Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 4

Sponsored Links

💖💖 *NIHAAD*💖💖

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Related Articles

 

~~~~

Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga manya manyan fans dina irinsu.. Fatima Arebia, Aisha Abubakar, Maman Shukrah (Banatsapparel and more) Khadijah Dutse, mu’azatu😂, infact da duk wani member na Khaleesats palace da ban ambato ba a nan ku sani ina son ku har raina, ina yin ku, ina maku fatan alkhairi Allah ya dafa maku a duk lamuranku, My respect to many of my fans da suka fara patronizing Nihad without even waiting for the end of free pages, yawancin ku ba biyan littafin ku ka yi ba kyauta ce kawai kuke min, kuma ina alfahari da ku, ina maku fatan alkhairi da Zuri’a dayyiba. Allah ya bar xuminci, ya saka da Alkhairi ya karo maku yalwataccen arxiki, na kuma sadaukar da page din nan gare ku.

 

Bayan minti talatin da biyar Nihad ta gaji da jiran Abbanta don har sannan bai fito daga gidan ba, ga kiran da Husnah ke ta yi mata taki dagawa don bata son tace mata bata gida tasan baxata jira ta ba, kallon agogon dake makale hannunta tayi ganin sha biyu har da minti goma ta tashi daga kan kujerar da take ta nufi khalil, Babu yabo babu fallasa tace “Hey xan koma gida kayi dropping dina yanxu” Sai da ya fara kallon mai gadi dake gefensa kamar dai da mai gadin take, ta daure fuska tace “Malam da kai fa nake?” Sai a sannan ya kalleta ya d’an kara kunnensa gaba yace “Na’am” Rasa ma me zata ce masa tayi saboda bakin ciki, har sannan fuskarta a daure tace “Ina ga dai kana da matsalar ji, dalla malam ka tashi ka maida ni gida” Yace “Naga ai Alhajin bai fito ba” Tana masa wani kallo tace “Eh na fi ka sanin bai fito ba” Yace “To kar ya fito ya tarar bana nan” Ta rike kugu cike da masifa tace “Sai ka maida ni, idan ka maida ni xaka iya dawowa idan ka ga dama” Ya dauke kai yayi shiru bai ce komai ba, shi dai mai gadi sai mazurai yake da ido babu damar ya kwaba ma khalil, shi tsoronsa ma kada wnn ɗan abin ya sa ya rasa aikinsa, yana ga kamar Khalil bai ta6a aiki gidan masu hannu da shuni bane shi yasa har ya tsaya suna ja in ja da Hajiya karama banda haka ina shi ina biyeta, ai duk abinda tace haka xa ayi, tsawar Nihad ne ya dawo da mai gadin reality don sai da ya tsorata, “Dalla Malam kana bata min lkci, are you even okay, how dare u query my order? Ko dai kana shaye shaye ne???” Khalil ya ɗan kalleta, sae kuma ya mike ya nufi motar, ta ja wani dogon tsaki ta bi bayansa kamar xata tashi sama tana harararsa, duk sai taji ranta yayi mugun baci, bayan mota ta bude ta shiga, tuni mai gadi har ya wangale gate yana daga mata hannu alamar Allah ya tsare, Khalil yayi reverse ya fita daga compound din, cikin mintuna kadan ya isa gida da ita, yana parking dai dai gate ta ja tsaki ta bude motar ta fice without closing the door, da ido ya bi ta har ta shiga gate din gidan, ya fi minti biyar tsaye da motar, daga bisanni ya sauka ya kulle door din motar, sannan ya shiga yyi reverse ya bar layin ya koma can gidan da Abba yake. Nihad na shiga gida bangaren Umma ta nufa, jefar da jakarta tayi saman kujeran parlon tana kallon Umma tace “Umma wani irin driver ne wannan Abba yayi employing, who even linked them? wllh yaron bai da kunya ko kadan Umma, kinga abinda yayi min kuwa??” Umma ta ajiye kayan hannunta tana kallonta tace “Me yayi maki?” Nihad tace “Wllh rashin kunya yayi min, ni babu wani wanda ya ta6a min haka ma tun da nake, wai yaron ya maida ni gida yaki fa” Umma tace “Aa abu me sauki sae ayi ma Abban naku magana ya sallamesa, halan d’an kauye ne?” Nihad tace “Toh ae dama su ne masu wannan tsagerancin da rashin ta idon, wllh Umma wannan idan yayi wata daya a gidan nan daina kai mu duk inda xa mu xae yi, Allah cewa xai dinga yi baxae je ba kansa tsaye idan ma bai hada mana da zagi ba, gwara kawai Abba ya dawo ya sallamesa a samo wani dama ni bai min ba from the start, irinsu ne idan an shigo da su inuwa su maida mutum rana, wai kinga me yayi min ne, jayayya fa muka tsaya muna yi da shi” Daga haka ta fice daga parlon ta tafi dakinta don ta shirya xuwa inda xa su hadu da Husnah, sae dae tana tsaka da shiryawa ta dinga kiran wayar Husnah ta ji a kashe, lkci daya ranta ya baci, kaddai har tayi tafiyarta, ta zauna gefen gado tana ta trying din layin amma ya ki connecting. Ana kiran sllhn Azahar Abba ya fito daga gidan tare da wata tsohuwa, Khalil ya mike tsaye ganinsu, suna karasowa inda yake Abba yace “Sabon drivern da na dauka kenan Hajiya, yau ya fara aiki…” Tsohuwar ta kallesa daga sama har kasa tace “To ba laifi, kuma da ganinsa xae fi Habibu kwazo duba da halittarsa, kawai dae sai mu yi fatan Allah ya sa ya fi Habibu nutsuwa, don Habibu ni kadai nasan ɗan iska” Khalil yayi kasa da kai tare da risinawa yace “Ina yini Hajiya” da fara’a tace “Lafiya lau, amma kai buzu ne koh?” Ya murmusa yana girgiza kai, Tsohuwar tace “Toh a dai kula da dukiyar mutane ka ji, kai ma sai kaga Allah ya kula da kai, baka ga motar da Habibu ya ajiye kafin ya tafi ba, duk ta fita hayyacinta daga karshe konden konden aka siyar ma, su ma din dai a walakance suka siya, ya sunanka?” Yace “Ibrahim” Buda baki tayi tace “Ikon Allah, Kai ae kawai ka zama d’an gida abun ka daga yau ka ji, babu me raina ka ko waye shi, kanka tsaye kar ka yarda da hakan, ae sunan Uban gidan naka kenan, kuma ni na haifesa, Allah yayi maku albarka gaba daya” yana murmushi yace “Ameen” Abba yace “Toh ki koma haka Hajiya, ni xan tafi” Tace “To Allah ya tsare, idan Habubakar din ya dawo xan tattauna da shi” Yace “Ba laifi, sae anjima” daga haka ya nufi motar, Khalil na biye da shi a baya. Yana ajiye Abba a gida, Abba yace “Ka tafi islamiyya ka dauko yara nasan sun tashi ynxu” Khalil yace “Toh in sha Allah” hanyar makarantar ya nufa, yana parking bakin gate sae ga Nihal, sannan Fadil da Sudais, Amina ce karshen fitowa duk suka shige bayan motar, ita kuma ta xauna gaba, ta madubi yake kallon Nihal, tace “Barka da rana” xai amsa Sudais da Fadil suka gaishesa su ma, amsa masu yayi gaba daya sannan ya maida hankalinsa kan driving din da yake. Nihad na tsaye bakin parlon Abba tana jiran ya amsa sallamar da tayi, yana amsawa ta shiga, ta karasa parlon ta xauna saman kujera tace “Abba ina yini” yace “Nihad me yasa kika ki shiga ku gaisa da inna da mutanen gidan?” Ta langwabar da kai bata ce komai ba, glasses dinsa ya saka yana maida dubansa kan laptop din gabansa, tace “Abba i came to report this new driver to you” Sake kallonta yayi yace “What about him?” Tace “Abba kawai don nace ya maida ni gida i am press shine mutumin nan ya ki, infact yi yayi kamar bai ji abinda nake cewa ba ya bar ni a tsaye” Abba yace “Is that so?” Tace “Wllh Abba, and it’s not as if i was rude to him, kawai cewa nayi don Allah ka maida ni gida ina son xan koma, kawai sai yayi min banxa, wllh Sagir mai gadi ne shaidata” Abba dai yayi shiru yana kallonta, bude kofar parlon Abba aka yi sai ga su Sudais da Fadil sun shigo gaida Abban nasu ganin motarsa a gida, Nihal ce ta shigo bayansu, Abba yace “Welcome Nihal, tell the driver to wait me at the balcony….” Juyawa tayi ta fita, ba a wani dau lkci ba sai ga ta ta dawo tace “Abba na gaya masa” Abba ya ajiye laptop din kafarsa ya mike ya nufi kofa, Nihad taji wani dadi har cikin ranta dama babu abinda xata ce ma Abbanta tana so da baya yi, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa Nihal ta bi ta da kallo, Abba na kallon Khalil bayan ya zauna saman daya daga kujerun dake wajen yace “Ibrahim me yasa tace ka maido ta gida ka ki?” Khalil ya durkusa kasa yace “Yallabai ban ki ba, ce mata nayi kar ka fito ka tarar bana nan kace inyi jiranka, amma daga karshe na daukota na dawo da ita gidan” Nihad dake jikin kofa ta hade rai jin abinda yace, Abba ya juya ya kalleta yace “Is that so?” Tace “To Abba sae fa da ya ja min rai, maimakon ina gaya masa kawai ya tashi ya kai ni gida” Abba ya kalli khalil yace “Je ka” Mikewa Khalil yayi yana kallonta yace “Kiyi hakuri, ban san haƙan xai bata maki rai ba” Wani shegen kallo tayi masa ta juya tayi wucewarta ciki. Bangaren Umma Nihad ta koma, Kamar xata fashe da kuka tace “Umma kin ga Abba bai dauki ko wani action ba dai ko?” Umma tace “Sai yace masa me?” Tace “Ba abinda yace masa, ni wllh sai dai duk abinda xai faru ya faru, da kaina xan dinga driving kaina, gashi gobe ina da lectures karfe goma a haka xai kai ni schl din? Nooo i will prefer to drive my sef” Umma tace “To idan kika tafi da motar da wanne xa a dauko kannenki daga makaranta?” Tace “Ba ga motar yaya Farooq ba ko yaya Usman” Bata jira me umma xata ce ba ta fita daga parlon xuwa kitchen, Aminu mai gadi ta gani a windown kitchen din ta baya, mai aikinsu Hafsah tana xuba wani abinci a plate, kallonta tayi tace “Abincin waye wannan?” Kafin tayi magana Aminu yace “Na sabon dreba ne” Buda baki tayi tace “Shi ma din sai an dinga basa abincin a nan? Waye yace haka?” Daga mai aiki har mai gadin suka yi shiru, tace “Ohh kawai ku kuka tsara hakan sbda ku ke siyan kayan abinci?? To Abba bai ce haka ba, ni ma kuma bance ba, saboda haka ajiye abincin nan dake hannunki baxa a kai ba, kai kuma Aminu ka kama gabanka, ba shi da portion din abinci a gidan nan” juyawa Aminu yayi ya bar wajen a sanyaye, Hafsah ta nemi plate ta rufe abincin ita ma a sanyaye, tsaki Nihad tayi ta dau plate ta debi abinda xata deba ta cika nama sannan ta fita, tana fita Nihal ta shigo kitchen din ita ma xata xuba abinci, ganin wanda Hafsah ta rufe tace “Hafsah wannan wa ya ci ya rage?” Hafsah dake wanke wanke tace “Aa ban dade da xubawa ba, Aminu ne ya xo amsar ma sabon dreba abinci Aunty Nihad ta hana” Nihal tayi shiru da mamaki, can tace “To saboda me?” Hafsah tace “Nima ban sani ba wllh” Nihal ta buɗe abincin tana kallo, can ta rufe ta kalli Hafsah tace “Ki kai masa” Hafsah ta xaro ido tace “Ta fa hana Aunty Nihal” Nihal bata kuma cewa komai ba ta dau spoon ta daura saman abincin ta fita daga kitchen, xaune ta tadda Khalil bakin gate da mai gadin, mai gadin ya dauko masa wani guntun bread dake ta ajiye dakinsa da pure water ya basa, kallonta suke gaba daya, shi dai Khalil yana kokarin gane wacece, don kamarsu ta ɓaci da Nihad, sai da ta karaso ya gane ba Nihad bace don Nihad ta fi ta haske har ma da tsayin hanci, amma both suna da dimple, ta mika masa abincin tace “Ga abincin” Amsa yayi ya d’an yi murmushi wanda iyakarsa Lips yace “Nagode” Juyawa tayi ta koma ciki, Mai gadi yace “Kaga er albarka, muna ganin abubuwan al’ajabi fa a gidan nan, halaye iri iri in gaya maka, kaga Nihal din nan da kake gani, ko kadan bata yi halin uwarta Hajiya ba, yarinya ce nutsatssiya ga sanin ya kamata, uwa uba ga girmama d’an adam ko da kuwa almajiri ne, ba dai ka ganta da kawaye ba kuma, uwarta kuwa ban ta6a ganin mace mara kirki mara mutunci irinta ba duk nan hakuri muke da ita, gashi bata da aiki sai shige ma matan manya manyan kasar nan, sannan ita kadai ce bata yarda Habibu ya ja ta a mota ba, duk sanda xata fita sai ta bari Alhaji ya fita sannan ta ja mota ita ma, bata dawowa kuma sai dab da magariba motar nan kaga duk yayi butu butu da laka malam, tana dawowa kuma xata sa Habibu ya wanke motar, ita kuma wancan Ja’irar da ta hanaka abinci ban ta6a ganin me kirki irin uwarta ba, wato matar Alhaji ta biyu kenan, ga dai ita ce ta fari gun uwarta, tsakaninsu da Nihal kwana daya tak, shi sa xaka gansu kamar yan biyu, sai kuma Allah ya basu kama daya, komai nasu iri daya ne, to wllh Hajiya Mumy uwar Nihad mace ce me mutunta mutum babu ruwan baiwar Allahn nan da duniya, sai gashi Allah ya hadata da shaidaniyar yarinya, bata da aiki sai na bitar kawaye da rashin daraja ɗan adam, to haka Allah yayi ikonsa a gidan nan, kyansa ace Nihad uwarta Umma, ita kuma Nihal uwarta Mumy kaga dai dai kenan, amma Allah bai tsara hakan ba, ni fa da rana daya aka haifesu sai muce canja su aka yi a asibiti, amma Nihal aka fara haifa er baka da ita washegari aka haifi Nihad ita kuma fara tass, kaga ko ai ba ayi canje ba” Khalil dake kallonsa yana sauraronsa attentively yace “Ita Umman yaranta nawa?” Mai gadi ya gyara xama irin abun nema ya samu din nan, yana kirga su da yatsa yace “Kaga Farouq shine ɗan ta na fari, a Habuja yake aiki, ya kan yi wata biyu ma bai leko gidan nan ba, ba laifi yana da kirki da faram faram da jama’a, shi ma kuma bai yo halin uwarsa ba gaskiya, sai Usman shi kuma kadaran kadahan, shi ba a ma gane alkibilarsa, yana da kirki oho, bashi da kirki oho, atoh a haka na san sa gaskiya, sai Kamila warce tayi aure shekara biyu kenan, wani shegen mai kudi Umman tasan yanda tayi ta hadata da ta aura, sai Nihal sannan autarsu Amina, amma fa ta fi ji da Nihal din don ita ma auta take kiranta, ita wannan Aminar ma mara kunya ce gaskiya amma fa akwai son karatun addini, tana ajin karshe na sakandari, Nihal kuma ABU Zaria take, ita Nihad makarantarta ance yayi Miliyan biyu xuwa uku, haka naji su Saminu ke cewa, Maryam Abatcha naji suka ce sunan makarantar” Khalil yace “Toh ita me xuwa Maryam Abatcha din su nawa ne gun Mamarta” Mai gadi yace “Ai ita ce ta fari, sai kanninta biyu duk maza, Sudess da Fadil” Khalil bai ce komai ba ya bude abincin hannunsa ya dau spoon ya fara ci. Nihad na gama cin abinci ta tafi bangaren Mum dinta, shiryawa ta sameta tana yi hankalinta a d’an tashe, Nihad tace “Mumy me ya faru?” Mumy tace “Yanxu Jamila ta kirani wai kanwar mijinta ta rasu” Nihad ta dafe kirji tace “Kaddai Aunty Salma?” Mumy tace “Ita” Salati Nihad ta saki tace “Allah sarki, Allah ya ji kanta, Mumy in sa Hijab mu je” Mumy tace “Ki sameni a waje, drivern bai fita ba dai ko?” Nihad tace “Mumy kiyi driving din mana ko kuma ni inyi” ko tanka ta Mumy bata yi ba ta dau handbag dinta ta fita, bangaren Umma ta fara shiga ta sanar mata rasuwan, Umma tace “Allah Ubangiji ya ji kanta, in sha Allah idan xaki koma gobe sai mu je muyi gaisuwa mu ma, Allah ya ji kan musulmi” Mumy tace “Ameen, Allah ya kai mu goben” Part din Abba ta nufa, shi ma ta sanar masa rasuwan daga haka ta fita compound, Mai gadi yayi kasa da murya yana ma Khalil magana yace “Yauwa kaga Hajiya Mumyn ita ce uwar Nihad, ina ga fita xata yi” Muryar Mumy suka ji tana cewa “Aminu Drivern ya fita ne?” Mai gadi ya mike da sauri yace “Aa gashi nan Hajiya a kusa da ni” Khalil ya mike ya gaisheta da ladabi, Mumy ta amsa cikin mutuntawa tana kallonsa daga sama har kasa, sai kuma tace “Shi ne Drivern?” Khalil yace “Ni ne Hajiya” Mumy tace “Don Allah xaka ajiye ni nan Hotoro ne idan ba damuwa” yace “Toh Hajiya” Makullin motarta ta mika masa, ya amsa da ladabi Aminu ya nuna masa motar Mumy, gun motar ya nufa, Mumy ta daga wayarta dake ringing ta kai kunne, Nihad ce ta fito ita ma sanye da Hijab har kasa, tana ganinsa cikin motar Mumy ta wani daure fuska, bayan yayi warming motar ya karaso da motar har inda Mumy take ya tsaya, Mumy ta bude bayan motar ta shiga, Nihad ma ta bude baya xata shiga mumy tace “Baxa ki xauna a gaba ba” Without looking at her mum tace “No, i will be more comfortable at the back” Kulle motar tayi ta bude handbag dinta ta ciro tsadadden shade dinta ta saka, Khalil ya ja motar Mai gadi na daga masu hannu har suka fita compound din ya kulle gate, cike da nutsuwa Khalil ke driving din xuwa hotoro da Mumy tace daga Nasarawa GRA. Suna isa dai dai family house din mijin kanwarta Jamila ta sa yayi parking, Mumy ta fara sauka daga motar tana kallonsa tace “Ko xaka je ka dawo xuwa bayan magrib ka daukemu, kar a bar ka kayi ta jira a nan” Yace “Aa babu komai xan jira daga can tsallaken in sha Allah” Jin haka Mumy tace “Toh shkkn” Daga haka ta juya ta shiga gidan rasuwar Nihad na biye da ita a baya. Nihad bata yarda ta xauna cikin jama’a da suka fara taruwa gidan ba ana koke koke, ta nemi waje at the far end of the compound ta inda generator din gidan yake ta xauna ita daya a wajen, Iphone dinta ta ciro a jakarta, taga missed calls din Husnah da Naf, da sauri tayi dialing Number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga tace “Ina kika shiga ne babe” Nihad tace “Wllh mun fita tare da Abba ne, and i left my phone at home, what’s up kun fitan ne?” Husnah tace “Tun yaushe, ke in gaya maki akwai labari wllh” Nihad tace “Yanxu dai kuna ina?” Husnah tace “Tahir guest palace, kiyi kokari ki taho yanxu kar ayi ba ke” Nihad tace “Husnah Hijab fa ne a jikina, mun xo wani gaisuwa da Mumy a hotoro” Naf ta amshe wayar don a handsfree Husnah ta sa, tace “Haba dai minti nawa kin shiga boutique Nihad” Nihad tace “Toh shkkn bari in amshi makullin motar Mumy a hannun driver in taho kawai, nasan before magrib xata koma gida kafin nan na dawo” Naf tace “Shkkn xa mu jira ki a Tahir din be fast pls” Katse wayar Nihad tayi tana bin compound din da ido trying to figure out where her mum is, har ta kare xaga tsakar gidan da idanuwanta bata ga mumy ba alamar dai ta shiga cikin gidan, tashi tayi da sauri ta nufi gate ta bude ta fita, nan ma ta dinga waige waigen inda xata hango drivern, tun da ta fito ya ganta, don yana xaune daga tsallaken bakin titi wajen mai siyar da Fruits, hada ido suka yi ta tsallaka da sauri ta nufesa babu yabo babu fallasa tace “Hey ka bani makullin mota xan mika sako in dawo yanxu” Kallon me siyar da fruits din yayi kamar dai da shi take, nan da nan Nihad ta harxuka cikin tsawa tace “Malam da kai nake fa kake kallon wani” Ya kalleta sai kuma ya kara kunnensa gaba yace “Na’am?” Nihad was soo mad at him, xuciyarta ya dinga tafarfasa ta rasa abun ce masa, shi ma kuma bai kuma cewa komai ba sae ma dauke kansa da yayi, ruwan da ta gani cikin roba gun me siyar da fruits din ta fixgo a fusace ta juye masa gaba daya tun daga saman kansa, duk mutanen dake wajen suka kame a inda suke baki bude suna kallonta da mamaki, Tana huci cikin bacin rai tace “Kai din banzaaa kana driver din gidanmu har xan dinga maka magana kana mayar ni mahaukaciya, who do u think u are?? Waye kai??”

 

To gain access to the book, contact me directly via👇🏻

 

07087865788✍🏻

Leave a Reply

Back to top button