Furar 2Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 18

Sponsored Links

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣

 

………*_CANADA_*

Sosai Lulu ta riga ta sakama ranta tsoron haihuwar ne, duk yanda su Usman suka so ta haihu da kanta hakan na neman gagara. Ga naƙudar tata da gani mai zafi ce, dan tayi wujiga-wujiga a ƙanƙanin lokaci. Tun ma tana hawayen har idanun sun bushe, Ummita dai nata maimaita mata addu’a tana faɗa. Har ALLAH ya isa sai da tama Smart cikin fitar hayyaci😜, akace kuma sai anyi Shari’a da shi yayi jail😂. Abin yaso bama Usman dariya ya dai danne da ƙyar. Dr Lameer yaja Usman gefe cikin damuwa ya ke faɗin, “Ussy inaga fa muyi mata CS ɗin nan kawai, ta riga ta saka tsoro a ranta ga shi kuma jinjirin yayi girma da yawa sosai saboda ciye-ciye data dingayi. Sannan an taɓa taɓa cikin hakan ya raunana mata mahaifa. Amma da ace bata saka tsoro a ranta ba wannan bakomai bane zata iya haihuwa da kanta. Yanzu kam ina tsoron kar wahala tasa mu rasa abinda ke cikinta”.
“No no Doctor bana fatan a rasa babyn nan wlhy, inaga kawai ayi mata cs ɗin”.
“Shike nan babu damuwa, wazai saka hannu a cikinku?”.
“Bara na saka hannun kawai ni”.

Alhamdullah an samu nasarar zaro baby boy a jikin Lulu ƙamshi. Lafiyayyen yaro ƙyaƙyƙyawa da bai baro komai na ubansa ba, ga shi ƙaton gaske masha ALLAH. Dan hatta wani tawadan ALLAH da Smart ke da shi a gefen kunnensa babba shima jinjiri na da shi. Ankai Lulu ɗakin hutu, yayinda Ummita ta rungume yaro tana mai jin ƙaunarsa a ranta kamar jininta. Shi kansa Usman yaron ya shigar masa rai. Bai kira Alh. Sulaiman da ke can yana jiran ace Lulu ta haihuwa ɗa a ruɓe ba, dan yau shine target ɗinsa akan kuɓutar da su Lulun dama. Shi yay duk wani tsare-tsarensa na nemawa Lulu transper da taimakon Dr Lameer zuwa wani ɓoyayyen ƙaramin asibiti a Derby city. A wannan daren aka fita da Lulu cikin ambulance da Ummita, abinka da turai tsaro kaca-kaca hankalinsu kwance suka iso Derby city zuwa gabannin asubahi. Sanin Alh. Sulaiman zai iya bibiyarsu komai ya tafi ne akan tsari da kulawa. Dan wani gida ne a kusa da asibitin aka ajiyesu, acan gefen gari wajen ana noman fruits, sai gidan abinci da ke gaba kaɗan kasancewar babban hanya ce, sannan bature shi babu ruwansa da daji duk inda yay masa alƙarya ce. Komai da Lulu zata iya buƙata na kulawar lafiyarta su Usman ya tanada a gidan, dan bashi da damar barin ƙasar da su a yanzu kasancewar passport nasu na hannun tsule, fita dasu kai tsaye zai zama mai wahala.
Kusan ƙarfe takwas Lulu ta dawo hayyacinta, inda cikin amincin ALLAH ta farka bakinta ɗauke da addu’a. Da sauri Ummita da ke zaune a gefenta rungume da jariri dake ta barcinsa tai saurin kallonta da faɗin, “Alhamdullah aunty kin farka?”. Idanu kawai Lulun ta zuba mata ita da jaririn, sai kuma ta sauke numfashi a hankali da motsa lips ɗin ta tana mai bin ɗakin da kallo. “Ina ne nan Ummita? Miya faru da ni?”. Cike da farin ciki Ummita ta ce, “Aunty an miki C’S ne ga baby boy mun samu, nan kuma sabon wajene da Usman ya kuɓuto damu da ga hannun kawunki.” Lulu batace komai ba sai idanu data zubama jaririn hannun Ummitan, da sauri Ummita ta miƙe zuwa gabanta da jaririn, Lulu ta zuba masa ido zuciyarta na wani irin harbawa na masifa. Dan duk da yaron da sauran ɗanyantakarsa ta kasancewa jinjiri kamaninsa da mahaifinsa a bayyane suke. A hankali ta lumshe idanunta tana sakin wasu irin ajiyar zuciya a jajjere, sai kawai ta samu kanta da sakin kuka. Hankalin Ummita ya tashi, ta shiga jera mata tambayoyi akan ko wani waje na mata ciwo ne? Bata iya bata amsa ba har su Usman suka shigo, Dr Lameer ya dubata yayinda Usman ke faman lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta, insha ALLAH sun kuɓuta kenan, zai kumayi duk yanda zai yi na ganin sun koma gida Nigeria. Ummita ita ta bada shawaran ya kamata ama jaririn huɗuba fa, dan haka suka tambayeta wane suna take so a saka masa. Ita kanta batama san lokacin da ta furta, *_“ALIYU”_* ba. Usman da ya saki wani ɗan murmushi ya ɗauki jinjirin yaymasa huɗuba da suna ALIYU HYDAR ZAKIN FAMA. tare da masa addu’a dan duk lalacewar Usman yanada iliminsa na addini. Kawai zama a waje ne ya sashi zama mara jin magana.
Lulu da idonta ke a lumshe a zuciyarta ta furta (ALLAH ya albarkaci rayuwarka *_Aliyu Aliyu Mika’il Mawashi_*) sai kuma ta ɗan yamitse fuska kamar wadda take jin hakan banbarakwai a zuciyarta…

_(To muma dai munce ALLAH ya raya Aliyu Aliyu Mika’il Mawashi. Dangin Smart kar ace bamuyi Barka ba🥱🚴)_
*_NIGERIA_*

Sosai Daddy ke fama da ciwo a tsaitsaye, sai dai yanata dauriyar ganin bai bari ko Mommy ta fahimta ba. Sai dai ya gagara ɓoye damuwarsa akan halin da suke ciki tsakaninsa da ɗan uwansa Yousuf. Yousuf nada matuƙar muhimmanci a garesa ta yanda baki bazai iya furtawa ba. Su fa kaɗaine ƴan uwansa shi da Mommy sai zuri’ar da suka tare a yanzu. Tunda yake da ɗan uwansa bayan rikicin Kasancewar Mawaddat (Maman Lulu) a rayuwarsu baya jin akwai wani saɓani daya taɓa shiga a tsakaninsu kamar haka da Yousuf ɗin ya ɗauki zafi da shi. Ba wai baya son fitowa ya faɗa masa gaskiyar al’amari bane, bai son tada masa da hankaline kawai ko sakashi a matsala. Shiyyasa ya zaɓi shanyewa shi kaɗai a tsahon rayuwa. Amma yana gani a wannan gaɓar in har yana son ɗan uwan nasa ya fahimcesa dolene ya buɗe masa sirrin nan dai da yake ta faman biznewa a tsahon shekaru badan tsoro ba sai don dalilai guda biyu. Na farko baya son tarwatsa farin cikin family ɗin mutum mai mutunci da daraja a rayuwarsa irin Alhaji Sufi Ado Garko. Ya taka rawar gani a rayuwarsa da har a yanzu ake iya kallonsa a nuna a matsayin wane. Duk da yasan wannan rubutaccene daga UBANGIJI ko babu shi ɗin komai zai iya tabbata. Amma UBANGIJI ya sakashi zama matsayin sila. Idan ya kasance mai tarwatsa farin cikin wannan ahali yana jin kamar ya rama sharri ne da alkairi. Na biyu shine kare rayuwar yarinyarsa duk da yasan shi bai isa hana komai ba daga ƙaddarar ALLAH. Tunda gashi nan a sanadin hakan har Lulun ta faɗa shaye-shaye batare da ya iya bata kariya akan hakan ba. Hasalima bai taɓa sanin tanayi ba sai a shekarar nan. Tun daga ranar jikinsa yay sanyi matuƙa da sake tabbatar da wayo ko dabara bata kare maka abu sai UBANGIJIN talikai masanin sirrin fili da ɓoye. A hankali ya kai hannu ya ɗauke ƙananun hawayen da suka ciko masa idanu. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da ɗaukar wayarsa ya rubuta gajeren text message wa Uncle Yousuf ya tura masa, duk da yasan a gajiye yake dan jiya ya dawo daga UK kamar yanda yake ji a bakin Mommy dan shi dai Uncle Yousuf ɗin bai sanar masa ba sam.

Uncle Yousuf na tsakiyar iyalinsa suna kallo, yayinda Deen da Ra’is ke home work text ɗin Daddy ya shigo masa. Kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka ya duba ganin kallon da aunty Saliha tai masa. Shiru yay yana kallon text ɗin da bai wuce layi biyu da rabi ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya dan shima harga ALLAH yana azabtuwa da rashin ɗan uwan nasa a kwanakin nan. Dauriya kawai yake yi. Tunda ya san kansa bai taɓa wayar gari da yini harda kwana baiyi waya da yayan nasa da yakema kallon kamar mahaifi ba. Dan ko baya ƙasar sukan yi waya sama da sau uku a rana. Dan ƙa’idarsa ce duk safiya ko suna a ƙasa ɗaya ko basa nan zai gaishesa, sannan da dare kafin ya kwanta zai kirasa yay masa sai da safe. Idan ma bai kira ba bisa wani uziri na yau da gobe shi daddyn zai kirashi da kansa. Bayan wannan wayoyin biyu na ƙa’ida wasu wayoyin kan shiga a tsakaninsu game da Business ko wani muhimmin abu da ya shafesu. Jin zuciyarsa ta kasa nutsuwa waje guda ya miƙe yana kallon aunty Saliha. “Sweetheart ɗan bani key Please”. Da mamaki ta ce, “Key kuma?. Ina zakaje kaiko a daren nan kamar wanda ke a tarkon mace?”. Karan farko yay murmushin da bai niyya ba. Dan tun a kallon da tai masa sanda text ɗin ya shigo yasan akwai magana a bakinta. Komai baice ba sai wayar da ya miƙa mata. Dan tsakanin shi matarsa akwai yarda mai ƙarfi da fahimtar juna. Duk inda ƙofar zargi ta nema buɗe musu sukan yi saurin tosheta kafin a samu ɓaraka. Cikin sanyin jiki ta miƙa masa wayar da faɗin, “I’m sorry dan ALLAH, ALLAH ya bashi lafiya”. Murmushin kwantar da hankali ya mata da nuna mata hanya alamar taje ta ɗakko masa. Babu jimawa kuwa sai gata ta dawo. Ta miƙa masa tare da ɗan rungumesa. Bayanta ya ɗan bubbuga yana faɗin, “Thanks” daga haka ya saketa ya fice yanama su Deen bye bye.

Duk da dariyar dake tasoma Daddy ganin yanda Uncle Yousuf ɗin yazo a ƙanƙanin lokaci yay ƙoƙarin danneta. Sai ma sake langaɓewa da yay. Cikin sassarfa da ruɗani Uncle Yousuf ya ƙarasa garesa. Sai faman jera masa tambayoyi yake a jajjere. “Yaya mike damunka? Dama baka da lafiya? Tun yaushe kake a kwance? Kasha magani? Miyasa baka kirani munje asibiti ba?”. Cikin murmushi Daddy ya kamo hanunsa dai-dai yana kaiwa zaune kusa da shi a bakin gadon nasa. “Irin wannan tambayoyi haka a jere auta wanne zan amsa a ciki?”. Kai Uncle Yousuf ya langaɓe gefe kamar mai shirin fasa kuka, dan da gaske yaga yayan nasa ya rame masa a idanunsa sosai. Daddy ya sake sakin murmushi tare da lumshe idanunsa. Sai kuma ya yunƙura da niyyar tashi. Da sauri Uncle Yousuf ɗin ya taimaka masa ya zauna da ƙyau. Shima sai ya zauna gab da shi sosai hannayensu cikin na juna. Cikin tausasa murya Daddy yace, “Kana fushi dani saboda ɗiyarka ko? Kayi haƙuri Yousuf kaji. Yayanka ba son zuciya bace ta lulluɓe masa ido. Idan ma a kwaita to ajizancine kawai irin na ɗan adam. In sha ALLAH yau zan fiddaka a cikin duhu tun daga lokacin da kuka fara tuhumata kai da Kareema har zuwa yau ɗin nan. Amma dan ALLAH ina son kai min ƙyaƙyƙyawar fahimta kaji.”
“Insha ALLAH Yaya”. Uncle Yousuf ya faɗa a sanyaye…….✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

Leave a Reply

Back to top button