Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 31

Sponsored Links

Page 🖤31🖤

 

“Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato.
Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa.
Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara haihuwa,dole sai dawowa gida sukayi,dan su inna laari sun matsa kan ayi na gida mana.
An fara na gidan,a daren ta haifi ɗa namiji wanda dama ya daɗe da mutuwa a cikimta,dan har hakan ya shafi mahaifarta itama tabiyo ɗan tare.
Jinya tafarayi duk da bayan rashin ɗan.
Koyaushe tana ɗaki komai sai anyimata na taimakawa.
Sai bayan wani lokaci abin yaƙi mlm Ahmadu ya maidata asibiti shida inna laari,a nanne aka tabbatar masa da cewar ta kamu da matsanancin hawan jini.
Wanda shiya taba mata ƙwalkwalwa da kuma idanuwanta,wanda sanadiyyar kullum da zurawa waje ɗaya babi ƙiftawa har suka mutu suka daina gani.
Magana kuwa duk abinda za’a faɗa babu wanda zata amsa,shima duk yanada nasaba da ciwon daya sameta”
Lokacin da muruje yafaɗawa su Hajiya zeenah matsalar Danejo haƙiƙa sun tausaya mata,kuma daman sun ganta a hakan ai lokacin da suka shiga gidan.
“Wai amma tayi tsawon rai,hawan jini yayi mata wannan cin amma tana raye?”
Hajiya zeenah ta faɗa cikeda mamaki.
“Shekara uku kenan data samu lalurar,dan tadaɗe tana jinyah kafim hakan yasameta,kuma har yanzu ana yimata maganin gargajiya dana asibitin”
“To ya Bombee kuma tayi data dawo taga yanda innarta ta koma,sannan yaushe ta dawo”
“Hmmm Bombee fah watan ta kwata kwata biyu da dawowa garinnan da zama, dan da zuwa tayi ta koma a cikin mission ɗin aiki, shima kuma daman ba’a gidansu take zaune ba,dan mlm Ahmadu yace badai gidansa ba,farkon dawowar a gida ta sauƙa,wani abu da tayi masane yace bazata zauna a gidansa ba.
“Mai tayi masa?”
Hajiya zeenah ta faɗa cikim zaƙuwa.
“Ummm bayan dawowarta garinnan tayi taimako ɗayah amma kuma tayi lahani shima.
Zuwan ta ne takafah ƙungiyar Black blood,wanda tayita da taimakon wasu mutanenta fararen fata guda biyu da kuma masu baƙar fata guda uku,dukkansu kuma matane masu jarabar ƙarfi.
Duk wanda yashiga ƙungiyar zai dunga yin tuƙin hawan mambila,ita kuma in yana wajenta babu wani ɗan fashin dazai tareshi a hanya,da sharaɗin zai kaimata kuɗin ta itakuma duk wata.
Matasa ƴan iskan gari da sukaji haka tuni suka shiga,aka basu training ɗin tuƙi na musamman,ga kuma yanda take basu lasisin yin abinda suka ga dama,indai ba gonarta suka shiga ba,nan da nan tafi uwarsu ma muhimmanci a zuƙatansu.
Ta gina wani gida a can cikin duhuwar daji,inda take masa laƙabi da yankinta kuma fadarta,saidai har sannan bata komaba”
“Meyasa to ta ginashi idan ba shiga zatayi ba”
“Zuwan ta shekara biyu baya kafin ta ginashi a gidansu ta zauna,wanda dama wannan ba zuwa tayi zaman dindin ba.Tazone kaman gida daga aiki,wanda aka turo ta garin tareda wasu sojojin. A lokacinne ma tafara kafah kungiyar dana baku labari a bayah”
“Eh munji labarin wannan kungiyar muma shigowar mu cikin garin a bakin wani mutumi toro”
“Hakane tana da mutane masu tarin yawa a ƙarkashinta”
“Dawowarta zaman dindin shine ko dariyah bata fiye yiba,sannan kuma bakowa ne yake kallonta ba saida gaske,ita kaɗai ta dawo daga ita sai wata matsashiyar budurwa kaman sa’arta,sannan yanayinta batayi kamada ƴar ƙasar nan ba.
A lokacin ko sunan sojiji batason a anbata a kusada ita,bamusan dalilin ba,wata biyu kenan da faruwar hakan.

______***DAWOWAR BOMBEE GEMBU***_____

 

 

Shaƙar iska tayi a bakin ƙofar shigowa garin daga cikin baƙar motarta ƙirar daraja😀.
Hakan dataga bayyi mata ba fitowa tayi daga cikin motar ta tsayah tana kallon wani dutse dayake gabanta,wanda yayi kore sharr dashi. Idonta a rufe tajiyo muryar HILYAAAN daga cikin mota tanayi mata magana da hausarta da bata gama iyawa ba.
“Anty Maryam (Bombee),shin zan sanarda su Zeezah da Khamees shigowarki ne?”
“Ahah kyalesu ba fadata zan tafiba tukunna,zanje gidane,sai an koroni saina tafi nawa gidan da dalili”
“Kaman ya ban gane ba,sai an koroki kuma,ai gidanku a cikin garinnan da waccer shekarar mukaje?”
“Eh shifah can zan tafi in sun koremu saimu shige can ɗin,karki faɗamusu zuwana,duk da nasan inashiga garin zasusan isowata,inasone naje naga wanne aiki sukayimin a wajen,sannan wannene kuma a cikin dajin ya tsallake umarnina,uhhhhh kinsan inason naga mutum yayimin kuskure,na matsu naje naga wannne irin gini sukayimin.
Saidai nafison naje naga ya fuskar tsofin can zatayi idan suka ga mai zan kai musu hhhhhh”
“Toh shikenan,ya labarin wannan matar kuma dakikace zakiyi maganinta,koba yanzu bane lokacin?”
“Ba yanzu bane lokacin,sai nan da zuwa wani lokaci kaɗan………..ina baby boy ɗina yayi bacci yanzu ko har yanzu bai koma baccin ba?”
Juyawa Hilyaan tayi bayan motar inda kyakykyawan jaririn yake kwance yana zuba baccinsa hankali kwance.
“Yayi bacci,saidai kinsan jikinsa yayiwa wajennan kaɗan,satinsa fah biyu,kema kuma bakisha maganinki bah na 4:00 pm.”
“Mtsww nagaji da wannan maganin wlh,jiri yake sakani sannan kuma yana ƙaramin yawan jin yunwa”
“Uh ai dole kisha tunda wannan kika zaba,babu yanda dr Na’im bayyi ba wajen karkiyi zirga zirga amma kinƙi ji”
Dawowa motar Bombee tayi tashiga,kafin Hilyaan ta tuƙa motar zuwa cikin garin.
Tun a nesa da bakin kofar gidan Hilyaan ta ajiye motar,tareda ɗakkowa jinjirin a showel dinsa tabiyo Bombee a baya,wacce har ta fara tafiyah zuwa cikin gidannansu.
Wani yarone yasha gabanta tareda cewa.
“Lahhh Bombee soja ta dawo ta dawo”
Cakk Bombee ta tsayah jin abinda yaron yafaɗa,hannunsa ta riko tareda juyashi kansa yana kallon ƙasa,yaran wajen ta kalla tareda cewa.
“Wani ya ƙiramin uban yaronnna lo uwarsa yanzu nna”
Da gudu kuwa labari ya iske larai saigata ta fito,dan jikanta ne ɗan ƴar ta wanda yake wajenta.
“Ke wane shegene zai kashemin jikan……..”
Kirifff taja bakinta ganin Bombee ta ɗaga yaro yana wutsil wutsilll.
“Ohh ashe kece kika dawo,dan Allah meya miki haka yaro dashi”
“Tambaya ma kike mai yayimin,amma a sanina kinsan halina,bana tsallakewa daga ƙarami har babba koh. Ƙirana yayi da wancan sunan,wanda yanzu na tsaneshi fiyeda mutuwata……..misali zanyi akan sa kowa yagani,idan na kuskura naji wani yakirani da wancan sunan uwarsa ta haifi wani a garinnna kowaye shi kuwa”
Taugunnawa larai tayi tana roqon Bombee,amma haka tayi mursisi tasaki yaron yafaɗo takayi,larai dama tana ganin idon Bombee ta saita faɗowar sa,dan haka da sauri tayi kifiyah ta cafeshi a hannunta,jikinta har rawa yake saboda tsoron Bombee da kuma tashin hankalin data gani.
Dauke kai tayi tashiga gidannansu,wanda kafin sannan har labarin isowarta cikin garin da abinda tayi ya zagaya a bakin magulmata,kuma daman takeso.
Yanzu zuciyarta tayi baƙi ta dafe,batajin ƙwarin gwiwa sai mutane suna yaɗa abinda ta aikata,tun gulma tanayi mata tabo har tazamo maganinta nasha a yanzu.
Ko sallama batayi ba tasaka kai cikin gidan,bata samu kowa ba dan haka ta wuce ƙofar ɗakin innarta.
A zaune take akan kujerarta ta zubawa gabas ido.
Bombee ta daɗe a bakin ƙofar ɗakinnata tana kallonta batareda tace komai ba.
Muryar inna laari ta jiyo tafito daga ɗakin girki,da alama abinci dare takeyi,dan laasar tayi sosai.
“Wanake gani a ciki gidannan yau mun shiga uku”
“Ba tara ba iya uku kika shiga laari,niɗince dai ganinan da raina ina shaƙar iska”
Tafaɗa tana jan iskar da ƙarfi,tareda yin wani dan banzan murmushi.
“To komai kikazo dashi ma munfi ƙarfinki,ta allah bataki ba,tun wurima kizo ki fice daga gidannan”
“Saboda gidan ubanki nake ciki,saiki bari mai gidan yazo ya koreni da kansa,hhhh kika ce wai kin fi ƙarfin abinda nazo dashi,wannan kuma zancene,abinda na zo dashi baki tabayi ba laari,saboda nafiki iya shege ta wata sigar,duk da nasan ta wani gun kinfi gaban kwatance,saboda keɗin kurace da fatar akuya kike zaune a garke”
Zaro ido inna laari tayi baki sake tana kallon Bombee,anya kuwa bata shaye shaye take gaya mata wannan maganganun.
“Bombee kekuwa ɗiyar arziƙice,karki manta fah innarki tana jinki kike wannan maganganun”
“Saime dan tanaji,tunda bazata iya hanani ba kuma bazata ganni ba ina amfani jin toh,keda kike ji dake nake”
Yaron dayake hannun Hilyaan ne yafara kuka da alama ya tashi.
“Ohh laari bani kujera zan zauna na shayar da jaririna mana”
Bata ɗauki maganar Bombee da wasa ba dan haka ta gara mata kujerar cikin gatse dan a tunaninta Bombee duk iya shegenta ne.
Ga mamakin ta kuwa ta zauna a tsakar gidan babu ko kunyah a ƙarkashin inuwar bishiyar gidan tafara bashi mama,bayan ta ɗan ɗage gyalen dayake wuyanta.
Zaro ido inna laari tayi tareda cewa.
“Yau ni laari mai zangani,ƴar nan ɗan me nake gani haka”
“Ɗana ne mana,mata mazace ni danna haihu kike mamaki,shikenan mutum bazai iya haihuwa ba,ko ke kaɗai ce mace kai. Zaki wani tambayi tayaya,ta yanda mlm Ahmadu yayi miki cikin Innayi mana,nima ta haka nayi cikin nawa ɗan tareda wani daga cikin mazajena”
Mari inna laari takaiwa Bombee cikin zafin nama,jin abinda Bombee take fadamata,wanda ko kare bazai ciba.
Saurin riƙe hannunnata Bombee tayi tareda wullata can gefe tafaɗa cikin kwatar dake wajen wanke wanke.
Tashi tayi daƙyar saboda yanda kwankwasonta yabugu,daidai lokacin tana ɗagowa ta hangi mlm Ahmadu wanda yake tsaye yana kallon su.
Kuka inna laari tasaka tareda fitowa daga wajen.
Hanyar ɗakinta tayi tareda cewa.
“Mlm barin na tattara kayana natafi garinmu nikam,kishiya bata fiddani ba,amma wannan ƴa kam bazan iya da ita ba dam annoba ce”
“Ina zaki laari,duk naji munanan kalaman data faɗa,basai an maimaitamin ba,miye na tafiya tunda bada ita na gina gidan ba ai yanzu zata barshi basai anjimaba.
Kizo ki fitamin a gida na sallamaki,sannan abinda kika zo nunamin naganshi na kuma gode,bana son duk abinda zai tunamin ke daga yau”
Wani murmushi Bombee tayi mai dauke da ma’anoni kala kala.
“Har zan wuce gidana na tuna cewar karka bar gida har sai an koreka,shiyasa nazo a koreni na tafi fa dalili,amma kafin sanann bari ɗana ya ƙoshi tukunna.
Kayi haƙuri baba da naso yimaka mai suna,sai kuma nasaka masa sunan…….kodayake shikenan dai”
Tafaɗa tana jan numfashi,a yanda take magana kaman ba ita ubannata yafaɗawa kalmomi masu girgiza duk wani ɗa ba,musamman ƴa mace.
Miƙewa tayi tareda miƙawa Hilyaan ɗanta Haidar,wanda take ƙira da young Haidar.
“Toh baba ni zan wuce saina shigo garin sainaxo mu gaisa,Laari karki manta fah wasa tsakanina dake bai soma ba tukunna…..sai wani jiƙon”
Duk maganar datake mlm Ahmadu bai cemata kanzill ba dan takaici,mai zaice mata da wannan maganar,shi bai taba ganin wannan iftila’i ba a rayuwarsa,idan wani yace masa Bombee zata zama haka zai iya buga ƙasa yace bai yarda ba.
Daga haka tafita daga cikin gidan cikin izza da ƙasaita.

 

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button