TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 25

Sponsored Links

 

 

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI
,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

 Ki daure ki biya ba
tare da shiga hakkin wasu ba yar uwa zaki karu na karu har wasuma su karu damu.

    Eh Dije ina son
jin kudin mota zuwa can ne don naji idan nisa ko yawan kudin mota ya hana
mahaifina zuwa ya dubani har wanan lokacin na kuma san shin yana raye ya watsar
dani haka na zama mara gata a cikin garin mutane ko wani dalili zai ban nayin
hakan dani.

   Amadi meye damuwan
ka ga hakan yanzu don ibrahim ya tafi ya barmu da kai hakan ya hanaka rayuwane
a duniya ba komai yasa yai muna hakan ba sai kawai don muki yarda da bukatanshi
na rafiya da mahaifiyanka can kasar tasu.

       Yanzu Dije da
kuka hanashi tafiya da inna a wancan lokacin yau ina innan take ?

   Amadi auren ta da
dan gida yafi muna kwanciyan hankali don ko banza dai munajin labarinta ai jefi
jefi kuma nan da can din inda take zamu iya yinshi a cikjn wuni daya mu isa
gareta.

   Humm Dije ke nan
yana fadin hakan ya girgiza kai kawai ya juya ya nufi dan dakin da yake kwana a
cikinsa ya turo kofan bayan ya shiga da karfi ta tsaya tana kallon kofan dakin
dake makwabtaka da kofan gidansu.

   Magana ta farayi
ita kadai a bakin murhun da take aiki abinda kowa ya gujewa yarinyar nan ke nan
tunfarko da auren bako.

   Amma dan uwan
ubanta ya tsaya ya kafe cewa tunda shi din musulmine da uwan mu kuma tana so
yana so gara kawai a hadasu ai matar mutum kabarisane.

    Yau me gari ya
waya a hakan da yake mayaudarine yaso cuta bai tashi cewa zai koma gida ba
gaban iyayyen shi saida yaga sun samu rabo a tsakanin su ya bijirowa mutane da
zancen barin gari.

   Ina zan yarda ya
tafi min da ya wani uwar duniya can me nisa da kowa ka tambaya yace ma bai taba
zuwa ba yana dai jin sunan garin a bakin mutanene kawaishi.

   Wama ya sani ko shi
din wani halin banza ke gareshi dama ya baro gida yazo nan ko kuma ya dauketa
yaje ya sayar irin haka anyi sunfi goma muna ji a jakkar mogori ana fada.

   Har dije ta rarage
aikin nata bata bar wanan jininin da takeyi ba ita kadai a tsakar gidan nata
kamar tababa sai yankan fada takeyi.

   Yan dabbobinta na
gefe tsaye sunyi shiru suna kallonta kamar mutane suna  saurarenta dan ko motsi basayi a lokacin sai
gidan da yayi tsit lokaci guda.

     Kwana hudu ke nan da sallah amma gidan namu
babu dadin zama ga iyayyen mu don haka fitama a lokacin baida dadi ga kowa dama
can ni din ba ma,abociyar yin hakan bane.

   Dan dama lokacin da
muka dawo sabo sabo garin muna dasawa da mama a lokacin idan na dawo daga
school naci abinci zandan je part din ta mu danyi hira da ita.

  Sai na fahinci yin
hakan wani hanyane da mama din kanyi amfani dashi wurin zolayana taji wani abu
game da ummah na saina daina yawan shigan har haka yazo ya faru yanzu.

   Don yanzu saidai
idan mun hadu zan gaida ita kota amsa min ko kuma ta kyaleni saidai hakan baisa
na fasa gaida ita din ba .

   Wanka nayi na
shirya don tun ranan sallah da nayi kwalliyan sallah din ban kara saka sabbin
tufafina da ummah ta tura kudi har Abuja aka dinko min su ba ina kwance ina
fama da dogayen riguna irin na shan iskan zaman gida.

   Abba ma dukda suna
garin ban sakashi a idona ba tin ranan da yai min fada din nan tace kuma in
turo mashi Ahmed idan nafita.

   Sai yau da korafin
ummah dake yawan min fada kan rashin zuwa nagaida mutane yasa na shirya tunda
safe na fito dakinta na fara zuwa nagaida ita da kwana.

  Kafin na dago na
fita zuwa part din mama da nayi sa,a tana falo zaune da yaranta yanayin su
kawai zaka kalla kasan wani abu mai muhinmanci suke tataunawa a tsakaninsu.

   Dagani fitowan dole
tayi lokacin zuwa falon nata ta zauna tana saye da hijjab mai ruwan makuba har
kasa suma yaran da hijjaban su sun dunkule sama
kujera.

   Nayi sallama a kofa
suka kalloni na karaso har inda mama din take zaune na dan rage tsawo na gaida
ita ta amsa a cikin irin izzanta na manyan mata.

  Tare da fadin yau an
tuna da gaisuwan ke nan ko dan kuya ya kamani nace kiyi hakkuri mama kwana biyu
ina daki bana jin dadine sosai.

  Na juya wirin yan
uwana da suka kyaleni nace ina kwanan ku lafiya kawai suka amsa min dashi suna
kawar dakai ga kallona lokaci guda.

   Na juya zan fita
muryan mamane ya dakatar dani tana fadin Zahra kuna dai ganin irin cin fuskan
da mahaifin ku ke muna a gidan nan yanzu don yayi sabon aure ko ?

   Mamah Aisha ta fada
daga inda take zaune tana jan tsuki ta kawar da kanta gefe daya ta nuna bata so
uwar ta fito min da zancen ba a lokacin .

    Dan dawowa nayi
ina fadin mama kuyi hakkuri ku barshi kome yayi shida Allah don Abba ba yaro
bane yasan abinda ya kamata da wanda bai kamata ba.

   Ita kuma idan tazo
maku da wata manufane donta musguna maku kanta hakan zai koma watarana don
Allah bai yafe hakkin wani kan wani.

    Shiru tayi nasan
don diyanta da suka nuna basu so tafito min da zancen ba wanda ni kuma nasan
damuwa ne ya saka mama yin wanan zancen dani a ranan .

   Na dan tsaya nayi
jim don narasa abinda zan fada bayan hakan don ban saba irin maganganun nan
tsakanina da ummah na ba yasa naji abin bambarakwai sai wanan amsan Allah yaban
ikon in bata a lokacin.

 Allah ya sauwaka na
fada naja kafata zan fita koda ban waigo na dubaba nasan cewa tsukin Aishace
mama waida wanan banzan zakiyi wanan maganan kome ?

    Ni dai na fice na
basu wuri dakin mommy na nufa yana rufe na kwankwasa sai wanan matarce a ciki
muka gaisa take fada min cewa tana part din Abban mu na nufi can din don mu
gaisa dasu da kwana.

    Suna zaune suna
karyawa a dining nayi sallama suka amsa min na shigo suka kalloni nakai gurfane
Abba na fara gayarwa sai ita saidai Abban tunda ya amsa min bai kara kallon
inda nake ba sai ita ke fadin.

   Dama kina gidan nan
na daina ganin ki ko part din ku na shiga nadan murmusa kadan tare da fadin ina
nan mommy yanzu na fito part dinki akace kina nan.

   Daughter ke nan ko
fushi kikeyi da kowa a gidan a, a nace da sauri lokaci guda don tsoron Abba
dake wurin kuma banso ta furta hakan ba gareni.

    Yaushe zakuyi
hutune nace nan da one month in sha Allah OK zan turo a daukeki zuwa Abuja daga
can zamu tafi buki gidan mu autan mu zaiyi aure.

   Kallon Abba nayi da
sauri don sanin ba zai yarda da hakan ba shima sai ta juya tana fadin Alh kaji
na rokawa daughter tare da ita zamuyi wanan tafiyan idan lokaci yayi.

   Ba ruwana da zancen
ta yanzu tunda bata jin magana ta a yanzu har zahra ce zata fara soyayya da
wanan yaron da baida asali baida sana,an yi takamaimai ko wani jigo mai karfi
don kawai ta bata min sunan iyalina a gari gaba daya kallon Abban mukayi lokaci
guda.

   Idona ne ya kawo
hawaye lokaci guda don jin abinda Abba ya fada game dani din sai naji tace daga
inda take zaune ina wanan zancen anyishi ya wuce ko, Alh bai kamata kana kara
tayar da zancen ba a yanzu kuma.

  Ya juyo da kyau yana
fuskantana tare da min kallon ido da ido yafara fadin kuma ki sani duk na kara
jin cewa kin kara kula wanan yaron nan saina saba maki a gidan nan  .

   Kasa nayi da kaina
kafin na iya budan baki da kyar ina fadin kayi hakkuri Abba niba soyayya nakeyi
dashi ba dama muna mutuncine dashi kawai a makaranta don taimakona da yayi
ranan da kowa ya gudu a wurina da ciwona ya tashi sai ya kawo min taimako tun
wanan ranan muke gaisuwan mutuci dashi.

   A zatona kamar
jikin Abba din ne yayi sanyi a lokacin amma sai naji yace koma meye na fada
maki bana son in kara ganin kuna hurda dashi
again don yaron bakma kwanta min a raina ba.

   Jeki daughter
zamuyi maganan dake daga baya zan shigo part din ku in sameki hjy karima din ta
fada da sauri na mike zuwa waje kafin nakai part din mu kukan da nake rikewa
yaki tsaya min dole da kuka na shigo part din namu.

    Kallona umma da
kannena da sukai cirko cirko suna min kallon mamaki dakina na nufa ban tsaya
gun ummah ba don nasan hakan kara min wani laifin zaiyi kuma.

   Gado na fada na
fara kuka ina hadiyan zuciya kafin can na mike zuwa bandaki na wanko fuskana na
dawo na kara hayewa saman gadon na zauna ina faman tunanen abubuwa da dama a
zuciyana.

  Kofa aka turo
azatona ummace  ta shigo dakin don ban
dago kai na duba wanda ke shigowa dakin ba lokacin muryan Tani naji a kaina
tana fadin .

   Haba uwar dakina
meyayi zafi haka zaki kulle kanki a daki kina kuka haka kome yayi zafi
hakkurine maganin shi kibi umurnin iyayye a zauna lafiya yadda suke son .

  Don jayayya dasu
baida amfani wani lokacin don abinda babba ya hango yaro baya hango hakan don
haka shawaran da zan baki shine kibi umurninsu a yanzu kiyi yadda suka amince
maki dayi sai komai ya wuce a tsakanin ku.

   Yanzu share hawayen
ki barin kawo maki abin karyawa ki karya saiki sake jiki ki nuna komai ya wuce
a wurin ki koma kamar kowa a gidan nan.

    Don kinsan dama
hakan akeso aga kin samu matsala da mahaufin ki shine farin cikin wasu gidan
nan ki nuna masu cewa ke din mai tarbiyace da bin umurnin iyayyenki.

    Maza ki mike ki
saki jikin ki kada ki yarda mahaifinki ya wuce da fushin ki a zuciyarki nan zan
kawo maki ko falo zan kai maki abincin naki ?

   Da kyat na iya
budan bakina da yai nauyi lokacin nace a barshi zan fito falo in karya a nan na
fada mata ta juya zata fita nace nagode tace kai ba komai uwardakina ai muna
tare ina bayan ki har kullun don mu hjy tayi muna komai wallahi dolene mugani
ko mu maganta a zancen.

    Ta fita na sauke
ajiyan zuciya ina tunane don a gaskiya ba zance ga dalilin kukana ba saidai
abinda nasani shine yin hakan da Abba yai min a yanzu zai iya jawo min matsala
a karatuna nishi nake ganin dalilin damuwana a lokacin.

     Mikewa nayi daga
zaune din na nufi falo kai tsaye wurin daning na nufa tun kan nakai zaune
kannena suka rufa min da taimakon hiran da suke min har na samu na dan sake .

  A wurin Abban mu ya
sameni zaune muna hira da yan uwana suna ganin shi suka nufeshi suna fadin
yaushe za,a kawo muna keken mu.

    Daga inda nake
zaune nake fadin welcome Abba ya amsa min yake fadawa yaran cewa yau idan na
koma zan sayo maku na aiko maku dashi.

    Hakan yasa na
fahinci cewa a rana  zasu koma ke nan
ashe bedroom din ummah ya nufa yaran suka dare don ba mai shiga idan Abba din
ya shiga nan din.

   Muna zaune tare
dasu suna murna ya dan jima sai gashi ya fito daga dakin a tsakiyan falo ya
tsaya yace maamah zo nan na taso da sauri daga inda nake din zaune nazo na
sameshi tare da dan rage tsayina gareshi .

   Hannuna ya riko ya
dagoni ya fara fadin ki kula da kanki
mamana bana son yawan shiririta ki natsu kiyi karatu yadda ya dace kamar
kowa ni da kaina zan zaba maki abinda ya dace dake in sha Allahu.

    Na amsa da to Abba
na gode in sha Allahu zan kiyayye ka yafe min abinda kake zaton inayi a bayan
ka wallahi Abba hakan ba gaskiya bane.

  Is OK ya fada yasa
hannu a aljihunshi ya ciro kudi masu yawa ya miko min yana fadin ki kula na
fada maki ga wanan ki mayar da hankalin ki sosai abinda baki dashi ki kirani ko
ki fadawa Hjy salma ta fada min.

    Nagode Abba na
fada yace wa kannena suzo suka taho yake binsu yana sallama haka muka rako shi
har kofan part din mu don ya nufi part din mama yasa muka tsaya a nan muna masa
Allah ya tsare.

    Koda muka juyo
zuwa ciki ummah ta fito falo a lokacin nan yaran suka rufeta da fadin Abba ya
bamu kudi ummah tace kun gode ai na  muka
fara mika mata kudin an kawo kaina tace ki rike naki a hannun ki tunda ba
tambayana kudi kikeyi ba.

   Sallaman mommy ce
hjy karima ta shigo da fara,a a fuskanta tasha kwaliya sosai a jikinta tana
fadin to uwargida rangida mu zamuyi maku ta baki fa don Allah a gafarce mu.

    Tare suka shigo da
wanan matar suna sallama ummah din kafin ummah ta kakaro murmushi a fuskanta
tana fadin muma ai ku gafarce mu zaku juya ke nan yau ashe ?

  To ba dole ba tunda
kun hana mu zama  lafiya a nan din kunce
bamuyi daidai ba ai dole mu juya kada azo rayuka suna baci a banza ni wanan
matar da ace garin nan nake zaune tare da ita da mun kwashi yan kallo a
tsakanin mu kullun.

  Mace haka ba tsoron
Allah sam a zuciyarta sai son kai da son zuciya kamar kowa ba mutane bane sai
ita ai bata cika yar sheri ba tunda harta kasa hanashi kara aure takuma zauna
da kishiyoyi aishe bata isa ba ke nan ?

  Murmushi ummah ta
kara sakewa tare da kallon matar da suke tare tana fadin baabba zaku koma ke
nan ashe yaune tafiyan naku ?

   Gashi dan tsaraba
ba a hada maki ba zaki tafi hannu sake babu komai wallahi ko wanan fuskan da
muka samu ai kin bamu komai sai kuma wani lokacin idan Allah ya kaimu.

   Aita hakkuri kiji
yar nan me hakkuri shike da riba wata rana in sha Allahu wata rana sai labari
haka rayuwa take wani lokaci ga bawa mai tawakkali da Allah.

   Nagode baabba ummah
ta fada ta mika hannu ta dauko wani leda da tun shigowan mu yake aje a gefenta
tana fadin hjy karima ga wanan a rikawa baabba ba yawa bamu sanda tafiyan ku ba
yau ban hada mata komai ba.

    Kai haba dai ba
zamu karbi komai naki ba gaskiya haba dai bafa ke nabawa ba baabban mu nabawa
don haka ki bar zancen nan don Allah.

   Gaskiya ni banda
bakin magana don ko hakan ai mun gode da karamcin ki garemu Allah ya kara bamu
hakkurin zama tsohuwar ta amsa da amin.

    Hjy kariman tace
to ni ina skn naje nayiwa wanan sallama bansan da wani ido kuma zata tarbeni ba
a yau don idan tayi min ba kyaleta zanyi ba.

  A,a a rabu a gana
alherine kada ki biyewa wanan aikin zama tare ne hakan don wanan zance ai ba
kyaki zuwa kuyi sallama ba musanman ma ba da zata tafi.

   Ke ke nan kika san
wanan din bari dai din muje sai munyi waya in sha Allahu kuma suka fara tafiya
don barin falon kafin ta juyo tana fadin daughter sai na aiko ke nan ko nidai
nayi murmushi kawai na mike na dan rakasu zuwa fita part din mu dagani har
ummah muka juyo muka dawo.

    Hankalina na mayar
ga tv da ake wani film din yara a cikin sa tani ce ta shigo tana fadin ashe yau
zasu koma shike nan har sun tafi ?

    To meye a ciki
yanzu bagashi sun juya sun tafi tare ba kuma ba a isa a hana hakan ba don
kwanan ni wallahi suyi ta kwana bashine a gabana ba.

 Mazan nan da zaka
mutu a kansu su kasa suma maka su wanan hauka hjy maimuna keyi tace wai bata
yarda don sunzo nan din tare ta amshi girki ba tunda a can tare suke dashi.

   Yanzu kinga ya
barta da kunya kuma girma ya zube kan abinda baikai bai kawo ba an tafi an
barta da bacin rai da takaici ga banza.

    Ta dauka irin kine
ai data saba takawa tana hawa yadda takeso a kullun tani ta fada yoni ina
ruwana da wanan bakin haukan ?

   Hjy ke wake daka ta
taki keda ke barin mutum da wutar shi ta konashi ai zama da irin ku yana da
wuyan sha,ani sosai idan mutum bai gama ganeku ba.

    Ina zaune ina jin
abinda suke fada gaba daya dana tattara sai na gane cewa abinda mama take son
fada min ke nan da safe dana shiga wurinta yaranta suka hanata fada min komai.

  Koma meye matsalansu
ce ta manya hakan don su hakan ya shafa ba zancen mu bane mu yara wanan maganan
tasu.

  Mikewa nayi da niyar
barin falon Tani ta kalleni tace dani uwar dakina komai ya wuce ke nan da
alaman haka ?

   In ma bai wuce ba
ai itabta sani yanzu da muka kyaleta da shirinta ba gashi abin ya koma a kanta
ba an watse a baram baram tsakanin su sheri ai dan aikene dama.

   Nayi mamaki matuka
da wanan zancen har yazamo hakan wani irin abune yaran nan basayi a garin nan
amma saina wanan kawai aka gani a gidan nan har ya zamo min abin fade.

   Yanzun dai ai
intana da hankali tagani ke nan  sai ta
shiga hankalinta idan zata shiga don abin kulin sheri yanzu baida kadan ta dai
rabu da yaron nan shima tunda har Alh ya iya kiranshi yayi mai warning nasan
zai rabu da itane .

   Haba hjy ki rabu da
aikin so yana da wuya ace an rabasu haka farat daya yadda kuke nufi din nan sai
dai ku bisu da addua shine mafita don uwardakina tana da saukin kai sosai don
gashi dan maganan da nayi mata dazun yasa ta sake harta fito yau din waje.

   Kuma fitowan ai ya
zama mata alheri tunda uban ya shigo ya samu ra sake naga aisun shirya kafin su
tafi hakan itama bai mata dadi ba yanzu ?

    Darene gabanin
asubahi lokacin sanyi ya sauko kowa najin dadin sanyin masu ibada a lokacin
suna jin dadin yanayin dije dake kwance tana barci a cikin yanayin da kowa keji
ta fara mafalki.

    Sai dan juyi
takeyi tana dan mutsutsuka kamar yarinya kafin ta mike zubur daga kwancen tana
sakin salati lokaci guda tare da fadin Amadi ?

Leave a Reply

Back to top button