Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 43

Sponsored Links

 

SAKAYAH

 

43

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

Tallah !! Tallah !!

 

Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce  ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* , yau ta sake dawo muku Domin tallata muku Littafin mai Suna ( Rai Daya Jan Zaki)  littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n’a cika Ku da surutu ba  Hausawa sukace Gani yakori ji.

 

Farashin wannan littafin Naira Dari biyar ne 500 kacal  postin biyu a arana  banda ranar Juma’a .

Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.

Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank

Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.

 

Jalaludeen kuwa cikin rauni ya ɗago idanunsa wanda suka zama tamkar garwashin wuta, saboda yanda sukayi ja-jawur yayin da baki ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa kar-kar tamkar wanda aka jona masa Shorking kuka yake mai shiga jiki tare da ratsa zuciyar duk wani mai imani daya saurara.

Da sauri Moddibo ya ƙara sa kusa dashi gefenshi ya zauna cike da matsanancin rauni da kuma famewar mikin dake zuciyarsa na rashin J ɗinsa ya shiga rera wani irin raunataccen kuka tamkar ransa zai fita, kukan wanda bai samu yayi shi ba a lokacin rasuwar, baka jin sautin komai acikin ɗakin, face Shesh-sheƙan kukan su dake cigaba da  wanzuwa aƙalla sun ɗauki kimanin minti goma sha biyar suna kuka batare da wani yayi yunƙurin rarrashin ɗan uwansa ba.

Cikin dauriya da ƙoƙarin son hana kansa kuka kana da shesh-sheƙa Jalaludeen ya ɗago tafin hannunsa mai masifar sanyi tamkar wanda aka ciro acikin dusan ƙanƙara ya manna aƙirjin Moddibo daya ke jiyo bugun zuciyarsa, cikin rauni yace.

“Kayi haƙuri Mouley haƙiƙa munyi rashi mai girma.

Munyi rashi mafi ciwo azuciyarmu. Kayi haƙuri Aliyu kaya femin tsawon lokaci baka ganni ba ina cikin haramine! shiyasa baka ganniba”.

Lumshe idanu Moddibo yayi wasu hawaye masu masifar zafi suka zubo akuncinsa yayin da sanyin tafin hannu Jalaludden ke ratsa zuciyarsa Jalaludden kuwa cikin raunatacciyar murya ya cigaba da faɗin.

“Saboda na shiga inayin I’itiƙafi tsawon lokacin nan shiyasa kuma koda na fito munyi tafiya nida Kakana munje ƙasar Sin shiyasa baka ganni ba bansan Jameelu yashiga wannan hali ba bansan Jameelu ya rasuba Mouley”.

Sai kuma ya fesar da numfashi mai zafi tare da cigaba da faɗin.

“Sai jiya Juma’a ne naje Taraba domin kai muku ziyara, kasancewar na daɗe ba muyi magana ba yasa na shirya muku Surprised sai dai kawai ku ganni, toh ina isa gidan innayi na nufa, naje gidan Innayi na samu babu kowa sai na wuce gidan Ummi”.

Kallonsa kawai Moddibo keyi hawaye na cigaba da silala daga idanunsa.

 

Cikin rauni Jalaludden yace.

“Acan na samu Innayi suna hiran. Jameel ya rasu kuma na tsinkayi cewa kana ƙasar Morocco, nazo ƙasar Morocco na bibiyi al’amarin ka har na gane cewa kana cikin Fadar Rabat!”.

Kuka ne yaci karfinsa cikin kuka kamar ƙaramin yaro ya cigaba da cewa.

“Mouley munyi rashi.

Jameel ya tafi ya barmu  Allah yajiƙan Jameel Allah yayi mishi rahma!”.

 

Cikin sanyin murya Moddibo yace.

“Amin Ya Allah. Amman nayi mamaki rashin jinka Jalaladdeen ina ka shiga, tsawon lokaci ba ɗuriyarka. Na shiga matsanancin damuwa Jameel ɗina ya ɓace tsawon lokaci, bamu sameshi ba.

Naso ace kana kusa damu kayi mana amfani fiye da amfanin da kayi mana abaya ka faɗa mana inda J.yake”.

Kai Jalaludden ya girgiza still hawaye na kwaranya daga idanunsa ya riƙe hannun Moddibo kana yace.

“Bana kusa Aliyu, sannan kuma koda ina kusa muma kanmu jinnu. Ubangiji bai sanar damu gaibu ba Aliyu,

da ace Allah ya sanar damu ilimin gaibu ko a inda nake zan iya sani da zan faɗa maka, amma Allah bai sanar damu gaibu ba.

Sanin gaibu sai Allah kaɗai bansan haka zai faru da Jameel ba.”

Numfashi Moddibo ya fesar kana ya dafe goshinsa da hannunsa na dama tare da faɗin.

“Tabbas munyi rashi mafi girma ban taɓa sanin ya ɗaci da zafin mutuwa yake azahiri ba har sai da na rasa J ɗina, mutuwar J mutuwa ce da bazan taɓa mancewa ba. Sannan bazan daina jin zafi da raɗaɗinsa ba har sai ranar dana koma ga Ubangiji na!”.

Kai Jalaludden ya gyaɗa kana yace.

“Sosai ma kuwa Aliyu, amman haƙuri zamuyi, domin babu abinda Jameel yafi buƙata agaremu yanzu face addu’a addu’ar mu”.

Kai Moddibo ya jinjina tare da cewa.

“Zan cigaba da yiwa J ɗina addu’ar samun rahamar ubangiji har zuwa numfashina na ƙarshe”.

Haka suka kwana suka yini suna hira.

 

Washe gari da safe koda Sarki Youseef Mouley da Didi suka shiga wajen Moddibo suna tare da Jalaludden sai dai su basu da ikon ganinsa kasancewar bai bayyana musu kansa ba,

ko Moddibo ba ma asiffar mutum yazo masa wanda sukayi karatu dashi.

Bayan fitansu ya kalli Moddibo yace.

“Kana kama da Mahaifinka”.

Da mamaki Moddibo ke kallonsa kafin ahankali yace.

“Mahaifina ko?”.

Kai Jalaludden ya gyaɗa Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

“Eh Mahaifinka mana, shin ban taɓa faɗa maka cewa kai ba ɗan Nigeria bane, har kaita dariya kana tambayata to kai ɗan ina bane?”.

Kai Moddibo ya jinjina tuni lokacin suna Jami’atul Madina bayan sun fito daga darasi suna shan shayi Jalaludden ke sanar masa.

Still da murmushi afuskarsa ya cigaba da faɗin.

“Har kace min kai ɗan ina ne nace kai ɗan Morocco ne,  kace ba haka bane.

Amma ni nasan hakane saboda nayi bincike ne akan Innayinka na kuma fahimci haka”.

Zazzafan ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe cikin tsira masa idanu yace.

“Kenan kana nufin nan ƙasatace?”.

Murmushi Jalaludden yayi ta gyaɗa masa kai kana yace.

“Sosai ma kuwa ƙasar kane, tsatsonkane, Mahaifarkane. Wa’annan kuma Mahaifanka ne”.

Cikin girmamawa lamuran Ubangji mabuwayi gagara misali Moddibo yace.

“Ya Salam shin taya akayi wanna al’amarin yakasance ya akayi abin ya faru a haka, abin ne yazo min tamkar amafarkaina na yau da kullum”.

Gyara zama Jalaludden yayi tare da faɗin.

“Kada kayi mamaki,Ka cire al’ajabi da mamaki acikin lamarin Ubangji ya wuce mamaki. Kai dai kawai kayi godiya ga Allah”.

Ahankali Moddibo ya motsa laɓɓansayace.

“Alhamdulillah Allah kulli halin”.

 

Kai Jalaludden ya jinjina haka suka cigaba da hira kafin daga bisani Jalaludden ya kalli Moddibo da murmushi afuskarsa yace.

“Sannan kuma akwai al’amarin da naje na samu ranan juma’a ya kasance amma bazan faɗa maka ba sai ka ganin da idonka”.

Ware idanu Moddibo yayi kana ya langwaɓar da kai tare da cewa.

“Jalaluddeen nawa dan Allah ka faɗa min mana”.

Ƴar dariya Jalaludden yayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoransa yace.

“Ok naje na samu Ummi ta shiga damuwa sosai akan tsawon kwana uku kenan tana kiran wayar ka amma bai shiga har Abban Jameel yazo da kanshi dan Maganar dana samu suna tattaunawa da Innayi kenan”.

Lumshe idanu Moddibo yayi yasan dole hakan zai kasance rashin jinsa awaya zai ɗaga musu hankali musamman Innayi da Ummi shima Abba sai dai kawai yayi dauriyar maza.

 

Da murmushi Jalaludden ya cigaba da cewa.

“Ya faɗawa Innayi shima ya kira wayarka baya shiga tsawon kwana uku kenan, amma kuma Innayi sai dariya take tana ce musu kada su damu kawai afara shirin kawo maka”…

Sai kuma yayi shiru tare da yin mgnar zuci. Alhamdulillah gwara da ban faɗa masa ba saboda naji suna faɗin cewa Moddibo bai san anyi masa Aure ba..

 

Ɗan ware idanu Moddibo yace.

“Ana shirin kawo min me?”.

Buɗe hannu Jalaludden yayi kana yace.

“Kai dai ana shiri kawai abinda naji sun faɗa kenan”.

Langwaɓar da kai Moddibo yayi cikin Muryansa mai cike da sanyi yace.

“Kai dai Jalaludden baza ka faɗa min ba kawai”.

Kai Jalaludden ya girgiza kana yace.

“Um-um iya abinda naji kenan, kasan na faɗa maka bansan gaibu ba Allah ne kaɗai mafi sanin gaibu”.

Kai Moddibo ya jinjina cikin gamsuwa da maganarsa yace.

“Toh shikenan”.

 

Washe gari Litinin ya kama kwanan Moddibo biyar kenan acikin Masarautar Mouley.

Misalin ƙarfe tara na safe Moddibo ne zaune acikin tangamemen Falon kamar yanda ya saba ko yaushe yaji an buɗe ƙofar falon anutse ya ɗaga kyawawan idanunsa tare da kallon ƙofar.

Idanunsa suka sauƙa akan.

Didi da Sarki Youseef Mouley sai wani kyakykyawan Matashi mai masifar kama dashi kallo ɗaya ya masa ya fahimci shine Ibraahim ƙaninsa ne da Didi ke yawan bashi labarinsa duba da kamannin dake tsakanin su. Sai kuma Lalla Khadijah da Lalla Hafsat, sai ƴar auta Rahama.

Ibraahim kuwa yalwataccen murmushi ya sakar masa domin shi yakasance mutum ne mai fara’a da son Mutane kana da abin dariya

 

Suna haɗa ido da Moddibo ya ƙara fara’ar fuskarsa kana ya tafi cikin sassarfa ya rungumeshi yana mai jin farin ciki da nutsuwa agaba ɗaya ilahirin jikinsa cike da shauƙi ya ɗago kansa kana yace.

“Yaya zance maka? Ko kuma Usaini? ko kuma Hassan ɗina?”.

Moddibo kuwa lokaci ɗaya ya tsinci kansa da ƙaunar yaron aransa rungumesa yayi kana cikin ɗan sakin fuska yace.

“Koma me ka kirani dashi zan amsa”.

Sai kuma suka sake rungume juna yayin da ƙaunar junansu ke ratsa ko wani lungu da saƙon dake jikinsu…

Cikin tsanananin so da ƙauna Lalla Khadijah tace.

“Kai Ibraahim ka sakeshi haka mana”.

Kalla Hafsat dake ruggume da ɗiyarta ce tayi dariya tare da zama tana kiciniyar bawa baby nono, tace.

“Ai dai kam ya maƙaleshi kamar ya fimu sonshi”.

Didi da Abualeey kam kallonsu kawai suke cike da jin daɗi mata misaltawa.

Rahama kuwa cikin tura baki ta harari Ibrahim cikin yanayin tsamar saƙo-da saƙo tace.

“Ai shi haka yake ga yadda ya maƙaleshi kamar shine auta”.

Cikin jin daɗi Abualeey yace.

“Toh mu zauna dai kafin ai ta yiwa Ibraahim ƙorafi”.

Shiko Ibraahim signal yayiwa Rahama tare da cewa.

“Ai shi nawane ni kaɗai ba dama cewa kike nine bani da ɗan uwaba toh Allah ya dawo min da ƴaƴana dama yafi Yayunki kyau”.

Lalla Khadijah ce ta ɗan zuggure ƙayarsa.

Ɗan tsalle yayi tare da

ɗago kansa ya kallin Moddibo kana yace.

“Kaga abinda suke minko ko Yah Aleey”.

Murmushi Modibbo yayi tare da ɗan janye jikinshi gefe yana mai kallonsu ɗaya bayan ɗaya yakejin sonsu da ƙaunarsu na ratsa mishi zuciya.

Shi kuwa Ibraahim baki ya ɗan tura tare da cewa.

“Kayi haƙuri ɗan uwana”.

 

“A kan me?”. Modibbo ya jefa mishi tambayar.

da sauri yace.

“Sabida rashin dawowata da wuri, sabida ranar da kazo ranar na tafi Turkiyya dan daga nan muke kai musu dabino, toh nike wakiltan lamarin, koda Lalla Hafsat ta gaya min ji nayi kamar inyi fiffige in dawo gashi naga dan ban dawo da wuriba kamar kafi sonsu a kaina”.

Dariya sukayi baki daya.

Sai kuma duk suka tsagaita tare da zubawa Modibbo ido ganin yadda yake dariya tare da shafa kan Ibraahim dan ganinshi yake kamar Bashir.

Didi kuwa da su Kalla Hafsat murmushi dukeyi ganin yadda ya jawo Ibraahim ya ruggumeshi yana mai cewa.

“Waya ce maka nafi sonsu, suda zasu koma gidajensu su barmu tare”.

Cikin dariya yayi musu gwala.

Rahama kuwa ɗan rawa tayi tare da faɗin.

“Ni dai muna tare”.

Shi kuwa Ibraahim

juyowa ya kalli Didi da Abualeey tare da cewa.

“Dan Allah Didi ku aurar da ita ta bar mana gida mu sake”.

Baki ta tura tare da cewa.

“Ba ruwanka da ni”.

 

Didin kuwa fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallin ƴaƴan nata dake zaune reras agabanta kana tace.

“Alhamadullah Allah na gode maka da ka cika min farin cikin ahlina”.

Kai Abualeey ya jinjina tare da faɗin.

“Masha Allah”.

Ibraahim kuwa

janye hannunsa dake cikin na Modibbo yayi kana ya juya tare da kallon Alƙibla yayi Sujudur Shukur.

Kana ya ɗago tare da komawa gefen Moddibo ya zauna still fuskarsa ɗauke da ƙayateccen murmushi ya kalli Sarki Youseef Mouley tare da faɗin.

“Abualeey Addu’ar mu ta karɓu Ubangiji ya dawo mana da Yah Aliyu alokacin da bamuyi zato ba sannan ba muyi tsammani ba sai nake ji kamar gaba ɗaya burikana na duniya aka gama cika min dan ganin ɗan Uwana kuma gudan jina”.

Kai Sarki Youseef Mouley ya gyaɗa kana yace.

“Tabbas kuwa domin babu abinda ya gagari Ubangji Allah da kansa yace mu roƙeshu zai amsa mana. Domin shi addu’a ba’a gaggawa dashi”.

Moddibo kuwa cike da tsananin so da ƙaunarsu dake ratsa ko wani magudanan jinin jikinsa yace.

“Tabbas kuɗin kun kasance min. Garkuwa ne atare dani ina jin ajikina babu abinda zanyi face godiya ga Allah daya haɗani daku kafin na koma garesa”.

Haka suka cigaba da hira tsawon lokaci ganin suna shirin tafiya yasa Moddibo ya sunkuyar da kansa ƙasa kana yace.

“Ayyah Abba dan Allah Ina bukatar wayoyina akawo min su”.

Murmushi Sarki Youseef Mouley yayi kana yace.

“Kada ka damu za’a kawo maka wayoyinka dan suna hannu na”.

Cikin sauri da mamaki Moddibo ya kallesa tare da faɗin.

“Abba toh a taimaka min dasu Ummi, Innayi, da Abba zasu nemini, musamman ma Innayina zata shiga damuwar rashin jina?”.

Kai Sarki Youseef Mouley ya girgiza kana yace.

“Kada ka damu In sha Allah babu komai rashin ɗaukar wayar yana da muhimmanci, da amfanin da zaiyi Kankane yace kada a ɗauki wayar shiyasa ma ban kawo maka ba”.

A ladabce Moddibo yace

“Abba zasu shiga damuwa saboda zasuji tsoro kada abinda ya faru da Jameel nima ya faru dani”.

Cike da kulawa Sarki Youseef Mouley yace.

“Wanene Jameelun naka?”.

Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa kana yace.

“Ai wannan Dr Jameel ɗin dana biyo, da fari ina bibiyarshi a zatona J nane sabida tsananin kamar da sukayi”.

Nan ya shiga basu labarin Jameel da duk abinda ya faru dashi.

Ya ɗaura da faɗin.

“Shiyasa lokacin da naga wannan Dr Jameel baki ɗaya na ɗauka cewa Jameelu na ne saboda kamanninsu yayi yawa, hatta maganarsu, tafiyarsu, muryar su babu abinda ya raba su sai dai ɗabi’unsu ya samu bambanci dana Jameelu na”.

Cikin raunin murya da tunowa da Jameelunsa ya basu cikekken tarihin abotarsu.

Sosai suma suka tausayawa masa tare da yiwa Jameelun fatan samun rahamar Ubangji kana ya cigaba da faɗa musu cewa aikine ya kawo sa kamfanin Baban Jameelu.

Cikin fesar da numfashi Ibraahim yace.

“Allah sarki Yah Jameel Allah ya gafarta masa”.

Cikin sanyi Moddibo yace

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

Lalla Khadijah ce ta gyara zama tare da fuskatarsa kana a mutunci tace.

“Da fari dai kaga iya mu yamune cikin mahaifiyarmu da wasu daga cikin amintattun fadane, suka san da isowarka wacce dole labarin ya bazu cikin Faɗa, to Alhamdulillah zan haɗa taro na musamman damon gabatarda kai a tsakiyar family’nka wato zuriyar sarki Aliyu Mouley, wanda zuriyace ta tun kakannin Abbanmu da kuma kakanninmu, mu da kuma iyayenmu da ƴan bappanayenmu dama goggoninmu, in Sha Allah zayi tarone na musamman dan dan haka ka shirya fuskatarta idanu mabanmanta. Alhamdulillah na gamsu da nitsuwarka zuwa yau kuma na fahimci kasan komai na tsarin al’adunmu da nake mamakin yadda akayi ka sansu”.

Da sauri Kalla Hafsat tace.

“Ke kuwa Lalla Khadijah ya za’ayi ya rayu da jakadiya kiyi tunanin akwai wata al’adar da bazai saniba”.

Murmushi Modibbo yayi domin shi dai innayi bata taɓa alaƙantashi da labarin fadaba, sai dai yasan komai na fadar ne a cikin mafarkansa.

Abualeey ne ya gyara zama tare da cewa.

“Zuwa yanzu mun gama shiryawa komai na taron”.

Haka dai sukaci gaba da tattauna lamurran.

 

Washe gari ranan Asabar misalin ƙarfe uku na yamma Jirginsu Innayi yayi landing a _Rabat Sale international airport_.

 

Suna sauƙa a airport motocine na alfarma guda biyar suka zo ɗaukar su bisa jagoranci Dr Ahmad abokin Abban Jameel.

Mota ta farko Dr Ahmad ke driving yayin da Abban Jameel ke gefensa daga can baya kuma Innayi ce tare da Hajja Nana da kuma Khausar.

Motar dake bima sa kuwa Ummi ce da Hajiya Bunayya sai kuma ƙanwar Momyn Khausar Aunty Hajara, sai Haiydar da yake gaba gefen direba.

Yayin da mota ta uku kuwa Asiya, Asma’u ce tare da Dija. Sai Aunty Ruƙayya ƙawar Mommy

Motar dake bayansa kuwa Baffa Jimeta ne da matarsa Hajiya Umma, kana da Babbar Ƴar sa mai suna Aunty Hawwa .

Yayin da motocin ke tafiya ajere cikin nutsuwa bisa Jagoranci Dr Ahmad

Bayan sun shiga cikin gari sun nufi unguwar Ben slimane, cikin sauƙe numfashi Innayi ta fesar da numfashi tare da buɗe Idanunta ta kalli cikin garin da tsarukan da kuma gine-gine suka sauya alamar garin ya sake samun cigaba fiye da da.

Cikin sanyayyar murya me cike da kewa da kuma bege ta kalli Dr Ahmad dake driving kana tace.

“Mubi ta unguwar El’gara sai mu ɓullo ta cikin Ben Ahmad dan Masarautar Rabat zamu nufa”

Cikin wani amintacciyar murmushi Abban Jameel ya juya ya kalleta kana yace.

“Kai tsaye kuma?”.

Kai ta jinjina kana tace.

“Eh can zamu nufa shine abinda yafi da cewa”

Still Idanunsa na kanta yace.

“Amma da ya kamata mu fara isa masauƙi mu huta tukunna!”.

Numfashi ta fesar tare da faɗin.

“A’a ai acan ya dace muyi hutun”.

Kai ya jinjina tare da faɗin.

“Toh shikenan”.

Shi kuwa Dr Ahmad juya akalar motar yayi, kana suma saura suma mara mishi baya.

Nan suka ci-gaba da tafiya cikin nutsuwa still motocinsu na jere.

 

Suna isa ƙofan Gate na farkon Masarautar Rabat ganin motoci ajere yasa cikin Sauri Hadiman dake bakin gate ɗin mutum biyar suka miƙe biyu suka tsa gefen damar motan biyu gefen hagun motar kana ɗaya ya tsaya agaba.

Cikin nutsuwa da yanayin jikin girma Innayi ta sanya hannu ta buɗe murfin motar kana ta fito yayin hannunta ke riƙe da wani abu kamar murfi kolbar Vaselin sai dai bisa ga alamu ginannene kana anyi sa da hatimin Masarautar.

Wanda ke kusa da ita ta miƙawa.

Karɓa yayi ya duba kana yayi saurin kallon fuskarta sai kuma ya juya ya miƙawa na gefensa shima ya karɓa ya duba.

Da wani irin sauri suka ɗaura hannunsu asaman ƙirjinsu kana suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa.

Kai ta jinjina musu.

Kana cikin sassarfa suka juya tare da buɗe musu Gate ɗaya daga cikinsu ya tsaya abakin Gate yayin da sauran huɗun suka marawa moticin baya cikin sassarfa suna isa Gate na biyu ɗaya daga cikin masu binsu yayi saurin buɗe musu Gate ɗin suka shiga kai tsaye har harabar fadar suka isa,  suna isa sukayi Parking atare.

 

Acan motarsu Hajiya  Bunayya kuwa Haiydar  wani irin zazzafan ajiyar zuciya ta sauƙe mai nuni da zallan mamaki kana ta kalli gabas da yamma kudu da Arewa wani irin daular duniya da suka shiga wanda ya kamata akirasa da Aljannar duniya cike da al’ajabi ta maida idanunta kan Ummi kana tace.

“Toh nan kuma ina muka zo haka”.

Lallausan murmushi Ummi ta sakar mata kana tace.

“Nan gidansu Moddibo muka zo gidan Mahaifinsa”.

Dariyar sheƙiyanci Hajiya Bunayya ta saki tace.

“Kai lallai wannan ta tsuniya yawa ne dashi nan ɗin ne gidansu Moddibo?”.

Kai Ummi ta jinjina tare da faɗin.

“Toh ki zuba ido ki gani”.

Baki ta taɓe tare da yiwa Ummi wani kallo kana tace.

“Caɓ amma Ummin Jameel banyi zaton haka daga gareki ba da girmanki”.

Ta ida maganar tare da ƙyalƙyalewa da dariya ita baki ɗaya ma maganar dariya yake bata yo ai ko amafarki Moddibo bai isa ya kasance jinin wannan ahali ba mutumin da ake kyautata zaton ɗan shegene.

Ummi kuwa da mamaki ta kalli yanda take dariya kana tace.

“Kina mamaki ne?”.

Hajiya Bunayya kuwa cikin taɓe baki tace.

“Sosai ma kuwa ai ba mamaki ba harda Al’ajabi na haɗa Moddibo fa”.

Sai ta kuma fashewa da dariyar sheƙiyanci data tuna wai Ummi tace nan gidansu Moddibo ne.

Kai kawai Ummi ta girgiza batare da tace Uffan ba tana mai bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo.

 

Acan Motarsu Asma’u kuwa cikin zumuɗi da ganin tsantsan kyawu da tsaruwan gidan Dija tace.

“Ehyeh”.

Asiya ma kallon coumpund ɗin tayi cike da shauƙi tace.

“Wowwww Masha Allah kaga wani daular duniya”.

Asma’u kuwa dogon numfashi taja tare da fesar wa tare da faɗin.

“Toh Masha Allah wannan al’amari da ban mamaki yake”.

Motocin kuwa re ras suka tsaya.

Fadawan dake tsaye bakin Fadar kuwa cikin sauri suka nufo motocin wanda aƙalla sun kai biyar isowarsu yayi dai-dai da fitowar Innayi daga motar.

Sarkin ƙofane idanunsa suka sauƙa akanta cikin sauri ya mutsi-stika Idanunsa kana ya sake kallonta sama da ƙasa cikin al’ajabi da mamaki tu’ajubi yace.

“Innare Jakadiyar Gimbiya Ruƙayya?”.

Murmushi Innayi tayi kana ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.

“Eh”.

Duk da yawan shekaru kuwa sun gane juna

Cikin wani irin sauri ya juya tare da nufar cikin Fada yana shiga ya durƙusa agaban Sarki duk da cewa yana tare da mutane na hannun damansa suna tattauna akan al’amarin Moddibo da yanda zasu bayyanar dashi a Masarauta ga yan uwansa.

Ganin yanda ya gurfana ne yasa Sarkin zagi cewa.

“Hattara dai Sarkin Ƙofa, mene tafe da kai?”.

Cikin rawan murya tare da tsantsan farin ciki yace.

“Al’amarine mai girmane yake tafe dani”.

Duk idanu mutanen Fadan suka zuba masa ganin yanda fuskarsa ke ɗauke da tarin zumuɗin isar da labarin.

Sarkin Fada kuwa cike da kulawa yace.

“Shin wannan wani al’amari ne?”.

Aƙage Sarkin ƙofa ya sake risinar da kansa kana yace.

“Ina so abani izini ne nayiwa Innare Tsohuwar Jakadiyar Gimbiya Ruƙayya iso wacce ta ɓace tare da Alieeyu tsawon shekara talatin”.

Wani irin murmushi Sarki Youseef Mouley ya saki mai cike da zallan farin ciki da jin daɗi acikin ransa yace.

Alhamdulillah ta amsa kiranmu kenan lallai wannan ya nuna ta riƙe mana ɗanmu da amana da aminci bata kuma wofintar da al’amuran sa ba tana bibiye dashi, yanzu tsawon kwanaki biyar bataji labarinsane ta bibiyi al’amarin sa gashi ta nufo nan ne kuma da yaƙinin cewa tabbas daya shigo ƙasar nan zai dawo Mahaifarsa.

Afili kuma murmushi ya sakarwa Sarkin Ƙofa kana cike da nutsuwa da kamala kana da ƙasaita irin na sarauta ya masa alama da hannu ta shigo…

 

Cikin sauri Sarkin Ƙofa ya miƙe kana ya fita kallin Innayi dake tsaye jikin mota yayi tare da faɗin.

“Bismillah”.

Innayi kuwa juyawa tayi tare da kallon su Abban Jameel kana tace.

“Ku ɗan yi haƙuri ina zuwa”.

Su kuwa baki ɗaya cike da ɗumbin mamaki suke kallonta.

Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyaɗa kai tare da cewa.

“Toh mu dai munfi karfin saiduwa, koda an kawo mu nan da za’a sayar damu ne bazamu saiduba”.

Sai kuma ta juya ta kalli Khausar dake zaune gefenta wacce idanunta suka kumbura sukayi ja jawur gashin idanu suka jiƙe yayin da suka ƙara tsayi kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar tasha kuka tamkar mai isarta cikin taɓe baki tace.

“Toh kuma kukan me kikayi tunda, ai burinki ya cika, ba dai auren wanda ba’asa asalinsa ba, ai gashi dai kinga kuma wata duniyar da aka kawo mu, ko mai za’a ce mana ko mai za’a mana kuma oho domin wannan al’amari dai yafi kama da almara”.

KhausarMouleey ya jinjina tare da faɗin.

“Ai nan Fada ce mai mutunci da karrama baƙo”.

Sake sunkuyar da kanta tayi kana tace.

“Ranka ya daɗe baƙin suna da yawa”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Koda ace baƙi ɗaya Yan yanki da kuke kika ɗebo ba zasu rasa muhalli acikin wannan Masarautar tamu ba”.

Lallausan murmushi ta saki tare da jinjina kai kana tace.

“Toh abani jagora wanda zai kai mu masauƙin baƙin namu.

Kai ya jinjina kana yace.

“Toh shikenan babu damuwa”.

Kallon Jakadiyar sa yayi tare da faɗin.

“Jakadiya Bismillah akai su sashen Yamma a saman za’a sauƙi”.

Bi’ana saman inda Modibbo yake kenan

Sake sunkuyar da kai Innayi tayi tare da faɗin.

“Ranka ya daɗe Akwai maza tare kuma damu mata”.

“Baki da matsala”.

Ya faɗa tare da kallon Sarkin Ƙofa kana yace.

“Kai kuma ka kai Mazan Ƙofan Gabas”.

Kai ya gyaɗa cike da girmamawa yace.

“Toh”.

Kana suka fice yayin da Jakadiya ta yiwa Innayi, Hajja Nana, Ummi, Hajiya Bunayya, Asma’u, Asiya, Dija, Khausar, Aunty Hawwa  da Hajja Umma Baki daya bayan Jakadiya suka bi tayi musu Jagora.

Yayin da Abban Jameel, Baffa Jimeta, Lamiɗo, Haiydar suka bi bayan Sarkin ƙofa wani babban Hanya suka bi kana suka hau Upstairs

Suna haura wa saiga wasu Ƙofofi biyu ɗaya aɓarin dama ɗaya aɓarin hagu Jakadiya takai su Innayi ƙofar dama yayin da Su Abban Jameel aka kaisu ƙofan hagu ta can gefen yamma wanda bata cikin falon da Modibbo yakeba suka ɓula ba sai dai in zadu sauƙo in sunbi ta ƙofar tsaki ta cikin falon zasu bulla…

 

Jakadiya kuwa tana fita daga masauƙin su Innayi kai tsaye ɗakin Didi ta nufa tana shiga falon ta zube agaban Didi tare da faɗin.

“Albishir”.

Fuska ɗauke da murmushi Didi tace.

“Goro”.

Sake risinar da kai Jakadiya tayi kana tace.

“Fari ko Ja?”.

Still Didi na murmushi tace.

“Faro soll Dan ƙwalele”.

Washe baki Jakadiya tayi tare da cewa.

“Toh Innare na cikin Fadar Masarautar Mouley ta iso tare da al’umma baki, daga cikinsu akwai masu tarin kamala da Alkunya kana tazo mana da kyakykyawan furanni masu haska gida”.

Didi kuwa cikin matsanancin farin ciki da jin daɗi ta miƙe kana tace.

“Masha Allah Alhamdulillah ta ina take, muje ki kaini gareta”.

Kai Jakadiya ta girgiza cike da ladabi tace.

“Amma da kiyi haƙuri ki koma ki zauna yanzu dai, farko a fara Marabtansu da abubuwan motsa baki saboda sun ɗebo hanya sannan asanar da hadimai afara yi musu girki na musamman domin maraba”.

Cike da gamsuwa Didi ta jinjina kai kana ta kalli Hadimanta dake durƙushe ƙasa tace.

“Maza kuje ɓangaren Hadiman dake Kichen kuce maza ashirya abinci na alfarma yanzu”.

Cike da ladabi suka amsa kana suka fita.

Didi kuwa cikin wani irin farin ciki da annashuwa kana da jinjina girma da mutuntaka irin na Innayi ta kalli Jakadiya tare da faɗin.

“Maza ashirya musu drinks, Fruits, Snack’s,da ɗan gashshen nama sannan akwai nono mai sanyi da kwakwa ahaɗa musu”.

Ta ƙare mgnar tare da kallon Lalla Khadijah sai kuma tace.

“Khadija keda Hafsat ku jagoranci aikin”.

Kai suka jinjina kana atake suka haɗa suka kai sashen su Innayi da kuma sashen su Abban Jameel…

 

Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa tunda tashiga tangamemen Falon da yaji komai na more rayuwa take kallon komai cikin ƙunan zuciya mamaki da kuma tarin takaici….

Innayi kuwa suna zama ta kamo hannun Khausar  da har zuwa lokacin take shesh-sheƙan kuka kana ta riƙo Asma’u yayin da Ummi ke biye dasu suka nufi ɗaya daga cikin ɗakin da yake  3bedrooms ne.

Ƙofar da shine na tsakiya suka shiga.

Suna shiga ta saki sassayyan numfashi tare da sakin hannun Khausar sai kuma ta zaunar da ita gefen gadon kana ta juya ta fita.

Fitanta yayi daidai da shigowar Hadimai mata suka shigo da Fruits suka ajiye cike da girmamawa suka gaishesu kana suka ce…

Gimbiya tace ayi muku sannu da zuwa sannan ga abubuwan motsa baki kuci kafin ta iso.

Godiya sukayi kana sukuma suka fice ba daɗewa suka sake dawo wasu hannunsu riƙe da drinks,wasu Snack’s wasu dambun dabbi da soyayyu.

Yayin da Lalla Khadijah da Lalla Hafsat ke riƙe da wasu Bowls manya da yaji Kindirmo da kwakwa da ayaba suka ajiye.

Cikin tsura musu ido Innayi ta kalli Lalla Khadijah kana ta juyo ta kalli Lalla Hafsat.

Sai kuma ta saki murmushi gani sun ruggumeta cikin bege da kewarsu Innayi tace.

“Allah mai iko da buwaya Khadijah kune kuka girma haka”.

Sai kuma ta kalli Lalla Hafsat dake faɗin.

“Innayi ashe dai rai kanga rai, baki wani canza ba”.

Cikin mamaki dai Hajja Nana Hajia Bunayyah da dukkan su suka zuba masu ido.

Gaisawa sukayi bayan sun zauna.

Cikin kula  Lalla Khadijah tace.

“Hafsat muje ko, mu barsu susha ruwa”.

Kai Hafsat ta gyaɗa kana suka juya suka tafi hadimansu na taka musu.

 

Kana acan ɓangaren su Lamiɗo suma haka aka kai musu.

Cikin sauƙe numfashi Baffa Jimeta ya kalli Abban Jameel bayan fitar Hadiman kana yace.

“Toh Alh Bashir wannan al’amari dai da ban mamaki da kuma ɗaure kai yake toh shi wannan yaro na rasa tantance inda al’amarinsa ya nufa”.

Murmushi Abban Jameel  kana ya yace.

“Nan shine gidansu Modibbo kamar yadda kakarsa ta labarta min shi ɗan wannan ahlin ne, gidansu ne kuma tsatso kuma jigo sannan kuma tushen sa mahaifarsa kenan”.

Kai Baffa Jimeta ya gyaɗa cike da gamsuwa yace.

“Ikon Allah wannan al’ajabi da yawa yake,ita kuma daga wannan ƙasa ta tashi ta koma Nigeria har Lungunmun can taje ta zauna dashi.

wannan wani irin al’amari ne yasa ta ficewa daga nan ta koma can”.

Zazzafan ajiyar zuciya Abban Jameel ya sauƙe kana ya gyara zamansa tare da cewa.

“Al’amarine mai girma mai kuma ban mamaki”.

 

Numfashi Lamiɗo ya fesar wanda tunda aka fara magana bai ce komai ba ya muskuta kana yace.

“Ai wato sha’ani  Masarauta sai ahankali idan bakayi Sa’a ba sai a saubata maka rayuwa! A banza”.

Abban Jameel na taunar Inabi yace.

“Hakanne ma yaso kasancewa shiyasa ta gudu da Moddibo domin tseratar da rayuwarsa”.

Baffa Jimeta na kurɓan drinks Mai sanyi yace.

“Allah mai iko”.

Daga nan kuma sai suka rufe maganar tare da cin kayan maƙulashen da aka kawo musu bayan sun gamane Dr Ahmad da sauran masu jan motocin suka sakkamesu suka tafi.

 

Ɗaya daga cikin Hadiman dake sashin ne ya shigo cike da ladabi ya kallesu kana yace.

“Ga banɗaki sannan ga ɗakuna akwai duk wani abin buƙata da zaku buƙace”.

Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.

“Mumgode”

Daga haka ya juya ya fice.

 

Bayan awa ɗaya, sun ci sun sha Hajiya Bunayya ta kalli Hajja Nana dake goge baki da Tissue tace.

“Wannan al’amari dai da ɗure kai yake”.

Cikin taɓe baki Hajja Nana tace.

“Toh Ni dai fatana dai Allah yasa basayar damu akazo yi ba ehee”.

Dariya mai sauti Innayi ta sanya ganin yanda Hajja ke magana tsakaninta da Allah cike da kamala tace.

“Babu Sai dawa sai karramawa wanda gadon mune, kuma ma in banda abinki a saidaku a nemi me, ki dai dubafa duk wata ɓukata da ɗan Adam yake dashi muna dashi a masarautarmu”.

Ummi kam murmushi kawai take, dan talura Hajja Nana da innayi har yanzu ba’a shiryaba.

 

Suna cikin haka sukaji sallama, tare da ganin jagorancin Hadiman Didi

Cike da zaƙuwa ta tashigo tare da Jakadiyar ta da kuma Kakar Moddibo Niyna sai kuma su Rahama bakinsu ɗauke da sallama.

Innayi na ganin Didi tayi saurin miƙewa tare da durƙusawa agabanta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa batare da tace Uffan ba.

Didi kuwa cikin yalwataccen farin ciki ta tsugunna tare da sanya hannunta akafaɗar Innayi kana ta ɗagota ta tsayar da ita suna fuskar juna, sai kuma kawai ta ruggumeta tare da faɗin.

“Kin gama min komai Innayi kiyi min duk kan abinda ɗan Adam zai yiwa abokin zamansa na halacci, daga yau na ƴan taki kin tashi daga Baiwa kin zama ƴa ƴan tacciya kuma Uwa amintacciya kuma kamila kuma cikekkiyar jakadar sarki mai jirangado”.

Dariya mai sauti Innayi ta sanya wanda ke nuni da zallan farin ciki kana tace

“Alhamdulillah Nagode wa Allah ina tahowa zuciyata na tsinkewa ina tunanin shin ya rayuwa ta kasance shin ana raye ko kuma anbar duniya zuciyata ta cika da fargaba”.

Baki ɗaya mutanen falon kallonsu suke cike da tsantsar mamaki musamman Hajiya Bunayya da wani irin zufan hasada ke fita agoshinta.

Innayi kuwa cike da annashuwa ta cigaba da faɗin.

“Amma Alhamdulillah nayi katari da Youseef akan karagar mulki kana kema nayi katarin dake acikin shigar Gimbiyya amma banga Ubangida naba Sarki Muhammad Aliyu Mouley”.

Kai Jakadiya ta girgiza kana tace.

“Allah yayiwa Sarki Muhammad rasuwa yanzu ɗanki ne Youseef akan Mulki”.

Cikin sanyi Innayi tace.

“Allah sarki, Sarki Muhammad Mouleey. Ubangji Allah yajiƙan sa da Rahma”.

Amin suka amsa a tare,

Ita kuwa innayi juyawa tayi tare da kallonsu Hajja Nana da suka zubo musu idanu sai kuma ta maida idanunta kan Didi tace.

“Yanzu dai idan na fahimta Moddibona Aliyuna shine Yariman Masarautar nan? kuma Sarki Mai Jiran gado?”.

Yalwataccen murmushi Didi ta Saki kana tace.

“Tabbas kuwa shine ɗa Namiji babba A masarautar nan kuma ɗa Mai jiran gado Ahamdulillah kuma ya dawo alokacin da Masarauta ke jiranshi”.

Kai Jakadiya ta jinjina kana tace.

“Sosai kam”.

Didi kuwa cike da nutsuwa ta nufi kujeran dake tsakiyarsu kana ta zauna murmushi ta sakar musu da lallausan murmushi tare da faɗin.

“Jaɓɓama Moɗon”.

Ga Mamakinsu sai sukaji tayi musu magana cikin Harshen Fullanci.

Cikin yanayin mamaki Hajja Nana tace.

“Allah bauɗo be Fulfulde voli, kamar da fulatanci kike yi mgn fa ko?”.

Murmushi ta saki kana tace.

“Sosai ma kuwa Asalina Bafulatanar Adamawa ce ni ɗuyace ga Sarkin Joɗah Sheiykh Jabeer”.

Kai Hajja Nana ta jinjina kana tace.

“Ai kuwa lallai gashi Yaren da kike mana dashi ya tabbatar mana da hakan”.

Wani irin zufa mai kamar tafasasshen ruwan zafine ke tsats-tsafowa Hajiya Bunayya abaki ɗaya ilahirin jikinta acikin ranta take mgn kamar zautacciya.

“Toh shin Me hakan yake nufi, kenan haka nufin Khausar tayi katari ta tsinci dami a akala? Ko shegiyar yarinyar da wayo kamar dala, ko dai dama ita tasan Modibbo ɗan manya ne, kaji shegiyar yarinya da iya bada kafa, yoh da na sani ai wlh shi Amina zata aura.

Ashe Samira da abinda ta hanga.”

Gaba ɗaya tayi kasake ta tafi dogon tunanin.

Ƙanwar Mommy Aunty Hajara. cike da farin ciki tace.

“Khausar Lelelwal asheko da gaske Lelelwal ɗince ke”.

Murmushi Aunty Ruƙayya tayi kana tace.

“Tabbas kuwa abu yayi yadda ran masoya ke so.   Dama wani hanin ga Allah Baiwa ce”.

Hira suka cigaba dayi cike da farin ciki da mutunta juna saɓanin Hajiya Bunayya dake cikin tashin hankali da ƙunan zuciya.

 

Acan ɓangaren su Abban Jameel kuwa Sarki Youseef Mouley da Sheik Jabeer ne suka nufi masauƙin su.

Sheikh Lamiɗo na kallon Sheikh Jabeer ya faɗaɗa murmushin fuskarsa cike da kamala yace.

“Allah nhokke sabugo Sarkin Joɗa kana shagaban ƙungiyar TABITAL POOLAKU, da mi yetti Allah da kansa ne a nan?”.

Kai Sheykh Jabeer ya jinjina kana cike da girmamawa yace.

“Ikon Allah Allah yayi mun haɗu kenan?”.

Murmushi Lamido yayi tare da zamewa gefensa dan shi kansa yasan idan ana batun sarauta toh in su Sheiykh Jabeer na kusa shi dole a ƙasa zai zauna.

Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin kamala da kulawa yace.

“Ikon Allah sai kuma muka haɗu anan, amma yanzu dai ku huta in Allah ya kaimu gobe sai muji meke tafe daku?”.

Cikin gamsu Lamido da Abban Jameel sukace to.

Su kuwa daga nan suka fice…

 

Acan ɓangaren su Didi ma Sallama suka yiwa su Innayi tare da faɗin su huta gobe zasu ci gaba da tattaunawa Godiya sukayi musu kana suka fice.

Washe gari da safe misalin ƙarfe 9:00am Innayi, Hajja Nana, Jakadiya Sheikh Jabeer, Sarki Youseef Mouley, Galadima, Waziri,  Didi Abban Jameel, Ummi, Baffa Jimeta Lamiɗo jakadiyarta zaune suke wuri na musamman kuma keɓantaccen palon Abualeey wato sarki Youseef Mouley kenan. yayin da baki daya idanunsu ke kan Innayi.

Innayi kuwa cikin sauƙe numfashi ta cigaba da basu labarin tun randa ta tafi da Modibbo ta wuce Nigeria dashi kana ta nufi Taraba yankin Gembulan sabida sanin yanki fulanine domin Didi na bata labarin, kuma ta iya fulatanci tun a lokacin domin Modibbo shine ɗa na shida a wurin iyayensa daga Khadijah da Hafsat sai da akayi ya’ya uku maza duk basa gama arba’in ake nemansu a rasa sai bayan kwanaki sai a tsinci gawarsu. A wannan lokacin kuma Khadijah da Hafsat sunyi girma da bazasu mance kamannin innayi ba shiyasa sunka ganeta.

Fesar da numfashi innayi tayi kana taci gaba da labarta musu, yanda ta rayu da Moddibo yanda ya taso da yanda yayi karatu, da irin ƙalubalen daya fuskanta, da amintakarsa da Jameel  har zuwa mutuwar M Jameel da kuma dalilin zuwansa Morocco da kuma irin ƙalubale da baƙaƙen magana da kuma hantara da suka samu awajen mutane kana ta ɗora kuma da wasiyyar da M Jameel ya bar musu akan Modibbo, haɗin da basu labarin Khausar da dole in dai za’a bada labarin Modibbo da Jameel toh dole cikaton na uku Khausar ce.

Didi Kam lumshe idanunta tayi wani abin idan taji tayi murmushi wani ta zubda hawaye saboda tausayin halin da ɗan ta yakasance cikin na rashin aminisa da kuma rashin su a kusa dashi da ya zame masa sanadin da ake shegantashi.

Cikin sanyin murya tace.

“Allah sarki ɗana Jameel Allah baiyi zamu ganka ba bare muyi maka godiyar kekkyawar amintakarka da gudan jinin, sai dai Alhamdulillah Innayi tunda Jameel bai mutu da rashin sanin iyayen amininsa, in Sha Allah mukuwa  zamu kasance mashinyi mishi addu’a a tsawon rayuwarmu. Ummin Jameel Ngd MATUƘA Abban Jameel babu abinda zance daku sai addu’a. tabbas Aliyu na kuma yaga jarrabawar rayuwa wanda nasan ya samu darussan rayuwa masu tarin yawa acikinsu  Innayi na gode kinyi min halarcin da bazan taɓa mantawa ba kin tseratar da rayuwar ɗana alokacin da ake neman hallakasa kamar yadda akayi ta hallaka yan uwansa da suka gabata”.

Murmushi Innayi tayi kana tace.

“Wannan yiwa kai ne sannan babu godiya tsakanin mu domin kin cancanci fiye da haka sabida matsayin uwa kika riƙeni ba Hadimarkiba, shiyasa nima nayi miki abinda zan iya yiwa ƴaƴana na cikina”.

Kai Didi ta jinjina tare da juyowa ta kalli Ummin Jameel dake sharce hawaye cikin sanyi tace.

“Ummin Jameel kada kiyi kuka ga Aliyu na in Sha Allah ya ishemu nidake baki ɗaya”.

Cikin gamsuwa  Ummu tace.

“In sha Allah kuwa”.

Innayi kuma gyara zamanta tayi tare da cewa.

“Toh Alhamdulillah bayan ta howarsa  nan.

Muka gama mgnar komai akan Khausar da bai sani ba. toh Alhamdulillah dama acikin labarin dana baku na faɗa muku wasiyyar da amininsa Jameel ya bari toh Alhamdulillah a makkoni biyu da suka gabata an Aura masa Khausar”.

Cikin wani irin Didi ta kalli innayi tare da cewa.

“Aliyun akayiwa aure!”.

Da sauri innayi ta gyaɗa mata kai kana tayi ƙasa da kanta.

Sai kuma innayi tayi saurin ɗago kanta jin Didina faɗin.

“A….!

 

Ba editing kam

 

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number’n nayine, ko kuma a’a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button