M SHAKUR NovelsMatan Ko Mazan Hausa Novel

Matan Ko Mazan 4

Sponsored Links

 

💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

 

 

✍🏻M SHAKUR

 

 

Novel din nan is FREE bana kudi bane.

Chat me up don saki a group

 

wa.me/+2347012181461

 

 

EPISODE 4️⃣

Wuraren 7:30 Hadiza tashigo gidan gabaki daya ranta amugun bace yake, Aman da Amal sai Ummi ne afalo dukansu ukun suna zaune kan dogon kujera suna kallon videos letters sound for Amal dudda Ummi bawani boko tayiba iya kanta JS3 but ta iya all this basic things na school shima sound din dan bata iyabane zamanin su da ABCD sukai karatu ba da sounds ba saisa suke koya tanan youtube yanda Amal ke koya itama haka take koya dan sabida koya musu, jin an bude kofa kai tsaye ba sallama yasa suka jujjuyo dukansu hada idanu Ummi tayi da Hadiza dake mata wani kalan kallo dayasa dasauri tamike tsaye daga kan kujeran ta duka kasa danta gane kallon me take mata cike da girmamawa tace “barka da dawowa Anty, ina yini” Hadiza da dama ta shigo da mugun bacin rai dan tun kiran da Nura yamata ashago ranta yake abace tace “ke ban gayamiki koda wasa kada duwawunki yazauna akan kujerun gidana ba, ke kinada darajan dazaki zauna inda nake zama ne yar aiki dake, ubanwa yagaya miki yan aiki nada matsayin zama akujerun gida” Ummi da kanta ke kasa ahankali tace “kiyakuri Anty mancewa nayi Amal muke koyama karatu” baki Hadiza tabude zatai magana daga Aman da Amal da duk suka tashi suna kallon Maman nasu Aman yace “stop shouting at Anty Ummi Mommy” dasauri takalli yaron ta ballamai harara, turo baki Aman yayi yace “u are always fighting and screaming Mommy our school teacher tace anger causes sickness” hararanshi Hadiza tayi bata tace “nakusan fasa bakin nan naka mara kunya kawai” turo baki yayi dan haushin Mommy shi yakeji sosai sabida yanda koda yaushe fada takema Anty Ummi su, bata sake cewa komiba tun maganan Aman tacire heels din dake kafanta awajen tawuce dinning straight taja kujera ta zauna tana sauke jakanta kan table din tace “idan kinga dama kizo kibani abinci” tashi Ummi tayi da sauri ta taho dinning din Aman kuma yakoma kan kujera yayi zamanshi yadauki IPad itakuma Amal tayi hanyar dinning din cikeda shagwaba tace “Mummy babuuuu, ki goyani zanyi bacci” cikeda masifa Hadiza ta nunata da yatsa tunkafin takarasa dinning din tace “don’t even come here wuce kitafi wajen Aman kiyi karatu yanzun nan nadawo zaku fara damuna, goyon kaniyanki zan miki, jeki jira yar aikinku tazo tagoyaki, Oya go back” juyawa Amal tayi tafashe da kuka dasauri Ummi takalleta kaman tadaina serving Maman taje ta dauketa, ta tsani taga yaran na kuka wlh har cikin ranta, ahankali tawuce wajen Aman tafada jikinshi rungumeta yayi yace “stop crying Amali Anty Ummi is coming yanzun nan kinji” Gyadamata kai tayi yana share mata fuska yace “let’s play game”.

 

Tunda Ummi tafara serving tuwo a plate Hadiza ke kallonta zuciyanta na wani kalan tafarfasa kawo tray gabanta Ummi tayi ta ijiye bata idasa jaye hannunta ba Hadiza ta daga tray gabaki daya ta mike tsaye ta kwarama Ummi akai da tuwon dake a leda da miyan taushen da kwanukan da cokulan duka suka bare akanta wani kalan mahaukacin azababben mugun ihu Ummi ta kwala tafashe da kuka dayasa su Aman suka firgita dukansu suka juyo ganin Anty Ummi ta tsugunna a dinning ga miya tundaga saman dan kwalin kanta har goshinta da idanunta ta kullen gam tana ihu sosai jikinta nawani kalan rawa kaman wace ta zare tsabagen azaban zafin datakeji na miyan dakuma yajin miyan a idanunta yasa suka taho wajen da gudu Aman yace “Anty Ummi” cikeda masifa Hadiza tanunata da hannu tace “kina gidana, kinacin abinci na, nabaki makwanci, nabaki kayan sawa, nabaki sabulun wanka dana wanki, sannan ina biyanki kizo bazakimin biyayya ba, sau nawa ina gayamiki ni bancin tuwo sau nawa nake gayamiki? So kike nayi kiba nai katon ciki? Zanje sama nai wanka ki tabbata kin dafamin wani abun kin kawomin dakina kafin nagama wanka inba hakaba wlh saina koraki daga gidan nan this night” ta dauki jakanta tawuce sama fuuuuu, tsugunnawa daga Aman har Amal sukayi agaban Ummi da jikinta har bari yake sabida zafin miyan dan bata dade da gama miyanba ta juye a kulan gidan ga kulan su irin na millions din nan ne masu rike zafi kaman me, dudda Aman yaro ne amman saida yakai hannunshi yacire tuwon daga jikinta yana kuka sosai ya yar akasa yace “Anty Ummi sorry stop crying” Amal tace “Mommy is badddd mommy” sosai Ummi ke kokarin tabude idanunta takasa sai kuka take dudda kukan take na tausayin kanta tariga tai alkawari komenene zatai hakuri tana bukatan albashinta dashi Gwaggo ke zuwa asibiti dakuma shi ake tara kudin auren kanninta, dole ta jure komi itane hanyan cin abincin gidansu, so take ta mike but tama kasa hannunta Aman yakama Amal ma takama dayan yace “let’s go Anty Ummi ki wanke fuskanki” gydamusu kai tayi tana tsayar da kukan datake ta yunkura zata tashi tama kasa saita kara fashewa da kuka daidai lokacin an bude kofa da sauri su Aman suka juyo ganin Baban su shima ya shigo ya tsaya chak yana kallon daga yaranshi har Ummi dake kuka sosai kaman anyi mutuwa agidan ga jikin Ummi duk miya, fuskanta ma haka takasa bude idanu yasa yayi wajensu dasauri baima cire takalmi ba yace “Subhanallahi meya faru faduwa kikayi Ummi” Tsayar da kukan tayi dasauri muryanta na rawan sheshekan kuka tace “eh” tana yunkurawa zata tashi dasauri Aman yace “is Mommy Dady, ita ta kwara mata the whole tray na abinci akai Anty Ummi has been crying” warware handky daya ciro Nura yayi daga aljihunshi baiyi wata wata ba yakai kan fuskanta cikeda damuwa ahankali yace “tsaya” batai musu ba tsayawa tayi kwashe miyan kan idanunwanta yayi tass, miyan yayi fasha fasha awajen harda gashin idanunta, sannan ya kwashe na goshinta dana kumata batare daya taba na wuyanta ba dudda baka ce but he could see yanda fatan fuskan yayi ja, ijiye handky yayi dasauri kafin ahankali yakai hannuwanshi duka biyun yakama kafadanta dagashi har ita atare duka sukaji wani iri dasauri tayi kokari fizge kanta strictly yace “stop banson gardama, tashi muje” yanda yayi maganan ba wasa hakan yasa bata kara gardama ba, yana rikeda ita haka yayi kitchen da ita su Aman suka bisu bude kofan kitchen din yayi zuwa nan backyard gaban wani tap dasuke dashi awajen, yabude tap din yajuyo yakalli Aman yace “je bayin Anty Ummi kadauko mini sabulun wankanta” “okay Dady” Aman ya amsa yajuya da gudu shikuma yabude tap din yace “tsugunna” ahankali Ummi ta tsugunna, gently yadinga tara ruwan da hannunshi yana watsa mata a fuska har saida miyan ya fiffita duka da wayanda sukenan asaman gashin idanunta daidai Aman yakawo sabulan, ga mamakinshi sabulun vivo yagani ahankali ya karbe yakama hannunta yasa sabulun aciki yace “wanke fuskan mugani da sabulu” shafa sabulun tayi ta dirdirje da kanshi yake zuba mata ruwa tana wankewa tass ta wanke fuskan, igiyan wajen ya kalla ganin wata singlet dinshi wanda yasan itane ta wanke yajawo yabata yace “share fuskanki saiki bude idanun nagani”

 

 

 

Share fuskan tayi ahankali sannan tashiga bude idanun yajin dataji yasa tamaida idanun ahaukace tarufe tafashe da kuka kunsan yanda yaji ke birkita mutum tace “wlh da kwai yaji sosai Alhaji, wayyoo Gwaggo na nashiga uku” shi arayuwanshi yanada tausayi, ya tsani aga ana hurting mutane in general balle kuma yaga mace in pains, da sauri yasa hannunshi ya karbi hanky yamikama Aman yace “hold it nagani“ sabulun yadauka daga kasa yasa a hannunshi ya fara wankewa sannan ya murza sabulun a hannunshi ahankali yadan kalli fuskanta yanda ta kankame idanunta gam jikinta har lokacin rawa yake tana dan kuka, dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakai hannunshi gently yashafa sabulun a fuskanta kaman yanda ake wankema yaro karami fuska, fuskanta is sooo soft kaman na dan yaro, almost 30sec yayi yana chuda fuskan sannan ya kunna pampoo yashiga wanke mata fuskan tass kafin yakarbi singlet din ya share fuskan da kyau ya tsane dogayen eyelash nata kafin ahankali yana tsugunne agabanta yaciro wayanshi dudda akwai haske wajen bauuu flash na wayanshi ya kunna yabama Amal yace “princess haskamin fuskanta” dasauri Amal ta karba ta haska fuskan Ummi, shima yana kallon fuskanta dake sheki yaji wanki da sabulu yace “bude idon nagani” gently tashiga bude idanun dake rawa sosai na haggu tabude tass na dama ne tabude kadan dan tanajin yaji sai yarfe hannu take ta rude sosai ganin yanda takeyi yasa ahankali yace “tsaya” tsayawa tayi ijiye singlet din yayi kan jikinshi yakai duka hannunshi ahankali yayi cupping fuskanta dasauri Ummi takalleshi tadade rabon dataji namiji dab da ita haka, ahankali babu komi aranshi yakai hannanyenshi ya ware kwayar idannun nata dake mata yaji kafin gently Ya hura iskan bakinshi ciki wani kamshi Ummi taji da sanyi daya ratsa jikinta feeling inama ace zata sami miji dazai dinga kula da ita haka kaman yanda Alhaji keyi yanz, Alhaji nada kirki gashi kyakkyawa fari dashi kaman wani balarabe ga bakin saje, tsayar da hura idanun yayi ganin tabude su rass tana kallonshi kaman yaune rana na farko datake ganinshi shima zuba mata idanu yayi yana kallon kwayar idanunta yanda suke walkiya sabida hasken flash da Amal ke hasko musu, idanun sunyi ja na kukan dataci da yanda tai looking so helpless dakuma yanda take kallonshi hakanan saiyaji kaman yasata ajikinshi ya lallasheta, there’s something about her da kawai he finds interesting baisan menene ba. “Anty Ummi yadena yajin”? Maganan Aman yadawo da dukansu daga duniyan tunani atare dukansu kowa ya janye idanunshi, Nura ya mike tsaye da sauri yawuce ciki batare daya kara kallonta ba itakuma ahankali tamike tsaye tana goge wuyanta, gyadama Aman kai tayi tace “yadena” dasauri sukazo kusa da ita suna kallon fuskan hakan yasa ta tsugunna dukansu taba fuskan nata sukayi cikeda so sukace “sorry Anty Ummi” murmushi tayi sosai cikeda kokarin cheering nasu up tawani daga hannunta sama tace “Anty Ummi jaruma ce kaman Amalili, ko Mudi da Kumurci tsorona suke menene yajin miya dashima bazai tsorata dani ba” haba zokaga yanda sukahau dariya, Aman yace “Anty Ummi yaushe zaki kaimu kauyenku muma muga Mudin nan da Kumurci” hannunta takai kan kumatunta kaman mai tunani kafin tace “wata rana zamuje” ihu sukahau yi suna tsalle Nura daya dade yana kallonsu ta window kitchen murmushi yayi yawuce yadauki mop yafice gyara dunning din yayi da kanshi.

Shigowa sukayi a kitchen din fita tayi taje dakinta ta chanzo kaya zuwa wani atampa dogon red yamata kyau sosai.

 

 

 

Tana fitowa hada ido sukayi da Nura dake zaune a dinning yanacin tuwo adan kunyace ta sauke kanta kasa tazo wajen ta duka har kasa tace “Nagode Alhaji, kana bukatan wani abune dazan kawo maka”? Sosai yake kallonta red yamata kyau dudda babu wani special abu game da atampan but yamata kyau, jin shiru baice komiba yasa tadago kanta ahankali hada idanu sukayi da sauri yadauke kai itama maida nata kasa tayi dasauri, ahankali yace “bana bukatan komi, thank u” mikewa tayi harta juya tafara tafiya kaman daga sama taji yace “abincin yayi dadi sosai, thank u Ummi” dadan sauri tajuyo ga mamakinta kallonta yake suka sake hada idanu sukayi, faduwa gabanta yayi dasauri tasauke kanta kasa tasake juyawa zata shiga kitchen batare datace komi ba yace “mezakiyi a kitchen”? Ahankali tace “Anty zan daurama wani abinci batacin tuwo” strictly yace “wuce kije ki kwanta kihuta” dudda bataso ba dan batasan mezai biyo bayaba kasa musu tayi tawuce takoma dakinta ta kwanta.

 

Fess yagama cin abinci yakai komi kitchen dakanshi yafito yaje sama fitowa yayi da paracetamol, bottle water yadauka mara sanyi yaba Aman yace “kaima Anty Ummi kace nace tasha” gyadamai kai tayi yawuce da gudu yatafi dakinta Amal na binshi yakoma falo yazauna yana saka news duk yanda yaso yama gane meke faruwa a news din kasawa yayi yawuce sama fuuu, bude kofan dakin Hadizan yayi ranshi abace tana zaune gaban dressing mirror daure da towel tana shafe shafen ta na night routine batare da tajuyo ba tace “ki ijiye abincin kiwuce kifita dakikiya kawai next time try this nonsense kinbar gidana kenan jaka kawai yar kauy…..” “Hadiza!” Nura yakirata da kakkausan murya saida gabanta yafadi dan baitaba kiranta da zafi haka ba juyowa tayi da sauri ta kalleshi ganinshi tsaye a tsakiyar dakin yana kallonta ranshi abace, haderai itama tayi tace “badai kahana yarinyar nan dafamin abinci ba dan idan kayi haka u will see the other side of me Nura” wani kallo yamata yace “inason naga other side of you din today are you crazy? Ke wace kalan senseless mata ce? Kissan kai kike kokarin yi agidana? Are you trying to kill that girl?” Hannu ta dagamai tace “please lower your tone ni matarka ne ba some yan aiki dazaka dinga dagama murya ba Nuri, I’m your wife not slave so keeep muryanka down by now kasan I don’t take that shit, namiji yazo yana wani mini ihu akai saikace ubana kuma ma idan na kasheta sai me? Eh? Ba yar aiki bace, yarinya mara galihu duk irinsu ne irin yaran da akauyen su akekai yara maza almajiranci mata kuma akaisu aikatau kota mutu sai me mezai faru? Almajirai nawa suka mutu wani abu yataba faruwa? Ai yara da iyayensu suka nuna basu da gata mutane ma basa gatanta su so bakaina farau ba dan yar aiki ta mutu agidana ehe” Sosai Nura ke kallon Hadiza shi baimasan tayi nisa haka ba sai yau wato tanada answer for anything, at this point baimaso maganan nasu yayi nisa dan kar zuciya ya debe shi yadauketa da mari hakan yasa cikin kakkausan murya yace “duk randa kika sake trying nonsense din nan wlh saikin bar gidane duk wani abu dake gidan nan fara tundaga kan gateman suna karkashina ne, hakki na ne nakare kowa na tsaresu dan haka don’t ever try hurting mutanen dakemin aiki inba hakaba u will leave this house!” dudda maganan ya mugun mugun sosama Hadiza rai amman daurewa tayi dan bataso yagane tai wani kalan shewa. “Ahayyeeee nanaye ance dama idan baka mutu ba bakagama sanin halin maza ba, Nuri ni kakema gorin zaka kora daga this rat hole dakake kira gida”? Ta nuna dakinta da ko’ina da hannu, tsaki kawai Nura yayi yajuya yafita tabishi da sauri dan idan bata bashi amsan maganan nan ba hankalinta bazai kwanta ba kai zazzabi ma zai iya kamata, tana biye dashi yana tafiya tace “zan iya gina gidan dayafi nakan nan sau dubu a kyau dakuma girma Nura kada kayi kuskuren yimini gorin gida, duka duka yaushe kayi kudin lokacin dana aureka kagama masters akan architecture kanama wani building agency aiki har kazo kabude naka kampanin na harkan filaye da gine ginen estate anan Abuja, who do you think you are dazaka min gorin gida nixaka kora Nuri, au ina maka magana ka maidani mahaukaciya kayi tafiyan ka wlh wlh yanda ka batamin rai dinnan saina huce akan mahaifiyark…….” Chak Nura ya tsayar da tafiyan dayakeyi akan staircase yajuyo ahankali yakalleta itama daidai tana tsayawa dab da shi tana kara rike gaban towel nata da kyau tana kallonshi tace “da ilimina da sana’ata da darajata har ka isa kazo kana gayamin na kara dukan wata yar aiki sainabar maka gidan ka, sabida yar aiki Nuri zakace zaka koreni, what on earth do you take yourself for? Are you God? Sabida kaganni mace kadauka I am weak ne I can’t defend myself? Zakace zaka korini daga gidanka u think bazanyi speaking up ba, Listen Nuri, me and you are two equal people! Baka fini da komi ba, duk inda kasa kafa nima zan iya saka kafan, nasan kimata nasan daraja ta and my worth u cannot downgrade me or downgrade my status and for batamin rai din nan dakayi this night wlh saina batama mamank…….” Azuciye Nura yadaga hannu zaikai mata mari kaman daga sama sukaji Aman yace “Daddy!” Chak Nura ya tsaya da hannunshi batare dayakai marin ba, he don’t ever wants yaranshi to have a memory of him yana dukan mahaifiyar su, dunkule hannunshi yayi tareda saukewa kasa ahankali yajuyo yakalli Aman din,  dasauri Aman yazo ya rungumeshi tsamtsam yana kuka sosai yace “Daddy sorry kayakuri Mommy is sooo baddd but don’t slap her okay Dady, beating girls is not good katuna ranan dana daki Amal haka kagayamin” daukan yaron Nura yayi ya rungume ahankali tareda mannamai kiss akai yama kasa magana yashiga tafiya dashi yana sauka, Hadiza dake kallonsu tace “ai naso ka maren wlh danai suining naka for domestic violence, try that next time kagani I will mess you up Nura” sauka yashiga yi kasa yana dauke da Aman a hannunshi gaban dakin Ummi yakaishi yace “shiga” shiga yayi sannan yajuya yawuce yafita daga gidan yashiga motanshi yamabar estate din gabaki daya zuciyanshi daci takemai da gaske idan Allah yabaka mata nagari wlh ka gode kama kara godemai dan shaidanun mata azaba ne, they will so push you to the wall kaji kaman zaka kashesu, yayi tafiya mai nisa sannan yayi parking yakalli wayanshi yadade yana kallo kafin yasauke ijiyan zuciya yakai hannunshi yadauka yabude yaciro wani lomba yakira wayan na gab da katsewa aka dauka daga dayan bangaren wata yar dattijuwan manyantaccen murya ne tai magana. “Nura barka da dare ya wurinku yasu Amalily?” Ahankali yace “lafiya lau” saikuma yayi shiru all this years baitaba daga waya yakai karan matanshi ba sai yau jin yanda baiyi magana ba yasa tace “lafiya Nura Maiya faru? Ina ganin wayan nasan da wani abu duba da lokacin dakama kirani, what happened?” Ahankali yace “Hadiza bansan menene damuwanta ba, tunda na auri Hadiza Anty Jamila for once bantaba kokarin takata ba ko shut her up, ni mutum ne dana tsani takurama mata ko basu damuwa I have 4 sisters dukansu mata nataso da sanin yanda ake girmama mace kare mace dakuma daraja mace” Anty Jamila tace “kwarai Nura wannan haka yake zan shaideka ako’ina” ahankali yace “the whole idea da concept na feminism ya shiga kanta, I’m not saying feminism is wrong no, ko Allah yasani inaso naga matata tacigaba, banki duk matakin dazan taka aduniyan nan matata ta takashi ba, I empower her nabata jari tafara business nakaita su dubai oman Egypt dasauran kasashe alokacin sabida ta saro abayoyi tafara, bansan gobeba I believe empowering matata will go a long way for yaranmu incase of gobe dabata da tabbas, bantaba ma Hadiza kallon wata baiwa ko yar aiki ba rather I see her as life partner dina wacce nakeson to go through every phase na Rayuwa together mu tsufa together but ita bahaka take ganin komi ba, gani take anything daya kamata tayi agida nima yakamata nayi nida ita we are equal, yimin girki gaidani bani abinci is not her duty duka abubuwan nima nayi we are equal afterall, gaidani akan me zata gaidani nima na gaidata…” dasauri Anty Jamila tace “subhanallahi” dan ijiyan zuciya yasauke yace “Anty Jamila the whole feminism din nata haukane kawai, rashin kunya menene menene babu wanda bata mini nakasa gane kanta balle kafanta, i can’t even talk to her kafin nayi magana daya tayi dari, Anty Jamila I am tireddddd nagaji, I want peace of mind at this my age” yanda yayi maganan saida yabama Anty Jamila tausayi tasan yanda Nura keda hakuri tasan for Nura yadauki waya yakirata takaishi bango anatse tace “Nura kayakuri kayakuri shikenan abinda zan iya fadi kaga wannan halin shine dalilin dayasa maza da yawa basason bama matayensu freedom har subarsu suyi sana’a dan wasu matan dazaran sun soma taba kudi shikenan sai sudinga jin kansu kaman giwaye suma yanzu sun faso, amman kabarni da ita zan kirata zan kira Mama kuma” ahankali yace “please kada ki sanarda Mama tana fama da hawan jini saisa nakiraki ban kirata ba” murmushi tayi tace “to shikenan amman dan Allah kayakuri” ahankali yace “to saida safe agaida yara” yakatse wayan yadade ahaka yau bacin ran yasa he wanna be alone ma inda bahaka ba zai iya kiran abokan shi yaji inda suke yaje yasamesu, yayi kusan 3hrs awajen sannan yatada mota yabar wajen.

Domin magana dani M shakur koso nasaki a group dina chat me up tanan wa.me/+2347012181461

 

Yana katse wayan Jamila ta danna mata kira wayan harya katse bata dauka ba akaro nabiyu ne tadauka tace “Hellooo Anty Jamila” cikin fushi Jamila tace “ke wace irin mahaukaciya ce Hadiza? Ni wlh I don’t even need to ask you nasan kene da laifi dan nasan kalan hakurin Nura tunda yau dakanshi yadaga waya yakirani nasan kin mai babban laifi” tsaki Hadiza taja dayasa Anty Jamila tasake baki, cikin fushi Hadiza tace “ohhh kiranki yayi yahada mini munafinci? To wlh zaizo gidan nan yasameni ina jiranshi” jin yanda yake magana kaman tana jiran wani saran wasanta yasa Anty Jamila tace “Hadiza are you okay kuwa? What has gotten into your head? Nuran kike magana haka akanshi?” Cikin fushi sosai Hadiza tace “Anty Jams bazaki gane bane, Nuri finds every little way to belittle me, nan Abuja ne fa ba kano ba but kullum so yake ina shiga kitchen namai abinci, a Abuja yan aiki ke girki matan gida relaxing take bayinta namata aiki, inada yar aiki ai nama baki labari wacce nace miki su Aman na sonta, ita ke kula dasu I am busy da shigo gida nawa yake so naraba kaina? Sai nasa yar aiki tamin wani abu yahanata yimin sabida shike biyan kudin shine nacemai yadena daga this month nizan cigaba dabiyanta sabida I should be the one in control of her, ina shago dazu yakirani wai Mamanshi zatazo gobe taga Dr kinji fa Anty Jamila sabida ya rainama kanshi wayau danni bai isa ya rainamin wayau ba, gidan nan belongs to two of us baida right dazai kawo koma uban waye into this house without asking permission dina, what did he take me for eh? Wlh wlh jiransu nake suzo goben dagashi harsu saina kuntata musu bakin cikin da bazasu kara marmarin zuwa gidana ba me akeyi da yan uwan miji banda hauka mtswwww” “Innalillahi wa innailaihi raji’un” Anty Jamila tafadi tana tafi da hannunta cike da mamaki tace “Hadiza giyar kudi ko giyar karatun wannan femi ah’ahhh Feminism ko oho dai ke damunki” Hadiza tace “feminism wai? I know my right I can fight for my right duk inda nake aduniya tunda mata suka gano this feminism sun samu yanci sun samu cigaba, a woman can stand aduk inda namiji ya tsaya aduniyan nan” “dalla rufemin baki sai idea bature yasa kin rasa mijinki tukunna zaki dawo hankalin ki” Anty Jamila tamata ihu tace “wannan ba shine tarbiyan da aka baki agida ba, keda mijinki can never be equal ko awajen Allah domin ko aljannanki na karkashin tafin kafanshi, mata dakika ganmu daga rib guda daya na maza aka hallito mu, kada ki mata, Allah yafadi acikin suratul Nisa’i aya na 34, Arrijalu qawwamuna Alan nisa, bari madai naja miki ayan gabaki daya

ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍۢ وَبِمَآ أَنفَقُوا۟ مِنْ أَمْوَٰلِهِمْ ۚ فَٱلصَّـٰلِحَـٰتُ قَـٰنِتَـٰتٌ حَـٰفِظَـٰتٌۭ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُ ۚ وَٱلَّـٰتِى تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهْجُرُوهُنَّ فِى ٱلْمَضَاجِعِ وَٱضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا۟ عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيًّۭا كَبِيرًۭا ٣٤

 

Men are the caretakers of women, as men have been provisioned by Allah over women and tasked with supporting them financially. And righteous women are devoutly obedient and, when alone, protective of what Allah has entrusted them with. And if you sense ill-conduct from your women, advise them ˹first˺, ˹if they persist,˺ do not share their beds, ˹but if they still persist,˺ then discipline them ˹gently˺. But if they change their ways, do not be unjust to them. Surely Allah is Most High, All-Great.

 

Allah ne yafadi da kanshi, idan kuma u are talking about rights da yanci ne tun zamanin Annabinmu ya kwatoma mata yancinsu idan wani yaji kina magana haka idan ba’asan Nura ba zaa dauka wani abu bawan Allahn nan yake miki, kin sami miji nagari bawan Allah shiru shiru mara magana kinamai irin abubuwan nan ke kinada baki kice sai da izinin ki mahaifiyarshi zatazo gidan danda tahaifa, matan da komu nan last week saida muka kirata muka mata yajiki wlh maganan ki yasama ina jin kunyan Nura, Hadiza sau nawa da ni da yarana harda Mama muke zuwa gidan ki every now and then duk wani abu dazai shigo damu Abuja gidanki ne masaukinmu we don’t even ask for permission sabida anzama daya, ace yau mahaifiyarshi zatazo for treatment na rashin lafiyanta kina maganganu haka ina imanin ki? Wani kalan tsantsan son kai ne wannan”? Cikin kunkuni Hadiza tace “ai dama side dinshi zaki dauka nasani mutum yana nema ya maidani yar aiki bazakice komiba ace nine zan shiga dakinshi na gyara namai girki bayan inada yar aiki mai yi” Anty Jamila tayi shiru na kusan 5min sannan tace “danace basai na sanar da Mama ba but Hadiza kinyi nisa Mama dole ta shigo zancen nan, yar aiki itane ke gyara dakin mijinki tamai girki? How many minute zai daukeki kima mijinki girki? Bawai nace yar aiki is bad bane ai ko ni inada yar aiki tadan taimaka maka da one or two things but that does not mean zaki barmata ragaman gidanki menene haka Hadiza ke kina ganin wayau ne hakan kin cika yar boko ko? Kin waye  kinada kudi kinyi kawaye matan Abuja kema kin dauki sahunsu kirasa wanda zaki mawa sai mutumin da shine yabaki jarin mutumin that made u Hadiza” ihu Hadiza tayi tace “me  aciki Anty Jams ai sai nabiyashi kudin daya kashemin nafara business din harda riba indai hakan zaisa yafita harkata yabarni na Sarara nayi yanda naga dama” dasauri Jamila tace “wai kinsan wane kike aure kuwa? Nura fa kampanin shi shike tashe yanzu ko su cosgrove abayansu suke, ga kyau ga aji ga hakuri baki tunanin yazo yahadu da wata kinamai haukan nan yakaro aure abinshi” har cikin ranta Hadiza taji maganan ya soketa dasauri tace “Nuri baida ra’ayin mata biyu tun kafin muyi aure yamin alkawarin ni kadaice matarshi har abada and Nuri baya taba karya alkawari, he’s a man of his words” dan murmushi Anty Jamila tayi tace “to inhar bakison alkawarin nan ya karye take care of mijinki ki sauke pride din nan youu are under him and u will always be, kidaina mai kallon keda shi are equal kina rainashi, keda mijinki can NEVER BE EQAUL, and Bari nagaya miki ki gaggauta gyarawa kafin Nura ya rufe babinki yabude sabon babi,_ saida safe kuma zan sanar da Mama yanda mukayi” ta katse wayan batare data karabi takanta ba shiru Hadiza tayi tana kallon wayan ranta ya mugun sosu da kalman kishiya. Da Yayanta tayi tsaki tayi ta yarda wayan gefenta tace “shiya isa yama mini kishiya, tsorona bazai ma barshi yayi wannan kuskuren ba, banda hakama mata basa gaban Nuri sai business kuma Nuri baida ma yawan sha’awa kaman nine saimuyi watanni bamubi takan shimfidan juna ba ninama fison haka dan ba haihuwa nakeson nakarayi ba inaso nai maintaining this body da shape shi aina zai taba samun kyakkyawan mata fara hausa fulani komi yaji irina” tayi dan murmushi tanajan bargo takoma bacci abinta.

 

 

MAISA WASU MATAN KE GANI SUDA MAZAJENSU ARE EQUAL????

Leave a Reply

Back to top button