Bakar Ayah Hausa Novel

Bakar Ayah 29

Sponsored Links

Page 🖤29🖤

 

A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai.
Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka.
Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin.
Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska.
Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka ba a rayuwarta.
“Na ɗanɗin inane,sannan kuma waye ya kawoni wajen?”
Ta faɗa sanyaye,bata kai ga tantance hakan ba daga mariƙar ƙofar ya murɗa,wanda lokaci dayah ya murɗa da tunaninta,dan kuwa batasan wata ƙofa mai hannu yana motsi ba.
Haidar ne yashigo ɗakin,fuskarsa ɗauke da mamakin ganin idonta a buɗe.
Ɗaga murya yayi yanda na wajen ɗakin zai jiyoshi yace.
“Mommy kizo da sauri ta farka”
Ƙarisowa yayi cikin ɗakin tareda zama a gefen gadon da take kwance.
“Sannu Bombee yakinki,amma wannan mutane basuda imani a ransu”
“Meyafaru bayan wanda ya auku a jejin,sanann inane nan haidar ka kawoni”
“Muna zuwa mutanen suka gudu,sannan yau kwananki uku a kwance,nan kuma gidanmu ne”
Yana cikin yimata bayaninne wata ƴar dattijuwar mata ta shigo ɗakin,a kallon farko zaka hango kamanninsu da haidar ɗin,saidai matar tafishi hasken fata da kuma manyan idanuwa.
Murmushi tasakar wa Bombee mai taushi tareda zama akan kujerar dake madaidaicin ɗakin.
“Sannu yarinya yajikinnaki,gaskiya a yanda suka dake gidannan kinji jiki sosai,mai kikayiwa wannan mutane haka?”
“Babu abinda nayi musu Mommy,yaran tsohon mijina ne da muka rabu shekara biyu baya”
Tare haidar da mahaifiyar sa suka haɗa baki wajen cewar.
“Tsohon mijinki shekara biyu baya,yanzu ma nawa kike daza’ace shekara biyu baya kinyi aure?”
“Uhm hakana babana ne ya auraminshi saboda naƙiyin jarabawar tafiyah makarantar kwana,to a ranar farkon aurenmu ne…….yazo yimin fyaɗe na farmakeshi shine……….aka raba auren. Yanzu kuma yazo daukar fansar abinda nayimasa,saboda illar danayi masa na bazai sake haihuwa ba”
Dakatar da Bombee Hajiya tayi da maganar,dan tun a bayani farko tagano abinda ya faru,ita kanta tayi mamakin karfin halin Bombee ɗin,amma kuma saita barshi akan tayine dan ƙoƙarin kare kanta.
“Kinga ki daina yawan magana dan baki gama warkewa ba,Allah ya kiyaye nagaba,haƙiƙa kinyi bajinta sosai,dan dama haidar yasha bani labarinki tun kafin yamiki magana,koyaushe sai yazo yacemin yaga mace a jeji tana koyon faɗa.
Yanzu dai ba wannan ba,yakamata ki faɗamana gidanku domin a sanar da inda kike,danna san dole zasu nemi sanin mai ya faru dake”
Shuru Bombee tayi tareda tafiyah tunanin abinda yafaru kafin zuwanta jejin a ranar,abinda ta aikata a gidansu tasan babu wanda zai nemi sanin inda take,kuma ba wannan ne ma babban abin dakuwar ta ba. Ita kanta innarta fama take da lalurar rainon ciki,sannan asibiti sun tabbatar ba’ason ta dunga shiga damuwa,sannan kuma ga uwa uba abinda tayiwa mahaifinta.
Babu abinda take sakawa iyayennata sai tashin hankali,dan haka lokacin yayi daya kamata ta dakata da wannan abin haka.
Numfasawa tayi kafin tace.
“Iyayena basanan,a wajen maharbi uwaisu nake zaune”
“Uhm kaji ba dama saida nace maka mukaita can kace wai bananne gidansu ba,kana ganinta tana shiga gari”
“Eh inazuwa gidan yan uwana ne s garin”
Bombee tayi saurin kare kanta kafin wani ruwan yasake bullowa.
“To shikenan amma tunda yanzu kika tashi,ki bari nan da gobe sai mu maidaki can ɗin,yanzu zansaka haidar yaje ya faɗamusu abinda yake faruwa”
“Ahah Hajiya nagode da ɗawainiyar da kukayi dani na wannan lokacin,amma inason tafiya yau”
Hajiya Zulaiha ce mahaifiyar haidar ɗin ta taimaka mata tayi wanka da dabara. Saboda har yanzu akwai ciwuka a jikinta sosai,ƙarfin hali kawai take danta nuna taji sauƙi.
Abinci Ta haɗamata marar nauyi taci,tareda magungunan da mahaifin haidar ɗin ya siyo mata wato Janar Muhammad Bello.
A leda Hajiya Zulaiha ta ɗaure mata maganin dakuma wasu abubuwan makulashe wanda zasu tafi dashi.
Ɗakin da take kwanca ta shiga,suna ta hira da Haidar cikin raha da nishadi,kaman sun shekara da sanin juna.
Dukkan hiran dayake mata bai wuce na labarin yayunsa biyu mata ba,da kuma ƙannesa ma biyu mace da na miji,wanda suka tafi makaranta basu dawo ba.
“Uhm kace kana da yan uwa sosai,ni kam mu biyune kawai a wajen mahaifinmu,daga ni sai ƙanwata,itama tana wajen innarta”
“Bombee kin shiryah tafiyar kuwa yau,bazaki sake yimana kwana ɗaya ba”
“Ahah zan tafi ai zan dunga kawo muku jiyara”
“Wai ai inaga nanda sati ɗayah zamu tafi,kafin sannan kam ki kawo mana ziyara idan kin samu sauƙi,yanzu ki fito Baban su haidar na nemanki a falo,zai maidaki gida shida Haidar”
Ɗaga kai tayi cikin girmamawa alamar taji abinda Hajiya Zulaiha tace.
Mutum ne mai yawan murmushi kaman haidar ɗin,sannan gashi dogo kakkarfah……uhm soja mazan fama kenan.
Tsugunnawa Bombee tayi kaɗan ta gaisheshi cikin girmamawa.
Ga mamakin ta kuwa bai ƙyamaceta ba kaman ƴan garinsu,dan da fara’ah ya amsa mata. Har yana tsokanarta wai tafi ɗannasa jarumta.
“Da haidar yabamu labarin yanda kika tareshi har ya samu guduwa a lokacin naji kin burgeni sosai,kuma fah ko kunyah bai jiba yana namiji wai mace tatare masa faɗa,mai makon ya tsayah yaji dasu……”
Dariyah dukka wajen aka saka banda haidar wanda ya cune fuska kaman ƙaramin mai yaro mai feeder.
Kuɗi ya ciro ya miƙa Bombee,amma juyin duniyar nan taƙi karba,dan ita tun lokacin da Innarta tayi mata magana akan kuɗi,sai ya zamo bata fiyeson ko kyauta tadunga karba a hannun mutane ba,ballanta na kuma sata.
Haka dole ya ƙyaleta ganin duk ƙoƙarinsa amma taƙi karba,Hajiya Zulaiha yabawa a ƙarshe kan tayimata siyayya to takaimata.
Da haka Bombee tayi sallama ta matarda taji tashiga ranta,bayan innarta da kuma inna shatu Hajiya Zulaiha itace mace ta biyu data jita a ranta.
A bakin ƙofar gidan suka ajiyeta,bayan Haidar yabata ledar ta Hajiya Zulaiha tace yabata.
Inno tana tankaɗen tuwo taganta tashigo tana tafiyah a hankali,alamar babu lafiya,dan dama kwana biyu tana cikiyarta shuru.
“Ahhh Bombee mai ya sameki haka?”
Bata kai ga amsawa ba taji muryar Haidar yana gaisheda inno,mamaki tayi dama biyota yayi?
“Uhm baka tafi bane dama?”
“Ah iya abbane ya tafi,ni sai anjima zan tafi idan naci tuwon inno”
Yakarisa maganar yana ƙifta mata ido,bai san mutane ba amma har ya shige gaba,ta faɗa a ranta,a fili kuma tana binsa da harara.
Shine yabawa inno labarin abinda ya faru,inda suka jajanta sosai.
Sai bayan ya tafi da daddare Uwaisu yanayimata sirace na maganin gargajiya yake cewa.
“Kwananki uku kenan a gidansu,amma kuma maimakon ki wuce gida sai kika iyo nan meyasa,innarki fah jiya taxo nan tana tambayar ko kinzo nan,inno tace mata kinzo amma kin fita.
Nasan tayi hakanne domin ta kwantar mata da hankali,nima tun a jiyan nake nemanki”
“Ahah baffah bazan iya komawa gida yanzu ba,saina samu sauƙi tukunna,Saboda abinda na aikata,wanda kuma duk inna laari ce ,ni banason matar nan wlh,inna kuma ji takeda ita kaman innarta,shikuma goje…….hmmmm”
Tafaɗa tana cizon baki.
“Kee Bombee to miye dalili ciki danta ji da ita,ke kanki shaidace yanda ta riƙe innarki hannu bibbiyu sanda aka kaita gidanku,kowa yana shaidan halinta na kirki”
“Eh kowa yana shaidanta,amma ni zuciya ta abu daban take faɗamin gameda itah,kuma da sannu zan gwadata domin share tantamata. Shikuma goje aradu ko banyi masa komai ba dolene na ajiye masa Gargaɗi mai tsaurin gaske”
Shuru sukayi babu wanda ya tankama ballantana ya bata yawun bakinsa.
Washagari da safe Bombee ta tashi da ƙarfin jikinta ba kaman jiyan ba,saboda magungunan da take sha akan lokaci.Ranar bata fita taje ko ina ba.
Da daddare bayan anyi isha inno ta shiryah domin zuwa sanarwa innarta labarin ganin Bombee.
Bata hanata yin hakan ba saboda itama tanason kar innar tata tashiga damuwa sosai na rashinta.
Tare suka fita da inno har zuwa ƙofar gidannsu kafin tajirata tashiga tafito.
Duk wanda zai shige tana daga zaune tana kallonsa,harda mahaifinta wanda yadawo daga masallci. Ƙureshi tayi da ido har yashige gidan.
Tunawa tayi da idan yadawo daga isha a irin daidai wanann lokacin yake sake niyamata karatu,sannan suci abincin dare tareda.
Runtse ido tayi tareda saurin kawar da tunanin hakan a ranta,dan a ganin ta bashida amfani a wajen yanzu ba,domin ba komai zai ƙaramata ba sai baƙin ciki.

A zaune suke a bakin ruwa inda suka saba zama kullum,dan tun bayan abinda yafaru da ita,bata koma gidaba yau sati guda kenan.
Haidar ne ya kalli Bombee tareda cewa.
“Yanzu kam kin samu sauƙi sosai koh,dan Allah kidaina yawan biyewa mutane,wanda yanuna baya ƙaunarki ki ƙaurace masa kawai shiyafi,bakiyi tashin hankali dashi,ki tuna koma mai zai faru kefah macece”
“Bakaine nafari wajen faɗamin haka ba,sanin ni macece yasan ma nakeyin hakan,duk rintsi bazan bari wani yaci mutuncina yanda yake so ba,sannan duk wanda yayimin abu naji bazan iya bariba to saina rama ”
“Oh mai yayi zafi ni bance kada ki rama ba,kawai dai ina faɗamikine saboda jibi zan bar garinku ba,wanda nasan banida tabbacin sake haɗuwa dake nan gaba”
“Hmm kuma wannan shine maganar bankwanar dazaka min,maizai hana kacemin duk wanda yayi miki ki rama.
Jiya danaje gidnasu na kula Abba naso kazama soja,a haka zaka zama da wannan zuciyar?”
Dariyah haidar yayi tareda cewa.
“Hhhh shiyasa fah inaga jininku yazo ɗaya da Abbanmu saboda kinada zafin zuciyane wanda ake so a wajen sojoji.
Yanzu ya maganar tsohon mijinki,i hope zaki barshi ya wuce koh?”
“Babu wannan maganar,yau zanje izuwa gareshi kuwa da daddare”
Zaro ido haidar yayi daga nan bai sake cewa komai ba.

 

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

Leave a Reply

Back to top button