TUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 48

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/11, 11:10 PM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣8️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Kai yadauki zafi kowani part na gidan mu ana sha,anin buki
amma hakan bai hana a saka ido aka  ummah
ba don ganin abinda take gudanarwa a nata bangaren.

   Don mutane da yawa
suna kokarin son zuwa suba idanun su abinci don su samu abin fada gaba idan
magana ya taso wurin yinshi duk da ansan tallaka zan aura amma bai hana mutane
kwadayin son zuwa gidan nawa ba su ganewa idon su abinda ake fadi game da auren
nawa.

   Yan fammanin
mahaifina sun tafi sunyi min jere da kayan da Abba yasa hjy karima ta saya min
washe gari kuma kayan ummah suka iso suma aka kaimun su gidan aka jera min su
sai aka fitar da nasu Abban aka mayar a dayan dakin a take part din nawa ya
koma abin kallo  .

   Duk sunyi wanan
abin ne ba tare da sanin kowa ba sai gwaggo shafa da gwaggo Ai da suka tausaya
muna kan irin abinda Abba yake nuna muna a bukin.

   Dawowan sune har
wasu daga cikin dangi sukaji irin dukiyan da ummah ta kashe min wanda al,adan
uwan kasan hausane ta fitar da duk wani tanadin a bukin auren yarta idan ya
taso.

   Haka mutane zasuyi
ta sintiri wurin zuwa ganin daki da abinda aka kaiwa yarinya a dakinta koda
kuwa zuwa nisan inane garin sai an samu wanda yaje ya gano ya dawo ya fada.

   Hakan ne ya faru
dani don su gwaggo na dawowa suka fara fadin hidiman da suka gani a dan gidan
nawa da mutane suka raina saiga labarin abinda ummah da yan uwanta sukayi min
ya karade kunnuwan mutune lokaci guda har yakai kunnen mama da hjy karima har
zuwa wurin Abba din.

    A gaskiya Abban
yaji mamaki yadda za ace wai kudin daya bayar har ummah tafishi yimin kayan
kwarai sai jikinshi yai sanyi da jin hakan kamar wanda aka tunatar da wani abu
daya manta a baya.

    Munyi walima gidan
baffa Abubakar na mazon Allah an dauki waliman na yaku bayi da farko amma ganin
yadda yan uwa da abokan arziki suka tsaya suka tsara abin da yadda akai
kwaliyan titin unguwar gabaki daya da malaman da akaji an gayato sai mutane
sukai ta tururuwa zuwa wurin waliman har ma da wanda ba a gaiyata ba lokacin
don sauraron wa,azin.

    Ga kawayen ummah
sunzo da sebeniya masu kyau na rabo sai hakan ya kara daukan hankalin mutane
har yaja kowa zuwa wurin waliman don komu bamu zaci hakan ba gaskiya.

    Har an fara taron
lokacin da mukazo tare da yar ummah wace ta tayar da ita a kaduna har Abba ya
ganta ya aureta da kawar ummah da wata gwaggon su ummah din a cikon dirkekiyar
motan da tazo dashi.

   Nayi adon lafaya
mai shegen tsada takalman kafana kwaliyansu daya da lafayan jikina hakama
jakkar dana rika shima kala daya da lafayan jikin nawa.

   Sam bansan cewa an
gaiyato Ahmed ba wurin sai ganinsa mukayi yazo da tawagarshi nan dai aka nuna
masu inda zasu zauna shi kuma suka sa muka shigo filin a tare dashi.

   Anan kowa ke dage
yana son yaga mijin dana aura din da ake shati fadi a kansa din babu inda za a
rainawa Ahmed wurin halitta saidai a kirashi da fakiri wanda baida halin ko
zarafi something dai hakan.

    Wa,azi akayi akan
hakkin aure daya kamata namiji ya sauke da wanda ya haukan mace itama sai kula
da hakkin makwabtaka da malama ta karshe ta fadakar   damu lokacin.

   Inda akasa nayi
karatu a cikin suratul maryam shima yayi a cikin suratul yusuf ikon Allah
malamin ya fada yace kafin nazo wurin taron nan nayi ta tsuntan maganganu a
cikin wani unguwa dana sauka akan auren nan.

    A gaskiya ni a
ganina wanan hadin shine hadi irin wanda ya dace ayi a musulnce nan dai yayi
bayanin yada ya dace ya wayar dakai yaja hankalin mutane akan hakkin aure.

   Kafin aka fara raba
abubuwan ci dana sha da kyaututuka na ban mamaki bamu tashi ba sai gab da
magariba taron ya watse kowa na sam barka ga taron.

    Mun dawo mun samu
masu shirin zuwa dinner suna ta shiryawa masu bada labarin walima suna bayarwa
abin mamaki saiga sako daga hjy mama cewa wai ummah ta shirya da mutanenta
angaiyacesu zuwa wurin dinner su Aisha.

    Tadai amsa amma ba
wanda ya leka a namu bangaren saida safe muke jin cewa wai walimana yafi dinner
nasu kyau sosai don ba a tsara abin yadda ya dace ba karshema fadane ya watse
taron da yan gidan angon Aisha da tawagan mama a wurin.

   Har mazan na fadin
cewa sun fasa tunda mutanen banzane su inbashi da ya mayar da kanshi baya ba
dama har Aisha macen aurene bayan kowa yasan irin watsewan su.

   Shima angon yai
fushi dama a buge yake ya nuna mama yace ta kwashi yarta ya fasa auren gobema
barin zaiyi da safe dama ita ta matsa mai akan ya auri yarta.

   Nan dai sukayiwa
juna tonon asiri sosai itama da borin kunya tace ta fasa bashi yar nata
mashayin banza da wofi kawai ai dama taimaka mashi tayi har ta dauki yarta ta
bashi.

   Zance dai har wurin
maza da safe haka falon Abba ya cika da mutane kowa da kalan zancen da yake
zuwa dashi itama Rukkaiya dai an samu matsala wai gidan da zai ajeta yayi masu
kadan su kuma sukace idan bai masu ba sai a fasa.

   Anan Abba ke jin
cewa wai mijin Rukkaiya din ashe dan damfarane yana sayar da filayene a
garuruwa da haka ya tara arziki yake karya dashi a gari.

    Kai rikici dai
gashi nan da tonon asiri kala kala kowa yazo ya fadi nasa gashi da karfe biyu
za a daura auren mu ga abubuwa sun dagulewa mama sai jiki yayi sanyi a lokacin.

  Dole Abba ya kira
taron gagawa don samun mafita don abokan shi wasu na nisa harsun iso gusau
lokacin gashi kuma rikici nata kara bulo kai.

    An samu an sasanta
da iyayyen angon Aisha sun yarda an daura auren bayan Abba yaje har gidan da
kanshi yaji ba,asin fada  nasu yaba da
hakkuri kada yaji kunyan jama,an daya tara din.

 Karfe biyu da rabi
aka daura aure har zuwa ranan ba a kawo lefena ba abinda ni kuma mutane ke
gulma a kanshi ke nan kaina wai duk talauci ne haka ya hana mutanen Ahmed su
kawo min laife ?

   Dangin mahaifinshi
sukazo da kayan lefen nawa wurin daurin aure kamar yadda al,adansu yake sai
bayan an tashi taron ne aka shigo dashi cikin gida aka gani nan gwaggo Shafa ta
sake guda saida hankalin kowa ya dauku da hakan wajen.

  Tana fadin
Alhamdullahi aure ya dauru tsakanin Aisha da manbo Rukaiya da sha,ibu gaye
Zahra uwa bada mama don sunar uwan mu taci da angonta Ahmed.

   Alkawarin Allah bai
tashi yau dai Allah ya nufa mun sheda wanan ranan kai ku shigo da abin arzikin
nan a bajeshi tsakar gida kowa ya gani tana fadawa masu shigo da akwatinan
acikin gida.

  Ta sake aza wani
gudan tana fadin lalai a haifi da arzikin shi yafi a mutu a barmai gado daki
auri mai arzikin ga mara arzikin na shirin fidda yarmu a kunya wana  kaya haka kamar matar dan gwauna fa.

    Kayan sunyi kyau
sosai don ba zakace kaya daga hannun mutum irin Ahmed mara gata suka fito ba
saida wata yar uwa  mu ta dakatar da
gwaggo shafa ta daina sake magana.

    Ni dai ko a idona
banga kayan lefen nawa ba sai sha,anin buki da mukeyi saiga sakon mama cewa na
bada key din motana inji Abba.

   Wanan kuma wani
irin zancene haka harda motan nata zai karbe saboda kiyayya wanan wani irin cin
fuskane wai haka yayar ummahce ke wanan maganan ga gwaggo Sa,a datazo karban
key din motana.

   Don ita da mama
aminan junane sosai a yadda naji ance itace kawar mama duk da suna da zumunci
amma ta sanadin ta Abba ya auri mama kuma har yanzu suna tare duk da kowa ya
girma.

   No ku basu don
Allah Allah ya horewa mijinta wata rana ya saya mata motan da kudin shi badai
za a karbi rayuwanta ba ai iya mota zancen zai tsaya ai.

   Motan da banje
gidan Ahmed dashi ba ke nan kuma su ummah basu tayar da zancen ga kowa ba suka
bada key din salin alin zancen ya wuce duk da hakan ya tabawa ummah zuciya
sosai.

   Motar yan uwan
ummah dana  kawayenta akai amfani dashi
abindai kawai in fada a dunkule don zakace nidin ko yar rikoce a gidan ko wata
yar rikon tafini samun gata a lokacin  .

   Don abinda mamaki
yadda aka nuna min lokacin ko an kawo tsegumi wanan yayan ummah din ita ke daga
hannu tace a kyalesu su fatansu Allah yaiwa aurena albarka.

  Don hakane suka sani
zama a sakin tare dasu wai gudun wani ya hure min kunne a can dakina nazo na
tubure masu daga baya.

  Gashi duk da banyi
gaiyata ba amm hannatu ta gaiyato yan course mate din mu dama wasu da muke
shiri dasu a school din namu dakin nawa ya cika fam da kawayen mu.

    Magariban farko
gwagwanin  mu suka shigo dakin waina fito
za a kaimu wurin Abba daga can za a wuce damu gidan hjyn su Abba sai gidajen
mu.

    Tunda na sallame
sallah nake daman kuka don irin nasihan da ake min a dakin da jan hankalina na
tsaya na rike aurena da hannu biyu don shirun da mukayi nida ummah harsu yana
sakasu wasi wasin din mu.

   Nikan kuka nake da
daya da biyu har zuwa uku sau uku amma nabar komai a cikin zuciyana ina addua
ashe banji abin kuka bama tukun sai lokacin da mukaje sallaman Abban mu.

   Inda ya kara
jaddada muna musanman ni kamar yadda yace don a gareni yake hango matsalan
farko a gidan shi na ba yaji ba kuma zuwa gida neman wani abu don ya riga ya
gama damu ko a cewan shi.

   Kai har dai yar
ummah data biyomu zuwa falon tare da babban aminiyar ummah din suka kai ga
tankawa a lokacin inda tace kamar yadda akewa kowa fatan zama  lafiya a dakin shi insha Allahu ko ita haka
zata zauna a dakin ta lafiya da yardan ubangiji.

    In har ana gason
hakkuri a duniya ai Zahara ta gaji hakkuri a wurin uwarta meya rage na hakkuri
yanzun wanda bata sani ba kuma ai saidai wanda ba,ayiba a duniyan nan.

    Kowa yayi shiru
sai cewan da gwaggon mu daya tayi ku tashi mu karasa gidan hjy kuyi mata
sallama daga can zamu wuce daga can baya wata ke fadin su angwanan zahra sun
kawo motan daukan amaryan sune.

   Aminiyar ummah hjy
kubura ta bude baki tace ko basu kawo ba mota ba matsala bane ai shima angon
yanzu ya zama dan mu da akwai motoci sai mu kaita fatan mu dai Allah ya basu
zaman lafiya aka amsa da amin.

    Haka suka rikomu
zuwa waje muka taka da kafa zuwa gidan hjy din nan ma irama tayi muna nata hudu
ban mai kama da jurwaye tare da fatan lafiya gare mu aka kwasa akafito wajen
gidan .

  Ina jin mommy kubura
na waya cewa sauran su fito idan an shirya motocin tafiya ba afi yan mintuna ba
sai gasu gidan sun samemu da motoci hudu muka shiga gwaggo shafa tana cikin
mu  tare da wasu yan uwa da basu bamu
baya ba marasa tsoro ke nan su.

    Tunda muka shiga
motan muna tafe suna fada min naja Tawakhaltu illallah lahaula wallakuwatu ina
billahi aliyal azeem sau uku sai na dinga jan,
Hasbunallahu wani imal wakil har zuwa shigan mu gidan shi na dinga ja a
bakina ina hawaye.

   Ba zan iya fadan ko
hawayen me nake sakewa ba har wanan lokacin asalima ba bace ina cikin hayacina ba
gaskiya don sai yadda aka juyani kawai nasan dai ina dan picking din wasu
abubuwa dake gudana dani lokacin.

    Jin mota ya tsaya
lokaci guda ga guda da ihun yaran yana tashi lokaci guda yasa na lumshe
idanuwana a hankali naji mommy kubura dake gefena zaune ta dan kwanto min tana
fadin yawaita karfin zikirinki a wanan lokacin ki fara da ya Rabbi ya rabil ya
rabil alamin ya Allah ina rokonka a ckkin kyawawan sunan ka daka baiyana suga
bayin ka ya Allah ka suturani a dakin mijina har Abada ka kawar da duk wani
shedan da shedaniya a tsakanin , , , , , , ,

    Nasan ina maimaita
abinda mommy din tace in fada daga haka na rikice masu har zuwa cikin dakin
nawa saisune suka san halin da nake ciki kan gadon dakin ta kaini ta zaunar
dani da bissimillah tare da adduan koran shedan gareni.

    Anyi adduoi daya
dace ayi a lokacin kafin manya su fara watsewa bisa umurnin mommy kubura dama
suna sauri su koma suje kai sauran amaren gidajen su haka yasa bata samu wani
matsalaba wurin sallaman mutanen.

    Muka rage daga mu
sai su su hudu sai yan matan dake falo su hannatu sai zuwa can na fara gane
inda nake zaune duk da ban sheda a dakin da nake zaune ba lokacin.

    Kai gaskiya idan
Allah ya hadaka da mutanen arziki a rayuwanka ka godewa Allah don sai ka
daukama sunfi wani dan uwanka na jini wani lokacin.

   Don ko ni naga
hakan a wurin uwata don ko yan uwa da abokai sun nuna mata gata sun fitar da
ita kunyan kishiyoyi dana mutanen gari tare da bakin cikin mahaifin mu.

   Yan kawo amarya sun
koma cike da mamaki tare da labarin abinda idonsu ya gane masu a gidan kowa
saidai ashe mu munbar baya da kura don Aisha dai ba a samu kaita nata gidan
mijin ba.

  Saboda mijin nata
yana nan aka  bakan shi naya fasa auren
nata tunda har tai sanadin data tozartashi a gaban mutane ya baiyana halinshi a
cikin rashin sanin kanshi lokacin.

   Wanan yasa ya rufe
gidan shi ya juya zuwa portakut inda yake aiki ya fita zancen su ya kumabar
sakon cewa ya fasa sai ya dawo suzo su kwashe kayan su.

   Mamakan da yarta
ranan sun kwana da bakin ciki ita kuka yarta kuka ga zagi da Abba ya dinga
surfan su dashi na tozarci a bainan jama,a kowana jinsu.

    Tsab hannatu ta
gyara dakin ko ina duk hjy kubura na tsaye har aka saka kamshi kafin ta kara
lekani inda nake kwance mukayi sallama ta fito tabar su hannatu su uku a dakin
tare dani.

    Tana jin daga
dayan lungun da akace na  iyayyenshine
ana fadin wai Dije mutanen nan sun tafine basu kawo muna amaryan nan dakin ba
ko meye ?

   Ato ina muke da
kimar da zasu kawo muna yarsu nan ai bai nuna masu cewa muna da wanan matsayin
ba gareshi aiko zanga yadda zaiyi  yau
yace zai shiga lungun nan.

   A,a ki barshi ai
yana da hankali koma meye dalilinsu nayin hakan zamuji ai daga gareshi suna
hakan sukaji sallaman hjy kubura duk sukaja bakin su sukai shiru.

    Su biyune suka
shigo ta gaisa dasu take fadin kun jimu shiru ko wallahi mun kawo yarmu sai ya
kasance bata da lafiya tana can kwance kafin mu fito saida akai mata allura
amma kuyi hakkuri idan Allah ya kaimu gobe zamu kawota gareku.

   Yanzun ma na
shigone in fada maku don kada kuga kamar an raina makune anki kawota nan wurin
kune ayi hakkuri don Allah lalura ya kawo hakan.

  Nan take su Dije aka
shiga fadin jam Allah ya bata lafiya daga jigilan buki sai kuma ciwo haka Allah
ya sauwaka.

    Tayi masu sallama
ta tafi mahaifiyar Ahmed dake tsaye tana jiran kaucewan ta tace aiko ba gidan
nan ba dama nasa  badon Allah aka aura
mashi yar nan dole da wani dalili a kasa da yaron nan yake boye muna.

 

Leave a Reply

Back to top button