Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 6

Sponsored Links

_Arewabooks@Mamuhgee_
6
Anne data fisu jiqata sbd ba zato tana barci taji saukan masifar tako ina gashi daman bata da lafiya kasa kuka tayi sai wani wahalallen numfashi datake saukewa tana daga kwance kanta na juyawa,

Sumayyah ma kusan kaman a sume take dan bata iya jan numfashi daidai cikin tsananin firgici da azaba take koina nata rawa yake ta qame guri daya idanuwanta a kafe da tsananin tsoron da tashin Hankali ina safnah ta gudu ta tafi tabarsu cikin masifar barnar data aikata dan kuwa har ranar da Allah zai yanke musu wannan wahalar sune zasu ringa azabtuwa da hukuncin wannan abin data aikata.

Benazir kuwa data fi sumayyah da Anne dakuwa sbd kusan itace ta ringa hawa samansu sbd dukan ya fi sauka akanta,bakinta jini yakeyi sosai ga gefen fuskarta ya kumbura a take kaman wadda mashin ya kade,
Wasu hawaye ne masu dumi da bayyanarda radadi da ciwon dayake cikin zuciyarta suka gangaro daga cikin idanuwanta ta rintse idanuwan a hankali tana kasa cewa komai dan kuwa a yanzu qaddararsu ita da ‘yar uwarta da mahaifiyarsu ta sauya ne zuwa wani yankin azabar da zatace safnah itace mummunar sanadin sauya musu rayuwa zuwa wata sabuwar wahalar da basusan inda zata kaisu ba.

Shiru dakin yayi tsit babu motsin kowannensu sbd babu mai iya maganar ko abin cewar,

Har tsakar dare kowannensu na makure a inda yake batareda sun motsa ba.

Rawar da kakkarwan da jikin Annensu keyi sosai yasa Benazir da jikinta yayi tsananin tsami motsawa ta isa gurinta da qarfin hali sbd bakinta itama ya kumbura ya sauya kamanni sosai,
Kamo Annen tayi taji jikinta yayi wani irin zafi mai tsanani
Numfashi ta sauke a kasalance sbd rashin sanin abin yi amma kuma ko yayane dole zata rage mata ko zafin jikin ne dan haka ta miqe da qyar ta dafe cikinta dayasha harbi da qafafun Ababa din tana takawa ahankali ba kuzari ta fito ta debo ruwa a roba ta dawo ta zauna gefen Annen tafara goge mata jikinta da fuskarta da itama yaji mata ciwo gurin dukan.

Sai data gama goge jikin Annen taji sumayyah itama jikinta yayi zafi sosai har taja jijjiga dan haka itama ta dawo kanta ta ringa goge mata jikinta tana rungumeta sbd sumayyar tafi Anne jigata gashi daman rauninta yafi na Annen.
Daqyar benazir din tasamu jikin sumayyah ya dena fizga tana neman sumewa,

Kwantar dash tayi ta rufe kowannensu sbd baccin wahala dasuka samu ya daukesu.

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke a hankali tareda jinginar da bayanta jikin bango taba cusa kanta cikin qafafunta daga zaunen tana rintse idanuwanta sbd itama wani azababben zazzabi da tsamin jiki takeji mai radadi amma batada mai dubata bare bata kulawa dan haka a hakan baccin wahala ya dauketa.

Da sassafe itace tafara tashi tafara duba jikin nasu kafin ta miqe daqyar sbd jiki daya qara tsami ta fito tayi alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta tada Sumayyah da itama jikinta ke tsananin ciwo da tsami ta fito daqyar tayo alwala tazo tayi sallar suna idarwa suka fito dan ayyukan dasuke dole akansu.

Da Ababa suka fara cin karo ya fito cikin farin yadi fuskarsa a hade tsaf babu sakewa bare rahama,
Da sauri dukkaninsu sukai qasa suka gaishesa cikin girmamawa da ‘da,a mai tsanani kansu a qasa.

Ko kallonsu baiyiba ya wuce kai tsaye dakinsu ya fada bai tsaya komaiba ya damqo Annensu dake zaune tana rarraba ido cikin azaba ya fara janta ya fito da ita yana cewa
“Zamanki a nan ya qare sbd daman na fada muku tana bayyanarda haukarta ta gama zama a nan bolar mahaukata zan kaita tabi mahaukata yan uwanta can su qarata a bola bola”

A tare Benazir da sumayyah suka zube qasa gabansu suna wani irin hawayen mafi munin tashin hankali suna rokonsa akan karya rabasu da mahaifiyarsu.
Ko sauraronsu baiyiba sbd basu kai matsayin da zaiji ko rokonsuba, sake jan uwar tasu yakeyi wadda take riqe Benazir da qarfi kaman ranta duk da hankalinta bai gama dawowa daidaiba dika tasan su din yayanta ne da bazata iya rabuwa dasuba ba koda zaa rabata da ranta ne tafison a rabata dashi a tana tare da su.

Sumayyah kuwa a neman rasa kanta takeyi sbd itama qwaqwalwan tata neman juyewa takeyi da uwa da ake kokarin rabasu da ita dan haka ta dunqule guri daya tana kasa motsawa sai fizga da kanta keyi.

Benazir data ke neman zaucewa itama kuka ta fasa mai qarfi tareda rarrafawa ta riqe qafafunsa tana rokonsa cikin qasqantar da kai tana masa Alqawarin yin duk abinda yakeso na ‘yan uwanta dasuka tafi samirah da safnah indai zai bar musu Annensu koda bangaren dabbobinsa ne sun yarda zasuyi duk abinda yakeson harda nasu safnah data gudu da samirah data rasu.

Da farko dakatawa yayi sbd dama baida niyar yafewa ko bata fada ba daman rabonsa na sisi da kwabo akanta da sumayyah zai fanshe harna samirah da safnah.

Hande da sai alokacin ta fito ta kalli su benezir din da uwarsu kafin ta maida kallonta kan Ababa daya tsaya lissafin yanda zaiyi amfani da Annesu ya juya rayuwarsu yanda yakeso hankali kwance koda kuwa karuwanci ne indai zai fanshe kudinsa akansu.

Hande kuwa tana kallonsa tace
“Kai yanzu Abubakar Tinanin me kayi daka yanke shawarar korar Benazir bayan kasan matuqar ka koreta rubatacce ne guduwar ‘yayanta daga gidan nan dan kuwa koda namansu zaka yanka ka tsaga qashinsu ka saka musu kwado da kaca ka daure wlh matuqar sun san uwarsu na can tana yawon bola wlh sai sun gudu sun nemota kaga kuwa asarar dai da kake gudu itace zata bika dan haka maza ka sauya shawara ka barsu da uwarsu idan kanason zamansu a qarqashinka itace jigo”

Shiru yayi tabbas yasan ko zai kashesu ya binne bayan rabasu da Annensu sai fatalwarsu ta fita nemanta musamman Benazir,
Sakin Annen yayi tareda saka qafa yayi ball da ita yana sakin hucin bacin rai ya kalli benazir data sauke kanta kasa tana kallon yanda yasa qafa yayi ball da mahaifiyarta.

Mahaifiyarku itace a tafin hannuna ku sani daga yanzu ko kofar gida wani a cikinku yakuma kalla da wani nufin guduwa wlh tallahi uwarku ce zataji a jiki da jininta.

Qafa yasa ya take hannuwan Benazir din dake gabansa ya wuce yabar gidan yana cewa Hande kar wanda aka bawa abincinsa sai washe gari.

Yana fita Benazir ta rintse ido tareda zubewa zaune hawaye na tsiyayo mata mai zafi da radadi dan kuwa tabbas akan Annensu babu kalar azabar da bazasu iya jurewaba.

Hande Annen tasu dake kwance ta kalla tareda nufarta ta kamata ta tayar tsaye saidai bata iya tsayawa
Kallon Benazir data kasa motsawa sbd nauyin zuciya tace”
Kizo ki kamata kuyi ciki baqi zanyi kada suzo su sameku anan ku ja mana abin magana asan kiwon mahaukata mukeyi a gidan.

Bude idanuwanta da sukai jajir tayi ta tareda miqewa ahankali tazo ta kama Annen takai daki ta dawo ta kama sumayyah da itama kanta ke neman juyewa takai daki bata tsaya musu komaiba dan batasan me zatai taimaka musu dashi ba dan haka ta fito tahau ayyukan gidan datasan wajibinsu ne yinsu kuma sumayyah bazata iyaba a halinda take ciki.

Sai magriba ta gama ayyukan dasuka saba yi su biyar harda Annensu a baya amma ayau ita daya ce tayi aikin dan haka koda ta gama ta dawo dakinsu tayi sallar magrib da ishai kwanciya tayi gefen sumayyah da har lokacin take kaman bata dawo hayyacinta ba.

Washe gari daqyar ta iya ayyukan gidan tasamu aka basu abincinsu ta kawo daki suka rufa su ukun suka cinye batareda ko wannensu ya koshi ba dan haka gurin wanke wanke wanda Ababan ya rage ta kawowa Annensu ta qarasa cinyewa ta koshi ita kuma sumayyah wanda Hande ta rage ta kawo mata itama ta qarasa koshi.

Washe gari ma haka itace tayi ayyukan gidan sbd har lokacin sumayyah bata gama dawowa daidaiba.

A cikin kwana biyu ta qarasa zabgewa sbd wahala da rashin bacci ga damuwa da tinanin da yayiwa rayuwarsu daurin minti.

*********A hankali sumayyah da Anne suka warke suka dawo daidai
Annensu ta dawo saidai kaman batai haukar kwana biyu ba tadawo yanda take saidai kullum cikin fargabar kada ciwon ya sake tashi suke dan haka suketa kokarin hanata tina su Samirah da safnah suka dage suka maye mata gurbinsu batareda bata dama ko kankanuwa ba ta tinasu dan sai saukin haukan yazo mata da mantuwa mantuwa kwata kwata sai tana mantawa da basu biyun ne kawai yayanta ba sai can lokaci lokaci tace ina samirah?ina safnah?

Data fara maganarsu da sauri suke dubarar dasuka mantar da ita zancen sbd kada ciwonta ya tashi komai ya lalace musu.

A yanzu rayuwa tayi musu wani irin juyi zuwa mafi wahala da ukuba sbd wahalarsu tafi yawa a yanzu da suke iya su biyu kawai,
Ababa a yanzu Annensu itace mukullun daya kama na juya rayuwarsu yanda yake so sbd yagama gane itace kawai abinda zai kama yace su fada wuta su fada batareda tinanin komaiba,

A yanzu daya dauki wannan tsarin sai haukarta dake hawa tana sauka tayi masa daidai,
Ya zauna ya tsara sabon lale ga rayuwarsu gabaki daya ta hanyar miqasu ga auren jari ga wasu dilolin miyagun qwaya da masu safarar mutane da ya samu amma sam hadin bazaiyi ba saiya wadatar dasu da ilimin boko mai dan zurfi dan haka kai tsaye ya fidda kudi aka nemar musu gurbin karatun diploma wanda yafi wata yana lissafin kudin dazai kashe kafin yakai ga maida kudinsa yana jinjina maqudan dukiyar da zai samu daga manyan dealers din na qwayoyi da akace suna sakarwa matayensu da iyayen matansu.

Ita benazir kai tsaye Wani hamshaqin drugs dealer dake zaune a lagos da qasar Germany ana tallata masa hotonta yace ya amsa aurenta sbd dari bisa dari tayi masa dan haka ita take yafara yiwa Ababa barin kudi dan haka koda Ababan ya dawo dag lagos ita take aka sauya mata karatun da zatayi zuwa degree.

Cikin saa Tana rubuta jamb taci Admission dinta bai wani zama wahala ba sbd komai acikin saa ta rubuta taci.

Sumayyah ma kusan komai nata ya kammala itama Aminin Ababan Alhaji Sadau shine ya gabatar musu da komai aka jira lokacin fara karatun nasu.

A rayuwar quncin da suke ciki babu abinda ya sauya saima qaruwa sbd duk ya kallesu a yanzu tsagwaron dukiyarsa yake musu kallo dan kuwa kudin daya kashe a shigar dasu makaranta jin yake idan kudinsa basu dawoba ko qasar qetare sai yaje ya nemo masu siyan bayi sun siyesu an basa kudinsa.

Tsananinsa akansu ya qaru fiyeda ko yaushe sbd wasu irin dokoki da tsananin daya dora musu akan ko kallon wani namijn sukai a waje wallahi saiya maidasu makafi dan babu wadda bai gama jingar aurentaba ga wainda zasu maida masa asararsa.

Maganar kula kowane irin namiji a waje ko makaranta ya tsayar dasu ya maimaita musu kusan fiyeda yanda yake maimaita musu qiyayyr dayake musu,

Daga qarshe yayi musu alqawarin binne uwarsu da rai duk ranar dayaji koya gan dayarsu tareda wani.

Hankalinsu tashi yayi da maganar dan kuwa sai tsoron karatun gabaki daya ya shigesu sukaji basa shaawa musamman daya shimfida sabuwar dokar duk wahala da aikin gidan akan uwarsu zai koma duk suna fita harsai sun dawo.
#MAMUH#
#LOVE
#QADR
#MARRIAGE
#BILLONAIRES KAANTES#
#BENAZIR ABABA
#ROMANCE#

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-FURAR DANKO
Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at

Leave a Reply

Back to top button