Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 31

Sponsored Links

 

SAKAYAH

 

31

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

*Littafin nan dai ba free book bane, na kuɗine ko kin gashi a wasu wuraren da ba Group na da ake biya insa mutum, littafin 1k ne kacal in sha Allah zaki karanta shi daga forko har ƙarshe akan 1k kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki yar uwa*

 

 

 

Sbpndegoo. LamiÉ—o kuwa cikin yanayin, tausayi da jinĆ™ai da Ć™auna mai haÉ—e da taraddadi da tsoro, ya sanya tafin hannunsa na dama ya tallafo, fuskar Ramadan ya juya gefe da gefe  ga mmkinsa gaba É—aya uwayan yaron ya koma lagob-lagob cikin yanayi da kiya da son aro Jarumtaka ya runtse Idanunsa tare da maimaita kalmar Hasbunallahu wani’imal wakil. Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n.

Cikin sauri Hajiya Bunayya dake zaune ta buga hannunta aƙirji tare da kallon Lamiɗo daya zubawa Ramadan ido tace.

“Mai Martaba ya rasu ko?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago ido ya kalleta kai ya girgiza mata batare da yace komai ba.

Da sauri Mommy dake tsaye tayi baya tare da zama da É“as akan kujeran dake bayanta, baki É—aya jikinta ya saki Atake ta fara Maimaita kalmar.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin”,ta faÉ—a hawaye na bin kuncinta Shar-shar.

 

Khausar kuwa juyawa tayi ta kalli Hajiya Bunayya kana ta mayar da kanta kan Mommy da hawaye ke bin kuncinta ahankali ta sake maida kallonta kan LamiÉ—o da yayi shiru yana jan yatsun Ramadan alamar yana dai-dai-tasu.

Cikin wani irin yanayi tace.

“Abba mu tafi dashi asibiti,Abba mu kaisa asibiti”.

Jujjuya kai LamiÉ—o yayi kana yace.

“Khausar ki nutsu”.

Kallon Hajiya Bunayya da Idanunta ke kan Ramadan yayi yace.

“Hajiya Bunayya kama khausar ki zaunar da ita”.

Mommy kam tana zaune akan kushin babu abinda take maimaitawa face kalmar Innalillahi still hawaye na bin kuncinta.

 

Ganin haka yasa Lamiɗo fesar da numfashi kana ya miƙe tare da ɗaukar Ramadan awuyansa ya fice.

Da sauri Khausar ta miƙe tare da bin bayansa  tana cewa.

“Abba inzo mu tafi Asibitin ne!?”.

Tsintsiyar hannunta Hajiya Bunayya ta riƙe tare da gyara zamanta tace.

“Khausar ki nutsu mana ki dawo ki zauna?”.

Kai khausar ta girgiza cikin rawan murya tace.

“Ki sake ni zamu tafi asibiti ne kiga Ramadan fa”.

Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da faÉ—in.

“Ki zauna mana ba kiji Abbanku yace ki zauna ba.

Kai ta gyaÉ—a cikin wani irin yanayi ta koma ta zauna.

 

LamiÉ—o kuwa yana fita kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya shiga bakinsa É—auke da Sallama zaune ya samu Gimbiya Dadu afalon.

Ganinsa Rungume da Ramadan yasa cikin sauri tace.

“Ya dai lafiya Lamiɗo meke faruwa?”.

Cikin sanyin murya yace.

“Ramadan ne fa ki duba min shi”.

Kai ta gyaɗa tare da Matsawa gaban Ramadan dake kwance ƙasan ɗakin yatsunta biyu ta kai saitin hancinsa sannan ta riƙe jijiya hannunsa kallon Lamiɗo tayi cike da mamaki tace.

“Ha’a bashi da rai ai ajikinsa?”.

Araunane LamiÉ—o ya É—ago idanunsa da suka kaÉ—a sukayi jawur jijiyoyin kansa ya tashi cikin raunin murya yace.

“Nima dai kamar haka na gani ahannuna na ya cika kamar babu rai atare da shi.

Jinjina kai Gimbiya Dadu tayi cikin rawan murya tace.

“Tabbas ba Rai atare dashi Ramadan ya rasu fa”.

Ta ida maganar tare da É—ago hannunsa ta juya sangalam duk ta inda ta juya sai ya tafi luuuu zai fadi kana ga bakinsa dake aÉ—an buÉ—e idanua kafe.

 

Ahankali LamiÉ—o ya sunkuyar da kansa akan Ramadan hawaye masu É—umin gaske suka shiga zubo masa asaman kincinsa, suna É—iga kan fuskar Ramadan tal-tal yayinda jinkinsa ya shiga tsuma.

Gimbiya Dadu kuwa bayanta ta jingina da jikin kujeran cikin sanyin murya tace.

“Allah sarki Ramadan ashe dai ciwon kan nan na ɗauka ne? Ciwo lokaci ɗaya!?”.

Akuma dai-dai lokacin Uncle Naseer ya shigo falon ganin yanayin da suke ciki ne yasa ya zauna gefen Gimbiya Dadu tare da cewa.

“A Lafiya meke faruwa?”.

Ahankali Gimbiya Dadu ta É—ago kai tare da Kallonsa tace.

“Wallahi Ramadan ne Allah ya masa rasuwa!”.

Arazane Uncle Naseer ya Kalli Gimbiya Dadu tare da kallon Ramadan dake kwance cikin wani irin yanayi yace.

“Ha’a wani irin magana ne Gimbiya Dadu ya zakice Ramadan ya rasu!? Ko ke Dr ce ya za ayi kice ya rasu taya kika gane hakan?”.

Kallonsa ya mayar kan LamiÉ—o daya zubawa Ramadan ido kana yace.

“Yah Lamiɗo mu kaisa asibiti”.

Kallonsa Lamiɗo yayi tare da Girgiza masa kai still Idanunsa na nan ja jawur ruwan hawaye na kwance acikinsu yayinda jikinsa ke cigaba da tsuma zuciyarsa na harbawa da masifan ƙarfi.

 

Uncle Naseer kuwa hannu yasa a aljihu tare da ciro wayarsa yayi dearling number family Dr su  yana ɗagawa yace dan Allah yazo ya duba yaro agida Dr ya amsa da toh.

Bayan minti 16 minute  Dr yazo bayan ya duba ya tabbatar musu da Ramadan ya rasu kimanin minti talatin da suka wuce.

Sai asannan Uncle Naseer ya yarda kana ya raka Dr ya tafi yana dawowa.

Sashen Gimbiya Dadu ya hadu da LamiÉ—o ya fito da Ramadan Rungume akafaÉ—arsa bayansa yabi LamiÉ—o kuwa kai tsaye Falonsa ya nufa yana shiga ya kwantar da gawar Ramadan Atsakiyar É—akin kana ya cire masa suturar jikinsa É—en oh foÉ—imo.

 

Cikin rauni da tsinkewar zuciya ya nufi ɗakin Mommy a inda yabar Mommy zaune anan ya dawo ya sameta still Idanunta na zubar da hawaye masu zafi da ƙuna a zuciya.

Khausar dake gefenta ta kalleta tare da cewa.

“Mommy Meye faru me yasamu Ramadan?”.

Ahankali Mommy ta janyota jikinta tare da kwantar da ita akan cinyarta kana ta sanya hannunta akanta tana shafawa cikin sanyin murya mai cike da rauni tace.

“Khausar muyi haƙuri Ramadan kam ya tafi ya barmu.

Ubangiji Allah yajiƙan sa Allah ya masa rahma Allah yasa mai cetone”.

Cikin tsananin tashin hankali Khausar ta fashe da matsanancin kuka me tsuma zuciya yayin da ta shiga girgiza kanta kallon Mommy tayi Muryanta na rawa tace.

“Mommy Ramadan kike cewa ya rasu!? Mommy wannan wani irin magana ne!?

Dan Allah Mommy kice mafarki nake Mommy kice ba gaskiya bane!”.

Girgiza kai Mommy tayi still Hawaye na bin fuskarta amma ta gaza furta komai.

 

Cikin sauri Khausar ta toshe bakinta jin wani matsanancin kuka ya taho mata.

Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da ƙarasawa cikin falon ya zauna kusa da Mommy, kasancewar akan 3sitter take.

Cikin sanyi murya yace.

“Khausar kiyi haƙuri kinji ko?”.

Kallonsa tayi da jikaƙƙun Idanunta kana tace.

“Abba da gaske wai Ramadan ya rasu!?”.

Nunfashi Abba ya fesar tare da jinjina mata kai yace.

“Da gaske ne Khausar ya muka iya da hukunci Ubangiji, dama shi ya bamu Ramadan kuma shi ya karɓesa, kiyi haƙuri ki daina kukan nan kinji ko!?”.

Girgiza kai tayi tare da sake fashewa da matsanancin kuka mai gunji.

Dafa kanta LamiÉ—o yayi cike da tausayawa yace.

“Kiyi haƙuri yanzu ma Naseer ya kira Dr yazo ya dubasa sannan ya tabbatar min da cewa ya rasu!”.

Cikin wani irin yanayi mai cike da ruɗu Khausar ta miƙe da gudu tare da shiga Bedroom ɗinta ta faɗa kan gado tare da sakin marayan kuka.

Lamiɗo kuwa bayan ya sake rarrashin Mommy tare da bata haƙuri da kuma nuna mata muhimmanci tawakkali da haƙuri ya mike ya fita.

 

Bayan angama shirya Ramadan an masa wanka an suturtasa yanda addinin Musulunci ya tsara aka kaisa gidansa na gaskiya.

 

Bayan andawo Lamiɗo da ƴan Uwansa da kuma Abokan arziƙi aka zauna zaman Makoki.

Wunin wannan ranan haka Mommy da Khausar suka yini cikin alhini da jimamin rashin Ramadan Hajiya Bunayya kuwa sosai tayi farin ciki sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci mutuwar ta shigeta domin ayanda take nunawa tafi Mommy damuwa wani abin ma Mommy ke tausarta tana bata haƙuri.

Washe gari Khausar ce zaune a ƙasa Mommy na Kan kujera gabansu Kuma kayan Breakfast ne.

Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Khausar tare da cewa.

“Khausar ki matso kici abinci”.

Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Mommy da kumburarrun Idanunta kana cikin sanyin murya tace.

“Mommy ba najin yunwa”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.

“Khausar ki matso kici abinci bana son haka zamuyi fushi da abinda Ubangiji ya jarabcemu da shine Allah daya halicci Ramadan yafimu son sa shi ya bamu Ramadan kuma shi ya ɗauke mana shi!”.

Wasu hawaye masu masifar zafi ne suka zubowa Khausar akuncinta cikin matsanancin kuka tace.

“Mommy shikenan!, Shikenan Ramadan ya tafi baza mu sake Kallonsa ba shikenan mun ransa shi har abada. Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

Kallonta Mommy tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye Akuma dai-dai lokacin wayarta ya É—auki ruri.

Kallon screen É—in wayar tayi nan taga sunan Hajja Nana na yawo.

Cike da ladabi tayi Picking tare da kaiwa kunnenta tace.

“Hajja ina yini?”.

Daga É—aya É“angaren Hajja Nana tace.

“Lafiya lau ina Khausar!?”.

Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Khausar da hawaye ke zuba a Idanunta kana tace.

“Gata nan”,

“Toh ki bata wayar”, cewar Hajja Nana ta.

Kai Mommy ta gyaɗa tare da miƙawa Khausar wayar.

Amsa Khausar tayi cikin Muryan kuka tayi sallama.

Cike da kulawa Hajja Nana tace.

“Ke kuma lafiya ya naji muryanki haka kukan me kike!?”.

Cikin sheshsheƙan kuka Khausar tace.

“Hajja Nana Ramadan ɗin mune ya rasu”.

Hajja Nana kuwa cikin sauri tace.

“Innalillahi Wa’inna Ilahi rajiu’n Ayyah Allah sarki Ubangiji Allah ya jiĆ™ansa da rahma Allah yasa maicetone ai bamu da labari bamu sani ba bawa Mommy naki”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa Mommy wayar.

Jin Mommy ta amshi wayar yasa Hajja Nana cewa.

“Wai ashe Ramadan ya rasu!?”.

Kai Mommy ta gyaÉ—a kana cikin sanyin murya tace.

“Eh Wlh”.

Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauke tare da cewa.

“Ikon Allah Meye sameshi haka?”.

Numfashi Mommy ta fesar tare da gyara zaman ta kana tace.

“Wallahi ciwon kai ne mako ɗaya”.

 

Cikin sanyin murya da tausayawa Hajja Nana tace.

“Allah sarki Allah ya gafarta masa Ubangiji yasa maicetone! Dama yanzu Malam Liman zai shigo Gembulan Insha Allah zan biyo shi muzo”.

Jinjina kai Mommy tayi cikin sanyin murya tace.

“Toh Allah ya kawo ku Lafiya mungode sosai”.

Bayan Mommy ta kashe wayar ta kalli Khausar data zubawa kayan Breakfast Ido Cike da tausayawa ta shiga lallashinta.

 

Acan gidan Ummi kuwa Moddibo ne zaune afalon ya tsurawa waje É—aya Idanu yayin da Ummi kanta ke Ć™asa hawaye  zira-zira baki É—ayan sun zurfafa acikin tunanin da suke Asma’u ta fito daga kitchen cikin mutuwar jiki ta tsugunna kusa da Ummi kana cikin sanyin murya tace.

“Ummi”.

Ahankali Ummi ta É—ago Idanunta dake zubar da hawaye kana cikin sanyin murya tace.

“Na’am”.

Lumshe idanu Asma’u tayi tare da faÉ—in.

“Ummi yanzun nan mukayi waya da Khausar tace in gaisheki”.

Kai Ummi ta gyaÉ—a cikin sanyin murya tace.

“Ina Amsawa”.

Asma’u kuwa cikin raunin murya tace.

“Ummi wai Ramadan ya rasu fa”.

Cikin sauri Ummi ta É—ago kanta dake Ć™asa ta kalli Asma’u shima Moddibo cikin sauri ya kalli Asma’u zuciyarsa na cigaba da  bugawa da masifar Ć™arfi.

 

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe cikin raunin murya tace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n yaushe ya rasu!?”.

Gyara zama Asma’u tayi cikin sanyin murya tace.

“Shekaran jiya fa take cemin randa tazo bayan ta koma ciwon kan ya fara mishi, sunyi ta sintirin asibiti a banza, tace shekaran jiya kuma haka aka kwana dashi haka jiya da Asbah ma ya tashi dashi washe gari da safe bayan sallar Asbah ya rasu sai bayan Azahar akayi jana’izar sa!”.

Girgiza kai Ummi tayi tare da fesar da numfashi kana tace.

“Allah sarki rayuwa Ayyah Aysha ta ɗanɗani Mutuwa mai zafi da raɗaɗi mutuwar ɗa akwai ciwo Allah ya masa rahma Allah yasa maicetone”.

Cikin sanyin murya Asma’u tace.

“Ameen Ummi”.

Jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.

“Insha Allahu zanyi ƙoƙari muje”.

Moddibo kuwa ahankali ya buÉ—e Idanunsa dake lumshe ya kalli Ummi tare da cewa.

“Allah yajiƙan sa da rahma, shine yaron da Mota ya buge ko?”.

Kai Asma’u ta gyada tere da cewa.

“Eh shine”.

Cije lip ɗinsa na ƙasa yayi tare da cewa.

“Allah sarki kwanansa na gaba alokacin Allah ya gafarta masa”.

Cikin sanyi murya Ummi tace.

“Ameen”.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.

“Ummi bari in tashi Inje wajen Abba naji ya ake ciki muji daga Jiya zuwa yau ko sun kira”.

Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh shikenan”.

Cikin sanyin jiki ya miƙe tare da ficewa kai tsaye gidan Abba ya nufa.

Bayan ya isa gidan ya shiga falon Abba nan ya samu Dr Muktar zaune zama gefen Abba yayi bayan sun gaisa Moddibo ya sauƙe numfashi kana cikin sanyin murya yace.

“Abba har yanzu basu kira ba”.

Kai Abba ya gyaÉ—a masa tare da rintse Idanunsa kana yace.

“Basu kira ba Aliyu bansan me mutanen nan suke nufi da muba”.

Tagumi Moddibo da Abba sukayi duk sunyi jugum-jugum dasu.

 

Misalin Ć™arfe biyu da rabi na rana Hajja Nana da Malam Liman suka iso gidan LamiÉ—o bayan sun gama gaishe-gaishe suka zauna har aka Idar da La’asar LamiÉ—o ya shigo tare da kallon Hajja Nana kana yace.

“Hajia ki fito malam Liman yana jiranki”.

Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh gani nan fitowa”.

Kallonta ta mayar kan Mommy dake jan Carbi kana tace.

“Yanzu kam ba abinda zance miki, ta’aziyya muka zo miki amma Insha Allah kwanan nan zan dawo kan batun Khausar”.

Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.

“Toh shikenan Nagode Hajja Nana Allah ya saka da alkhairi”.

 

Miƙewa Khausar tayi tare da bin bayan Hajja Nana jikinta sanye da dogon hijabi har ƙasa yayin da hannunta ke riƙe da wayarta Idanunta sunyi luhu-luhu dasu suna fita coumpund ɗin taga Malam Liman acikin mota amazaunin Driver.

Wara kumburarrun Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.

“Iyeee lallema tsohon nan ashe ka iya mota?”.

Murmushi malam Liman yayi tare da gyada mata kai kana yace.

“Eyyy sosai ma kuwa dama lokacin da kikaje ai mota ta talalace ne shiyasa ankaita wajen gyara to wata aka sake siya min”.

Murmushi tayi kana tace.

“Ashe kunji daɗi ƙauyenku akwai mota”.

Jinjina kai yayi da murmushi afuskarsa yace.

“Hadda ke ai acikin ƙauyen ya zaki cire kanki?”.

murmushi tayi cikin yanayin sanyin tace.

“ai Lallai dai kam to Allah ya tsare muku hanya”.

Ta faÉ—a tare da komawa cikin falon Ummi.

 

Kallon Hajja Nana Malam Liman yayi bayan ya dai-dai-ta motar akan kwalta yace.

“Addah Nana za muje gidan Malam Arɗo wannan ɗaliban nawa”.

Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh ba matsala muje mana”.

Jinina kai Malam Liman.

bayan sun isa gidan malam Arɗo yayi Parking tare da isa falon baƙinsa wanda ke harabar gidan bakinsu ɗauke da Sallama.

Daga ciki malam ArÉ—o wanda ke zaune tare da Moddibo ya amsa tare da basu Izinin shiga.

Bayan angama gaishe-gaishe Malam ArÉ—o yace.

“Lafiya Malam Liman yau ziyarar yamma”.

Cikin jimami Malam Liman yace.

“Wallahi É—an gidan Mai martaba LamiÉ—o ne  ya rasu shine muka zo Ta’aziyya”.

Jinjina kai Malam ArÉ—o yayi tare da faÉ—in.

“Bashakka hakane ai yaron É—alibin mune, wallahi ni lokacin da akayi jana’izar nasa banji ba amma Insha Allah zanje ta’aziyya da izinin Ubangiji”.

Kai Malam Liman ya gyaÉ—a tare da gyara zamansa kana yace.

“Wallahi kuwa rasuwa abin tausayi wai ciwo dare ɗaya ya tsananta”.

Girgiza kai Malam ArÉ—o yayi da alamun damuwa atare dashi yace.

“Ayyah haka fa kwanaki mota ta bigeshi abakin Makarantar mu fa. Yaron ya samu karaya wannan bugewan ba wanda yayi tunanin zai warke Allah sarki ashe ajalin nakusa”.

 

Kai Hajja Nana ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Haka fa rayuwar take ciwon Ajali lokacin ɗaya zai shige mutum sai dai kaji ance babu shi saidai fatan Allah yasa mu cika da Imani”.

Baki daya suka amsa da Ameen banda Moddibo daya zubawa ƙasan ɗakin Idanu da alama ya zurfafa acikin tunanin da yake.

Ahankali Malam Liman ya juya tare da kallon Moddibo kana ya maida kallonsa kan Malam ArÉ—o tare da cewa.

“A’a Malam ArÉ—o wannan jikan namu dashi kaje kwanakin baya ko?”.

Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da kallon Moddibo da har zuwa lokacin kansa ke ƙasa yace.

“Eh jika nane kuma Malamine Amakaranta na”.

Murmushi Malam Liman yayi tare da faÉ—in.

“Ayyah Masha Allah Yayi kyau amma lafiya na ganshi haka baki ɗaya ya canza ko bada shine ku kaje Jauro yaya kwana kiba”.

Cikin sanyi malam ArÉ—o ya gyaÉ—a kai kana yace.

“Eh da shine mukaje”.

Cike da mamaki Malam Liman yace.

“Amma lafiya kuwa?”.

 

Numfashi Malam ArÉ—o ya fesar tare da Girgiza kai kana yace.

“Ina kuwa lafiya wannan zamani da Allah ya kawo ku. Malam Liman kai dai Ubangiji ya rufa mana asiri”.

Anutse Malam Liman ya gyara Alkyabbar dake jikinsa kana yace.

“Amin ya Allah”.

Kana ya É—aura da cewa.

“Amman Meke faruwa?”.

Gyara zama Malam ArÉ—o yayi tare da fuskantar Malam Liman cikin sanyin murya yace.

“Akwai wani Amininsa Yaron Alhj Bashir mai Dala Jameelu da aka sace baki É—aya abin ya fitar mana hayyaci mun rasa wani irin tunani zamuyi ma acikin wannan al’amari”.

Cikin sauri Malam Liman yace.

“Sunhanallah”.

Cike da damuwa Malam ArÉ—o ya gyara zama tare da zayyane musu duk abinda ke tafiya yanda aka sacesa da kuma yanda akanemi kuÉ—in fansa kana da yanda suka daina jin labarinsa kwata kwata.

Girgiza kai Malam Liman yayi kana yace.

“Subhanallah”.

Ya faÉ—a tare da maida kallonsa kan Moddibo wanda shima adai-dai lokacin ya É—ago Idanunsa da suka kaÉ—a sukayi jawur baki É—aya fuskarsa tayi fayau ya rame.

 

Cike da tausayawa Malam Liman yace.

“Amma yanzu baku da labarin sa!?”.

Girgiza kai Moddibo yayi kana cikin raunin murya yace.

“A’a bamu da labarinsa yau kusan kwana goma sha biyu kenan bamu da labarinsa, sannan wayarsa bata shiga suma kuma sun daina kiran mu abinda yafi komai tayar mana da hankali kenan, bamusan Inda J yake ba”.

Malam Liman kuwa Anutse ya fesar da nunfashi cike da tausayinsa kana ya gyara zamansa tare da cewa.

“Bakomai Insha Allah za muyi addu’a da izinin Ubangiji duk inda yake a faÉ—in duniyar nan Ubangiji zai bayyana shi”.

Kai Moddibo ya gyaÉ—a tare da Gyara zamansa Malam Liman ya cigaba da cewa.

“Da Iznin Ubangiji Allah zaiyi dalilin da za’a ganshi zan baka addu’a’o’in idan har zaku jure kuyita yi da kai da mahaifiyarsa da kuma Mahaifinsa, to za ayi nasara kuma nima zan tayaku”.

Cikin sauri Moddibo ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da cewa.

“Munaso Malam ai addu’a’u Saiful mu’uminun ce ita addu’a itace makamin bawa  dama ita muke tayi ai”.

 

Kai Malam Liman ya gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh shikenan zan baka adduo’i Insha Allah da izinin Ubangiji Allah zai bayyana shi, aduk inda yake afaÉ—in duniyar nan sai dai walau ko araye ko amace amma Ubangiji zai bayyana shi insha Allah za’a ga walallanilansa”.

Cikin sanyi Moddibo yace.

“Mun gode Malam”.

Cike da nutsuwa da kamala Malam Liman ya fara bashi Adduo’i Moddibo kuwa cikin sauri ya É—auki jotter da biro ya fara rubutawa wasu da yawa daga cikin Adduo’in Moddibo ya sansu wasu kuma baisan suba sabida shi ilimi kogine faÉ—i gareshi. sosai ya riĆ™a faÉ—a masa adduo’in Moddibo kuwa yana rubuta adduo’in yana bitar su yasan da izinin Ubangiji idan ya zauna na awa biyu yayi research É—insu zai haddace su.

Bayan Malam Liman ya gama bawa Moddibo adduo’in Hajja Nana ta saki ajiyar zuciya kana tace.

“Toh Ubangiji Allah ya karesa Allah ya bayyana sa aduk inda yake”.

Cikin sanyi murya suka amsa da Ameen.

Kallon Malam Liman Hajja Nana tayi tare da faÉ—in.

“Ai wannan Jikanmu ne ka tuna ƙawata Innare?”.

Kai Malam Liman ya gyaÉ—a mata tare da cewa.

“jikanta ne?”.

Jinjina kai Hajja Nana tayi tace.

“Eh shine”.

Murmushi Malam Liman yayi tare da faÉ—in.

“A Masha Allah Yayi kyau”.

Ita kuwa maida kallonta kan Moddibo tayi wanda gaba É—aya ya zubawa takardan adduo’in ido kana tace.

“Idan ka koma ka gaishe min da ita yau kam bazan samu zuwa ba yanzu ma munyi yamma”.

Kai ya gyaÉ—a kana cikin sanyin murya yace.

“Toh mun gode Allah ya saka da al’khairi Insha Allah zataji”.

Miƙewa Hajja Nana da Malam Liman sukayi tare da yi musu Sallama suka tafi Moddibo kuwa yana fita daga gidan Malam Arɗo kai tsaye gidan Abba ya wuce Bayan sun gaisa Abba yayi shiru tare da tsirawa waje ɗaya ido gabansa da magunguna da alamar bai daɗe da gama shaba.

 

Ahankali Abba ya maida kallonsa kan Moddibo da yaga yayi mugun rama ya sake zama wani so silent duk da dama can bamai yawan magana bane amma yanzu shirun yayi yawa.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da faɗin.

“Aliyu kaga yanda ka koma kuwa ka dawo kamar wanda yayi shekara yana jinya”.

Kallon Abba Moddibo yayi tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo kana ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da cewa.

“Abba”.

Still Idanun Abba na kansa yace.

“Na’am”.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.

“Insha Allah Abba inaji Ajikina J ɗina ya kusa bayyana”.

Numfashi Abba ya fesar tare da sakin murmushi na alamar jin daÉ—i kana yace.

“Allah yasa haka Aliyu”.

Ahankali Moddibo ya amsa da Ameen kana yace.

“Abba ya zun nan akwai wani malami da muka haÉ—u dashi agidan malam ArÉ—o ko Malam ArÉ—o da kansa wajensa yake zuwa É—aukan darasi  ya bani adduo’i masu tarin yawa”.

Sai kuma ya lumshe idanunsa tare da cije Lip ɗin sa na ƙasa kana yace.

“Adduo’in da nake ji ajikina insha Allah Ubangiji zai amsa mana, gashi ya bani adduo’i da dama yace mu riĆ™a yi  dani da kai da Ummi. Insha Allah duk inda J yake afaÉ—in duniya Allah zai bayyana mana shi za muji labarinsa aduk inda yake”.

Murmushi Abba yayi tare da faÉ—in.

“Mungode ƙwarai Allah yasa adace”.

 

“Ameen yace kana yaci gaba da cewa.

“Kyansa ma mu ƙara harda Azumi amma dama Ni tuntuni ina Azumin Abba kaima ka gwadayi.

In Sha Allah ni  zan shiga itiƙafi na tsawon kwanaki uku Insha Allah”.

Kai Abba ya gyaÉ—a kana yace.

“Toh shikenan Moddibo Allah ya temaka”

Nan Moddibo ya bawa Abba adduo’in kana ya tafi kai tsaye gidan Ummi ya nufa itama ya bata Adduo’in cikin sanyin murya tace.

“Toh Babana Insha Allah zanyi”.

Kai ya gyaÉ—a kana ya fice kai tsaye gida ya nufa yana isa sashen Innayi ya wuce sannan ya mata bayanin duk abinda ya faru tare da bata Adduo’in da Malam Liman ya bayar kana ya faÉ—a mata saĆ™on gaisuwar da Ć™awarta ta bata.

Kana ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

“Toh zan shiga ‘itiĆ™afi a É—aki”.

Jinjina kai Innayi tayi da faÉ—in.

“Toh me dame kake bukata?”.

Girgiza kai yayi kana cikin sanyin murya yace.

“Bana buƙatar komai Akwai Friuts a Fridge sannan akwai kayan tea kuma azumi zanyi”.

Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh Allah yatemaka Allah ya bada sa’a.

Ameen ya amsa tare da nufar Bedroom É—insa.

Yana shiga yaja ƙofa ya rufe tare da nufar toilet ya ɗaura alawala yana fitowa ya zauna bisa salla ya fuskanci gabas.

Ya fara rera karatun Al’Ć™ur’ani sai karfi É—aya ya fara jero Adduo’i yanayi yana kuka.

Sai Ć™arfe  uku ya kwanta Ć™arfe huÉ—u dai-dai ya farka yasha tea da fruits Washe gari ya tashi da Uzumi haka ya yini da azumi yaita Adduo’i da karatun Alkur’ani idan dare yayi haka zaita nafilfili sai karfe uku zai kwanta Ć™arfe huÉ—u zai tashi yayi Sahur haka ya cigaba da rayuwa har tsawon kwanaki uku aÉ—aki yana fadawa Ubangiji bukatarsa AÉ“angaren Abba ma haka ya É—auki tsawon kwanaki uku yana bautar Ubangiji haka Ummi ma baki É—aya ta miĆ™awa Ubangiji lamuranta.

 

Yau ya kama kwana na huÉ—u kenan ahankali Moddibo ya fito daga falonsa tare da tsayawa abakin farandar.

Innayi dake tsaye ta zuba masa ido lokaci ɗaya taji hawaye na zubo mata ganin yanda yayi wani masifar ramewa idanunsa sunyi luhu-luhu dasu yayinda sajensa ya cika fuskarsa kasancewar gashi mai santsi da laushi yasa sai sheƙi yake fuskarsa nan tayi fayau sai sheƙi take alamun a ɗan kumbure take sabida yawan kuka da rashin isasshen bacci.

Lumshe Idanu Innayi tayi hawaye masu zafi suka zubo ganin kamar daga jinya ya tashi.

 

Moddibo kuwa ahankali ya É—aga kai ya kalleta jin yandata tsaresa da ido.

Cikin rawan murya tace.

“Moddibo kaga yanda ka dawo kuwa?”.

Murmushi mai ciwo yayi tare da Girgiza kansa cikin sanyin murya yace.

“Innayi bari na tafi wajen Ummi”.

Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.

“Toh baka tsaya kaci abinci ba”.

Girgiza kai yayi kana yace.

“A’a Innayi na Ć™oshi”.

 

Kallonsa Innayi tayi Idanunta cike da ruwan hawaye tace.

“Dan Allah Moddibo ka tsaya kaci wani abu dubi yanda ka dawo fa”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

“Toh shikenan Innayi ki bani tea”.

Cikin sauri ta hado masa tea ta kawo masa karɓa yayi yasha bayan yasha ya fita kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga falon.

Ummi na ganinsa tayi saurin miƙewa tare da fashewa da kuka mai cike da rauni.

Moddibo kuwa cikin sauri ya ƙarasa kusa da ita tare da riƙe tafin hannunta kana cikin raunin murya yace.

“Ummi meyafaru Ummi kuka kuma?”.

Cikin zubda hawaye ta kallesa tare da cewa.

“Babana abubuwan sun haɗu sunyi min yawa acikin kwanaki Ukun nan Ba Jameelu na sannan kai ɗinma da nake gani inji sanyi na daina ganinka. Babana kaga yanda kadawo fa”.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da lumshe idanunsa kana yace.

“Ummi Insha Allahu in Allah ya yarda hawayen mu ya kusa daina zuba inaji Ajikina J yana kusa damu”.

Numfashi ta fesar tare da cewa.

“Allah yasa hakan Babana dubi yanda ka dawo fa kamar wanda aka sallamo daga asibiti kana tafiya Iska na ɗibarka”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Asma’u data zabga tagumi tana binsu da kallo baki É—aya itama ta rame ta sake zama shiru.

Cikin sanyin murya tace.

“Asma’u kawo masa abinci yaci”.

Kai ya Girgiza Asanyaye yace.

“Ummi bana jin yunwa”.

Cikin sauri da sanyi Ummi tace.

“Zafa kaci abinci matuƙar kana son hankalina ya kwanta to kaci abinci Babana”.

Cikin sanyi yace.

“Toh Ummi”.

Ahankali Asma’u ta fito hannunta riĆ™e da Plate É—in dambun shinkafa dayaji Vegetables ya na fidda Ć™amshi da soyayyan naman kaza akai da kwalin exotic.

Agabansa ta ajiye masa kallon Ummi yayi ganin yanda ta tsare da ido tana zuba masa, ahankali ya fara cin abinci duk da yana jin cikinsa ya cushe yaci ya kai rabi kana yasha lemon KaÉ—an.

Ture Plate din yayi kana yace.

“Ummi bari Inje gidan Abba”.

Kai ta gyaɗa da fadin. “Adawo lafiya”.

 

Moddibo na fita kai tsaye gidan Abba ya nufa yana isa ya shiga falon bakinsa É—auke da Sallama Atare Abba da Malam ArÉ—o dake zaune suka amsa masa cikin sanyi Moddibo ya nufi gefen Abba ya zaune tare da Gaishe su.

Kallon Moddibo Malam ArÉ—o yayi kana yace.

“Moddibo yau kwana uku bakai babu dalilinka sannan wayarka bata shiga shine nace bari inzo tambayi Abban Jameel ko lafiya kaddai wanda suka ɗauki Jameelu ne suka ɗauke mana kai”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

“Nima da ban ganshi ba gaba ɗaya hankalina ya tashi duk da cewa nasan yana gida lafiya amma rashin ganinsa ya sake tayar min da hankalin rashin ganin Jameelu na”.

Cikin sanyin murya Malam ArÉ—o yace.

“Toh Allah ya bayyana shi Alhj Ubangiji Allah ya bayyanar dashi aduk inda yake!”.

Cikin rauni Moddibo ya kalli Abba tare da cewa.

“Abbah basu kira ba atsawon kwana ki ukun nan”.

Girgiza kai Abba yayi da faÉ—in.

“A’a basu kira ba Aliyu kuma ga wayar Jameelu na ta daina shiga, yanzu sannan suma sun daina kira”.

Moddibo kuwa ahankali yace.

“Bakomai Abba Insha Allah Allah zai bayyana shi akan al’khairi Alfarman Annabi da Alkur’ani”.

Atare suka amsa da Ameen Hajiya Turai ce tashigo bakinta É—auke da sallama bayan sun gaisa da malam ArÉ—o ta kalli Moddibo da faÉ—in.

“Moddibo kwana biyu shiru gashi babu wani  labarin Jameelu Ubangiji dai Allah ya bayyana mana shi”.

Cikin sanyin murya suka amsa da Ameen kana ta juya ta fice.

 

Kallon Moddibo Malam ArÉ—o yayi kana yace.

“Moddibo muje ka rakani wani waje mana”.

Kallonsa Moddibo yayi da faɗin Ni kuma?”.

Kai Malam ArÉ—o ya gyaÉ—a masa kana yace.

“Eh”.

Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.

“A’a kayi haĆ™uri ni kam babu inda zanje”.

Kallon  Moddibo Abba yayi kana yace.

“Aliyu kaje ka rakasa mana”.

 

Gyara zama Malam ArÉ—o yayi tare da faÉ—in.

“Kuma ta’aziyya ne ma zai rakani, gidan LamiÉ—o tunda akayi rasuwar yaron nan yau wuni na biyar kenan ban samu naje ba, kuma kaima ya kamata kaje amatsayin ka na Malaminsu”.

Shiru Moddibo yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa.

Ahankali Abba yace.

“Aliyu kuje mana zama waje ɗayan nan ma bashi da daɗi”.

Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.

“Abba ni dai banason zuwa”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe da faɗin.

“Kuje mana Aliyu Ubangiji Allah yasa zuwan ya zama alkhairi”.

Cikin sanyin murya yace.

“Ameen”.

Sannan ya miƙe Malam Arɗo na biye dashi suka fita.

 

Acan gidan su Khausar kuwa LamiÉ—o ne zaune afalon tare da wasu baĆ™i guda biyu da suka zo daga Taraba Alhj Ibrahim da Alhj Musa suka zo yi masa ta’aziyya sai kuma Uncle Naseer dake gefe.

Mai gadi ne ya shigo bakinsa É—auke da sallama kana yace.

“Ranka ya daɗe ga Malam Arɗo da Malam Moddibo Malaman su Ramadan sunzo”.

Kai LamiÉ—o ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.

“A’a kace su shigo harda malam ArÉ—o da kansa”.

Kai ya gyaÉ—a sannan ya fice ba dadewa Malam ArÉ—o suka shigo tare da zama kana suka yi Masa ta’aziyya ahankali Moddibo yace.

“Ashe Ramadan lokaci yayi Allah ya masa rahma”.

Cikin sanyi LamiÉ—o yace.

“Ameen Moddibo ya mukaji da taraddadin rashin Jameelu har yanzu shiru ko?”.

Cikin sanyi Moddibo yayi ƙasa da kansa tare da matse yatsun hannunsa batare da yace Uffan ba sai kai da ya gyaɗa masa.

Da-dai lokacin mai gadi ya sake shigowa tare da cewa.

“Ranka ya daÉ—e ga ĆŠan gidan ArÉ—o Ja’eh yazo yi maka ta’aziyya”.

Kai Lamiɗo ya gyaɗa da fadin kace ya shigo”.

Fita mai gadin yayi tare da sanar da baƙon.

 

Da Sallama Bararojin Fulanin dajin yashiga falon LamiÉ—o cikin shigarsu irin ta Fulani hannunsa riĆ™e da sanda kusa da Ć™afar LamiÉ—o ya zauna kana suka gaisa sannan ya musu ta’aziyya.

Juyawa yayi ya kalli Malam, ArÉ—o, Moddibo, Alhj Musa Alhj Ibrahim ya gaishesu tare da yi musu ta’aziyya.

 

Kallonsa LamiÉ—o yayi kana yace.

“Ori ya Baban naka?”.

Cikin yanayin rashin wadatacciyar Hausa yace.

“Ai bashi da lafiya ne shiyasa bai samu yazo ba, na wakilcesa munji labarin Ramadan ya rasu Allah ya masa rahma”.

Baki É—aya suka amsa da Ameen.

 

Ahankali LamiÉ—o ya juya tare da kallon Moddibo kana yace.

“Moddibo da gaske wai har yanzu babu labarin Jameelu”.

Ahankali Moddibo ya ɗago kansa dake ƙasa ya  kalli Lamiɗo cikin rawan murya.

“Eh har yanzu babu labarinsa, yanzu kam ma sun daina kira, sannan kuma wayarsa ma da ake kira ta daina shiga zuwa yanzu munsa hukuma a cikima sunyi iya bincikensu ba labari”.

 

Malam ArÉ—o ne ya gyara zamansa tare da faÉ—in.

“Ai wannan Zamani da Allah ya kawo mu sai dai Ubangiji ya rufa mana asiri amma an maida satan al’ummar kamar satan Ć´aĆ´an awaki”.

Ido Ori ya zuba masa tare da sakin Ajiyar zuciya.

Malam ArÉ—o yace.

“Kisan rai kuma ba adaukesa abakin komai ba, ran mutum ya dawo kamar ran kishiya, baki ɗaya duniyar nan ta canza ta burkice ta koma abin tsoro, in ba haka ba kamar Malam Jameelu asace sa bashi babu labarinsa”.

Alhj Musa da Alhj Ibrahim kuwa kai suka jinjina da faÉ—in.

“Sosai kuwa yanzu idan kana da dukiya hankalin ka ba akwance ba, haka zalika idan kana talaka ma baka da nutsuwa, sai dai Allah ya kawo mana É—auki amma baki É—aya jama’ar duniyar ta canza, yanzu ma idan muka fita daga nan zamuje wajen Alhj Bashir É—in muyi masa jaje”.

Malam ArÉ—o ya gyaÉ—a kai tare da cewa.

“Muma yanzu daga can muka fito”.

Jinjina kai Alhji Musa yayi da faÉ—in.

“Allah sarki Jameelu yaro mai mutunci da karamci, ga sanin darajar manya Ubangiji ya bayyana shi”.

 

Gyara zama Ori yayi tare da fuskantar LamiÉ—o cikin rashin ingantaccen hausarsu yace.

“Hmmm Lamiɗo wato ai wannan duniyar ta zama abin tsoro kwanan nan abinda na gani acikin dajin mu, saman dutsen Membilla aƙasan wata bishiya har zuwa yau hankalina bai gama dawowa jikinaba har zuwa yanzu wanda yasan ni da ya ganni ayanzu yasan ban gama dawowa cikin hayyacinaba”.

 

Atare Moddibo da sauran jama’ar dake falon suka juya suka kallesa  kusan a tare  sukace.

“Me ka gani?”.

Girgiza kai yayi da faÉ—in.

“Kai tashin hankalin fa ya tsananta, muda muke daji ai munfi ku ganin tashin hankali, ku ai kuna cikin gari ba abinda kuke gani sai dai in an ɗauke muku mutum kuke ganin tashin hankali”.

Lokaci ɗaya zuciyar Moddibo ya tsinke da masifar ƙarfi yana bada sautin dib-dib-dib cikin sauri ya sanya tafin hannunsa na dama ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa kana ya runtse Idanunsa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya hau kyarma wani zufa mai ɗumi ya keto Masa daga tsakiyar kansa cikin raunin murya yace.

“Amma meyafaru meka gani bawan Allah!”.

Girgiza kai Buba yayi da faÉ—in.

“Abinfa ba daɗin gani, domin ya wuce tunanin mutum”.

Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.

“Toh Allah ya rufa mana asiri amma baki ɗaya zamani ya zama abin tsoro, to amma Ori mai kagani acikin dajin da har ya gigita ka haka, bayan ku Fulani daji kun saba ganin abubuwa!”.

Cikin sauri Ori ya girgiza kai da faÉ—in.

“Kai gane ganen da muka saba ba irin wannan bane! Duk abinda muke gani na yau da kullum lamuran iska ko halittun dajine”.

Alhj Musa dake fuskantarsane yace.

“To amma meka gani haka?

Ya kamata idan kunga abu irin wannan na tsoro Ku riĆ™a faÉ—a acikin gari wurin jami’an tsaro”.

 

Girgiza kai Ori yayi cikin sanyin murya yace.

“Uhm muna tsoro ai”.

Lamiɗo ne ya sauƙe Ajiyar zuciya da faɗin.

“To amma meka gani?”.

Gyara zama yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

“Abinda nagani abin tsoro ne, to amma dai  banga amfanin ɓoye muku ba, yau tsawon  kwana bakwai kenan ina kiwon shanu na akan Dutsen Membilla”.

Duk ido suka zuba masa tare da maida nutsuwarsu kansa suna saurarensa.

Gyara zama Ori yayi kana ya cigaba da cewa.

“Ina nufar kan dutsen sabida ɗebo kanya, naji wani irin wari mai gigitarwa da fitar da hayyacin ɗan Adam Atake tsoro ya kamani na rasa wani irin wari ne wanan.

Saboda ban taɓa jin wari makamancin wannan ba!”.

Cikin sauri LamiÉ—o ya kallesa da faÉ—in.

“To wannan wani irin wari ne!?”.

Ajiyar zuciya ya sauke da faÉ—in.

“Hmmm Lamiɗo nima kaina na gigice.

Saboda ban taɓa jin makamancin  wari irin wannan ba a duniya!”.

Alhj Ibrahim ya fesar da numfashi kana yace.

“To amma me kagani awajen haka?”.

Girgiza kai yayi da alamun damuwa atare dashi yace.

“Ban taɓa ganin abinda ya tayar min da hankali ya kiɗimani ba irin wannan domin ina jin warin na haura na nufi wajen agindin wata Bishiyar kanya”.

Cikin zaƙuwa da gajiyawa za tsinkewar zuciya Modibbo yace.

“Uhmmm!!”.

Shi kuwa Ori runtse Idanunsa cike da damuwa ya cigaba da cewa.

“Ina haurawa kan dutsen. Naga  gawa ɗaure a jikin bishiyar, da igiyoyi tako ina.

Wanda da alamu abin ya kwana biyu domin tuni mutumin ya rasu gawace aɗaure, bisa ga duk kan alamu tunda ransa aka dauresa har ya rasu  domin har ya kumbura  yayi dam sai wani irin sheƙi fuskarsa duk sauran jinka keyi, fuskara ɗauke da murmushi duk da ya rasu, sai kuma alamun kwaranyar hawaye a kan kumatunsa gemunsa da sajensa sai sheƙi sukeyi tamkar wanda kullum ana shafa masa maine kai in ka ganshi kace balarabene wannan warin ne kaɗai ke nuni da gawane, domin a  lokacin bai fasheba jikinsa fes”.

Cikin sauri da wani irin azabebben tsinkewar zuciya Moddibo ya runtse Idanunsa tare da taune lips ɗinsa na ƙasa kana yace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakil”.

Malam ArÉ—o kuwa cike da tsoro ya kalli Ori kana yace.

“To amma kai Meyesa baka zo ka faɗa acikin gari ba!?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

“Tsoro nakeji domin Atake awajen na fara sheƙa amai da gudawa saboda warin dana shaka karshe ma agigice na koma gida, domin bana cikin nutsuwa ta kuma tunda na koma saida nayi kwana uku bani da lafiya ko kiwo sai ƙanina ne ya karba, kuma dole muka canza wajen kiwo saboda warin da wannan yankin keyi”.

 

Cikin sauri da É“acin rai LamiÉ—o yace.

“Haba Ori ya za ayi kuyi haka kuda kuke tare dani ai idan kunga makamancin abu irin wannan, sai ku kirani ku faɗa min idan yaso in tura ƴan sanda su duba ko menene ya za ayi kuyi shiru!?”.

 

Cikin tsoro da cikekken gaskiya Ori ya sauƙe ajiyan zuciya tare da Girgiza kai kana yace.

“Hmmm ire-iren waɗannan abubuwan gaba ɗaya mu Fulani ma zauna daji ake ɗaurawa alhakin sa, wanda bamusan komai ba banda Bautar Allah da kiwon dabbobin mu, amma baki ɗaya an ɗauki baƙin jini da tsana an ɗaura mana”.

Kallonsa kawai suke zuciyarsu na tsinkewa.

Shi kuwa a hankali ya cigaba da cewa.

“Mutanen gari na cewa Fulani sune ƴan Kidnapping, to idan mun faɗi ire-iren waɗannan abubuwan sai azo ace mu muka aikata ayi ta kamamu, shiyasa mukeyin shiru, kuma nima Aruɗe na koma gida baki ɗaya bana cikin nutsuwa ta shiyasa”.

Cike da damuwa Malam ArÉ—o yace.

“Allah mai iko kai wannan zamani Allah ya rufa mana asiri”.

Kallonsa ya mayar kan Moddibo da har zuwa lokacin jikinsa ke tsuma kana tun lokacin daya runtse Idanunsa har yanzu bai buÉ—e ba cikin sanyin murya Malam ArÉ—o yace.

“Amma Moddibo ka shirya muje wajen mu duba gawan waye!”.

Cikin sauri Moddibo ya buÉ—e Idanunsa dake rintse ya kallesa kana yace.

“Nikam bazan jeba Malam Arɗo me kake nufi kana nufin J ɗina ne?”.

Girgiza kai Malam ArÉ—o yayi tare da cewa.

“Ba haka nake nufi ba bakaji bahaushe yace idan raƙumin ka ya ɓataba ko cikin ramin allura ka duba ba to muje mu duba mana”.

Jinjina kai LamiÉ—o yayi da faÉ—in.

“Tabbas kam ya kamata aje aduba yanzu kuje ku faɗawa Mahaifinsa Ni kuma zan kira hukumar ƴan sanda sai muje dasu”.

 

Girgiza kai Moddibo yayi tare da fesar da numfashi mai zafi kana cikin rawan murya yace.

“Nifa bazan jeba dan nasan in Sha Allah ba J ɗina bane,  bakuji yace muku gawa bane kuma tuntuni ya mutu har ya kumbura ni kuma J ɗina bai mutuba inaji Ajikina in Sha Allah yana raye”.

 

Dafa kafaÉ—ar sa Malam ArÉ—o yayi tare da cewa.

“Moddibo kada kiɗima yasa ka furta kalmar alamar sanin gaibu”.

Cikin sauri Moddibo ya Girgiza kai kana muryarsa na rawa yace.

“Astagafirullah³ amma dai inaji Ajikina kamar  J ɗina yana raye”.

Cikin sanyin murya Malam ArÉ—o yace.

“Eh duk da haka dai muje”.

Girgiza kai yayi tare da cewa.

“Nifa bazan jeba”.

Cikin lallashi LamiÉ—o yace.

“A’a Moddibo ka daure dai kuje Allah yasa ba shiÉ—in bane amma dai aje aduba É—in”.

Kai Buba ya gyaÉ—a kana yace.

“Eh suje su duba kuma alokacin ma na samu an ajiye wayoyi agabansa da kuma goran ruwa fuskarsa ma bata wani kumbura ba dan kyanshi bai ɓaceba”.

Atsorace Moddibo ya kallesa zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yace.

“Harda waya kuma shikenan bari Muje mu gani ɗin?”.

Ya faɗa tare da miƙewa suka fita kai tsaye gidan Abba suka nufa kana malam Arɗo ya masa bayani.

Kallon Abba Moddibo yayi cikin raunin murya yace.

“Abba ni dai inaji Ajikina in Sha Allah ba J ɗinmu bane, amma dai tunda sunce muje to muje ɗin”.

Cikin rarrashi Malam ArÉ—o yace.

“Alhj kayi haƙuri muje mu gani”.

Cikin sanyi da rauni kana da tsinkewar zuciya Abba ya gyaÉ—a kai dai-dai lokacin da folisawan suka iso tare da LamiÉ—o.

 

Fita sukayi cikin shirin tafiya Abba, LamiÉ—o malam ArÉ—o da Moddibo suka shiga mota É—aya Ori kuma ya shiga motar Ćłan sanda suka tafi.

 

Suna isa dajin bayan sunyi Parking din Motar daga can nesa, suka fara haurawa saman dutsen.

Da sauri suka fara kallon juna sabida jin wani irin ni’imtaccen Ć™amshi mai sanyin shaĆ™a, babu wari kamar yanda ya faÉ—a musu yasa Moddibo juyawa ya kalli Ori kana cikin sanyi yace.

“Ya gaba ɗaya babu warin da kace sai ma wani irin amintaccen ƙamshi”.

Kallonsa Ori yayi da faÉ—in.

“Toh yaufa kusan kwana takwas kenan da labarin dana baku ai dole wari ya baje dan zuwa yanzu Nasan gawar ya fashe bare kuma ruwan sama da ake ai dole zai za gonye sai dai kuma nima nayi mamakin wannan ƙamshi!”.

Cikin sanyi Malam ArÉ—o yace.

“Allah mai iko wannan wani irin ni’imtaccen Ć™amshi ne a tsakiyar daji”.

Abba kuwa kasa furta komai yayi sai zuciyarsa dake bugawa da masifar ƙarfi yana jin wani irin masifaffen tsinkewar zuciya haka zalika Moddibo suna masu shaƙar ƙamshi.

Lamiɗo da polices din kuma sai lumshe idanu suke sabida daɗin ƙamshin da Ubangijin talikai ya wadata wurin dashi.

Yayinda suna kara haurawa suna ƙara jin ƙamshin.

Cikin tsanananin fargaba da tsinkewar zuciya suka cigaba da haurawa wajen  suna gama haurawa Ori yayi saurin cewa.

“Yawwa ga can bishiyar”.

Da sauri Moddibo ya ɗaga Idanunsa tare da kallon jikin Bishiyar ganin gawa ɗaure ajikin Bishiya yayi har ya zagwanye idanunsa sun rarake sai ramuka kaɗai sai kuma maiƙo dake zube aƙasa da wani irin sassayan ƙamshin dake tashi a wurin.

Cikin tsanananin tsinkewar zuciya ya sauƙe idanunsa akasa dai-dai kan ƙafar gawar dake maƙale da takalmin cikin sauri ya runtse Idanunsa tare da dafe ƙahon zuciyarsa dake bugawa da masifar ƙarfi.

Abba kuwa da sauri ya ƙarasa jikin Bishiyar dai-dai Inda goran faron ke ajiye Idanunsa suka sauƙa akan wayoyin dake wajen hannunsa na rawa ya ɗago wayar tare da jujjuyawa.

Cikin tsanananin tashin hankali da ruÉ—u yace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n!”.

Juyawa yayi tare da kallon Moddibo cikin raunin murya yace.

“Aliyu wayoyin Jameelu na neeeee”.

Cikin sauri Moddibo ya juya tare da dafe saitin ƙohon zuciyarsa cikin raunin murya mai cike da tsantsar tashin hankali yace.

“Abba wayar J kuma”.

Kai Abba ya gyaÉ—a yayin da wasu irin hawaye masu masifar zafi ke koro juna subabin kuncinsa murya na rawa yace.

“Eh”, Ahankali Moddibo ya juya ta gefen da gawar ke daure tare da tsaida idanunsa akan  hannun gawar na dama da har ya bushe idanunsa ya zubawa zoben dake hannu gawar.

Cikin tsanananin kaÉ—uwa da wani masifaffen tsinkewar zuciya mai cike da É—imuwa da tashin hankali Moddibo yace.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Abba kalli zobunnan hannunsa zobunnan hannun J É—ina ne da agogon”.

Ya ida maganar tare da yanke jiki ya faÉ—i babu numfashi atare dashi….!

 

 

Wannan littafin dai na kuÉ—i ne.

 

 

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button