Cinikin Rai Book 2 Page 14
Volume:14 Reasons.
Dakin Zeeno ya leka ya samu Inna tana tsokanarta. “Gawa taki rami!” “Kai Inna!” Ta faɗa tana shan kunun alkama, yadda ya turo kekenshi zuwa dakin ya zuba mata idanu. Dauke kai tayi kamar bata ganshi ba, ya ce .”Hajiya Inna barka da safiya.” Murmushi Inna tayi tana amsa mishi da cewa. “Barka dai, wai tsaya Malik idan son Yar kunama kake, ranar juma’a a daura aure, na gaji da ganin gamsheshen tsoho irinka yana sintiri akan yar jinjira irinta.”
Tsabar maganar Inna ya zo mata bazata bata san lokacin da ta furza da kunun da ta kurba a fuskarshi ba, kashe mata idanu yayi sannan ya juya ga Inna ya ce mata. “Hajiya Inna ai bazata ba zaki bani yar jikallenki bane, amma tunda kin yi magana ranar juma’a sai a bani ita, ni kuma na bada goro da alewa irinta al’adar bahaushe da shuwa arab. ” Ya karshe maganar yana kafeta da idanun. “Ni ba zan aure shi ba” sake baki Inna tayi tana faɗin. “Yau naga bakin ciki, yar Hajiya Inna ma da ya ce min zaki min bakin cikin da haka? Tow ahir dakin. Da kike kwance a nan ce miki aka yi kin tsira ne? Ai shine rufin asirinki, a waje za a iya cutar dake amma a cikin gidan shi sai inda karfinshi ya kare.
Ja’ira a ranki ba murna kike, kin zamu mijin nunawa sa’a amma kin wani kare da boyewa a ranki, ai kawai kazo ayi maganar bata yara da mata ba ne ta manyan maza ne, ” tana gama fadar haka ta bar dakin.” “Me yasa ba zaki aure ni ba?” “Saboda nima bukatarka zaka biya a kaina, idan ka samu yadda kake so zaka shafe babina.” Dariya ta bashi cikin sigar tsokana ya ce mata. “Kuma haka ne, idan na gama yadda nake so watsar dake zan yi na kuma niman wacce bata kai ki ba ”
“Allah ya min tsari da aurenka, wallahi tun wuri kada ka fara tunanin hanyar aure na”
“Ai ba iya tunanin nake ba, yadda zan mallake yar kwaila baki ɗaya nake ta nazari ”
“Kana da son zuciya.” “Eh a wurinki na koyi son zuciya, amma kin san me duk abin da zaki fada ba zai bani haushi ba, domin nan da kwana uku, kin shige daga cikin gidana.”
“Ai ba auren Allah da Annabi ba ne. Auren kwangila ce!” “Ai duk aure aure ne, tinda an karanto siga” “ni fa bana son auren nan, wallahi! Domin ba zan yarda kayi tsafi dani ba.”
“Bokana ya gaya min na nimo mace, yar siririya yarinya fara masifaffiya mara hakuri, idan na kawo ta aka yanke bakinta kudi xan samu na mahdi ka ture!” “Kai ko kunyar fadar abin da kake baka ji?” “Tow tsaya me yasa baki sona?” Shiru tayi tana kallonshi kafin ta ce mishi. “Saboda kana da budurwan zuciya!” Shafa kanshi yayi, tare da kallon yadda ta sunkuyar da kai kasa taki yarda su hada idanu. “sai me kuma?” “Hmmm!” Kawai ta ce matsawa gabanta yayi da keken ya zuba mata idanu ya ce mata. “kalle ni kika ce ba zaki aure ni ba kawai don ina da budurwan zuciya?”
D’ago kanta tayi ta kalle shi, kafin ta ce mishi. “Ni ka tafi bana son ganinka. Kuma bana son aurenka ka rabu da ni, idan kuma rayuwata kake so sai ka dauka ka huta, amma ba zan auri tsoho irinka bayan ga sa’o’i na, suna auren matasa ba.
A cire maganar wasa kai ina zaka kai ni? Ai matar nan tayi gaskiya ban da son zuciya ina zaka kai ni? Sannan idan ba kwadayin irin na Yaran talakawa irina ina zan kai ka? Ina son ka gane auren irina takura ne, ka je ka nemi wata yarinyar amma ni bana son aurenka!”
“Idan an daura sai ki mutu shi ne, karshen kiyayyar da zaki nuna mishi, kina tsammani zaki gaya mishi magana ne a Kyale ki, tow a hir ɗinki, kada na kuma jin kin mishi rashin kunya, aurenki da Malik an gama, ranar juma’a domin ta haka ne za a nunawa makiyanku a shirye kuke!”
“Amma Ammy gurgu ne!” Wani irin kallo Ammy ta mata, sannan ta ce mata. “Idan gurgu ne kece kika halicce shi?”
“Ni dai ba zan auri tsoho irinshi ba”
“Age is just a number, kyautatawa da sanin ya kamata shi ne shekaru, don haka kul na kuma jin kin ce tsoho ko wani nakasa, aure babu fashi.” “Ni dai aka min auren dole na mutu ba yarda zan yi ba, domin fatalwa zan yi na addabi wanda ya aure ni.” Ta faɗa tana wani hararan Malik, d’akka mata duka Ammy tayi tana faɗin ” Allah ya shirya ki, ki bar sakaci don Allah kayi hakuri yarinta ke damunta.” Murmushi yayi bai ce kome ba, ya bar dakin.
Wasa wasa Malik ya hana a sallame ta, duk da taji sauki, amma fir ya hana ta bar asibitin. Gidan da aka Ajiye Jalilah.
Tayi wani irin laushi, ya zuba mata idanu kafin ya ce mata. “Na barki ki tsira da mutuncinki amma kin gaza fahimtar haka, Tunda nace zan auri Zainab nasan dalilin da yasa na ce zan aure ta, amma kika gaza fahimtar haka. Domin ture dake a jikina Lalla Salmah da Shatima suka miki tarkon da kuka fita aka yiwa Nuratu fyade. Amma a duniya baki da masoya sama da su, lokacin da nayi hatsari na san ke aka fara biya ki zuba min guba kika ki, wannan dalilin ne ya saka har kwanan gobe kike da kima a idanuna. Ai wancan ranar ban yi niyyar tozartaki ba, kece kika bukaci haka.
A yanzu ma dama ce a gare ki, Dangin mahaifinki da mahaifiyarki, suna garin gere na garin Borno Maiduguri. Ba zan ce miki wani abu ba, amma ita yarinyar da kike kokarin cutar da ita yar Yayarki ce Ummu, idan kin so ga dama bindiga ce, ki je ki kashe Zeenobia domin ni. A wancan ranar da kike tsammanin na kwanta sake, ban yi abin da kike tsammani ba, domin babu wanda a cikin zuri’a na ya lalata yar wani, Shatima dai da kike ganin wani ne, shi ne wanda ya aikata miki kome.
…. …… “Lalla Salmah da take zuga ki, bata gaya miki me yasa take ingiza ki yarta ce take buƙatar na aura, idan kika ture Zeeno a jikina, ai dole kece ke kuma sai ta san yadda zata ture ki. Kenan dukkanku baku da alkibla, idan kin so ki bar ni na auri Zeenobia idan baki so ba, kofa a bude take ki kashe ta. ” Sannan ya tura kekenshi shi zai fita ta ce mishi. “Me yasa tuntni baka gaya min yar Yayata ba ce?” “Saboda zuciyarki ya makance da son zuciya, idan na gaya miki tunaninki bana son alaka dake ne, me zao saka na tsaya bata lokaci na akanki? Saboda ita na miki uzuri. Ba don kome ba, akwai Yar uwarta Yar sanda ce tana falo xata kula dake ki koma gidanta da zama, amma ki kame kanki a matsayin Uwa kike a wurinsu, surukar Malik Menk Jordan!”
A hankali ya fito falon, ya samu Asp Zulfa da Elbashir. “Ki kula da ita.” “Yes!” Ta faɗa tana sara mishi. Har zai tafi ya ce mata.” baki tambaye ta ba?” “Hmm wai naga tunda tana tare da kai, tana cikin koshin lafiya. Na ziyarci asibitin sau biyu. Idan Yasir yazo zamu kara zuwa, domin yace ma tsahirta zuwa ganinta.”
“Gaskiya ne, kema ba don kakinki ba da ba zaki kai wannan lokacin ba, ki kula da mutanen da kika mu’amala da su, duk nasan har yau kina kallona a matsayin makiyi, nima har yau binciken mutuwa Nasr Hadejia nake ”
Bata amsa mishi ba, sai dai kuma tayi shiru har ya saka kai ya fita Elbashir yana biye da shi. “Malik yanzu ya batun Lalla Salmah sa Shatima!”
“Ita Lalla Salmah, dawo da ita zamu yi daga majalisa, shi kuma Shatima board zasu cire shi daga matsayinshi.”
“Alhamdulillahi! Karshen azzalumai yayi!” “Eh haka ne, amma kuma tow Allah ya sa mu dace” “Amin Ya Allah!” Daga haka suka shiga.a cikin kwanaki da ake maganar za ayi aurensu, wato da Zeeno biya ta tashi hankalinta. Sai da tayi yunkurin cutar da kanta, amma aka samu nasarar mata Allura, dole aka d’aga lokacin domin ta kwantar da hankalinta, wannan abin yana faruwa ne, sakamakon yadda Shatima yake hure mata kunne, tare da bata misali da ina Jalilah? Malik ya batar da ita. Don haka haka ya gaya mata kada ta sake ta auri Malik bai da Qualitys din da ya dace ta aure shi. Domin ta sani rayuwarta tana cikin hatsari. Wannan dalilin yasa aka ajiye batun auren don tace matukar aka aura mata Malik gudawa zata yi ko ta sha guba kuma ajiye maganarta domin ba zata yi wasa da abin da tayi niyya ba. Wannan dalilin ba karamin ciwo yayiwa Malik ciwo, domin daga hakan tayi ta fadar abubuwan da ya haɗa su, A bangaren Ammy bata wani damu can ba, domin kuwa Malik shine daidai da Zeeno, sannan shi ne kawai zai zauna da ita babu cin mutuncin ko gori. Sannan babu wanda zai kyamaceta, amma baki daya ta lalata wannan sa ran. Shi yasa shima Malik shima daukar mataki, ya kuma ki fita harkanta. Domin yana fita harkanta Media zasu samu hanyar yayyata karya da gaskiya akansu.
Ba tare da jin kome ba, Malik ya shiga hada Meeting, da duk masu ruwa da tsaki na party ɗinsu. Ba a san yadda Lalla Salmah ta jiyo labarin ba, a masifar guje ta tawo, domin wanke kanta, tun safe take son ganin Malik, amma yana Meeting da board members na party ɗinsu. Sai bayan Azhar ta samu ganin shi, inda ta zubea gabanshi tana kuka tare da faɗin. “Don Allah ya mata rai, ya rufa mata asiri, ta san tayi laifi amma duk abin da ya faru, bata da masiniya Shatima ne ya shirya. Wallahi bata san kome ba, ko abinda ya faru da Nuratu shirin Shatima ne ya saka Jalilah cikinshi domin wanke kanshi, ita kanta Jalilah bata san da haka ba. Don Allah ya rufa mata asiri idan ya cire ta a matsayin assamblywoman za a mata dariya, sannan abin kunya ce a gare ta. Waye ya mutu waye ya dawo.
“Ki je zan nime ki.” Dakyar ta mike domin Malik ya girgiza yan hanjinta. A wannan karon ba karamin razanata yayi ba, iya abin da ya faɗa kenan da shirinsa, amma ta haukace ina kuma shi Shatima, koda yake Malik bai san shirin Shatima ba, shima kuma Shatima bai san shirin Malik ba. Don haka lokaci guda aka fara samun mummunar takun saka, ita kan Lalla Salmah, an dakatar da ita a majalisar domin karar da Al’ummar da take wakilta suka yi,. Idan ka ganta kamar ta yi hauka. Gefe guda an soke visa dinta, kawai kokari take ta koma matsayinta. Amma tayi rantsuwa sai ta ga bayan Zeeno domin ita ya saya masu Malik.
Satin Zeenobia biyar aka sallame ta, a asibitin. A lokacin Nadrah ta dawo daga Demark saboda abin da yake faruwa, a cikin kwanakin taso ganin Zeeno amma Allah bai nufa ba, domin kuwa ana gyaran unguwarsu Zeeno, Malik ya dawo da ita estate dinsa da yake bayan whiter town, ana kiransa da great town.
Sannan bai yarda a ranshi zata koma unguwar ba, domin yasan Shatima yana nimanta a ruwa a jallo, shi kanshi Malik tun da suka koma great town, ya saka Abbas dauko mishi wayarta ya cire layin ya bashi ya maida mata, yasan zugata ake, kuma ba daga mutanen gidan ba, sannan ya yanke hanyar da zata ganshi, ita ɗaya ya katse alaƙar shi da ita, Amma Ammy da Inna kan, shirya musu tafiya Umra yayi, bata sani ba. Ita kuma ya hana su gaya mata, sam bata san da tafiyar ba, sai a ranar da safe suna karyawa ta cewa Inna.
“Inna wai yaushe zamu bar gidan nan ne? Na gaji gara na koma inda nafi wayo!” Tabe baki Inna tayi ta ce mata. “Auzubillahi minna shaidanun rajim! Allah ka mana tsari da musu mana baki cikin da hassada.”
“Ikon Allah, Inna nice shaidaniyar?” Murgud’a baki tayi, ta ce mata. “Da yau Abbas mace ce, ai ba zai watsawa Uwarshi kasa a idanu ba, ya ce ba zai auri Malik ba, haka zai karba ya kuma yi biyayya amma sai kika nuna mata ba ita bace ta haife ki, ba ta isa ya saka ki aurenshi ba, Zainaba sai ki zuba ruwa a kasa ki sha mutumin da kika tozarta ya biya mana umra!” Sake baki tayi tana kallon Ammy sa ta fito hannunta dauke da ludayin miya ta ce. “A’a Inna ita fa Baby ta fasa auren ne, domin tsirar da Al’umma charity House, kamata yayi mu yaba mata!”
“Wani ya ba mata? Nace wani yaba mata? Yarinyar da ta watsa mana kasa a idanu ai kallonta nake kawai, sai anyi magana tazo tana narke fuska. Ai wallahi kin bani mamaki,yo ko mahaukaci tace ki aura kya kwantar da kai ki aura balle kuma mutum irin Malik me dinbin daraja!”
” Ammy me yasa baki gaya min kina son na auri Malik ba?” Murmushi tayi sannan ta ce mata. “Ai idan na miki bayani ba zaki gane ba, zaki ga kamar dole muke miki!”
“A’a Ammy da ko duka na kika yi zan fahimta. Amma abin da Inna ta faɗa ya min zafi, don baki haife ni ba sai nace baran miki biyayya ba, wacce Ni? Ban sani ba amma kin rike ni da gaskiya kamar kece kika haifan, Ammy na amince a daura auren na amince a daura aurena da Malik idan zai saka ki farin ciki na amince.”
Dariya Ammy tai, sannan ta ce mata. “A’ Zainaba idan baki so ai an shiga uku, gara ki samu wanda zaki so shi kamar kanki amma banda Malik, na san dai da ina da ya mace ce da dole na bashi ita.”
Ta faɗa tana dariya, domin kamar ta faɗa ihu. “Ammy wallahi na amince!” “Kin amince a aura miki ki kashe kanki, babu wannan zancen a bar shi kawai.” Ta rasa yadda zata yiwa Ammy bayanin na fahimta ta amince. “Ammy na amince fa!”
“Zaman aure da Malik zaki yi, ba da ni ba idan har aka damu matsala tow haushina zaki ta ji har karshen rayuwarki”
“Ammy ki fahimta mana ni na amince zan auri Malik yau ba gobe ba, domin kaina na kuma tabbatar miki ni yar halak ce ba wacce ta san halacci!” Gyada kai Ammy tayi ta ce. “Inna kinji ko? Kada gobe ta ce na zalunci ta.” “Ina jin ku, sai ki kira Liman da kawu ayi magana ta manya!”
Bata son ta nuna karayarta amma maganar gaskiya, bata shirya auren Malik ba, ta kowani fuska amma babu yadda ta iya. Wurin karfe daya na rana, aka ta taru har da Malik aka tambaye ta, ta ce ta shirya kallonta yake kawai, because bai zaci haka daga gare ta ba.
Kuma yasan tunda ya ce zata yi auren, akwai abinda ta shirya Zeenobia bata da kirki a idanun shi tunda ta fadi, ba zata aure shi ba, don yana da abin da yake bukata ne yasa ya nace idan ma tsafi ne ya je can ya nemi wacce ta dace da shi ba ita ba. Yasa shi jin babu dadi shi yasa ya ajiye ta a gefe guda, ya daina shiga harkanta. Duk da babu sauki daina ganinta da yayi ba karamin azabtuwa yayi ba, “Zainab kika ce kin amince zaki auri Malik, shin dole aka miki?” Kanta yana kasa, ta kasa d’ago kanta ta ce musu! “Na amince!”
“Kin amince ka da daga baya kice an kware ki, Gara ki fadi Gaskiya.”
“Na amince!”
“Jama’a kunji ta ce ta amince ko?”
“Eh munji!”
“Alhamdulillahi!” Daga nan suka saka.mata albarka, suka fita har da shi Malik. Karfe uku da rabi, aka shaida auren Malik Menk Jordan da Zainab Muhammad Nasr Hadejia! Akan sadaki me daraja, asalin danyen gold wanda ba a tacce shi an rage mishi Quality ba. Kafin karfe biyar magoya bayan Malik sun shirya yar karamar walima, wanda ya janyo hankalin mutane domin wasu dan niman suna live aka daura a social media.
Shatima da yake cikin tashin hankali, sai ganin bikin yayi jifa yayi da wayar shi, ranshi yayi masifar b’aci, shiru yahi yana jin wani irin bakinciki yana yana cika zuciyar, Me Malik yake nufi? Yasa an dakatar da shi, sannan ya cire mishi hannun jarinshi a kowani branches na Kamfanin shi, sannan ya saka an kama jiragen dakon kayanshi haka bai ishi Malik ba sai da ya saka aka ajiye shi a gida a matsayin ladabtarwa sakamakon rashin zuwan shi, lokacin da aka nime yazo ya kare kanshi……..
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata: ZINNIEE’s SECRET
(One stop shop for a new sensation)
Kina Neman kamshi mai sanyaya zuciya❓
Shin kina Neman kamshi da dada❓
Ko kuwa kamshi mai ratsa zuciya kikeso❓ko Kayan gyaran jiki kike nema dry skin ne dake ko hard skin tabbas kinzo inda za’a share maki kukan ki
Tabbas Zinniee’s secret ya gama da damuwarku Ina mata masu aji mace mai aji ai Sai da gyara .tabbas Zinniee’s secret sun gama da damuwarki Hajiya ta.
Zinniee’s secret sun tanadar muku Kaya kamar……
Room freshener
Toilet spray
Bed spray
Dish wash
Mopping mist
Kai har ma da
Feminine wash
Akwai
Glowing soup dinmu mai kyau da inganci.
Glowing cream
Face cream da kuma body scrub
domin samun dadadan Kayan kamshi.da Kayan gyaran jiki maza garzayo Zinniee’s secret
Zinniee’s secret DUNIYA ne !!
Zaku iya yi mata magana a wadannan kafafan sadarwar kamar su—IG-@Zinniee’s secret
TIKTOK@ Zinniee’s secret
Ko ku tuntube su a wannan number 08080840567 za kuma ku iya mata magana ta hanyar Watsapp da wannan number.
Zinniee’s secret suna nan a kano Hadeaja road Kano state.
Zinniee’s secret one stop shop for a new sensation.
Zinniee’s secret got u covered,a trial will convince you.