Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 6

Sponsored Links

 

Page 🖤06🖤

 

“Saki kuma ummah?”
“Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan”
Yawu ya haÉ—iya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin Æ™waÆ™walwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaÉ—ai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila’in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaÆ™wakiyar mata oho.
Biro ya É—auka tareda takardar baya ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
Hannunsa yana rawa yakafa biron akan takardar,ko meyasa hannunsa da dukkan gabobin jikinsa suke bijirewa umarnin mahaifiyar tasa,zuciyarsa sai bugawa take a matakin daya fi na bugawar kowacce zuciya,ji yake kaman wata boyayyar igiya ta riƙe hannayensa ta hanashi aikata abinda aka umarceshi dayi.
Sautin amon dariyar Lubnah ne ya hanashi fara rubutun.
“Hahhaha Hajiya zeenah kenan,a tunaninki dan kawai kin Æ™iramu kinyi wani Æ™ulunbotonki na lokaci kaÉ—an,saiki samu abinda kikeso daga gareshi?
Indai har duk lokacin dana É—auka ina tsaye akan sa,wannan maganin naki zayyi aiki mai nayi kenan duk tsawon lokaci?
Hmm to bariki ji na faÉ—a miki,…..koda kinyi nasarar fitarda Jabeer daga cikin ikona,bai isa ya sakeni ba dakansa,kuma ya waye washagari da numfashinsa,saidai idan nice da kaina nace ya sakeni.
Anriga an gama maganin,an zuba a kogi ruwa ya tafi dashi,aikin da baya taba karyewa kenan,sai ankai ruwa rana.
Kinga kuwa kozai karye ba’a wajenki ba.
Zabi ya rage gareki Hajiya zeenah,zaki iya sakawa ya sakeni yanzu,amma shima zai mutu,saiki zaba shin zama dani ko kuma gawar É—anki?”
Tana gama faÉ—in hakan ta tashi tabar falon É—auke da murmushin mugunta akan fuskarta,inda ta bar Hajiya zeenah a zaune tana buÉ—e baki a sake.
Maida kallonta tayi ga Jabeer wanda ƙarfin maganin ya sakeshi,ya kwanta a wajen jiki a sake,da alama bacci yayi ma bai san mai sukeyi ba.
“Me….me nakeji haka ni zeenatu da kunne na?”
Tashi tayi daga dinning É—in ta nufi É—akinta,ko kallon Jabeer bata sake ba wanda bacci ta É—aukeshi a wajen.
Bayan ta tafi iyani ce ta matso wajen tareda É—ebe kayan wajen,a ranta tana mamakin rayuwar masu kuÉ—i,ita kanta haushin Lubnah takeji,tana ga babu wanda yakaita jin haushinta,itace sanadiyyar mutuwar É—anta.
Dan kawai ya karza mata mota ta saka akayi ta dukansa saida ya suma,bayan sati guda a asibiti yace ga garinku. Wannan abun yana ran iyani,wanda bata ganin zai gushe daga ranta,har randa ƙasa zata binne mata ido.
Ƙarar waya ce ta tashi Jabeer daga baccin da yayi akan dinnimg table ɗin,yana dubawa ya missed call ɗin Khaleel har wajen goma.
Mamaki abin ya bashi,musamman yanda ya kwanta bacci akan table É—in cin abinci..
Lokacin wayarsa ya duba,kusan ƙarfe Goma,awa kusan guda kenan da rabi yana bacci. Motsa jikinsa yayi wanda yayi masa nauyi sosai. Tsayawa yayi cakk tunowa da yayi da abinda Hajiya zeenah ta umarceshi dayi.
To shida aka ce yayi saki mai yasa kuma yayi bacci,wata ajiyar zuciya yayi da godiya ga Allah da muryar lubna ta ceceshi dayin sakin,duk da baiji abinda take faÉ—a ba.
Lokacin dayake niyyar sakin baiji wanann tsoron dayake ji idan zai saketa ba,yanzu kuma tsoron yadawo cikin zuciyarsa sabo fill,bayason ma yaga takardar balle ya rubuta sakin a jiki.
Miƙewa yayi daga kujerar ya nufi ɗakin Hajiya zeenah,duk da cewar bayason abinda take buƙatar ya aikata,amma kuma yanajin babu daɗi ya tafi batareda yaji mai ya faru ba.
A zaune take akan Kujerar madubi tana kallon madubin.
Sallama yayi a hankali amma bata amsa ba,har zai ƙara wata sallamar a zatonsa bata ji mai yace ba,saikuma yaji maganarta.
“Sai yanzu ka tashi daga baccin?”
“Uhm mai ya farune na kwanta bacci nan take,sannan mai kuka tattauna da lubna”
“Babu komai,yayi kyau da baka san mai ya faruba,ka tafi aikinka kawai,nasan za’a nemeka,babu abinda ya faru,karka saka wani dakuwa a ranka”
Duk da cewar muryar mahaifiyar tasa ta faÉ—a masa sabanin abinda take faÉ—a,amma kuma tunda tace ba komai shikenan,shima sai yabarshi a akan.
Yana fita ya shiga motarsa driver yaja shi,har suka isa companyn yana tunani,amma yagagara samun Æ™waƙƙwaran wani abu guda É—aya da tunanin ya bashi mai ma’ana.
A bagaren Lubnah kuwa tana fitowa daga sashen Hajiya zeenah ta cize fatar baki,dama tunda taji wai ƙiran zuwan karin kummalo tasan ba abinda arziƙi bane,saidai ta yanke shawarar taje taji damai surukarta ta tazo,ga zatonta kuwa wani abu suke kitsawa.
Basu sani ba dukkansu tafi ƙarfinsu,kallonsu kawai take daga iya gudun ruwansu,da tayi niyyar a asirce Jabeer karya kula kowacce mace a duniya sai ita,amma yanzu ta sanja shawara,hakan ya nuna tamkar tsoro take bata yadda da kanta ba kenan,dan haka zata bar koma wacece ta shigo cikin gidan,koba komai tasamu abinda zata dealing akan mijinta.
Murmushin mugunta tayi taresa ciro wayarta tana neman number bokan nata,da alamar shawarar data yanke tayi mata,zata ga wace marar tsoronce zatayi kishi da ita,babu wacce take kawowa a ranta sai Jawaheer,wacce dama tasan tana crush akan mijinta,saboda tana tsoronta ne shiyasa taja birki.
Ringing biyu wayar tasa tayi ya É—aga tareda sakin wata dariyah.
“Madam Lubnah kin bani tazara,kuÉ—ina sunyi kasa fah,gashi ke ba a ganinki sai kinzo muhimmin aiki,ke kaÉ—aice kike Æ™irana na É—auka nayi miki aiki batareda kinzo ba”
“Kaga zulumgum ba wanann ba,wannan aikin dazayi min akan Jabeer,kabarshi kawai na fasa,bashshi ya kawo duk wacce yakeso cikin gidan,sanann suma iyayensa su aura masa duk wacce suka ga dama.
Inaso ne kowacce tayi danasanin saninsa,bazan iya hakan ba sai kowacce tashigo cikin gonata,sanann zan É—ana tarko na kama akuyar data ke cimin Danga”
“Yanda kika ce madam,hakan ma yayi,ta nanne zaki dunga yin aikinki akansu kina horar dasu”
Sun É—an daÉ—e suna maganar a wayar,dukka bai wuce na kisa ba da kuma na yanda zatayi nasara a rayuwa.
Iyani ce ta shiga É—akin Hajiya zeenah É—auke da lemo da kuma kofi a hannunta,dan dama ta saba takan kaimata lemo mai sanyi idan tayi irin wannan tunzurar,saidai na yau kaman yafi na ko yaushe,dan tunda ta shiga É—akin da safe har azahar bata fito ba.
Hakanne yasaka iyani cikin tunanin ko ƙalau.
A zaune take a bakin madubin kaman É—azu da Jabeer ya sameta.
A hankali iyani ta dan matsa kusada ita tareda yin magana a hankali.
“Hajiya yakamata ki dunga daurewa kina barin wani abun,girma yafara kamaki,karki jawa kanki wata matsala,tabbas babu dadi kam,amma wani abun a dunga bashshi shine yafi dacewa”
“Iyani iyani iyani na barshi ya wuce?…. Ke ganau ce ba jiyau ba akan abinda t tsinanniyar yarinyar tayimin,nifa na haifi yaron amma ta maidashi gabaÉ—aya Æ™arÆ™ashin ikonta,har faÉ—amin take tafi Æ™arfin babu abinda na isa nayi..
Taya kike ganin wannan abin zai fita a raina na mantashi? Ji nake kaman nayi a hauka a halin yanzu,wannan la’ananniyar ta kaini bango fiyeda yanda kike zato,ta kashe wasu ta Æ™untatawa wasu,ta zalunci wasu,tunda tazo gidannan babu wanda ya taba jin daÉ—inta,Æ™arin baÆ™incikin shegiya juya ce,bata komai saidai taci tayi kashi………”
“Eh to hajiya idan har abin ya dameki kuma kinaso kiÉ—au fansa har haka,mai zai hana nabaki wata hanya,saidai kafin nafaÉ—amiki zangaya miki gaskiya……..Ki gwada neman amincewar BOMBEE (BAƘAR AYAH)wataÆ™ila ta yarda ta aureshi,idan ta baki wasu sharuÉ—É—an,tabbas zata magance miki duk abinda Lubnah take ji dashi,saidai fah……….”
“Saidai me inajinki wacece ita a ina take?”
“Uhm kawota cikin wanann ahalin naki tamkar kin É—au wuÆ™a kin dabawa kanki ne,domin ko ke dakika kawota idan abinta yazo kanki bazata raga miki ba sam,ita din annoba ce da ba wanda ta bari,ko makiyinka bazaiso manna maka itaba ballantana kuma masoyinka hakan ma ke uwa ki aurawa É—anki ita……ina gwanda miki fitinar Lubnah da nata fitinar”
“A wane waje take,ki sanar dani naje na sameta,sannan menene labarin ta”
“Uhm a garinmu take,saidai nima bantaba haÉ—uwa da ita ba,kasancewar ba a garin na girma ba,a wajen yan uwana nakejin labarinta,Æ™arshen labarinta da naji ance wai Barikin sojoji sun koreta saboda fitinarta bazasu iya ba,ta koma jejin Garinmu da zama a can Gyembu”
“Soja kuma,soja ce ita?”
“Eh sojace tun tana da Æ™ananun shekaru da shiga,ban san mai yafaru ba dai kasancewar bandamu nasanta ba,amma naji dai ance ba kasafai yanxu ake ganinta ba,saidai in wani ya tabata tazo yimasa hukunci”
“Shekarar ta nawa,kinganin zata amince da abinda zan nema a wajenta,kincemin babu wanda yake sakata abu tayi sai taga dama,sannan kinsan fah lubna da asiri take kashe kishiyoyinta,bakya ganin itama zata kasheta? Koda yake in hakan yafaru ma babu abinda yadameni,indai zata min abinda nakeso shikenan”
“Hhhhh hmmmm hajiya kenan,ni kaina da labari kaÉ—an naji,nasan hakan bazai faru ba sam,amma dai tunda kinga zaki iya shikenan sai mu kama hanyar gobe inshaaallah,…..amma fah kiyi shawara kafin”
Iyani da faɗawa Hajiya da alamar ta farka da abinda take tunanin zatayi tun kafin lokaci ya ƙure mata.
Saidai Hajiya zeenah tayi nisa batajin ƙira,akan cikar muradinta na rusa Lubnah babu abinda bazatayi ba,inyaso koma mai zai faru ya faru daga baya.
Daga haka ranta yayi fari,ganin ta samu mafita akan abinda yake cimata tuwo a ƙwaryah.
Washagari da safe,da shirin tafiya Hajiya zeenah ta tashi,ina tayiwa Alhj aliyu daɗin bakin ta samowa Jabeer ne mata wacce zata aura masa,babu yanda bayyi ba akan karta kashe ƴar mutane a banza,amma kuma ta ƙeƙasa ƙasa,shiyasa ya ƙyaleta ya zuba mata ido. Wanda yace zai haɗiye gatari saika sammasa ƙota.
Itama iyani a daren tabawa mijinta labarin abinda yake faruwa,shi bai ce komai ba,dan dama hanyar dazai rama abinda Lubnah tayimasa yakeyi. Dan haka zanice ta tadda muje.
Bayan itada iyani sai mijinta,daga nan babu wanda yasan abinda zataje yi,shikansa Alhaji Aliyu bata sanar dashi wacece ba.
Da haka suka kama hanyar jihar taraba Hajiya zeenah iyani da kuma driver,sai tsarabar da sukayiwa iyayen iyanin.
Ita gaba takaita,koba komai zataje gida batareda ta kashe komai ba……….
Muje zuwa,yanxu labarin zai fara……….

 

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama’are

 

 

 

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

 

Leave a Reply

Back to top button