Bad Boys Hausa Novel

Bad Boys 21

Sponsored Links

021
____________________
“Miqdad, Ƙasan Ina da appointment da dr Dina a Cairo ko? Bisa wannan dalilin yasa na je gidanka jiya ,coz kasan dai ina buƙatar en kuɗi….”
Cikin dariyar yaƙe ya washe baki ,ya magantu muryarsa na rawa kamar zai fasa ihu “Na sani wlh na sani🥹..
Shine dama dalilin kiran? Ai da kin sani kawai kin turo Acc. details sai in saka maki….”

Ya ƙare magana yana cire glasses 👓 din Fuskarsa yana share gumi ,tamkar wanda yaci abinci mai zafin gaske.

Kallonsa tayi ta gefe ta ɗan kyaɓe baki saboda ta fahimci dalilin shigarsa wannan yanayin

“Hmm ai tunda kaga na tafi ban tambaya ba ,naga abunda yafi wancan girma….miqdad”

“Na’am Hajiya”

“Matarka Salima,ammm nace ba,kana jin daɗin ganinta a yanda take?”

“Ban ..ban fahimta ba ,Matana Salima kuma ,ha’ah ina jin daɗin ganinta yanda take mana…wani abune”?

“Oho🤔Wato bakajin kunyar nuna ta cikin matar abokanka?”

“Haah kinga matsalar kishin uwarmijin ba…mama ban sanki da haka ba ,karki sauya plz,wallahi Salima na Azabar sonki kamar mamanta..”

“Miqdad ban amsar tambayar da nayi maka”

“Me zai hana mama? Matana ai kyakyawa ce zan iya nuna ta a gaban ko waye”

“Tafɗi,to in kuwa haka ne i questioned your manners son,Nasan halinka irin na babanka ne kana da maƙon tsiya amma ,halin da Salima take ciki yakai wani ƙololuwa na tashin hankali duk wanda ya saka ido a kanta zai fahimci cewa Salima a furgice take…anya ma kana bata abinci? Miqdad yimun bayani yanda zan fahimta kodai kaci gundumemen bashin bankine kayi investing a wani business yanzu suke ciren huge task ? In ba haka ba I see no reason matarka zata wahale ta fice hayyacinta har haka….”

“Topah wata sabuwa! Ni banci bashin kowa ba ,haka zan mutu salin alin,in kwanta kabarina ba zullumin bashi ya jamun rataya a kabari ,don kinsan musulunci ya tabbatar da cewa duk wnada ya mutu ana binsa bashi Mala’iku rataye shi zasu yi a kabari bashi ba samun niima sai an biya masa….”

“Dallah yimun shiru ,irinkune kuma ranar lahira ake tula maku tarin iliminku a ka tamkar jaki da kaya…. kwatankwacin ilimin da ba aiki dashi kenan…”

“Innalillahi shiyasa akace matayenku da ƴaƴan ku fitina ne ,fahajiruhum! Ku kiyayesu!…..yanzu gashi tana nema ta hardasa mun rashin jituwa tsakani na dake …me tace nayi mata ? Hajiya? Nasan dai mun rabu dake lafiya”

“Batace kayi mata komai ba ,but allow your woman to breathe….” _President Bola tinubu’s quote_😆

“Au yanzu na shaƙe mata maƙoshine? Taja numfashinta daidai kyauta ne daga ubangiji…mata tana rayuwarta daidai Ni banga ma aibunta ba amma tunda na aureta taja mutane nata gallaza na da magana….”

Komawa tayi kan kujeran da take kai tayi relaxing
“Ashe ma ba nice na fara fada ba…..Huuhhhhh (She sighs) ynz dai ina buƙatar dubu ɗari biyu”

Gabanshi ne yace ras!!! Da sauri ya kame ƙirji “Dubu ɗari biyu kuma ? Me zakiyi da marga_margan dukiyar nan?hectan Fili ne kike son ki sake siya?”

“Kana haukane? Dubu ɗari biyun ne zai siya mun fili? To tunda ka tambaya,so Nike in bawa salima ,atleast zata siya wasu abubuwa datake da bukatar su… ”

“Mama😳In Baki dubu ɗari biyu ki baiwa Salima…dubu ɗari biyu fa? Hmm tirƙashi to wannan dubu ɗari biyun zai siya mun wata sabuwar saliman. Ras Zan biya sadaki inyi hidimar biki in auro wata macen sabuwa fil a leda da dubu ɗari biyu….”

“Ehoow yanzu na gano inda ciwon yake….wato a wancan karon auran gata akayi maka ,tundaga sadaki ,gaisuwar uwa da uba ,lefe ,muhalli abincin taron biki komai yin maka akayi shiyasa baka ɗaukan ta as worth as she deserves………..Miqdad ?! Zaka bani 200k ko bazaka bani ba”

“Hum hum mama don Allah mubar maganar nan don Allah”

“Miqdad I’m deep in serious ,bazan taɓa barinka ka tafi ba wlh tallahi sai ka bada kuɗin nan”

Ɗaura hannu yayi aka “Wayyo Allah na shiga uku! Hajiya kiwa girman Allah ki bar maganar kudin nan🥹 ,wallahi zuciyata na zafi zaku ɗaura mun hawan jini…😔”

Salati ta fara yi tana masifa cikin Muryar kuka “Ya Allah mijina ya azabtar da zuciyata da maƙo🥹 na jure ina addu’ar kar Allah yasa wani cikin yarona ya biyo halinsa ….amma cikin rashin Sa’a gani Allah ya bani kai miqdad😭” kawai sai ta fara sharce hawaye

Ga furgice Ya Sheikh ya sakko daga kan kujera yasa gwuiwoyinsa a ƙasa shima kamar zai kuka

“Kiyu hakuri karki mun kuka in ɗaiɗaice…na yarda zan bada amma ki mun uzuri ,in bada dubu ɗari ɗaya don Allah🥹🙏🏻”

Ɗauke fuska tayi ta miƙe taje ta buɗe diary dinta ta ɗauko acc detail dinta ta ajiye masa

Jikinsa na rawa ya kwashe ya tura mata 100k ,idonsa jajajir ya kalleta na tura hajiya”

Ƙirrr taji shigan kudin asusun ta ,tsaki taja ,ta koma wajen messages tayi copyng account Number din Salima ta tura mata duka . Tana turawa ta kira ta

“Hello sannu hajiya” ta dauki wayar cikin Muryar barci

“Ayyah sannu ƴar nan na tasheki kina barci ko….nasan gyaran gidan nan ba sauki sannu ko? Da sannu komai zai daidaita har mai aiki zaki samu ,yanzu ki duba wayarki na turo maki dubu ɗari kya rage wasu hidimomin….”

Wani ihun murna tayi “Hajiya dubu ɗari? Duk nawa? ”

“Eh karki manta da maganar mu kinji ƴata, sannu da ƙoƙari Allah ya baki ladan haƙuri”

Har Hajiya ta kashe wayar Salima na zuba godiya ,fuskarta taf hawaye

_Allah baka bani dacen miji ba ,amma ka bani dacen suruka ,ko anan I thnk You God_

Hajiya dawo da kallonta tayi kan ya Sheikh da ya gurfana kamar Almajiri sai zufa yakeyi ,duk ya buɗe botiran gaban jallabiyarsa ya cire hulan kansa sai fifita yake da hulan
Dukda fankokin da suke ta gudu a ɗakin amma zufa yake tsatso masa .

“Tashi na sallame ka”
Ta masa magana cikin tsawa

Zumbur ya miƙe“To Hajiya Nagode Allah ya huci zuciyarki”

Ya fice sunsunsun,ai yana shiga mota ya daddage ya kurma ihu
“Wayyoooooooooo🙆‍♂️”

 

 

Its Oum Aphnan
#BAD BOYS

_*Amana ce tsakaninmu ,kin siya ke kaɗai ba tare da wani ba,in har Zaki baiwa wani Littafin nan kiwa Allah kizo in Baki kuɗin ki…*_
_*It’s #500 Regular*_
_*09065990265*_

Leave a Reply

Back to top button