Matan Ko Mazan 6
đ« MATAN?? Ko MAZAN??đ«
âđ»M SHAKUR
BONUSđ
EPISODE 6
Dum dum dum!! Hadiza taji kalman sakin ya daki zuciyanta kaman saukan aradu cus ko amafarki, like ko amafarki dai wannan bata taba tunanin Nura zai taba bude baki yace yasake ta ba, duk yanda takeson tai kokarin controlling yanda hannunta ke rawa kasawa tayi wani kalan reflex rawa hannayenta suka fara tama kasa magana sai idanunta data kwalaloo kaman zasu fadi akasa tana kallon Nura daya hade rai kaman wanda baitaba murmushi ba aduniya ya nuna mata kofa yace âget out of my house, out!â Yadaka mata tsawan da saida ta firgita, ganin taki motsi yasa yayi inda take azuciye yasa hannunshi yakama hannunta datake rike da key motanta yawani jata dan ranshi yabaci ainun ta daukoma Mamanshi da kanwarshi Police haba nooo enough! Dasauri Hadiza tashiga cewa. âNuri, Nuri, Nuriâ bude kofa yayi yafito da ita har zuwa wajen motan ta yace âget out of my houseâ dasauri tace âNuri ni zaka cewa kasaka are u for real? Wait mafarki nake? Nine zaka saka because of your family now can u see why I was against zuwan family miji cause all they bring into your home is chaos? Nuri ni Hadiza zaka saka? Ni zaka kora from my homeâ? Wani kallo yamata yace âyou are dumb, foolish and you are crazy Hadiza, bakin halinki yasa I donât have any feelings left for you azuciyana, duk matan da have no regard towards my mother can never have space in my life or home dan haka get out, go and do your feminism awani waje not inda uwata takeâ yana maganan yawuce ciki ya maida kofa yarufe da key yabarshi ta yanda she canât come in, Hadiza was completely in a state of shock ita Nuri zai saka, ita Hadiza, wajen kofan tayi tadaga hannu zata buga saikuma tace ai sai su Meena su mata dariya damai gadi, tama zubar da ajinta kenan rokonshi zatayi yabude mata kofa kome? Yasaketa tayi tafiyanta mana, deep down zuciyanta cike yake fal da damuwa sai tambayan kanta take ita Nuri yasaka just now? Ita Hadizan nan saki fa? Saki dai datakeji anama wasu matan itama yau anmata so yanzu sheâs a divorcee? Ta tambayi kanta saikuma ta juya tashiga motanta tazauna takai awa daya ahaka dataga dai da gaskene yasaketa ta tada mota ta tafi yanzu inama zataje ta tambayi kanta taje gidan kawarta ne? Ina zata? Parking tayi cikin premises na shagonta tai dialing number yayanta ringing daya ta daga kafin Anty Jamila tai magana Hadiza tace âAnty kinga yasakeni koâ? Shiru Anty Jamila tayi irin shirun son gane abinda tayi, saikuma tace âai yamiki kyau gashinan jikinki yayi sanyi hankalinki yafara dawowaâ cikeda karfin hali da tsiwa tace âjikin wa yayi sanyi? Da ace namai laifi ne sai jikina yayi sanyi? Ni Nuri zai saka sabida yan uwanshi wlh zai gane heâs mistaken idan yana tunanin yasakeni kuma na sakun mai wlh karya yake yacimini mutunci haka yakoreni wlâŠ..â takasa karasa maganan sabida kukan daya taso mata tai shiru Anty Jamila tace âkinason mijinki Hadiza, kina mutuwan son mijinki amman bakin hali da alâadan yahudu da nasara yasa kin zama shaidaniya, shine your eye and accept keda shi are not one amman kin dage ke da shi are one kin dage, kin dage kaman bakar mayya accept cewa ba komi ne arayuwan nan must always go your way ba, idan haukan dakikeyi ko feminism din dakikeyi na solving matsala go and solve this one mana da feminism din look at abinda shegen feminism din yasa kika girba saki and this is just the beginning saikin rasa mijinki sannan zaki gane kene da kanki kika saka kanki a wahala, yanzu bama wannan ba Meya hadakuâ?
Dudda akule take ahaka tabawa Anty Jamila labarin komi salati Anty Jamila tayi tace âwlh da niyyata muna gama maganan nan nakira Nura nabashi hakuri amman wlh, wlh bazan kiraba saidai Mama takirashi, Hadiza uwarsa kika zaga? Wai aljanu gareki ne koko kin fara having mental disorder ne? Konine bazan tsaya wata tazagi Mama agabana ba sai inda karfina yakare, Meena tamin daidai ke baki girmama nagaba dake ba tayaya nakasa dake zasu girmama ki? Kadan kika gani Allah yabâŠâŠ.â Ihu Hadiza tayi tace âni dama nasan u will never support me whatâs wrong with abinda nakeyi? I am just going with the trend? A home belong to the woman so she should be the one to call the shot, Anty Jamila fisabilillahi da aurena agidana amman bazan fadi ajiba banda say, haka akeyi eh? Nasa yar aiki tamin girki yahanata, yasa yan uwanshi suzo bazai tambayi permission dina ba ita Hajiyan haka aka mata eh? Ta kawai shigo gidana tahanani sakat ana cewa batada lafiya kinga abincin danaga tana zakalkala aciki ne tana zuba surutu? Tanaji aka sakeni aka korani bata fito tasa baki ba thatâs shows plan work ne, All I ever yearn for and I ever do was to be incharge of my home, kome zai faru inhar it has to do with gidana nizan fadi ayi ba Nura ba, duk fadan dazanyi dashi akan abinne, idan zaimin haka nima zanmai komi yanada abokai yasan haka akeyi a Abuja har kunya nake kar kawayena suzo suga abinda ke faruwa agidana su bahaka sukeyi agidan su baâ dan ijiyan zuciya Anty Jamila tayi tace âHadiza baka forcing control da ownership, Nura zai iya bari kina calling shots agidanshi idan yaso amman means dakike bi is not right, tell me one thing dakike yima mijinki tell me?â Cikeda bakin takaici kaman ta make Anty Nafisa ganin taki fahimtan ta tace âAnty Nafisa pls pls understand nan ba kano bane this is FCT for crying out load, city of wealth, a Abuja u donât have to do anything for mijinki as a wife, a woman is a queen dayakamata tanada maâaikata which I have, su yakamata suyi komi, in this aspect banyi any laifi ba nagaya miki Iâm just going with the trend zamanin damuke kenan, I donât have to cook, sweep, take care of the kids or anything akwai masuyin aikin abiyasu duk wata Anty Nafisa nan ba kano bane kigane thereâs nothing extraordinary anan abinda ke faruwa kenan wlhâ hmmm! Anty Nafisa tasauke ijiyan zuciya dan lamarin Hadiza mai girma ne tace âHadiza kinyi nisa are you saying yanzu kuka koma Italy alâadan Italians zaki dauka kicema mijinki dan Nigeria dole sai yayi? When will u understand mijinki bazamfare ne girman kano, Sanaâa ce takawoshi Abuja, Nura is educated but rayuwan bokon nan da wayewa tamasu kudi dakikeso shi baya gabanshi, ace yana aurenki bazaki bashi ruwa dakanki yasha ba menenen ma amfanin ki? Wai kuma ahaka bakimai komi kuma kinaso shi yamiki komi, kome kikace yace Naam ko tunda gaki mamallakiyan Nura sannu Hadiza mai fadi aji, yanzu kina ina?â âShago naâ cikeda isgilanci Anty Jamila tace âmaisa bakije gidan kawayen naki ba toâ? Ahankali tace âai abin kunya ne suji abinda yasameni, that means I donât even have any power or influence agidana inhar mijina zai koreni daga gidana sabida yan uwanshi wlh wlh abin nan yamini ciwo Anty Jamila, you have no idea yanda matan Abuja are powerful agidan su amman ni Nura bazai bari nai enjoying that luxury ba, kuma wlh wlh wlh zai saniâ anatse Anty Jamila tace âHadiza keba yarinya bace youâre 32, ke kinsan abinda kike bai dace ba, uwarmiji uwarkice, ita tahaifo abinda kikeso and nurture him, groom him into the man heâs today, miji ba abin wasa bane dazaki dinga experiment naki akanshi, this is just 1saki Nura yabaki, idan ba u wanna loose him for ever ba ki gyara, all it takes is apology, kije kibama mahaifiyar shi hakuri kibashi hakuri ki gyara the way kike abubuwa agidan ki before it will be too late for u kina jina? Idan zaki dawo kano ne kidawo, zandai gayama Mama nasan zata kirashi amman ni Allah yasan bazan iya kiranshi ba take care Allah kuma ya ganar dake kafin lokaci yakure mikiâ.
Katse wayan tayi tadade zaune amota saida aka tafi magrib sannan tafito ta tafi sama tabude shagon tashiga tamaida tarufe tawuce sama office nata ta shiga kwanciya tayi kan dogon kujeranta tayi shiru tanada kudin kama hotel ta kwana abinta amman takasa, takasa zuwa wajen kawayenta kada amata dariya tagama cika baki, da kyar ta lallaba taje tai salla wasa wasa har 12 nadare takasa bacci sai juye juye take yanzu shikenan Nura yasaketa ya koreta daga gidanta shikenan bata da gata? Itane yau da kwana a shago? Hakanan kawai saitaji tana kewan yaranta koba komi kobadan suzo wajenta ba amman muryansu da hayaniyansu datakeji da Ummi is something sai kawai taji tayi kewansu sosai din nan, lema lema dataji akan fuskanta yasa takai hannunta dasauri ta taba ashe kuka takeyi dasauri ta tashi zaune tace âno feminist donât cry, with or without Nura I can create my world why am I sad? Dan yace yasakeni, yakoreni daga gidanshi? Why nakejin badadi nakasa bacci 9 nayi bacci jibi lokaci yanzu nakasa why?, Yanzu Nura harya isa yacusamin bakin ciki? Then menene amfanin the belief I stand for? The whole feminism an fito dashi ne dan anunama mata they donât need men or approval na men to survive on this world, all she need is herselfâ share fuskanta tayi tass tace âNura kayi kadan kasamin kunciâ ijiyan zuciya tasauke tafara fadama kanta words of affirmation. âIâm Hadiza diyar Tijjani, Iâm strong, independent and beautiful dudda tsinanniyar yarinyar nan tamin scars din yakushi yanzu awuyana, Iâm smart, unapologetic, resilient and bold, I donât need a man ko anybody to be happy, Hadiza is enough for kanta, a man canât downgrade or belittle Hadiza, Iâm as tall as the mountain ,as hard as rock, as thick as thicker, no one can break Hadiza saidai ni nai breaking, Iâm unbreakable, Iâm happy, Iâm happy, yesss I am happy!!â Tafadi ma kanta tana murmushi tana dukan kirjinta saikuma wasu munafukan hawaye suka kara fitowa daga gefen idanunta tadaura hannunta akan fuskanta tafashe da kuka sosai tace âna shiga uku why am I sad? Nura ni zaka saka awanan sad mode din? Ni Hadiza zakama saki Nura? Ni kanwarka zatama duka sannan kayi throwing dina out kahadan da saki jibeni a shago zan kwana? Ni Nura?? Wlh saina gwada maka kayi da diyar halas wlh kuwaâ wani shegen kunci takeji the state datake ciki ita kanta batasan Nura is this important to her ba sosai take sonshi but bata saniba, sheâs extremely sad takasa bacci, kaman ta hadiye zuciya takeji tamutu.
Wajajen 3:30AM Hajiya ta tashi daga bacci, Meena tagani agefenta dasu Amal duk suna bacci komi daya faru dazu dawo mata yayi sauka tayi daga gadon da dafa bango tafito dakin Nura taje sallama tayi ahankali ga mamakinta bude kofan yayi yana sanye da jallabiya hannunshi rikeda charbi dasauri yariketa yace âHajiya kin tashiâ shigar da ita dakin yayi yamaida kofa yarufe akan couch na dakin ya zaunar da ita shikuma yazauna agabanta akasa yakama hannunta yarike ahankali yace âHajiya kiyakuri sabida ni Hadiza tamiki rashin kunya yauâ girgixamai kai tayi kafin tazare hannunta daga nashi daya rike ta tallabo fuskanshi cikeda tsantsan soyayya irin na dâa da mahaifi tace âmaisa baka taba sanar dani abinda ke faruwa agidanka ba? Nura yaushe Hadiza takoma haka? Kamata wani abu neâ? Duk yanda yaso ya daure kasawa yayi ahankali yadaura fuskanshi sanan cinyan Hajiya murya chan kasa yace âHajiya nagaji Iâm tired, sometimes I feel maisa namayi aure? Da auren nan gwara rashin sa but then nakalli yarana Aman and Amal sainace Alhamdulillah Allah has already blessed me with the most beautiful kids aduniyan nanâ yayi shiru yace âHajiya I donât have peace of mind idan nabar gidan nan kaman kada nadawo tunanin yarana kesa nadawo, babu one single thing da Hadiza kemin amatsayinta na matana and bantaba mata wani abuba, Hajiya sometime ina zama na gayama kaina indai this is wat comes out of auren educated mace to gwara auren gidahuma jahila dazata maka biyayya and be a wife for you cus Hadiza is a wife for herself not for me, tanada masters in business Administration tanada business kudin sun shiga hannunta, yanzu taga am useless koda ace yau zan rabu da ita tanada future she has money, and money is everything idan kanada kudi baka bukatar komi kuma zata iya kula da kanta, everything data mini I tolerated it dudda sheâs 32 but kallon mahaukacin yarinya nake mata Hajiya she insulted you today tayi magana dake kaman ita ta haifeki saisa nace tabarmini gida taje na sake ta saki dayaâ dasauri Hajiya ta kalleshi dago kanshi yayi idanunshi sunyi jaaa sosai yace âHajiya kin sanni sama da kowa kinsan inada hakuri kawaici juriya dakuma yafiya yaune rana na farko dazan rokeki Al farma kada kice nadawo da ita please I want a break from this auren mu besides Iâve grown feelings for someone kuma inaso naje garinsu na nemi aurentaâ Hajiya na kallon fuskanshi tace âUmmi?â Dasauri yace âtayaya kika sani Hajiyaâ? Dan murmushi tayi tace âsabida nina haifekaâ dan shiru yayi chan yace âHajiya nakamu da son Ummi sosai, tagayamin ta taba aure tama haihuâŠâŠâ yabama Hajiya labarin yace âHajiya inason Ummi sabida some odd dalilaiâ ahankali yace âHajiya nakamu da son Ummi sabida duk wani abu da Hadiza kedashi ita batada shiâ yadan sauke ijiyan zuciya yace âinason ta sabida sheâs not educated, sabida batada kudi, sabida sheâs not independent, sabida sheâs innocent, sabida sheâs polite, sabida she respects me, sabida she pay attention to me, sabida tanason yara na, sabida she feed me, sabida tana magana dani calmly her voice is so soothing to my heart, I love her sabida sheâs weak, fragile, sabida sheâs a soft woman not strong woman, ina sonta sabida matace da idan na aureta nine zan zama ragamar rayuwanta and she will let me be the husband and above all nayi istikhara akanta naji azuciyana na natsu da ita, Hajiya inason na aureta amman saikin bani go aheadâ murmushi Hajiya tayi tana kallonshi hannunta takai ta share dan guntun hawayen daya fito daga gefen idanunshi tace âna amince kaje kauyensu ka nemi aurenta amman da sharadin kadawo da Hadizaâ dasauri yakalli Hajiya, murmushi tamai tace âNura no marraige is perfect, kowani aure da crisis din dake ciki har Ummin idan ka aureta you guys will have ur differences and issues but what makes Marraige works and last is the ability to work on your issues understand each other better, forgiveness and moving on without holding grudge, kaga all this fadan yanasa akara fahimtan juna, kuskuren Hadiza shine tunanin datake itada mijinta daidai kuke wanda bahaka bane u are the leader and sheâs your subordinate dole ta bika, but Iâm sure yanzu she learnt her lesson sabida duk ranan da mace zata kwana awani waje ta dalilin saki ranan bata iya bacci mai kyau ko itace da laifi ko ba itace da laifi ba, saki babban abune, saki is powerful, duk randa aka yishi alarshin Allah na girgiza, duk randa akai saki shaidan na partyâs jin dadi, duk inda Hadiza take yanzu tana cikin damuwa sosai, kayakuri kadawo da ita kodan yaranku, kada ka manta Annabi yace akama mace saki daya yakamata tana zaune agidanta ne kacigaba da bata ci da sha har zuwa ka maidata dan haka bring her back karka sabama koyarwan addinin muâ dan ijiyan zuciya yasauke yace âdazu Mamanta takirani tabani hakuri I just told her najiâ dasauri tace âyauwa ka kyauta, yaushe zakaje neman auren Ummin? Ka sanar da ita kana sonta?â Girgizama Hajiya kai yayi yace âsaina kaita kauyensu zan fada mata inaso sai mun koma
Munga Dr gobe naji mai zaice game da ke, kafin nasan ranan dazan kaitaâ shiru Hajiya tayi ita bataso tacigaba da zama agidan nan ahankali tace âkoma me ake ciki gobe daga asibiti ka kaini gidan kanin marigayi mahaifinku daganan suma ai zasu dinga iya kaini asibitin ballama nasan magani zaa bani ace nadawo bayan one week, koma menene inason jibi ka maida Ummi gida ka sanar da yan uwanta banson yanda soyayyanta ya kullu aranka tana zama karkashinka shaidan is real kana jina kaje garinsu jibi ayi magana muji me ake ciki idan da hali zasu baka sai adaura auren achan ma sai kaje tareda kanin Babanka da wasu abokan naka, da Meena kuma Ubangiji Allah yasa albarka ni kaina na yaba da natsuwan yarinyar kuma ta kwanta mini arai.
Ba karamin fada mahaifiyar Hadiza tamataba kuma tace tabama Hajiya hakuri da Nura, washe gari ba dudda idanunta a kone suke amman kana ganinta tai zuru zuru sanda Mamanta tagaya mata Nura yace takoma har ijiyan zuciya tasauke aboye baro shagon tayi wajajen 8.
Around 9 takai gidansu tana parking motanta Nura na fitowa daga gidan rike da Hajiya da Meena suna hira suna dariya yayi wani irin kyau yana sanye da soft material milk yasa sunglasses a idanunshi, hada ido tayi dasu dasauri ta dauke kai haderai tayi tamau ta taho saida tazo dab dasu tace âsannu ya jikiâ bata jira amsan Hajiya ba tawuce ciki tabude kofa ta shiga ta bugo kofan Nura yajuya yakalli kofan Hajiya tace âmuje kaga 10 fa likita zai ganmuâ wucewa sukayi suka tafi.
Tunda Ummi taga Hadiza tadawo ta shiga ta natsu tana gama aikinta ta tafi bayan gida a garden ta zauna akan kujeran lilon su Amal da wayanta a hannu tana buga game, ringing wayanta yayi dasauri ta kalla batasan number ba amman tadauka takai kunnenta ahankali tace âhelloâ anatse Nura yace âHajiya Ummiâ batasan lokacin datace âlaaaaa Alhaji yakuri bansan kai bane, ina yini, Ya Hajiya kunkai asibitin? Wani abu kake bukata nayi?â Duk ta jero mishi tambayan atare, cikin kwantacciyan murya yace âHajiya natare da Dr, tagama ganinshi kuma zan kaita chan Gwarimpa anan zata cigaba da zama gidan kannin Abba naâ âokayâ Ummi tafadi but zaka iyajin nuna jin dadin ta a muryanta, ahankali yace âkinada katinki na kasa? National identity card?â Dasauri tace âeh inada shiâ shiru yasakeyi yace âkituramin hoton shi ta whatsapp sannan ki shirya kayanki gobe zan maidaki kauyenku Adamawa ko?â Maganan yazomata abazata dasauri tace âehâ saikuma chan asanyaye tace âwani laifi nayiâ? Ahankali yace âkin manta alkawarin dana miki zan kaiki kiga Gwaggon ki shine zan cikaâ murmushi tayi taushi tace âAllah yasaka maka da alkhairiâ murmusawa yayi shima yace âkinga kayanki cikin kayan danasa gateman yakawo miki?â Dasauri tace ânaga slippers dina na dauka, naga wasu kaya duk sainakai store na ijiyeâ cikeda so yace ânakine akwai wani black abaya mai stones ahannunshi shinakeso kisaka gobe kinjiâ gyadamai kai tayi kaman yana gabanta tace âto nagode Alhajiâ shiru yayi bai sake cewa komiba tagaji da shirun tace âhelloâ kaman daga sama yace âzaki aureni Ummi?.
Matan Abuja!
Matan Abuja!!
Matan Abuja!!!
Haaaaa, HADIZA has been making countless reference daku, the women of Abuja come close are you all the way Hadiza ke suffanta ku? Ance idan miya yayi yaji??? Ai dole yaji ne zai saka miyan yaji ko??
So kunada dogon explanation you guys need to come cleanđ€Ł
But then again all I see in Hadiza is so much soyayya for her man but this stupid mentality nata is leading her astray, why must you be the one to call shots agidan mijinki? To shi mijin is there for what? Name ko fame????
Hello Ladies both married and unmarried are you learning one or two lessons from this novel nawa???
But again kuma letâs not be sentimental, mu kalli Hadiza da kyau, all she ever wanted is power which is normal akwai dominating mata dama, itama tanason kawayenta susan tana juya mijinta but maganan yayanta is valid sabida kunje Italy saikice saikin maida mijinki Italian???
Share your 2cents ladies and gentlemen â€ïž
See you asabarđ