Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 41

Sponsored Links

41
Shiru dakin ya dauka bayan lokacin da benazir ta dauka tana kukan da bazata iya sanin ko yaushe tsawon rayuwarta tayi irinsa ba sbd duk masifa da tashin hankali Bata cika Kuka ba kukan ta Dade da qafewa saidai tayi hawaye ko mara sauti Amma a yau din har Kukan shekaru Sha sha dake cikin zuciyarta tayi zuciyarta ta rage mata nauyi.

Tashi tayi ta fito daga daki jiki ba qwari ta nufi toilet tayo fitsari tayi alwala ta dawo dakin,
Sallah tafara Yi ta magrib kafin ta fito ta Dora ruwan zafi ta dawo daki ta hadawa baby Madara ta karbeta daga hannun Anne datayi shiru tana bin benazir din da Kallo duk inda ta motsa tinda tasan itama rabuwarsu tazo din.

Bude fuskan babyn benazir tayi ta zuba mata idanuwanta dake kumbure tana kallanta soyayyar uwar data tsuguna ta Haifa ‘da na shigarta akan yarinyar,
Ko Ababa ya fada ko kada ya fada soyayyar datakewa babyn na irin Wanda tasan sumayyahn ma zatai mata ne.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda gyarata jikinta tafara Bata madaran ahankali tana Dan rufe Idanuwanta sbd kanta dake tsakanin ciwon da kaman zai sauka daga jikinta.

Shiru dakin ya sake dauka babu me magana har tagama bawa babyn ta koshi ta miqe ta bawa Anne ita ta tsaftace mata fidan da cup din data hada Madarar ta kaisu inda take adanawa ta ajiye.

Sauran ruwan ta debo ta shigo daki dasu a babban roba Anne ta kama mata tayi mata wanka suka sake shiryata tsaf tini Takoma bacci Dan haka Anne ta goyata ita Kuma benazir jiki ba qwari ta fito tattara gidan da kitchen kafin su shige.

Har ta gama komai ta shigo musu da abincinsu hande Bata fito ba hakama Ababa Bai dawo ba Dan haka Suka shigewarsu.

Da daddare bayan benazir ta kwanta duqunqune da babyn ciki abin rufa sbd sauro da sanyi tayi shiru tareda shiga tinani Mai zurfi jikinta na mutuwa daga kwancen datake.,

Anne data kasa bacci Jin shiru benazir tayi bacci
Ta tashi zaune ahankali zuciyarta na karyewa kukan Datake ta riqewa tin lokacin ya subuce mata Mai tsananin ciwo da quncin zuciya ahankali ta fasa shi cikin qanqanin sauti kada ta tada benazir wadda idonta biyu tana jin saukan sautin kukan Annen hawaye masu dumi suka gangaro gefen idonta batareda ta motsa ba sbd Daman ta sani qunce ne Mai tsanani a ran Annen ta danne Dan kawai tana son fiddata wannan gidan zuwa Wani gidan.

Anne da batasan benazir na jinta ba Kuka sosai Tasha Mai ban tausayi tsawon lokaci kafin ta rarrashi zuciyarta ta kwanta bayan benazir din hawayenta na cigaba da gangara gefen idanuwanta daga kwance,

Benazir dake tsiyayan hawaye daga kwancen itama rintse idanuwanta tayi tana fatan wannan ya zama shine alkhairi ga rayuwarsu su ukun ita da babynta da Annenta.

 

Washe gari daga Annen har benazir din kasa kallan juna sukai sbd kowannensu fuskarsa da idanuwansa a kumbure suke sbd kukan dasuka kwana Yi mara sauti.

Ta bangare Daya Kuma kowannensu ya dauki dangana da qarfin zuciya ya sake sakawa Kansa Dan haka ayyukan gabansu sukahau Yi Wanda kusan wannan Karan Anne ce tafi Benazir din Aiki sbd babyn da benazir keta dawainiya da ita gashi yau din tanata Kuka daqyar benazir ta samu tayi bacci ta Kwantar da ita taje tayo wanka tana dawowa ta shirya tana Shirin goyata Ababa yace Akai masa ita.

A dakinsa da komai na hutawa yake yasa aka Kwantar da ita kan gadonsa Takoma bacci abinta hankali kwance.

Aiki benazir tazo ta karbanwa Anne suka gama kan lokaci suna shiga daki Akai sallama gidan Wanda ya saka Anne fitowa tana amsa sallaman sbd hande na daki ba lallai ta fito ba.

Budurwar yarinya kyakyawa Anne tagani tsaye a tsakar gidan hannunta riqe da babbar qatuwar leda tana kallan Annen itama cikin muryar me nutsuwa tace

“Sannu Ina wuni.”

Kallanta Anne takeyi kafin ta Dan sauke kallanta ta amsa a sanyaye ta Dora da cewa

“Bari a kira hande.

Juyawa tayi zata nufi dakin hande Zeenah ta katseta da cewa

“Nan ne gidan su benazir????

Dakatawa Anne tayi tareda juyowa tana kallan Zeenah din kafin tayi Wani motsin Ababa da hande suka fito lokaci Daya Jin ana tambayar benazir Dan kuwa yanzu bazaiyi wasa ko barin kowance kuskure ba Dan haka ya fito yaga waye ke nemanta Kuma lafiya.

Kallo Daya Ababa yayi mata yaga kammanin zuriar kaantes take zuciyarsa tayi Wani tsalle ta dawo kirjinsa ya Dan saki fuska Yana cewa

“Barka da zuwa,daga Ina?
Benazir kike nema?

Numfashi Zeenah ta sauke ahankali tareda kallan Ababan ta Dan gaidasa a jagarce kafin ya gaida hande itama tace

“Daga kaantes nake baby nazo Gani”

Wani farin ciki Mai girma ne ya rufe Ababa yace Mata ta qaraso ciki

“Bismillah Bismillah”

A palonsa aka sauketa ta zauna ahankali tareda ajiye ledarta hannunta tareda key din motanta da wayarya gefe tana Dan kallan yanayin palon.

Ababa da Kansa yaje ya kirawa benazir yace taje da kanta ta dauko babyn ta kawowa baquwar.

Jiki sanyaye benazir ta shigo palon da siririyan sallama ta qarasa Kai tsaye dakin Ababan dama suna shiga tinda sune masu gyarawa ta dauko babyn dake bacci hankali kwance ta fito da ita hannuwanta da zuciyarta na rawa sbd daga wannan lokacin dai ya tabbata itace tayi cikin Kuma ta haihu,tazama uwa ta zama mahaifiyar babynta har abada.

Rintse idanuwanta tayi ahankali tareda sauke numfashi da ajiyar zuciya Mai sanyi ta Bude idanuwanta daidai lokacin da ta iso gaban Zeenah wadda itama ta zubawa benazir din da babynta idanuwa tanajin hawaye na ciko idanuwanta da tsananin son babyn harma da benazir din da tausayinsu na rashin jigonsu Bilal.

Cikin nutsuwa benazir ta miqa mata babyn bayan sun gaisa kowannensu cikin sanyi.

Hannuwan Zeenah har rawa suke gurin karban Babyn tana amsarta ta rungumeta a hankali tsawon mintina biyu kafin ta Kwantar da ita cinyarta tana kallan fuskarta da babu Abinda ta baro na kamannin kaantes saima sake a girma zatafi yin kama dasu din.

Ahankali ta dago ta Kalli benazir da kanta ke qasa tana kasa kallan Zeenah sbd kunyar qaryat Datake dabaibaiye da ita.

Cikin kulawa Zeenah tace

“Yaya babyn lafiyanta kalau right?
Kema duk Kuna lafiya Amma ko??

Gyada Kai benazir din tayi tana cewa

“Eh alhmdllh”

Ababa na ganin Hakan ya fita yana cewa hande ya biyosa sbd Ababa Zeenah din Daman ganin babyn da kyau.

Suna ficewa Zeenah ta Kalli babyn hawaye na gangaro mata na rashin dadyn yarinyar
ahankali itama benazir nata hawayen suka gangaro na rashin tata yar uwar Amma ba Daman nuna ma tanada yar uwa sumayyah kaman yanda Ababa ya a fada har abada saidai tayi kukan kewanta cikin ranta badai a fili ba.

Ganin hawayen benazir yasa Zeenah kasa riqe kukanta cikin tausayin benazir datai rashin Bilal din itama sai ta ringa rarrashinta sbd kukan benazir da yayi karfi a hankali.

Sun jima a palon su kadai daga Kuka Zeenah ta gabatar mata da kanta tareda Bata tabbacin duka familynsu suna tsananin son babyn kaman yanda suke son Dan uwansu dasuka rasa Bilal.

Hotunan da zata Kaiwa Umme Zeenah ta dauki babyn kafin ta bawa benazir kayan data kawowa babyn kafin su karbeta ta dawo hannunsu.

Zeenah kaman kada ta tafi tabar babyn taji Amma haka ta daure ta tafi tana zuwa gida takaiwa ummensu hotunan wainda suka saka hankalin Umme sake tashi akan sai ankarba babyn Bilal din tadawo hannunsu kokuma kawai tabar kaantes din su koma gidan DD ta Reni jikarta acan.

Wannan Kalmar tata da tashin hankalin datai harma da hoton babyn yasaka dad kaante da ubangayya DD Jin buqatan dawowar ‘yar hannunsu cikin gaggawa shi Kansa dd babban baisan Yana son ‘yar ba Saida yaga hotonta abin tausayi kayan jikinta ma masu tsananin arha da rashin nauyi ne da zai saka sanyi shigarta ya illatata da wuri.

Washe gari Ababa Yanata Kai kawo tsakanin gida da waje Yana lissafin yaushe Kaantes zasu nemesa sai kwatsam ga Kiran Abbakar akan dd babba na nemansa.

Bai tsaya batawa Kansa lokaci ba ya nufi KAANTES din sbd zuwa lokacin ya matsu ayi me yiyiwa kafin DD kaante ya tattara ya koma inda ya fito lissafinsa ya Kuma watsewa a Karo na biyu.

Yana Isa kaantes Kai tsaye yanzu an tantancesa Yana zuwa ake barinsa shiga Dan haka shida Abbakar palon dd babba suka nufa Yana zaune Shima Yana jiransu.

Gaida dd babba yayi tareda dad kaante dake palon Shima kafin ya zauna a natse Dan Jin meye dalilin nemansa.

Numfashi dd babba ya sauke kafin ya dago ya Kalli Ababa cikin nuna manyanta yace

“Malam Ababa maganar jaririyar dake hannunku ce mun Yanke shawarar karbanta tin yanzu sbd a dauke muku nauyi dama duk Wani Barnar sunan da kuke gudu mu zamu ji da komai ba zaa San ‘yarka ta taba haihuwa ba inshallah.”

Numfashi Shima Ababa ya sauke Mai sauti kafin ya dago ya Kalli dd babba Bai tsaya kwana kwana ba Shima yace

“Ni yanzu na aminta na yarda sunan nawa Dana ‘yata ya lalace kowa zai San ta haihu ba aure ya sani Amma bazan taba raba ‘ya da uwa ba,
Yarinyar Nan tazo duniya a ranar da mahaifinta yabar duniya sannan Kuma a rabata da mahaifiyarta?
Harma da tinanin bazata San mahaifiyar tata har abada ba??
Daukan haqqin wannan marainiyar jaririyar ‘yar zaiyi yawa,

Nayi alqawarin barinta tareda uwarta tinda ta rasa ubanta inshallah zuwa gaba uwarta zata samu mijin dazai aureta da ‘yarta Dan Allah ya rufa musu asiri,
Maganar asan waye mahaifinta har sunanku ya Baci nayi muku alqawarin bama zamu taba bari tasan waye mahaifinta bare danginsa har sunanku ya Baci Dan haka daga yau na hakura zan dauki bacin sunan Amma abarni da jikata zata samu gurin agolanci Mai kyau inshallah.

Da gaskiyarsa yake maganar Yana bayyanarda qunci da damuwarsa akan zancen Dan haka take gabaki Daya palon ya dauki tsit.

Dd babba da dad kaante shiru sukai sbd har ga Allah zancensa da ya shigesu yayi magana Mai maanar da zaa duba idan har zaa yiwa marainiyar jinjirar adalci batareda sun duba sunansu sun cutatar da itaba.

DD kuwa daya shigo alokacin maganar agolancin da Ababa yafada tafi sokan zuciyarsa,
Idan har Yana Raye har abada ‘yar Bilal bazata taba agolanci gidan kowa ba.

Ababa miqewa yayi Bai Jira Mai zasu fada ba yace

“Insha Allah gobe zamu bar garin gabaki Daya zamu koma asalin mu acan kauye zamu samun kwanciyar hankali da rufin asirin renanta ba maganganu Dan haka idan Kuna buqatan ganinta ko so Daya ne zaku iya zuwa kafin mu wuce nagode sosai Allah ya saka muku da Alkhairi Yakuma ji qan Alh Bilal ya masa rahama.

kofa ya nufa Kai tsaye zuciyarsa na tsallen Allah yasa maganarsa ta Doki inda yakeso ta doka.

Dad kaante da Dawood ne suka Bude baki a tare suka ce

“Zamu karbeta har uwar idan tayi wayon shekaru biyu uwar ta dawo gida tayi auren……

Katsesu yayi ta hanyar juyowa ya katsesu da cewa

“Aa ni ‘yata yanzu zan mata aure bazata zo renan shekaru biyu ba ta qarasa lalata sauran rayuwarta,
Kuyi hakuri mu tafiyar mu ka…….

“ZAN DAURA MATA AURE DA QANIN BILAL IDAN HAR HAKAN ZAI SAKA KA BADA ITA DA BABYN”..

Kalmomin dd babba kenan dasuka saka Ababa dauke wuta Yana juyowa Wani haqayin farin ciki da firgita na fita daga Kansa da kunnuwansa.

Dad kaante kuwa ajiyar zuciya ya sauke Bai shirya sbd shock duk da kusan Shima Abinda ya shirya fada kenan.
##MAMUH#
#DD KAANTE
#BENAZIR
#BABY AMNAH
#MARRIAGE/LOVE/HOT HOT
#ROMANCE
#ZAFIN KAI/ZAFIN KAI

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Leave a Reply

Back to top button