[Music] Nura M. Inuwa – Rana Dubu
Nura M. Inuwa, mahadin mawaka mai dogon zamani ya saki sabuwar wakarsa mai taken, “Rana Dubu” (mp3 download).
Sakin wakar ya biyo bayan koken da masoyan Nura M. Inuwa suka yi kan ya sakar musu da sabon album ko waka domin sun kosa sa tsoffin wakokinsa.
Nura dai a tsakankanin ‘yan shekarun nan bai cika sakin wakoki daidaiku ba, sai dai album, kuma album din ma sai ya kai shekaru 2 bai saki guda ba.
Ko-da-ya-ke jira hadi da hakurin da masoyansa ke yi yayin da ya ke tsara sabbin wakokin nasa a karshe kwalliya na biyan kudin sabulu.
Kuma dama masu iya magana sun yi gaskiya, da suka ce rana dubu ta barawo, daya ta mai kaya.
Amma fa, wakar nan tayi dadi, saboda haka ina daukacin masoyan Nura M. Inuwa? To, sai ku hanzarta sauke wannan wakar yanzu haka.