zan saya ne.” Ikon Allah, anya Malik yana da lafiya kuwa? Ta tambayi kanta. Murmushi yayi yana me janyota yana shafa fuskarta. “Na sayi kwalliyar.” Tun a nan wurin ya fara tura rundunan yakin shi, kamar zata yi kuka domin baki daya so yake ya saka kanta yayi Bindiga, salon alamarin shi, babba ne don haka tana ji tana gani a falon sai da ya surfeta, tass sannan ya kyaleta. Shima don yaga kamar zata shid’e ne yasa shi kyaleta.
Tunda tayi wanka, ta shiga bargo bata kuma yarda wani abu, ya haɗa su ba. Dama tayi sallah tuntuni. Izuwa yanzu zata iya cewa amarcin dasu yi ba suke yi. Domin wallahi sai da taji baki daya garin Dubai ya dame ta, kwanansu uku ya fita da ita shan iska, da shopping ba laifi ya kashe mata kudi kamar hauka, domin bai ki ta kuma ɗaukar min wani cikin ba, an ce hali a jikin rai yake, babu me iya sauyawa. A dan tsakanin nan, ba karamin sauyi ya gani a wurinta ba.
Asalima babu zafin nan, ita take binshi a wannan kadamin. A bangaren da ya fahimci gazawarta wurin mu’amalar aure, shi kanshi har tausayinta yake ji, domin baki daya tayi laushi, sannan a bangare guda. Tunda yace zai kara aure ta saukar da duk wani abinda take yi, ta zubawa Sarautar Allah ido.
Duk da shima a na shi, bangaren yana lura da ita, ta saka shi hira. Duk wani abinda tasan zai faranta mishi yi take. Kwanansu biyar suka wuce China. Basu tsaya a ko ina ba, sai a garin Beijing.
Anan suka sauka, sannan ya tafi maganar kasuwancinshi. Baya dawowa gida sai dare, a wannan kwanakin ta fara period dinta, wanda ya shiga tsakaninsu. Dake baya dawowa da wuri, sai a asuba yake d’aga mata hankali da fitina. Don ma ba dogon kwanaki take ba, kwana hudu zuwa biyar ne. Tun a ranar na hudu yake rokonta don Allah idan ya dauke ta gaya miishi, yayi missing dinta. Dariya ya bata domin ta huta a kwanakin, ranar da ta gama ai kuwa bawan Allah nan, kiri-kiri yayi ta murna, har da ɗaukarta sama a kunne ya gaya mata cewa.
“In sha Allah, wannan karar idan na buga wasan yadda ya dace. Sai a amai da toshe hanci”
Murmushi tayi, wato tun da suka yi sallah isha, ta ci abinci Malik yake abu ɗaya. Tun tana daurewa har abin ya wuce tunaninta, sai da ya ga da gaske bata motsin arziki, ya kyale ta.
Ba karamin wahala take sha a hannunshi ba, baki daya ta zabge. Haka suka yi ta fama har suka bar kasar, suka yi ta yawo, watansu biyar, suka dawo kano. Har lokacin babu al’amarin zata kuma.wani cikin shima ya daurawa ranshi masifar son haihuwa. Haka yasa yake yawaita magana har ta fara jin babu dad’i.
Tana barci, ta ji hayaniyar yan mata a gidan, farkawa tayi ta fito falo. Malik ne da yan matan Cousins dinsu. Suna zaune sai hira ake. Murmushi tayi tana faɗin. “Sannunku da zuwa!” Kallonta suka yi, kafin suka ce mata. “Yawwa!” Daga haka suka cigaba da hiransu, tashi yayi ya nufe ta yana faɗin. “Muje kici abinci.” Wannan halin Malik ne, a gaban uban kowa yana nuna darajarta. A madadin wasu mazan da suna ganin danginsu zasu fara maka iskanci da renin hankalin. Yana musu girki yana bata labari, tana dariya. Har suka gama ya fita falon. Kus-kus suke suna zuwa suka yi shiru, anan yake janta da hira har ta sake aka yi ta hira da ita.
“Wai ba zaku bamu abinci ba ne?” Murmushi yayi, ya ce mata. “Ba zaki basu abinci ba ne?” “Zan basu mana, sai dai muje muyi abincin tare da kai!” A hankali suka nufi kitchen a tare, suna hira. Shinkafa da miya suka daura, yana kallonta yadda take ciro kayan, yana gaya mata abin da zata saka, tana gama cirowa ya nuna mata yadda zata gyara, shi kuma ya ciro kaza ya zuba musu ruwa, suna sakewa ya fara yankawa, yana gaya mata yadda zata yi, abin gwanin ban sha’awa, tana gama markade kayan miyar, wanke kasar ya zuba a tukunya ya shiga gaya mata. “Kina gama wanke namar, sai a zuba a tukunya, spicy da sauran kayan kamshi da dandano, zaki zuba.
Sai ki zuba, ba zaba daure a wuta ba, sai an soya wannan albasar da mai, sai mu cigaba da suya shi. ” Haka suka cigaba da hira, a waje kuwa kiran Rahmah yan matan nan suka yi, albasar nayi golden, ya juye mata kazar, ya haɗa kome ya rufe yana sumbatar wuyarta. “Kin yi kokari!” Juyawa tayi, tana sumbatar kirjinshi.
(Tsakani da Allah 😂😭💃🤔 saboda kishiya Zeeno ta sauko daga bishiyar kace)
Aikuwa duk abin da suke akan idanun Rahmah, ganin yadda suke cinye juna. Jikinta yayi sanyi, dake transparent glass door ne, su na ciki basu lura da ita ba, amma ita ta lura da su. Juyawa tayi jikinta a mace. Idan ta shiga tsakaninsu ita ce zata wahala, ita tana son mijin da zata gina mishi soyayyarta a zuciyarshi. Amma wannan maganar gaskiya Malik da Zeeno. Sun gama gina soyayyar junansu, zai yi wuya wani abu ya raba su. Don hakan tana ganinsu, tunaninta da lissafinta suka bata ta hakura da Malik d shi, har abada domin Malik na Zeeno ne shi daya.
Suna can suna girki, ita tana zaune a Falo, ana ta hira da ita suka gama abincin suna fara fito da shi suna shiryawa a tsakiyar falorn, suna gamawa suka nufi dakin Malik, suka yi wanka dake akwai kayanta a dakin ta saka, suna hira.
Abin burgewa suka shirya a tare suka fito, tana gudu yana Binta da gudu. “Sannunku da zama.” Idanun Malik sauka yayi akan Rahmah, tana murmushi. Bayan sunci abinci, ta kalli Zeeno ta ce mata. “Oum Hassan, bani aron Mijinki!” “Gaki gashi.” Ta faɗa muryanta a sake.
“Muje ko yallabai!” “Wai kin yarda na je?”
“Me zai hana!” Fita suka yi, bayan sun tsaya a jikin motar shi, Rahmah ta fi Zeeno a shekaru, amma bata da ra’ayi akan abubuwa dayawa, kallon shi tayi tana murmushi ta ce mishi.
“Kana son matarka sosai, me yasa ba zaka gayawa kowa ba? And ni a nawa ra’ayin aurenka babu wani cigaba da mace zata samu? Kasan dalilin haka. Kai da matarka kuna haukar son juna, idan har nace xan shiga, karshe zamu bawa juna wahala ne, Ni ban same ka yadda nake so ba, ita kuma ban barta ta same ka kamar yadda kake mata ba, kai kuma baka samun kwanciyar hankalin da ya dace ba, tsakani da Allah waye azzalumi? And shawara daya xan baka, shi ne ka dauki matarka, ka koma dasu inda ya dace. Ana maganar mutane ba zai taba barinku, ku zauna lafiya ba me saka muku idanu, anan kuwa awa society zasu iya haifar maka Matsala tare da gurbata maka tunani, ina gaya maka ne bisa ga zaman da nayi cikin al’ummar mu, please ka tafi da ita. Yarinya ce sosai. Sannan tana bukatarka ainun.”
Rungume ta yayi yana buga bayanta. “Thank you ” ya fada yana sake ta. Dariya tayi tana faɗin. “Idan ka sake wani ya ga wannan abin sai ya maka kallon dan bariki!” Tsayawa yayi ya saka hannu a habbar shi, sannan ya ce mata. “Kuma haka ne fa, bari na fara barikin akan matata.” “Allah ya kintsa tsohon nan” ta juya wurin motarta, ta wuce abinta.
Wato da ana samun mata irin Rahmah da an zauna lafiya, domin cikin ruwan sanyi ta magance rikicin da zai iya kunno kai. Amma wasu matan da bala’i sai sun auri namiji. Kamar yaki idan suka ga namiji sai sun mallake shi, sai aka yi dace ita bata cikin irin wadannan matan, domin she only need love. Shi yasa ba zata tura kanta cikin yanayin da ba zata iya fita ba. Tasan me take yi ta san me take ji, tana son kanta da kuma yadda zata rayu cikin aminci da salama, bata son a rabata da mijinta, gara itama kada tayiwa wani balle a ce za amata….
*Maganar gaskiya akwai matan da sun san namiji baya sonsu, kuma baya kaunarsu, amma don bala’in sai sun aure shi, koda kuwa ajalinsu ne shi. Sannan sun san da haka kuma su hana shi auren wacce yake so, karshe su yi abandoned ɗinshi a duniyarsu! Let met in Nazneen*
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/28, 8:16 PM] Yan Mata: