Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 30

Sponsored Links

Page 🖤30🖤

 

Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai.
Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje.
Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin.
Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu.
“To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?”
Harzata shiga ɗakin kuma wata zuciyar tace baritaje ta duba tagani.
A hankali cikin sanɗa ta nufi sashennasa har ta samu shiga.
Kofar abuɗe take,hakanne yasake tabbatar mata cewar akwai mutum a cikin ɗakin.
A baƙin kofar ta tsayah tana shirin leƙawa,bata ankara ba sai ganin mutum tayi yafito daga ɗakin da sauri cikin baƙaƙen kaya.
Shima bai kulada indo a wajenba dan haka sai suka yi karo tareda faɗuwa a tare.
Mayafin fuskar mutumin indo takama saboda karta faɗi,aikuwa tajawoshi zuwa hannunta.
Hasken farin watane yasakata gane waye a gabanta.
“Bombee!!!!?”
Tafada cikin sanyin murya haɗe da razani kuma.
“Shiitttt tace tareda shaƙe wuyan indon. “Eh nice,kuma naji labarin kinganni a gidannan zakiga yanda zan miki ehe”
Taƙarisa maganar tana boye wukar datake hannunta duk jini a jikinta.
Tsallaketa tayi ta fita daga gidan da sauri,indo na nan zaune a wajen bata samu damar tashi ba har kusan Assalatu,dan tsoro takema karta tashi Bombee tadawo tasake yimata wani gargaɗin.
Ita kuwa tana fita daga gidan jeji ta nufah gidan su inno.
Har tazo shiga ɗaki taji uwaisu yana cewa.
“Ke Bombee daga ina kike da tsohon darennan,keda ba lafiya ce take ba sosai?”
Mayafin data rufe fusakarta haɗe da sukar ta boye a bayanta tareda cemasa,
“Bakomai baffah,kawai kawai wani ɗan abu nayi a jeji”
“To shikenan,amma jejinnan fah ki kiyayeshi Bombee”
“Tamm”
Daga haka ta wuce ɗakinta,bukkar datake gefen tasu.
Jijjigata taji anayi.
A hankali ta buɗe idonta tana kallon inno dakuma uwaisu a kanta,idanuwansu ɗauke da tashin hankali.
“Ke Bombee jiya ina kikaje da daddare dana ganki”
Shuru tayi bata basu amsaba,sai daga baya kuma tabuɗe baki a hankali tace……
“Uhm gidan su goje naje”
“Mekikayi masa a gidansu da tsohon dare”
“Uhm…uhm..”
Tana cikin inyinar ne goje nuna mata wuƙarta da kuma mayafinta na jiyah,wanda tana zuwa kwanciya tayi bata tsayah wanketa ba.
“Bombee na riƙeki tamkar ƴa ta,inda wani ne yazo yafaɗamin abinda kikayi,ba wai nina gani da idona ba,bazan taba yarda ba,Bombee kisa kisa fah kikayi,ina zakije da ran dayah rataya a kanki yanzu.
Duk wani rashin jikinki haka naji nagani na ɗauka,saboda nasan yarinta ce watarana zaki daina,amma kisa Bombee bazan iya rufemiki ba,inna faɗamiki zan taimakeki akai nayi ƙaryah”
Shuru Bombee tayi tanajin mai yake faɗa,runtse idanuwanta tayi da alama tatafi cikin wani tunanin.
“Yanzu bazancen bata lokacin bane,Bombee yakamata ki fita daga gidannnan ki buya wani wajen,domin indo tasanarwa ƴan sanda taganki kin fito daga ɗakin goje da tsakar dare,ɗauke da wuƙa mai jini.
An bazama ko ina ana nemanki tun safe,nan ma ba wajen buya bane zasu iya zuwa,domin gidanku sunsan kina nan wajen.
Dan Mlm ma yace gidanku sunce kina nan wajen,nasan bazai wuce innarki ba,dan ita kaɗai tasan inda kike”
Tasho Bombee tayi cikin sanyin jiki ta yafa gyale akanta,wuƙar tata dake gefen Uwaisu ta ɗauka ta saƙala a kunkuminta.
Bakin ƙofa ta nufah kafin tayi magana cikin sanyin rai.
“Nagode da hidimarku a rayuwata,haƙiƙa a yanzu nakai matakin da bazan kusanci masoyana ba,saboda suma bazasu iya tsira daga kaidina ba.
Ni makashiya ce yanzu a idon kowa,dan haka wanda yarabeni ma za’a fara ganin sa a matsayin hakan.
Nizan tafi sai wata rana”
“Ina zaki tafi yanzu”
“Inno ta faɗa cikin raunin murya”
“Can da nisa,inda nima bansani ba,amma zanyi iya koƙarina wajen ƙauracewa nan wajen”
Daga haka tasaka kai tafita a cikin gidan.
Saida tayi gudu mai nisa kafin tajuyo ta kalli gidan da yake ɗauke da rabin yarintarta,motar ƴan sanda taga ta nufo gidan,hakanne yasa ta tabbatar da maganar baffannata,kuma bazata ga laifinsu ba gameda furucinsu gareta,ta cancanci fiyeda hakan ma a gun kowa.
Cikin dajin ta nausa ta gudu,ko ganin gabanta batayi sosai,har saida takai gejin iya yanda jikinta zai iya ɗauka.
Gari ko ina ya ɗauka cewar Bombee takashe goje har cikin ɗakinsa,dan da safe ana zuwa aka sameshi anyi masa yankan rago a wuyah.
Bayan an ɗaɗɗaureshi da igiyah anyi masa duka.
Abu wasa wasa yakai ga ko ina labari ya watsu,Bombee kuwa anyi neman duniyar nan babu ita babu labarinta,ta bace battt kaman bata duniyar.
Mlm Ahmadu tunda yashigo da safe bayan labarin ya riskeshi yake cikin ɗakinsa,ko fitowa bayyi ba ballantana yace wani abun.
Danejo ce ta tashiga ɗakinnasa,yana zaune akan dadduma yayi shuru.
“Sannu mlm,baka ce komai ba shin anganta ne”
“Hmmm ina za’a ganta,ni ina kyautata zaton ma yanzu haka bata garinnan,domin bayan yanka shi datayi,wai hadda kuɗi ta ɗiba maƙudai a cikin ɗakinnasa,kinga kuwa mai zata zauna tayi a garinnan”
“Kuɗi?…..hadda sata kenan aka a ɗakinnasa?”
“To yanzu ai ba ta sata ake ba,ta kisan da akayi ake,wama yake ta wani kuɗi yanzu”
Shuru Danejo tayi tana maimaita ɗiban kuɗin a ranta,saidai bata ce komai kawai ta tashi tabar ɗakin.
Yanayin damuwar data shiga da ita ɗakin taragu daga kaso Ɗari zuwa kusan kashi talatin,dan tunda taji zancen hadda sata tasakawa maganar ayar tambaya.
Taga haka bata sake bi takan zancen ba ta nufi ɗakinta.
Saida Bombee tabari dare yayi kafin ta fito daga maboyarta.
Babban hijabi ta zunduma har ƙasa haɗeda nikaf.
Hanyar cikin garin ta nufah domin gani mai yake wakana.
Can nesa da ƙofar gidansu ta tsayah,yara sunata wasan dare.
Ahhh kaman hakan bai faruba a rayuwarta,saidai ta sabanin farincikin da sukeyi itakuma cikin baƙin ciki take. Koyaushe saidai ace mata zai wuce,bata taba tunanin dagaske bane sai yanzun daya wuce tagani.
Wani yaro da ƙira yazo wuce ta gefentada kwano a hannunsa.
“Kai dan Allah ɗan zo na aikeka gidan can mana”
Zuwa yayi ya tsayah a gabanta,wata takarda ta fitar a nannaɗe a cikin hijabinta tabashi.
“Ka shiga gidan ka tambayi wacece Danejo,sannan sai ka bata,karka bawa kowa sai ita kaɗai”
Ɗaga kai yayi alamar yaji,daga nan yashiga gidan.
Jimm tatsaya tayi domin jiran fitowar dan aikan,bata ga ɗan aikaba shuru har na wani lokaci.
Wasu mutane tagani samari guda uku suna iyo hanyar da take,sannan kuma da yaron a bayansu yana yi musu magana.
Dan murmushi Bombee tayi ganin sakarcin da suke nuna mata,a zotonsu shin wayo suke mata zasu kamata,da alama labarin tana kallo da daddare bai gama karaɗe garin ba.
Saurin juyawa tayi tana tafiyah da sauri sauri tanufi jeji,suma suka bita a baya.
Sun danyi tafiyah mai nisa,dan zuwa yanda gudu suke itada dasu na tafiya.
Da alama ga wanda zata bawa saƙon subawa mutanen gari,ta faɗa a ranta.
Su su biyar ne,kasancewar darene kuma basanin hanyar wajen sukayi ba,nan da nan tayi nasarar rarrabasu a jejin.
Bayan wani ta dawo yana dube dube ta kifa masa naushi a kusan wuyansa,hakanne yasa ta jube yana dafe wajen.
“Kayi haƙuri da dukan danayi maka zaka warke,ni zan tafi daga garinnan,ina so kaje ka sanarwa gari bai ƙare iya nan ba ina nan dawowa watarana”
Daga haka tayi saurin barin wajen kafin abokanannasa su tarar da ita.
Hanyar gidan su haidar ta nufah,ta zauna a can nesa da gidan,tana jiran wani a cikin gidan ya fito,amma shuru har bacci ya ɗauketa a wajen.
Ba ita tafarka ba har saida alfijir ya keto.
Mahaifinsu Janar Muhammad Bello tagani ya fito daga gidan ɗauke da wani abu kaman drawer,a wajen motarsu ya ajiyeshi inda wasu kaya suke,da alama tafiyar zasuyi kenan.
A cikin booth ɗin motar yasaka inda wasu kayan suke,dayake Helux ce tanada ishashshen wajen ɗinban wasu kayan.
Duk abinda yake Bombee tana kallonsa har yagama ya koma cikin gidan.
Lallabowa tayi har zuwa bakin motar.
Idan tashiga motar nan zata samu damar barin garinnan batareda matsala ba,kuma dama batasan hanyar dazata bi ta tafi ba.
Cikin booth din motar da tsilliga tareda shiga ƙasan drawer daya saka a cikin motar.
Tana gama shiga kuwa haidar yazo da wata jaka ya ɗora a saman,yanda yayi mata sauƙi wajen buyar batareda gajiyah ba.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda fatan Allah yasa hakan da tayi shine daidai kuma mafita kaɗai a gareta.
Muryar haidar taji yana cewa.
“Bombee??me kike a cikin mota kuma,hakan ma a drawer,tsawon wannne lokacin kike ciki?”
Saurin buɗe idanuwanta tayi ganin hasken rana akanta,ga kanta wanda yakeyimata azabar ciwo,saboda gangarar dataji anayi a hanyar tafiyar har yasakata yin suman wahala.
Bata iyah buɗe baki tasake yimasa magana ba tafara komawa wata sumar,saidai taji muryar Hajiya Zulaiha tana cewa.
“Abban haidar kawai kashiga da ita cikin jirgin,bamusan mai yasa ta zabi biyomuba amma tabbas akwai dalili,kuma a yanayinta yanzu tana buƙatar hutu,mu kammu mun jijjaga da hanyarnan inaga ita”
Tana gama jin maganar taji an ɗagata ciɗak zuwa cikin jirgin.

__________DAWOWA WAJEN SU HAJIYA ZEENAH__________

 

Tunda aka tafi bada labarin,hajiya zeenah tareda idi masu yi wani kyakykyawan motsiba har aka gama.
“To wannan shine labarin rayuwar Bombee a garinnan tundaga tashinta,kuma itace wacce kuke nema,duk da bansan mai yasa kuke neman ta ba,amma wancan tana yarinya ne kukaji”
“Kan buuuuu Hajiya Inaga mukoma ki huta gobe mu ɗau hanyar gida kawai”
“Iliyah yafada yana dauƙe ajiyar zuciya”
“Ahah Muruje to ina kuma labarinta a wajen su Hajiya Zulaiha ɗin,sannan kuma ya akayi ta dawo garinnan har kacemana tana cikin garinnan?

 

Todai nasan kuma zakuso ku sani koh?????😂😂😂

 

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Leave a Reply

Back to top button