Furar Danko Book 2 Page 49
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣9️⃣
…….Kowa da abinda ya damesa. Duk da abinda ke faruwa a jihar ta Kano ya girgiza Abba hankalinsa a rabe yake gida biyu a dalilin halin da Ummah ke ciki. Duk da ma dai malaman da aka kawo a wannan karon su sunyi jarumtar tsayawa, sai dai daga kallo ɗaya da sukai mata sukace ta koma cikin ɗaki kawai. Sun tattauna da Abba akan dolene asan mushurikin da yay mata wannan aiki. Cikin nuna rashin amincewa Abba yace shi babu ruwansa. Babu inda zaije neman wani akan aikin da bai aiketa yi ba. Babu irin lallashin da ba’ai masa ba yace babu gudu babu ja da baya. Da ga ƙarshe dole ƴaƴanta ne suka nufi wajen Hajiya Naqiba da ke gida, dan asibiti sun sallamesu kamar yanda suka buƙata akaje akai mata ɗorin gida. Sun sami Hajiya Naqiba a yanayin daya tada musu hankali, dan ƙafarta tai wani irin mahaukacin kumburin da har tafi gangar jikinta girma. Kuka take sosai da ihu na azabar zogi da raɗaɗin da ƙafar kemata. An kira mai ɗori ya tabbatar musu ta sake gocewa, ma’ana dai ɗori baiyi ba. Ya kuma tabbatar musu da shi gaskiya bai san yaya zai yi ba, sai dai su nema wani kuma ya gwada sa’arsa. Daga haka yay tafiyarsa ma shikam. To shine fa ƴaƴan Umma suka samu ana shawarar neman wani mai ɗorin dan an tabbatar musu na gargajiyar dai yafi kar su maidata asibiti. Ga mijinta ya nuna kamar ma abin bai damesa ba duk da irin kiran sunansa da take famanyi shi da ɗanta Maheer. Shi Maheer ɗin da farko ya zauna, da ga baya yay ficewarsa acewarsa shi gaskiya ihun da take ya ishesa, yana fita suka haɗe da abokansa sukai tafiyarsu wajen ƙwalewarsu da kayan shaye-shaye. Dole yaran Umma suka dawo gida jiki a sanyaye. Sun sake iske tashin hankali Umma dake wani irin nishi a ɗaki amma kowa ya kasa shiga ya dubata, Ammah ce ma ta nuna zatai ƙarfin hali Abba ya tabbatar mata idan ta shiga sai ya ɓata mata rai, dole ta kama kanta cikin damuwa. Suma ɗin dai babu wanda yay yinƙurin shigar saboda tsoro….
Har yamma babu wanda yasan halin da Ummah ke ciki, sai yayanta Jibirin ne ma yay ƙarfin halin bada shawarar a sake kiran malaman nan koda taimakon da zasu musu. Kowa ya bada goyon bayan hakan. Dan haka akai kiransu. Babu jimawa suka iso kasancewar akwai sanayayya tsakaninsu da Jibirin ɗin. Addu’oi sukayi da ƙarfin halin cusa kai a ɗakin, sai gasu suna rige-rigen dawowa a guje. Har yaran gidan dake tsakar gida na tayasu da afkawa ɗakunan iyayensu. Sun tabbatar da gaskiya bazasu iya ba, wannan mummunar halitta ganinta ai tashin hankaline ma. Sun tabbatar da shawararsu kawai ya kamata a bi aje a nemo mutumin da yay musu wannan aiki zaifi sauƙi fa. Wannan al’amari ya sake tayarma da kowa hankali. Dole ƴan uwanta suka tattaru neman mafita su da ƴaƴanta. Dan Abba dai da gaske ya juya musu baya…..
________★
Al’amari kamar wasa Dada sai da ta kwanta asibiti na kwana biyu, randa aka sallamonta ta samu surukanta cike da gida sunata harkokin arziƙi akan zaman bakwai. Wannan abu ya sake dugunzuma mata zuciya. Baba Garko ya shigo dubata da daddare ta sanya masa kuka. Kallonta kawai ya tsaya yanayi, bawai baya jin tausayinta bane, ba kuma baya sonta bane. Ya riga ya ɗaura ɗammarar horatane kawai. Dan ko auren nan nashi yayisa ne da gayya danya ƙona mata rai tunda yasan babu abinda ta tsana a duniya irin kishiya. Kuma ya samu nasara. A yanzun ma cikin ɓacin rai yaja tsaki da faɗin, “Ni al’amarinki kam ya fara bani tsoro Hajara. Shin wai baƙin ciki kike da ƙaruwar dana samu ko yayane? An faɗa miki haihuwa kin yanke jiki kin faɗi sumammiya, yanzu kin sakani a gaba kina kuka. Kin ganni nan ni bana son damuwa ina cikin farin ciki a ɓata min shi. Idan kinga zaki sakama ranki dangana ki saka, idan kuma kinga wannan halin da kike neman jefa kanki ne abin burgewa sai ki cigaba. Dan bakin alƙalami dai ya rigada ya bushe. Takardu sun jima da rubutuwa babu wata cleaner ɗin gogesu. In sha ALLAHU nan da wata shekarar ma wasu biyun zata sake zubomin a gidan nan, sai ki shirya sake suma. Na barki lafiya”. Da ga haka yay ficewarsa. Sama da ƙasa numfashin Dada ya ringayi, jininta yay masifar hawan da har idanunta na koma mata dishi-dishi, ALLAH ne ya taimaketa Uncle Muneer ya shigo ya sameta a lokacin, da tabbas zuciyarta zata iya bugawa komai ma ya faru….
(To Baba Garko ALLAH ya raya ƴan biyu. Koda yake kace nanda baɗi ma wasu kake so. Kaga tsoho da rigima🥱😂😂🤣🚴🚴)
*_★UK★_*
Alhmdllh a ɓangaren ango da amarya komai na tafiya dai-dai. Basu da wata damuwa sai cilin ɗinsu sukeyi. Duk abinda kuma ke faruwa a 9ja a cikin kunnensu yake. Dan suna samun information sosai ta hanyar Ahmad da su Daddy da suka koma gida. A yanzu haka tarko na biyu suke shirin ɗanawa. Dan sun gama shirya komai tsaff lokaci kawai suke jira.
Soyayya suke zubama juna mai tsayawa a rai da zuciya harma da gaɓɓan jiki. Duk da Lulu na dojewa da ɓoye nata sirrin har yanzu ta gagara furtawa a baki sai dai Smart ya gani a aikace. Dan zuwa yanzu kam karatun malamin nata tsaff ta haddacesa tama koma ruɗa masa tunani da salo-salonsa. A ranakun da yake da wasa koda ba’a cikin London bane bata iya zama, binsa take su tafi ga ɗan yaronsu da kowa ya gani sai ya tanka. Dan haka Smart ya dage da tofe abinsa da addu’a itama yana cemata tai masa saboda baki.
Lulu aja rigima bayan ta kira Baba Garko sun masa barka ita da Smart, ta kuma kira maijego da zuwa yanzu sun ƙulle sun zama ƙawaye dan kawai ta turama Dada haushi. Waya ta ɗaga tai kiran Dada. Bayan su. Gaisa Dada na zaton Lulun ta sakko ne daga fushin da take da ita zatai mata yaya jiki sai taji ta fara mata barkar haihuwar gidan. Dada ma bata san ta lailayo ashariya ta makawa Lulu ba. Aiko ta kwashe da dariyar ƙularwa tana mai yanke wayarta. Murmushi kawai Smart da ke zaune yana saurarenta yayi. Dan shi rashin jinta zuwa yanzu tsoro ma yake bashi wlhy. Baice mata komai ba sai da zasu kwanta ya mata faɗa. Tadai nuna masa taji, amma yasan batajin ba. Dan a ɓoye ta haɗa kayan jarirai na gani na faɗa ta bada aka wuce da su Nigeria wai a kaima maijego da jinjiraye….
Ana kwana na biyar da kama Alhaji Sadi Dikko Aunty Bilkisu da Iya tabawa suka iso Unitet Kingdom tare da Ahmad. A ranar Smart baya gida sunje buga wasa. Sai Lulu ce taje tarbarsu duk da Ahmad yasan gidan. Sosai aunty Bilkisu da duk take a tsorace ta samu nutsuwa da ganin Lulu, cikin farin ciki suka rungume juna. Hakama Iya Tabawa yau Lulu harda rungumeta, yayinda Ahmad ya caɓe yaronsa a hannu shima. Cab suka shiga har gida, dan Lulu bata driving anan kasancewar bata da lasisi. Sai Smart kawai. Daga Aunty Bilkisu har Iya Tabawa gidan ya birgesu sosai. Sunata santi da jera addu’a ga Smart. Abincin da Lulu ta shirya musu sukaci, bayan sunyi nak Ahmad yace zai wuce can ya samu Smart. Zuwa gobe sa dawo tare ɗan ba’a ranar Smart ɗin zai dawo ba. Tafiyar Ahamd ta sake basu damar ɓararrejewa, dan ma Aunty Bilkisu ba daɗin jikinta take ji ba sai ƙarfin hali kawai. Sun ɗan taɓa hira kafin Lulu ta kwashesu zuwa asibiti dan a yau take son aunty Bilkisu ma ta fara ganin likita. Kuma ko Smart baisan da hakan ba, dan shi nashi shirin kawai sai ya dawo ya kaita da kansa.
Kasancewar Usman da Dr Lameer ne suka haɗasu da likitan basu wani sha wahala ba na ganinta. A take aka bama aunty Bilkisu gado. Abinka da inda aka san darajar ɗan adam babu ɓata lokaci suka fara mata gwaje-gwaje da duk abinda ya dace. Koda Smart yay kiran Lulu bayan sun tashi a wasan bata sanar masa suna asibiti ba. Sun dai gaisa tai masa congratulations dan ganin sunci wasan suka ɗanyi hirarsu ta soyayya sukai sallama. Da yace ta haɗashi da su yay musu barka da zuwa Iya Tabawa kawai taba tace aunty Bilkisu na barci. Bai kawo komai a ransa ba ya yarda. Sallama sukai fan yana tare da Ahamd daya sameshi a can. Da ga haka itama ta cigaba da kai kawonta tare da Dr Lameer dake taimaka mata. Kasancewar mai jiyya ba zama yake a asibitin bayan ayi mata abubuwan da duk suka dace na wannan lokacin suka dawo gida, sai bayan wasu awoyi zasu koma dubata kuma……
*_★9ja★_*
A gidan Baba Garko suna akaci na kece raini da nunawa tsara. Dan ƴan biyu kam sunyi goshi matuƙa sannan sunzo da farin jini a wajen dangi. Kai da kaga taron nan kasan da gayya akayisa. Kasancewar su kansu dangin Baba Garkon ba daɗin Dada sukeji ba yasa a wannan gaɓar suke maida murtanin bashin gaba. Dan raƙashewa akai iya raƙashewa. Ga matan ƴaƴansa da jikoki cike taf da gida. Su kansu ƴaƴan dole sukazo kowa kuma da tsarabar suna. In ba haka ba kaci ubanka hannun mai gayya mai aiki. Alh. Sulaiman ne kawai babu, amma iyalinsa duk sun zo a sace batare da ya sani ba. Dan sukam dai basu yarda sun saka kansu a cikin faɗan iyaye da ɗansu ba. Hajiya Turai kuma tsaye take akan ƴaƴanta bata basu fuskar da zasu guji kakanin nasu ba. Tace babu ruwanta suma babu ruwansu. Ko Tajuddeen dake a cikin case ɗin tsundum cikin hikima ta dawo dashi ga kakaninsa tsundum. Dan tasan abinda take yi.
A yanda Dada ta koma laƙwas sai ta baka dariya ma da tausayi. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai kufcewar duk wata power nata. Gaba ɗaya ta fahimci komai fa ya gudu. Dan hatta matan ƴaƴan nata da take bama gwale-gwale yanzu kar suke kallonta. Bama sa shakkar dubar tsakkiyar idonta su yaɓa mata habaici a kaikaice. Karo na farko a rayuwarta datai kuka mai yawan gaske a dalilin tuna mahaifiyar Lulu. Tasha gaya mata gaskiya akan ta rage tsananin da takema matan ƴaƴan nata, in ba hakaba watarana sai sun nuna mata sun fita iyawa. Hakama dangin babansu ta daina musu wulaƙanci musamman marasa shi ɗin nan, kada wataran a auro wata a gidan ta riƙesu su rama duk cin kashin da take musu. Amma akoda yaushe saita hantareta harma da zagi saboda takaici da baƙin cikin ta kira mata kishiya, takance badan tana kama da Baba Garko ba itako da tace an mata misayarta a asibiti ne. Iya ƙoƙari Mawaddat tayi a kanta wajen gaya mata gaskiya akan abubuwa da yawa, yau gashi bata kusa da ita balle taji mata ciwon abinda ke faruwa. Dan ta kula ƴaƴa mazan nan fa ƴaƴansu da matansu kawai suka sani, tunda gashi kowa gani yake ta tsananta da kishin amaryar ubansu, ko kunyar faɗa mata hakan basa ji. Ko yau da safe Uncle Khamil da yazo sunan shi da nasa iyalin takanas da ga Abuja sai da yay mata irin wannan ƙorafin. Hakama autanta daya aiko da shatara ta arziƙi tun daga Saudiya. Gaba ɗaya saita fahimci goyon bayan mahaifinsu suke sam bata sonta ita yanzu. Babu abinda yafi ƙona mata rai da zuciya sama da saƙon Lulu, ita sai yanzu ma take sanin wai Lulu bata Nigeria tabi mijinta, bama wannan ba, shi kansa Smart ɗin bata san ya zama wani abu ba sai yanzu………✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*