Cinikin Rai Book 1Hausa Novels

Cinikin Rai Book 1 Page 12

Sponsored Links

CINIKIN RAI….12
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
“Hmm! Dama cewa nayi ta kula da rayuwarta, wadannan yan siyasan ko yan daban ba kome zasu mata, domin daga lokacin da ta kwabe musu ba zai mata kyau ba.” Ta fada tana gyara hannunta.

Shiru suka yi, domin kamar maganar ya shige su. Juyuwa tayi zata bar gidan, kwallon yara ne yazo zai wuce ta gabanta, tayi maza tare shi, ta shiga d’aga shi a hankali tana jifa shi sama. Har tayi ta bugawa kafin ta tura musu kwallon tana murmushi ta sakar musu. Tare da barin gidan baki daya.
A can sama kuwa, tunda ta shiga É—akinta ta rufe kofar, bata yarda ta bude kofar ba, asalima duk buga kofar da ake taki budewa, kwanciya tayi ta lumshe idanunta, tun daga tasowarta har yau babu namijin da ya tab’a nimanta da harkan banza, domin bata cikin yan matan da suke bawa maza kanta. Har zuwa yau ita bata cikin yan matan da suke da mugun kwadayi da zallama, ta iyawa kanta, bata shiga abubuwa dayawa domin kare mutuncinta, shi yasa har ta gama makaranta, babu ruwanta da kowa. Kai saurayi wannan ba tab’a yi ba.
★★★
Washi gari.
Da wuri tazo wurin aiki, tana dakin da suke sauya kaya, Mss Mary ta shigo tana kiranta. “Zeeno kina ina?” Juya tayi tana gyara zaman rigarta. “Mene ne?” “Maza kizo chairman yake kiranki!” Karamar tsaki tayi tana faÉ—in. “Ok gani nan zuwa!” Ta fada tana cigaba da abin da take yi, domin tasan bai wuce bita akan Malik Menk Jordan, kuma indai shine ta rigada ta hadda ce, bata bukatar wani bita domin zata iya fadar abin da abin da zai ce mata.
Sake zuwa Mss Mary tayi, “Wai kina ina ne?” “Gani nan dai” ta fada tana tura baki, har zata wuce, sai kuma Mss Mary ta ja hannunta, zuwa wuni department na cikin kamfanin kaita wani daki, bude drower tayi kaya suka bayyana, kura mata idanu tai tana faÉ—in. “Ki zabi kayan da ya miki bari Dauduwa yazo.” A hankali ta kai idanunta kan drower din, ba karya kayan sun hadu, wani gown ta zaro green colour, ta tsaya gaban mirror din drower din ta gwada kayan, ta kuma juyawa daidai bude kofar. “Wow wannan kayan zai miki kyau, idan kika haÉ—a da takalmi grey da yar karamar pose, sai yan kunne babu bukatar ki saka abin wuya, ko me kika ce Mss Mary.” Murmushi tayi tana faÉ—in.

“Tabbas kuwa zata yi kyau, amma ta gwada kayan baki daya mu gani, ko zata samu wanda ya fi kyau.” Ta fada tana kallon ta, aikuwa haka ta kasance tare da gwada kayan, wato yarinyar nan da tayi ta sauyawa tana kara sakawa, abin ba a magana. Binka da matsakaiciyar mace, bata da tsawo can, sannan bata cikin layin gajerun, sannan bata da auki domin dai jikin daidai ne, skin É—inta fari ne me kyau, kasancewar mahaifiyarta Shuwa’arab daga yankin Chad.

Gashi ne da ita har baya, ba irin wanda za a kira shi har gadon baya ba, domin a cike yake, tsawon dan daidai ne, don ma yar kwalliya ce, amma duk lokacin da jagaliyarcin ya motsa takan iya wata uku bata murza kwalli a cikin Idanunta.

Zeeno tana da kyau, don fuskarta kamar ta Yara take, gashi fuskarta yana da dan tsawo, Idanunta kuwa yadda kasan yan Korea, a zahirin gaskiya idan tana jin yan gayun babu biyunta,. Amma idan abin ya motsa babu ruwanta sai tayi ta maimaita kaya, bai dame ta ba.

Sai da aka gama zaga kayan cikin drower kafin aka samu wani, Peach colour ta saka, aka yi mata makeup light, babu wani tarkace, haka suka fita tare kafatar sanye da takalmin Amina muaddi, sai yar karamar jakar Celine. A kafad’arta ta rataya jakar, suka fita tana tafiya a hankali gwanin ban sha’awa. Har suka isa office din chairman. Koda suka isa basu wani dauki lokaci ba, suka shiga da jagorancin Mss Mary. Har cikin office É—in. Idanunta ne ya sauka akan idanun wani kyakyawar matashi. Yana zaune hannun shi rike da mujallar Fashion. Juyowa yayi ya zuba mata ido. Itama shi take kallon shi take, kafin ta janye Idanunta daga nashi, domin irin mutanen nan ne, masu kallon kurilla. “Amjad ta hadu sama da jikin jaridar, a jaridar na ganta, ashe ta wuce haka ma.!”
“Zeeno ga shi, Akram Jafar Wazir. Yaga hotonki a mujallar Fashion ya ga hotonki, daga, Nigeria yaÆ™e!” Dauke kai tayi daga kallon Amjad, ta nime daya daga cikin kujerun office din, ta zauna tana kallon Amjad. “Ban fahimci me kake nufi ba? Ni fa ba gwanjo bace da zaka na gayyato min mutane, Amjad wannan ya zama na karshe na gaya maka.” Daga haka ta juya zata fita. “Zeenobia! Yes na yarda da abinda aka fada, kanta yana daukar wuta sama da fuskarta.” Cak ya tsaya, sannan ta ce mishi. “Na wuce yadda kake tunani, ka tsaya a iya inda kake!” “Ni ina da mugun naci, kamar kaska nake, matukar naga abu sai na manne mishi nake samun nutsuwa, domin matukar ban ja jinin ba, bana nutsuwa. Ki tanada min abubuwa yawa, har da bayanki…..” “Tasss” ta dauke shi da mari, wani irin dariya yayi yana faÉ—in. “Wow! Yes dole na mallake ki koda girma….” Wayar shi ce tayi kara ya É—auka. “Ok in sha Allah, zan biyo flight na yamma gani nan!” Ya juya ga Zeenobia. “Mark my words, babu wanda ya isa ya tsaya a gabanki sai ni, sai na lalata miki fuskar ki a gaban jama’a.” Takawa tayi gabanshi, ta kuma tsinke shi da mari, tare da cin kwalar shi. “Har gaban abada, na fi karfin jan kasar jahili irinka. Yar kunama nake” ta sake mishi kwalar shi, ta fita tun daga waje ta fara cire kayan jikinta, har ta isa dakin ta cire kayan, ta tsani kayan ban haushi.
“Amjad, yarinyar nan ta hadu.”
*Hi……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah:

Leave a Reply

Back to top button