Nihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 3

Sponsored Links

💖💖 NIHAAD💖💖

 

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Related Articles

 

~~~

Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga sauran membobi yan gurmin Khaleesats Palace, don gurminsu ya hana in saka sunansu jiya inga ta tsiya, Su Hajiya Aisha Bela, Hajiya Suwaiba, Hajiya Safiyya Usman😂 Hajiya Mardiyya mandy rice😜, Hajiya Sadiya uwar Hanan, Uwar Sa’eed, Hajiya Farida me kayan en gayu, Amzaj, Hajiya Zaarah, Wata ana ce mata me kayi nayi, Hajiya Aisha Macika, Hajiya Billy, Uwar Habee, har dai da wata me gawayin dare, duk na gaisheku kyauta… Sauran da basu ga sunansu ba a tsakiyar rubutu xa su gani😁

 

8months earlier…

 

Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da handkerchief din hannunsa, karamar waya ya fiddo aljihunsa yana duba agogo dake nuni da karfe biyar da rabi, ya juya ya kalli mai gadi dake xaune gefensa da radionsa a hannu, xai yi magana aka danna horn, da sauri mai gadin ya ajiye radion ya mike ya isa bakin gate din gidan ya bude, wata rantsantsiyar mota ce ta shigo compound din, mutumin dake xaune ya bi motar da ido har ta isa kantamemen space da aka tanadar don parking a compound din, mai gadin ya dawo bayan ya maida gate din ya rufe yace “Bari in sanar masa kana ta jira kar ya shige ciki kuma” Daga haka ya nufi parking lot din ya jira har dattijon dake cikin motar ya sauko yana gyara babban rigar jikinsa, da ladabi me gadin ya risina yace “Barka da isowa Alhaji” Alhaji Ibrahim yace “Yauwa Aminu… ” Mai gadin yace “Alhaji dama Habibu ya taho da baƙon tun daxu, shi har ya ma tafi yace yau xai koma, baƙon kuma gashi can yana jiranka tun karfe biyu” Alhaji Ibrahim ya kulle motar tasa yace “Ohk, to ya karaso” Mai gadi ya koma gun mutumin dake xaune saman farar kujera da sauri yace “Kaje nayi masa magana” Tashi mutumin yayi ya nufi parking space din, yana isa ya duka har kasa yana kallon Alhaji Ibrahim yace “Barka da yamma Alhaji” Alhaji Ibrahim na kallonsa yace “Yauwa kai ne wanda Habibun ya kawo kenan?” Mutumin yace “Eh ni ne” Alhaji yace “Ya sunanka?” Mutumin ya sauke idonsa daga kallonsa yace “Sunana Ibrahim” Alhaji Ibrahim ya jinjina kai yace “To madallah, amma ya ku ke da Habibun?” Mutumin yace “Garinmu daya da shi, ga gidanmu ga gidansu, babana aminin mahaifinsa ne” Alhaji Ibrahim yace “To ba laifi, ai har garin naku naje watanni da suka wuce” Shi dai mutumin bai ce komai ba, Alhaji Ibrahim yace “Shkkn babu damuwa, amma kayi karatu ne?” Mutumin ya girgiza kai yace “Aa iyakata sakandari, shi ma ban zana waec ba” Alhaji Ibrahim ya daga kafada yace “Ohk, xuwa kake ganin xaka dinga yi kullum ko kuma yaya tsarin naka yake?” yayi kasa da kai yace “Duk yanda ka tsara haka xa ayi Alhaji” Alhaji Ibrahim yace “Kaje dai gobe da safe ka dawo, ni yanxu xan shiga ciki in huta ne, dawowata daga aiki kenan…” yace “Toh nagode kwarai Alhaji, Allah ya kara girma” Tuni Alhaji Ibrahim ya nufi main entrance din shiga gidan nasa, ya mike ya bi sa da kallo, sannan ya kalli building din gidan wanda duplex ce gari guda, juyawa yayi ya koma gun mai gadi, mai gadin na ganinsa yace “Ya ake ciki?” yace “Yace in dawo da safe” Mai gadi yace “Ahaf ai ka ma samu, tunda ta hannun Habibu ka biyo, ai Alhaji sun fi shekara goma sha biyar da Habibu, har kauyensu ya je daurin aurensa kwanaki, in dai baka da rawan kai sannan uwa uba ace kana da nutsuwa gun aikinka to wllh tuni Alhaji xai ja ka jiki ka xama kamar d’an gida, ba ga mu ba duk mun dawo kamar yan gidan banda dai ba halinsu daya da wasu daga ahalin gidan nasa ba, to ya sunan naka?” Mutumin yace “Sunana Ibrahim” Mai gadi ya rufe baki yace “Yo ai sunan Alhajin kenan” yace “Allah sarki, Sai goben in sha Allah, xan tafi ynxu” Mai gadi yace “Allah ya kai mu” Gate ya nufa ya fita daga gidan. Alhaji Ibrahim ne xaune parlonsa, daga gefensa matarsa kuma amaryarsa Hajiya Maryam, Wasu yan mata ne biyu xaune daga kasa saman lallausan carpet dake malale parlon, Hajiya Maryam tace “Ayi hakuri Alhaji in sha Allah hakan ma baxai sake faruwa ba, ita ma Hajiya nasan bata fahimce su bane, amma xa su je su bata hakuri” Alhaji Ibrahim na kallon yan matan yace “Ku tashi ku bani waje” Duk a tare suka ce kayi hakuri Abba, yace “Ku fita nace…” Mikewa suka yi a tare suka fita daga parlon, daya daga cikin yan matan tace “Gaskiya ni ki daina ja min Nihad, ko me kika yi sai a hada mu a mana fada, da na sani da ban biki ba jiya, haba don Allah” Tsaki er uwar tayi mata ta bi wani corridor tayi gaba abunta irin ko damunta abun bai yi ba. Wata mata ce da baxata haura hamsin da bakwai ba xaune wani lafiyayyen parlor da ba a cika da kaya masu hayaniya ba, cike da ɓacin rai tace “Toh banda ma fitina da neman magana irin naku dole ne sai kun je? Me yasa baxa ku xauna inda Allah ya ijiye ku ba, maganinku kenan” Nihad tace “Ae wllh daga yau ko Abban ne yace mu je ni dai sai dai in fita inyi using opportunity din in xaga gari in sha iska in dawo abu na, i don’t care… baxan sake xuwa ba gaskiya” tana kai wa nan ta mike ta dau wayarta dake caji ta fita daga parlon, Hajiya Sumayyah tace “Atoh dai, da ya fi maku, don dama magana ta ce kawai bakwa ji banda haka na hanaku xuwa tun ba yau ba” Ita dai er uwar Nihad na kwance saman kujera bata ce komai ba, Hajiya Sumayyah ta bude kofar bedroom dinta ta shiga ta kulle. Washegari asabar kasancewar yan matan gidan basu da lectures duk suka yi shirin tafiya islamiyya amma banda Nihad dake kwance parlon step mum dinta tana aikin danna waya, Hajiya Sumayyah da suke kira da Umma da tace “Ke Nihad kina kallon lkci kuwa, ko baxa ki islamiyyan bane yau ma?” Nihad tace “Umma sai gobe i have something important to do” Umma tace “To ita Nihal ma cewa tayi ba xata ba?” Bata rufe baki ba sai ga Nihal ta shigo har ta gama shiryawa, Umma ta kalli Nihad bata dae ce komai ba ta ci gaba da abinda take, Nihal tace “Hope u are been cautious of time Nihad?” Tashi Nihad tayi ta fita daga parlon tana cewa “Ni sai gobe” Mai gadi ne tsaye tare da mutumin da ya xo jiya, bayan sun gaisa mai gadin yace “Yanxu xaka ga Alhajin ya fito xai tafi gun motsa jiki, don ma yau bai fito da wuri ba, amma dai bari in sanar masu a ciki kar kuma ka yi ta jira haka babu dadi” mutumin yace “To nagode” Xaunawa yayi kan farar kujera yana bin compound din da kallo don ya kayatu da kyawawan shukoki na flowers har ma da artificial flowers, daga can wani gefe wani karamin water fall ne me ban sha’awa ruwa na ta xuba ga artificial crocodiles da kifaye a ciki, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo yace “Ka ga wancan yar barandar?” ya kalli inda yake nuna masa yace “Eh na gani” Mai gadin yace “Toh kaje can kayi jiran alhajin, akwai kujeru ma a wajen” Tashi yayi ya tafi wajen yana bin ko ina da kallo, bayan kujeru masu kyau har da carpet grass malale a kasa daga gefe, ga artificial flowers da ya kawata wajen, ya xauna saman daya daga kujerun wajen surveying everywhere with his eyes, bayan kusan minti sha biyar aka bude kofar parlon, tsaye tayi tana kallonsa daga sama har kasa a bit flabbergasted, ya kalleta yayi kasa da kai yace “Ina kwana” tace “Wa kake nema Malam? Daga ina haka?” Yace “Mai gidan nake jira” ta fi minti daya tana masa kallon sama har kasa, ta ma rasa me xata ce, sai kuma ta sauka kasa xuwa compound din ta tafi gun mai gadi da sauri, yana gaisheta ta ki amsawa tace “Aminu waye wancan aka bar sa xaune a kofar shiga parlor? Waye wannan?” Yace “Ranki shi dade baƙon Alhaji ne wanda Habibu ya kawo jiya, shine sabon….” Ta gwalo ido ta dakatar da shi da sauri tace “Haba Aminu, Haba Aminu, yanxu kai rashin hankalin naka ya kai haka, a tunaninka ya kamata a bar sa yaje har can ya jira Abbanmu, privacy din mu ne can din fa? ga dai kujeru a compound amma har sai yaje balcony kamar xai shiga parlor, a ina aka ta6a haka?” Aminu yayi kasa da murya yace “Wannan gaskiya ne Hajiya, ayi hakuri anyi kuskure kam, ayi hakuri” Tace “To tun wuri ka tafi kace ya dawo nan kusa da kai ya xauna ya jira Abban” Aminu yace “Toh Hajiya” tabe baki tace “Ni dama tambayarka xanyi hope jiya baku mance feeding din tsuntsaye na ba?” Ya washe baki yace “Haba dai Hajiya, ai kullum safe rana da dare sai Saminu ya basu, yau ma da asuba ina kallo yaje ya xuba masu” tace “Yauwa toh nagode, bari in je in duba su, shekaranjiya da jiya duk bama nan ban gansu ba” Yace “Da yake sai dare ku ka dawo jiya din ma” Tace “Eh fa” daga haka ta wuce ta xaga ta inda tsuntsayen suke a backyard din gidan wanda nan dinma duk shuke shuke ne, ta fi minti bakwai tana kallon kyawawan tsadaddun birds din nata ko wani breeds a cage dinsu daban, birds din iri hudu ne ko wanne me kyau har kuma da Aku a ciki, ta tafi gun akun da aka yi Seperating da sauran tace “Hello cutie” The bird was only chirping and flying around the little cage alamar he appreciates seeing her, bayan wani lkci ta bar wajen xata koma cikin gida, tsaye taga Abba a balcony bakon nasa kuma ya sauka daga saman kujera ya durkusa kasa yana sauraren Abba, kallonta kawai Abba yake da mamaki yace “Nihad ke baxa ki islamiyyan bane?” Tayi gathering courage tayi kasa da murya tace “Abba assignment nake typing anjima xan yi submitting via….” Abba ya dakatar da ita yace “Why are u skipping Islamiyya this days Nihad, last week ma na ga baki je ba ko, hakan ba dai dai bane dear” Sunkuyar da kanta tayi bayan few seconds ta dago, kallon mutumin dake kallonsu ita da Abba tayi, ta wani daure fuska wondering why he was looking at them, tana tafiya a hankali ta shiga parlor ta kullo kofar, bayan minti shidda aka sake bude kofar, har sannan Abba na tsaye speaking with the man, su uku ne duk sanye da hijab din islamiyya har kasa, Abba ya kallesu, sai kuma yace “Ke xaki yi driving din?” Tace “Eh Abba ga makullin” Amsa yayi ya mika ma mutumin dake durkushe gabansa yace “Ka ajiyesu a makaranta, xan jira ka har ka dawo” Ya amsa da ladabi yace “Toh Alhaji” shi ya fara sauka Balcony din, Autan Mumyn Nihad da ake kira da Sudais yace “Abba is he our new driver” Abba yace “Yes he is sweetheart” Duk suka yi ma Abbansu sallama suka sauka xuwa parking lot, sai da suka tsaya dai dai motar xuwa makarantarsu sannan drivern ya nufi motar shi ma, bayan ya bude duk suka shiga back seat, ya shiga ya tada motar yana warming, shi dai Abba na tsaye balcony har sannan yana kallonsu, Drivern na warming motar yaji ance “Ina kwana” ya daga kai yana kallonta ta madubi da mamaki, sai kuma yace “Ina kwana” Bayan wasu yan mintuna ya ja motar suka bar gidan xuwa islamiyyan nasu with Fadil and Sudais directing him. Parking yayi bakin gate din islamiyyan, Nihal ta bude motar ta sauka su Fadil ma duk suka sauka, bayan ta kulle motar ta kallesa tace “Sai anjima” Yace “Sai anjima Hajiya” Suka shiga makarantar, reverse yayi ya bar wajen har sannan bai daina mamaki ba. Yana isa gidan bayan mai gadi ya bude masa gate ya shiga yayi parking ya kashe motar ya sauka, gun mai gadin ya nufa ya xauna, Mai gadin yace “Inji ka yi kumallo dai?” Driver yace “Aa” Mai gadin yace “Toh bari inyi ma mai aikin gidan magana in amso maka” Daga haka ya nufi backyard din gidan xuwa kofar kitchen dake baya, Drivern dai na xaune yana ta juya makullin motar hannunsa sai ga mai gadin ya dawo da plate din dankali da kwai da kofin shayi, ya amsa yace “Nagode sosai” slice din bread ne biyar a gefen irish din da kwai wanda aka matsa ketchup a gefe shi ma, irish din ya fara ci yana dangwalawa da ketchup din, Mai gadi yace “Amma xaka dinga tafiya ne da daddare ka dawo da safe ko gidan nan xaka tsaya?” ya kallesa yace “A ina xan tsaya a nan din?” Mai gadi yace “Ka ji ka, Yo ai har Habibu ya gama yayinsa a gidan nan kafin Alhaji ya bude masa shagon da ya bude masa na tayoyi a gidan nan yake komai nasa, duk tare muke, ga can boyis kwata, su Saminu da Shafi’u masu gyaran pulawa da sharan tsakar gida da Isiya me wanki da guga ai a nan suke duk” ya dau cup din shayin ya kurba yace “Dakin babba ne?” Mai gadin yayi dariya yace “Wai daki, to har parlor akwai a ginin, sannan dakuna uku ne ko wanne da bandaki, kai har ma da kitchen a nan din” yace “To shikenan” Aminu mai gadi yace “Kai ma kayi xamanka kawai a nan xa ka fi gane kan albashin naka, kaga babu xancen kashe kudin abun hawa xuwa da tafiya sannan xa a ciyar da kai a nan ba sae ka siya komai da neran ka ba, duk abinda yan gida suka ci a nan shi mu ma muke ci” Shi dai bai ce komai ba ya gama cinye irish din tass sannan yace “Toh xan xauna nan din in sha Allah, nagode da kulawa” Ganin ya ajiye plate din Aminu yace “Ya haka, naga baka ci kwan ba? Yanxun nan fa ta soya maka” Ya girgiza kai yace “Bana so” Aminu ya dau plate din yana kokarin cin kwan yace “Allah sarki, wasu haka suke basa cin kwai sai suce yana masu karni, mu dai kam ko danyensa ne baxa mu ki ci sha ba, wa yaƙi dadi” Sai da Aminu ya cinye kwan ya mike yace “Mu je ka ga Boyis kwatan” shi ma ya tashi, yana biye da shi, suka tafi far end of the main building in which stood a Beautiful Chalet, mai gadi ne ya fara shiga, shi ma ya cire takalminsa bakin kofar shiga Chalet din kamar yanda mai gadin yayi sannan ya shiga ciki, ba laifi parlon na da girma, sannan ga kujeru har ma da tv, kaya ne ko ta ina a parlon ga wani tashi da parlon yake, everywhere looks very untidy, isiya ne tsaye parlon yana ta faman guga a ironing board, Aminu yace “Ashe kana ta guga shi yasa baka fito ba, ina Saminu?” Isiya dake ta kallon wanda Mai gadin ya shigo da yace “Suna can daki” Aminu yace “To ga bako, kun samu karuwa a nan, shine ya maye madadin Habibu a gidan nan yanxu” Mutumin ya gaida isiya, isiya ya amsa yana ci gaba da gugansa, Aminu na kallonsa yace “Mu je ka xabi dakin da xaka xauna ko” Isiya yace “Ka dai san dakin dake daga dama ni ne a ciki, na hagu kuma Saminu, wanda ke jikin na hagun Shafi’u ne a ciki” Shi dai kallonsa kawai mutumin yake, Aminu dake kallon Isiya shi ma yace “To ya xa ayi kenan” Saminu da Shafi’u ne suka fito daga dakunan su, Isiya yace “Toh ai parlon ma na da girma sai kawai ya maida nan din wajen kwanansa ko” mutumin ya gyada kai yace “Ohk to shikenan” Isiya yace “Yauwa” Aminu ya kalli su Saminu yace “Sabon direban gidan ne shi ma kuma nan xai xauna, sunansa Ibrahim kun ga sunan Alhaji ne….” Saminu yace “To sannun sa da xuwa” Tuni ya juya ya fita daga parlon ya bar mai gadi, Aminu na ganin haka ya bi bayansa da sauri… Suna tafe mai gadi yace “Amma kasan da nauyi mu dinga kiran sunan Alhaji gatsau, baka da wani sunan ko inkiya da xa mu iya dinga kiranka da?” kallonsa yayi yace “Khalil Mahaifiyata ke kirana” Aminu yace “Allah sarki, to ai mu ma sai mu ce khalil din, suna me dadi kamar na larabawa wllh” Bayan sun koma mazaunin mai gadi sun zauna, Mai gadin ya kallesa yace “Yanxu kawai kayayyakin ka xaka je gida ka debo, aikin naka ma fa ba wani me wahala bane, kaga yan makaranta motar makaranta ce ke xuwa daukansu da safe, Yan matan nan biyu kuma daya a zaria ma take karatu, dayar ce ke karatu a nan, ita warce ke karatu a nan din sai ta kai karfe biyu ma bata tafi makarantar ba, Alhaji kadai xaka ajiye karfe tara gun aikinsa, ban ki ba dae Nihad don gantali gareta kamar ta ci kafar kare, kuma sae ta fake da makaranta, a takaice dai kai Alhaji wajen aikinsa da safe shine ainahin aikinka sauran duk masu sauki ne” Khalil da har ya gaji da surutun Aminu ya gyada masa kai kawai, for the next 30mins Aminu bai yi shiru ba, Khalil har ya daina tanka masa don ya ma yi nisa a tunanin da yake, dai dai nan Alhaji ya fito, Mai gadi yayi kasa da murya yace “Da alama yau baxai je motsa jikin ba kenan tunda har gashi sha daya ta yi” Sai kuma ya mike, Khalil ma ya mike yana kallon Alhajin a bit surprised at who is standing next to him, Khalil yayi kasa da murya yace “Yan makarantar har sun taso ne?” Mai gadi ya kalli Khalil da sauri yace “Ka je yana maka magana ne” Khalill ya nufi Alhajin da hanzari, Alhaji yace “Mu je xaka ajiye mu 3 streets away from this” Khalil yace “Toh” Motar da yayi parking bayan ya ajiye yan makaranta ya nufa, Abba yace “Wancan motar ba wannan ba” Khalil ya tafi gun motar da Abba ya nuna masa, Bayan sun fita gidan Mai gadi ya kulle gate, driving Khalil yake a hankali, lkci lkci yake kallon Nihad dake zaune bayan mota da Abbanta tana danna wayarta. Ganin Khalil a layin da Alhajin yace ya ajiye su, Alhaji Ibrahim yayi mamaki sosai, don shi ya ma mance ba Habibu bane ke jan sa, bai yi masa kwatancen inda xai kai su ba ya dai ce masa 3 streets…. Ganin yayi slow down Alhaji Ibrahim yace “Noo ci gaba da tafiya, gida na uku xaka tsaya” Dai dai gidan Khalil yayi parking, Alhaji yace “Kayi horn kawai” yana yin horn mai gadi ya leko ganin motar ya koma ya bude gate din da sauri, Khalil ya shiga ciki ya samu waje yayi parking , Alhaji Ibrahim yace “Maa sha Allah, kayi jirana har in fito” Khalil yace “To Alhaji” Nihad ta sauka ta daya side din wayarta kare a kunnenta, Alhaji Ibrahim ya sauka ya nufi entrance din gidan, Ta side mirror Khalil ke kallonta amma sai yaga kamar wannan fara ce ai, Nihad dake ta xagaye da waya a kunnenta da sunan she is making call, whereas she is not kawai bata son Abba yace su shiga ciki tare ne, tana ganin Abban nata ya shiga gidan ta turo baki ta tafi can karkashin wani Thatch dake compound din wanda aim dinsa wajen shan iska, xaunawa tayi a wajen. Khalil ya sauka daga cikin motar ya tafi gun mai gadin gidan suka gaisa, Mai gadin na kallonsa yace “Ko kai ne madadin Habibu” Khalil yace “Eh nine” Mai gadin yace “Maa sha Allah” Xaunawa khalil yayi yana bin compound din da kallo, wanda shi ma yayi haduwan karshe, ya d’an juya ya kalli Side din da Nihad take, she was so engrossed with what she is doing on her phone….

U can contact me directly via👇🏻

07087865788✍🏻

Leave a Reply

Back to top button